Surah: Suratul A’araf

Ayah : 130

وَلَقَدۡ أَخَذۡنَآ ءَالَ فِرۡعَوۡنَ بِٱلسِّنِينَ وَنَقۡصٖ مِّنَ ٱلثَّمَرَٰتِ لَعَلَّهُمۡ يَذَّكَّرُونَ

Kuma lalle haqiqa Mun jarrabi iyalin gidan Fir’auna da shekaru na fari da kuma tawayar ‘ya’yan itace, ko sa yi tuntuntuni



Surah: Suratul A’araf

Ayah : 131

فَإِذَا جَآءَتۡهُمُ ٱلۡحَسَنَةُ قَالُواْ لَنَا هَٰذِهِۦۖ وَإِن تُصِبۡهُمۡ سَيِّئَةٞ يَطَّيَّرُواْ بِمُوسَىٰ وَمَن مَّعَهُۥٓۗ أَلَآ إِنَّمَا طَـٰٓئِرُهُمۡ عِندَ ٱللَّهِ وَلَٰكِنَّ أَكۡثَرَهُمۡ لَا يَعۡلَمُونَ

Amma yayin da daddaxan abu ya zo musu, sai su ce: “Da ma wannan namu ne.” Idan kuma mummunan abu ya same su, sai su camfa Musa da waxanda suke tare da shi. Ku saurara, kawai dai mummunan abin da ya same su daga wajen Allah yake, amma yawancinsu ba sa sanin (haka)



Surah: Suratul A’araf

Ayah : 132

وَقَالُواْ مَهۡمَا تَأۡتِنَا بِهِۦ مِنۡ ءَايَةٖ لِّتَسۡحَرَنَا بِهَا فَمَا نَحۡنُ لَكَ بِمُؤۡمِنِينَ

Kuma suka ce: “Kowace irin aya ka zo mana da ita, don ka sihirce mu da ita, to fa mu ba za mu yi imani da kai ba.”



Surah: Suratul A’araf

Ayah : 133

فَأَرۡسَلۡنَا عَلَيۡهِمُ ٱلطُّوفَانَ وَٱلۡجَرَادَ وَٱلۡقُمَّلَ وَٱلضَّفَادِعَ وَٱلدَّمَ ءَايَٰتٖ مُّفَصَّلَٰتٖ فَٱسۡتَكۡبَرُواْ وَكَانُواْ قَوۡمٗا مُّجۡرِمِينَ

Sai Muka aika musu da ambaliyar ruwa da fara da qwarqwata da kwaxi da jini, a matsayin ayoyi daki-daki, sai suka yi girman kai, kuma suka kasance mutane masu babban laifi



Surah: Suratul A’araf

Ayah : 134

وَلَمَّا وَقَعَ عَلَيۡهِمُ ٱلرِّجۡزُ قَالُواْ يَٰمُوسَى ٱدۡعُ لَنَا رَبَّكَ بِمَا عَهِدَ عِندَكَۖ لَئِن كَشَفۡتَ عَنَّا ٱلرِّجۡزَ لَنُؤۡمِنَنَّ لَكَ وَلَنُرۡسِلَنَّ مَعَكَ بَنِيٓ إِسۡرَـٰٓءِيلَ

Kuma yayin da azaba ta sauka a kansu, sai suka ce: “Ya kai Musa, ka roqa mana Ubangijinka, saboda alqawarin da Ya yi maka; lalle idan har ka yaye mana wannan azaba, to tabbas za mu yi imani da kai, kuma za mu sakar maka Banu Isra’ila.”



Surah: Suratul A’araf

Ayah : 135

فَلَمَّا كَشَفۡنَا عَنۡهُمُ ٱلرِّجۡزَ إِلَىٰٓ أَجَلٍ هُم بَٰلِغُوهُ إِذَا هُمۡ يَنكُثُونَ

To yayin da Muka yaye musu wannan azaba zuwa wani lokacin da za su kai gare shi, sai ga shi suna warware alqawarin da suka yi



Surah: Suratul A’araf

Ayah : 136

فَٱنتَقَمۡنَا مِنۡهُمۡ فَأَغۡرَقۡنَٰهُمۡ فِي ٱلۡيَمِّ بِأَنَّهُمۡ كَذَّبُواْ بِـَٔايَٰتِنَا وَكَانُواْ عَنۡهَا غَٰفِلِينَ

Sai Muka azabtar da su, Muka dulmiyar da su a cikin kogi saboda sun qaryata ayoyinmu, kuma sun kasance gafalallu game da su



Surah: Suratul A’araf

Ayah : 137

وَأَوۡرَثۡنَا ٱلۡقَوۡمَ ٱلَّذِينَ كَانُواْ يُسۡتَضۡعَفُونَ مَشَٰرِقَ ٱلۡأَرۡضِ وَمَغَٰرِبَهَا ٱلَّتِي بَٰرَكۡنَا فِيهَاۖ وَتَمَّتۡ كَلِمَتُ رَبِّكَ ٱلۡحُسۡنَىٰ عَلَىٰ بَنِيٓ إِسۡرَـٰٓءِيلَ بِمَا صَبَرُواْۖ وَدَمَّرۡنَا مَا كَانَ يَصۡنَعُ فِرۡعَوۡنُ وَقَوۡمُهُۥ وَمَا كَانُواْ يَعۡرِشُونَ

Mutanen kuma da ake nuna musu fin qarfi a da, Muka gadar musu gabashi da yammacin qasar da Muka yi wa albarka; kuma kalmar Ubangijinka kyakkyawa sai ta tabbata a kan Banu Isra’ila saboda haqurin da suka yi; kuma Muka rushe abin da Fir’auna ya kasance yana yi shi da mutanensa, da abin da suka kasance suna ginawa



Surah: Suratul A’araf

Ayah : 138

وَجَٰوَزۡنَا بِبَنِيٓ إِسۡرَـٰٓءِيلَ ٱلۡبَحۡرَ فَأَتَوۡاْ عَلَىٰ قَوۡمٖ يَعۡكُفُونَ عَلَىٰٓ أَصۡنَامٖ لَّهُمۡۚ قَالُواْ يَٰمُوسَى ٱجۡعَل لَّنَآ إِلَٰهٗا كَمَا لَهُمۡ ءَالِهَةٞۚ قَالَ إِنَّكُمۡ قَوۡمٞ تَجۡهَلُونَ

Kuma sai Muka tsallakar da Banu Isra’ila kogi, sai suka tarar da waxansu mutane da suka duqufa a kan (bautar) gumakansu, suka ce: “Ya kai Musa, ka sa mana wani abin bauta, irin yadda waxannan suke da abubuwan bauta.” Sai ya ce: “Lalle ku mutane ne da kuke da jahilci



Surah: Suratul A’araf

Ayah : 139

إِنَّ هَـٰٓؤُلَآءِ مُتَبَّرٞ مَّا هُمۡ فِيهِ وَبَٰطِلٞ مَّا كَانُواْ يَعۡمَلُونَ

“Lalle waxannan abin da suke cikinsa halaka ne, kuma abin da suke aikatawa varna ce.”



Surah: Suratul A’araf

Ayah : 140

قَالَ أَغَيۡرَ ٱللَّهِ أَبۡغِيكُمۡ إِلَٰهٗا وَهُوَ فَضَّلَكُمۡ عَلَى ٱلۡعَٰلَمِينَ

Ya ce: “Shin yanzu wani wanda ba Allah ba zan nemo muku a matsayin abin bauta, alhali Shi ne Ya fifita ku a kan sauran talikai?”



Surah: Suratul A’araf

Ayah : 141

وَإِذۡ أَنجَيۡنَٰكُم مِّنۡ ءَالِ فِرۡعَوۡنَ يَسُومُونَكُمۡ سُوٓءَ ٱلۡعَذَابِ يُقَتِّلُونَ أَبۡنَآءَكُمۡ وَيَسۡتَحۡيُونَ نِسَآءَكُمۡۚ وَفِي ذَٰلِكُم بَلَآءٞ مِّن رَّبِّكُمۡ عَظِيمٞ

Kuma ku tuna lokacin da Muka tserar da ku daga mutanen Fir’auna, (waxanda) suke xanxana muku mummunar azaba; suna karkashe ‘ya’yanku maza, kuma suna barin ‘ya’yanku mata da rai, kuma lalle a cikin wannan akwai wata jarraba babba daga Ubangijinku



Surah: Suratul A’araf

Ayah : 142

۞وَوَٰعَدۡنَا مُوسَىٰ ثَلَٰثِينَ لَيۡلَةٗ وَأَتۡمَمۡنَٰهَا بِعَشۡرٖ فَتَمَّ مِيقَٰتُ رَبِّهِۦٓ أَرۡبَعِينَ لَيۡلَةٗۚ وَقَالَ مُوسَىٰ لِأَخِيهِ هَٰرُونَ ٱخۡلُفۡنِي فِي قَوۡمِي وَأَصۡلِحۡ وَلَا تَتَّبِعۡ سَبِيلَ ٱلۡمُفۡسِدِينَ

Mun kuma yi wa Musa alqawarin dare talatin, muka kuma cika su da goma, sai miqatin Ubangijinsa ya cika darare arba’in cif-cif. Sai Musa ya ce da xan’uwansa Haruna: “Ka wakilce ni a cikin mutanena, kuma ka daidaita (tsakaninsu), kada kuma ka bi tafarkin mavarnata.”



Surah: Suratul A’araf

Ayah : 143

وَلَمَّا جَآءَ مُوسَىٰ لِمِيقَٰتِنَا وَكَلَّمَهُۥ رَبُّهُۥ قَالَ رَبِّ أَرِنِيٓ أَنظُرۡ إِلَيۡكَۚ قَالَ لَن تَرَىٰنِي وَلَٰكِنِ ٱنظُرۡ إِلَى ٱلۡجَبَلِ فَإِنِ ٱسۡتَقَرَّ مَكَانَهُۥ فَسَوۡفَ تَرَىٰنِيۚ فَلَمَّا تَجَلَّىٰ رَبُّهُۥ لِلۡجَبَلِ جَعَلَهُۥ دَكّٗا وَخَرَّ مُوسَىٰ صَعِقٗاۚ فَلَمَّآ أَفَاقَ قَالَ سُبۡحَٰنَكَ تُبۡتُ إِلَيۡكَ وَأَنَا۠ أَوَّلُ ٱلۡمُؤۡمِنِينَ

Lokacin Kuma da Musa ya zo wajen da muka yi alqawari da shi, Ubangijinsa kuma Ya yi magana da shi, sai ya ce: “Ya Ubangijina, nuna mini kanka in gan Ka.” Sai ya ce: “Ba za ka iya gani Na ba[1], amma dubi dutsen nan, idan ya tabbata a bigirensa, to da sannu za ka gan Ni.” To lokacin da Ubangijinsa Ya bayyana (da haskensa) ga dutsen, sai Ya mayar da shi rugu-rugu, sai Musa ya faxi sumamme. To yayin da ya farfaxo, sai ya ce: “Tsarki ya tabbata gare Ka, na tuba zuwa gare Ka, kuma ni ne farkon muminai.”


1- Muminai a nan duniya ba za su iya ganin Allah () a fili ba, amma a lahira za su gan shi kamar yadda hadisai da yawa suka tabbatar.


Surah: Suratul A’araf

Ayah : 144

قَالَ يَٰمُوسَىٰٓ إِنِّي ٱصۡطَفَيۡتُكَ عَلَى ٱلنَّاسِ بِرِسَٰلَٰتِي وَبِكَلَٰمِي فَخُذۡ مَآ ءَاتَيۡتُكَ وَكُن مِّنَ ٱلشَّـٰكِرِينَ

Ya ce: “Ya kai Musa, Lalle Ni na zave ka a kan sauran mutane da saqona da kuma zancena, don haka ka riqe abin da na ba ka, kuma ka kasance cikin masu godiya.”



Surah: Suratul A’araf

Ayah : 145

وَكَتَبۡنَا لَهُۥ فِي ٱلۡأَلۡوَاحِ مِن كُلِّ شَيۡءٖ مَّوۡعِظَةٗ وَتَفۡصِيلٗا لِّكُلِّ شَيۡءٖ فَخُذۡهَا بِقُوَّةٖ وَأۡمُرۡ قَوۡمَكَ يَأۡخُذُواْ بِأَحۡسَنِهَاۚ سَأُوْرِيكُمۡ دَارَ ٱلۡفَٰسِقِينَ

Mun kuma rubuta masa komai a cikin allunan (Attaura) don wa’azi da bayani filla-filla na kowane irin abu, don haka ka riqe su da kyau, kuma ka umarci mutanenka su yi riqo da mafi kyawun abin da yake cikinsu. Da sannu zan nuna muku gidajen fasiqai[1].”


1- Wasu sun ce ana nufin wutar Jahannama. Wasu kuma sun ce, ana nufin Baitul Maqdis, saboda mazaunanta a wannan lokaci mushirikai ne. Wasu kuma sun ce, ana nufin qasar Masar da Baitul Maqdisi baki xaya.


Surah: Suratul A’araf

Ayah : 146

سَأَصۡرِفُ عَنۡ ءَايَٰتِيَ ٱلَّذِينَ يَتَكَبَّرُونَ فِي ٱلۡأَرۡضِ بِغَيۡرِ ٱلۡحَقِّ وَإِن يَرَوۡاْ كُلَّ ءَايَةٖ لَّا يُؤۡمِنُواْ بِهَا وَإِن يَرَوۡاْ سَبِيلَ ٱلرُّشۡدِ لَا يَتَّخِذُوهُ سَبِيلٗا وَإِن يَرَوۡاْ سَبِيلَ ٱلۡغَيِّ يَتَّخِذُوهُ سَبِيلٗاۚ ذَٰلِكَ بِأَنَّهُمۡ كَذَّبُواْ بِـَٔايَٰتِنَا وَكَانُواْ عَنۡهَا غَٰفِلِينَ

Zan kautar da waxanda suke yin girman kai a bayan qasa ba tare da haqqi ba daga (fahimtar) ayoyina; idan kuma za su ga kowace irin aya ba za su yi imani da ita ba, idan kuma da za su ga hanyar shiriya ba za su riqe ta hanyar bi ba, (amma) idan kuwa za su ga hanyar vata, to za su riqe ta hanyar bi. Wannan kuwa saboda sun qaryata ayoyinmu, kuma sun kasance gafalallu ga barin su



Surah: Suratul A’araf

Ayah : 147

وَٱلَّذِينَ كَذَّبُواْ بِـَٔايَٰتِنَا وَلِقَآءِ ٱلۡأٓخِرَةِ حَبِطَتۡ أَعۡمَٰلُهُمۡۚ هَلۡ يُجۡزَوۡنَ إِلَّا مَا كَانُواْ يَعۡمَلُونَ

Waxanda kuma suka qaryata ayoyinmu da haxuwa a ranar alqiyama, ayyukansu sun rushe. Shin kuwa za a yi musu wani sakamako ne in ba abin da suka kasance suna aikatawa ba?



Surah: Suratul A’araf

Ayah : 148

وَٱتَّخَذَ قَوۡمُ مُوسَىٰ مِنۢ بَعۡدِهِۦ مِنۡ حُلِيِّهِمۡ عِجۡلٗا جَسَدٗا لَّهُۥ خُوَارٌۚ أَلَمۡ يَرَوۡاْ أَنَّهُۥ لَا يُكَلِّمُهُمۡ وَلَا يَهۡدِيهِمۡ سَبِيلًاۘ ٱتَّخَذُوهُ وَكَانُواْ ظَٰلِمِينَ

Mutanen Musa kuma a bayansa sun qera wani xan maraqi daga kayan adonsu mai surar jiki yana wata qara (don su bauta masa). Shin ba su ga cewa ba ya yi musu Magana, kuma ba ya iya shiryar da su wani tafarki? Sun riqe shi (a matsayin abin bauta), kuma sun tabbata azzalumai



Surah: Suratul A’araf

Ayah : 149

وَلَمَّا سُقِطَ فِيٓ أَيۡدِيهِمۡ وَرَأَوۡاْ أَنَّهُمۡ قَدۡ ضَلُّواْ قَالُواْ لَئِن لَّمۡ يَرۡحَمۡنَا رَبُّنَا وَيَغۡفِرۡ لَنَا لَنَكُونَنَّ مِنَ ٱلۡخَٰسِرِينَ

Kuma lokacin da suka yi nadama, suka gane cewa sun vata, sai suka ce: “Matuqar Ubangijinmu bai ji qan mu ba, kuma bai gafarta mana ba, lalle za mu kasance cikin hasararru.”



Surah: Suratul A’araf

Ayah : 150

وَلَمَّا رَجَعَ مُوسَىٰٓ إِلَىٰ قَوۡمِهِۦ غَضۡبَٰنَ أَسِفٗا قَالَ بِئۡسَمَا خَلَفۡتُمُونِي مِنۢ بَعۡدِيٓۖ أَعَجِلۡتُمۡ أَمۡرَ رَبِّكُمۡۖ وَأَلۡقَى ٱلۡأَلۡوَاحَ وَأَخَذَ بِرَأۡسِ أَخِيهِ يَجُرُّهُۥٓ إِلَيۡهِۚ قَالَ ٱبۡنَ أُمَّ إِنَّ ٱلۡقَوۡمَ ٱسۡتَضۡعَفُونِي وَكَادُواْ يَقۡتُلُونَنِي فَلَا تُشۡمِتۡ بِيَ ٱلۡأَعۡدَآءَ وَلَا تَجۡعَلۡنِي مَعَ ٱلۡقَوۡمِ ٱلظَّـٰلِمِينَ

Lokacin kuma da Musa ya dawo wajen mutanensa a fusace yana mai damuwa, sai ya ce: “Tir da abin da kuka aikata bayana. Yanzu kwa gaggauto al’amarin Ubangijinku?” Sai ya jefar da allunan, ya kama kan xan’uwansa yana jan sa zuwa gare shi. Sai (Haruna) ya ce: “Ya kai xan’ummata, mutanen nan haqiqa sun raina ni, har ma sun kusa kashe ni, don haka kar ka sa maqiya su yi min dariya, kuma kada ka sa ni cikin mutane azzalumai.”



Surah: Suratul A’araf

Ayah : 151

قَالَ رَبِّ ٱغۡفِرۡ لِي وَلِأَخِي وَأَدۡخِلۡنَا فِي رَحۡمَتِكَۖ وَأَنتَ أَرۡحَمُ ٱلرَّـٰحِمِينَ

Sai ya ce: “Ya Ubangijina, Ka gafarta mini ni da xan’uwana, kuma Ka shigar da mu cikin rahamarka; kuma Kai ne Fiyayyen masu jin qai.”



Surah: Suratul A’araf

Ayah : 152

إِنَّ ٱلَّذِينَ ٱتَّخَذُواْ ٱلۡعِجۡلَ سَيَنَالُهُمۡ غَضَبٞ مِّن رَّبِّهِمۡ وَذِلَّةٞ فِي ٱلۡحَيَوٰةِ ٱلدُّنۡيَاۚ وَكَذَٰلِكَ نَجۡزِي ٱلۡمُفۡتَرِينَ

Lalle waxannan da suka riqi xan maraqi (abin bauta) fushin Ubangijinsu zai same su da qasqanci a cikin rayuwar duniya. Kuma kamar haka ne Muke saka wa masu qage



Surah: Suratul A’araf

Ayah : 153

وَٱلَّذِينَ عَمِلُواْ ٱلسَّيِّـَٔاتِ ثُمَّ تَابُواْ مِنۢ بَعۡدِهَا وَءَامَنُوٓاْ إِنَّ رَبَّكَ مِنۢ بَعۡدِهَا لَغَفُورٞ رَّحِيمٞ

Waxanda kuma suka aikata munanan ayyuka, sannan suka tuba daga baya, kuma suka yi imani, lalle Ubangijinka bayansa (tuban), tabbas Mai gafara ne, Mai jin qai



Surah: Suratul A’araf

Ayah : 154

وَلَمَّا سَكَتَ عَن مُّوسَى ٱلۡغَضَبُ أَخَذَ ٱلۡأَلۡوَاحَۖ وَفِي نُسۡخَتِهَا هُدٗى وَرَحۡمَةٞ لِّلَّذِينَ هُمۡ لِرَبِّهِمۡ يَرۡهَبُونَ

Yayin kuma da Musa ya huce, sai ya xauki allunan nan (na Attaura); kuma abin da aka rubuta a cikinsu shiriya ne da rahama ga waxanda suke tsoron Ubangijinsu



Surah: Suratul A’araf

Ayah : 155

وَٱخۡتَارَ مُوسَىٰ قَوۡمَهُۥ سَبۡعِينَ رَجُلٗا لِّمِيقَٰتِنَاۖ فَلَمَّآ أَخَذَتۡهُمُ ٱلرَّجۡفَةُ قَالَ رَبِّ لَوۡ شِئۡتَ أَهۡلَكۡتَهُم مِّن قَبۡلُ وَإِيَّـٰيَۖ أَتُهۡلِكُنَا بِمَا فَعَلَ ٱلسُّفَهَآءُ مِنَّآۖ إِنۡ هِيَ إِلَّا فِتۡنَتُكَ تُضِلُّ بِهَا مَن تَشَآءُ وَتَهۡدِي مَن تَشَآءُۖ أَنتَ وَلِيُّنَا فَٱغۡفِرۡ لَنَا وَٱرۡحَمۡنَاۖ وَأَنتَ خَيۡرُ ٱلۡغَٰفِرِينَ

Musa kuma ya zavi mutanensa, maza (na musamman) su saba’in don alqawarinmu[1]; to yayin da wata tsawa ta kama su, sai ya ce: “Ya Ubangijina, idan da Ka ga dama da tun tuni Ka hallakar da su har da ni kaina. Yanzu Ka halaka mu saboda abin da wasu wawaye daga cikinmu suka aikata? Lalle wannan ba komai ba ne face jarrabawa daga gare Ka, Kana vatar da wanda Ka ga dama; Kana kuma shiryar da wanda Ka ga dama; Kai ne Majivincin lamarinmu, don haka Ka gafarta mana, kuma Ka ji qan mu, kuma Kai ne Fiyayyen masu gafara


1- Watau ganawa da Allah don su gabatar da uzurinsu game da bautar xan maraqi da suka yi, su wakilci ‘yan’uwansu wajen neman gafarar Allah.


Surah: Suratul A’araf

Ayah : 156

۞وَٱكۡتُبۡ لَنَا فِي هَٰذِهِ ٱلدُّنۡيَا حَسَنَةٗ وَفِي ٱلۡأٓخِرَةِ إِنَّا هُدۡنَآ إِلَيۡكَۚ قَالَ عَذَابِيٓ أُصِيبُ بِهِۦ مَنۡ أَشَآءُۖ وَرَحۡمَتِي وَسِعَتۡ كُلَّ شَيۡءٖۚ فَسَأَكۡتُبُهَا لِلَّذِينَ يَتَّقُونَ وَيُؤۡتُونَ ٱلزَّكَوٰةَ وَٱلَّذِينَ هُم بِـَٔايَٰتِنَا يُؤۡمِنُونَ

“Kuma Ka rubuta mana kyakkyawan abu a cikin wannan duniyar, haka ma a lahira, lalle mu mun tuba zuwa gare Ka.” (Allah) Ya ce: “Ina saukar da azabata a kan wanda Na ga dama; rahamata kuwa ta yalwaci komai. Don haka da sannu zan rubuta ta ga waxanda suke kiyaye dokokin Allah, kuma suke bayar da zakka da kuma waxanda suke yin imani da ayoyinmu



Surah: Suratul A’araf

Ayah : 159

وَمِن قَوۡمِ مُوسَىٰٓ أُمَّةٞ يَهۡدُونَ بِٱلۡحَقِّ وَبِهِۦ يَعۡدِلُونَ

Kuma daga cikin mutanen Musa akwai wata jama’a waxanda suke shiryarwa da gaskiya, da kuma ita ne suke yin hukunci na adalci[1]


1- Su ne waxanda suka yi Imani da Annabi Muhammadu ().


Surah: Suratul A’araf

Ayah : 160

وَقَطَّعۡنَٰهُمُ ٱثۡنَتَيۡ عَشۡرَةَ أَسۡبَاطًا أُمَمٗاۚ وَأَوۡحَيۡنَآ إِلَىٰ مُوسَىٰٓ إِذِ ٱسۡتَسۡقَىٰهُ قَوۡمُهُۥٓ أَنِ ٱضۡرِب بِّعَصَاكَ ٱلۡحَجَرَۖ فَٱنۢبَجَسَتۡ مِنۡهُ ٱثۡنَتَا عَشۡرَةَ عَيۡنٗاۖ قَدۡ عَلِمَ كُلُّ أُنَاسٖ مَّشۡرَبَهُمۡۚ وَظَلَّلۡنَا عَلَيۡهِمُ ٱلۡغَمَٰمَ وَأَنزَلۡنَا عَلَيۡهِمُ ٱلۡمَنَّ وَٱلسَّلۡوَىٰۖ كُلُواْ مِن طَيِّبَٰتِ مَا رَزَقۡنَٰكُمۡۚ وَمَا ظَلَمُونَا وَلَٰكِن كَانُوٓاْ أَنفُسَهُمۡ يَظۡلِمُونَ

Mun kuma karkasa su qabilu goma sha biyu daban-daban[1], sai Muka kuma yi wahayi ga Musa yayin da mutanensa suka nemi ya shayar da su ruwa cewa: “Ka doki dutse da sandarka,” sai idanun ruwa goma sha biyu suka vuvvugo daga jikinsa. Haqiqa kowace qabila ta san mashayarta. Muka kuma yi musu inuwa da girgije, kuma Muka saukar musu da darva da tsuntsayen salwa; (muka ce:) “Ku ci daga daddaxan abin da Muka arzurta ku da shi.” Kuma ba su zalunce Mu ba, sai dai kansu suka kasance suna zalunta


1- Su ne zuriyyar ‘ya’yan Annabi Ya’aqub () goma sha biyu.


Surah: Suratu Yunus

Ayah : 75

ثُمَّ بَعَثۡنَا مِنۢ بَعۡدِهِم مُّوسَىٰ وَهَٰرُونَ إِلَىٰ فِرۡعَوۡنَ وَمَلَإِيْهِۦ بِـَٔايَٰتِنَا فَٱسۡتَكۡبَرُواْ وَكَانُواْ قَوۡمٗا مُّجۡرِمِينَ

Sannan daga bayansu Muka aiko Musa da Haruna zuwa ga Fir’auna shi da jama’arsa da ayoyinmu, sai suka yi girman kai suka kuwa zamanto mutane masu laifi