ٱذۡهَبۡ إِلَىٰ فِرۡعَوۡنَ إِنَّهُۥ طَغَىٰ
(Aka ce da shi): Ka tafi zuwa ga Fir’auna, haqiqa shi ya yi xagawa
Share :
فَقُلۡ هَل لَّكَ إِلَىٰٓ أَن تَزَكَّىٰ
Sai ka ce: “Shin zai yiwu gare ka kuwa ka tsarkaka?
وَأَهۡدِيَكَ إِلَىٰ رَبِّكَ فَتَخۡشَىٰ
“In kuma shiryar da kai zuwa ga Ubangijinka, sai ka ji tsoron Sa?
فَأَرَىٰهُ ٱلۡأٓيَةَ ٱلۡكُبۡرَىٰ
Sai ya nuna masa babbar aya[1]
1- Watau ya nuna masa hannun mai haske kamar fitila da kuma sandarsa mai rikixa ta zama macijiya.
فَكَذَّبَ وَعَصَىٰ
Sai ya qaryata ya kuma kangare
ثُمَّ أَدۡبَرَ يَسۡعَىٰ
Sannan ya ba da baya yana ta gaggawa
فَحَشَرَ فَنَادَىٰ
Sai ya tattara (jama’arsa) sai ya yi shela
فَقَالَ أَنَا۠ رَبُّكُمُ ٱلۡأَعۡلَىٰ
Sai ya ce, “Ni ne ubangijinku mafi girma!”
فَأَخَذَهُ ٱللَّهُ نَكَالَ ٱلۡأٓخِرَةِ وَٱلۡأُولَىٰٓ
Saboda haka Allah Ya kama shi da azabar lahira (watau Jahannama) da ta duniya (watau nutse wa a ruwa)
إِنَّ فِي ذَٰلِكَ لَعِبۡرَةٗ لِّمَن يَخۡشَىٰٓ
Lalle a game da wannan tabbas akwai izina ga wanda yake tsoron (Allah)