Surah: Suratul Baqara

Ayah : 154

وَلَا تَقُولُواْ لِمَن يُقۡتَلُ فِي سَبِيلِ ٱللَّهِ أَمۡوَٰتُۢۚ بَلۡ أَحۡيَآءٞ وَلَٰكِن لَّا تَشۡعُرُونَ

Kada kuma ku ce wa waxanda ake kashewa a kan hanyar Allah su matattu ne. A’a, rayayyu ne, sai dai ku ne ba ku sani ba



Surah: Suratu Ali-Imran

Ayah : 140

إِن يَمۡسَسۡكُمۡ قَرۡحٞ فَقَدۡ مَسَّ ٱلۡقَوۡمَ قَرۡحٞ مِّثۡلُهُۥۚ وَتِلۡكَ ٱلۡأَيَّامُ نُدَاوِلُهَا بَيۡنَ ٱلنَّاسِ وَلِيَعۡلَمَ ٱللَّهُ ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ وَيَتَّخِذَ مِنكُمۡ شُهَدَآءَۗ وَٱللَّهُ لَا يُحِبُّ ٱلظَّـٰلِمِينَ

Idan ma wani miki ne ya same ku a jiki, to haqiqa miki irinsa ya sami mutanen (Makka). Kuma waxannan kwanaki ne da muke jujjuya su tsakanin mutane domin Allah Ya bayyanar da waxanda suka yi imani (a gane su), kuma Ya riqi shahidai a cikinku. Allah kuwa ba Ya son azzalumai



Surah: Suratu Ali-Imran

Ayah : 157

وَلَئِن قُتِلۡتُمۡ فِي سَبِيلِ ٱللَّهِ أَوۡ مُتُّمۡ لَمَغۡفِرَةٞ مِّنَ ٱللَّهِ وَرَحۡمَةٌ خَيۡرٞ مِّمَّا يَجۡمَعُونَ

Kuma lalle idan ma har an kashe ku a hanyar Allah ko kuma kuka mutu, to kuna da gafara ta musamman a wajen Allah da kuma rahama, wanda shi ne mafi alheri fiye da abin da suke tarawa



Surah: Suratu Ali-Imran

Ayah : 158

وَلَئِن مُّتُّمۡ أَوۡ قُتِلۡتُمۡ لَإِلَى ٱللَّهِ تُحۡشَرُونَ

Kuma lalle in kuka mutu ko aka kashe ku, lalle zuwa ga Allah dai za a tattara ku



Surah: Suratu Ali-Imran

Ayah : 169

وَلَا تَحۡسَبَنَّ ٱلَّذِينَ قُتِلُواْ فِي سَبِيلِ ٱللَّهِ أَمۡوَٰتَۢاۚ بَلۡ أَحۡيَآءٌ عِندَ رَبِّهِمۡ يُرۡزَقُونَ

Kuma kada ka yi tsammanin waxanda aka kashe su a wajen yaxa kalmar Allah matattu ne. A’a, rayayyu ne a wajen Ubangijinsu, ana arzurta su



Surah: Suratu Ali-Imran

Ayah : 170

فَرِحِينَ بِمَآ ءَاتَىٰهُمُ ٱللَّهُ مِن فَضۡلِهِۦ وَيَسۡتَبۡشِرُونَ بِٱلَّذِينَ لَمۡ يَلۡحَقُواْ بِهِم مِّنۡ خَلۡفِهِمۡ أَلَّا خَوۡفٌ عَلَيۡهِمۡ وَلَا هُمۡ يَحۡزَنُونَ

Suna cike da farin cikin abin da Allah Ya ba su na falalarsa, kuma suna masu yin albishir ga waxanda ba su riga sun riske su ba daga bayansu cewa, babu jin tsoro a gare su, kuma ba za su yi baqin ciki ba



Surah: Suratu Ali-Imran

Ayah : 171

۞يَسۡتَبۡشِرُونَ بِنِعۡمَةٖ مِّنَ ٱللَّهِ وَفَضۡلٖ وَأَنَّ ٱللَّهَ لَا يُضِيعُ أَجۡرَ ٱلۡمُؤۡمِنِينَ

Suna ta farin ciki da ni’ima daga Allah da falala, kuma Allah ba Ya tozarta ladan masu imani



Surah: Suratu Ali-Imran

Ayah : 195

فَٱسۡتَجَابَ لَهُمۡ رَبُّهُمۡ أَنِّي لَآ أُضِيعُ عَمَلَ عَٰمِلٖ مِّنكُم مِّن ذَكَرٍ أَوۡ أُنثَىٰۖ بَعۡضُكُم مِّنۢ بَعۡضٖۖ فَٱلَّذِينَ هَاجَرُواْ وَأُخۡرِجُواْ مِن دِيَٰرِهِمۡ وَأُوذُواْ فِي سَبِيلِي وَقَٰتَلُواْ وَقُتِلُواْ لَأُكَفِّرَنَّ عَنۡهُمۡ سَيِّـَٔاتِهِمۡ وَلَأُدۡخِلَنَّهُمۡ جَنَّـٰتٖ تَجۡرِي مِن تَحۡتِهَا ٱلۡأَنۡهَٰرُ ثَوَابٗا مِّنۡ عِندِ ٱللَّهِۚ وَٱللَّهُ عِندَهُۥ حُسۡنُ ٱلثَّوَابِ

Sai Ubangijinsu Ya amsa musu (cewa): “Lalle Ni ba zan tozarta aikin wani mai aiki daga cikinku ba, namiji ne ko mace; sashinku yana tare da sashe. To waxanda suka yi hijira kuma aka fitar da su daga gidajensu kuma aka cutar da su wajen bin tafarkina kuma suka yi yaqi kuma aka kashe su, lalle zan kankare musu kurakuransu, kuma lalle zan shigar da su gidajen Aljanna waxanda qoramu suke gudana ta qarqashinsu. (Wannan) lada ne daga wajen Allah, kuma a wurin Allah ne mafi kyawun lada yake.”



Surah: Suratun Nisa’i

Ayah : 69

وَمَن يُطِعِ ٱللَّهَ وَٱلرَّسُولَ فَأُوْلَـٰٓئِكَ مَعَ ٱلَّذِينَ أَنۡعَمَ ٱللَّهُ عَلَيۡهِم مِّنَ ٱلنَّبِيِّـۧنَ وَٱلصِّدِّيقِينَ وَٱلشُّهَدَآءِ وَٱلصَّـٰلِحِينَۚ وَحَسُنَ أُوْلَـٰٓئِكَ رَفِيقٗا

Kuma duk waxanda suka yi wa Allah xa’a da wannan Manzon, to waxannan suna tare da waxanda Allah Ya yi musu ni’ima, su ne annabawa da siddiqai da shahidai da salihan bayi. Kuma madalla da waxannan abokai



Surah: Suratun Nisa’i

Ayah : 74

۞فَلۡيُقَٰتِلۡ فِي سَبِيلِ ٱللَّهِ ٱلَّذِينَ يَشۡرُونَ ٱلۡحَيَوٰةَ ٱلدُّنۡيَا بِٱلۡأٓخِرَةِۚ وَمَن يُقَٰتِلۡ فِي سَبِيلِ ٱللَّهِ فَيُقۡتَلۡ أَوۡ يَغۡلِبۡ فَسَوۡفَ نُؤۡتِيهِ أَجۡرًا عَظِيمٗا

To waxanda suke sayen rayuwar lahira da ta duniya, sai su yi yaqi don xaukaka kalmar Allah. Duk wanda yake yin yaqi don xaukaka kalmar Allah kuwa, sai aka kashe shi ko kuma ya yi galaba, to za Mu ba shi lada mai girma



Surah: Suratul Hajji

Ayah : 58

وَٱلَّذِينَ هَاجَرُواْ فِي سَبِيلِ ٱللَّهِ ثُمَّ قُتِلُوٓاْ أَوۡ مَاتُواْ لَيَرۡزُقَنَّهُمُ ٱللَّهُ رِزۡقًا حَسَنٗاۚ وَإِنَّ ٱللَّهَ لَهُوَ خَيۡرُ ٱلرَّـٰزِقِينَ

Waxanda kuwa suka yi hijira saboda Allah sannan aka kashe su ko kuma suka mutu, to lalle Allah tabbas zai arzuta su da kyakkyawan arziki. Kuma lalle Allah tabbas Shi ne Fiyayyen masu arzutawa



Surah: Suratul Hajji

Ayah : 59

لَيُدۡخِلَنَّهُم مُّدۡخَلٗا يَرۡضَوۡنَهُۥۚ وَإِنَّ ٱللَّهَ لَعَلِيمٌ حَلِيمٞ

Lalle tabbas Zai shigar da su wata mashiga da za su yarda da ita. Kuma lalle Allah tabbas Masani ne, Mai hakuri



Surah: Suratu Muhammad

Ayah : 4

فَإِذَا لَقِيتُمُ ٱلَّذِينَ كَفَرُواْ فَضَرۡبَ ٱلرِّقَابِ حَتَّىٰٓ إِذَآ أَثۡخَنتُمُوهُمۡ فَشُدُّواْ ٱلۡوَثَاقَ فَإِمَّا مَنَّۢا بَعۡدُ وَإِمَّا فِدَآءً حَتَّىٰ تَضَعَ ٱلۡحَرۡبُ أَوۡزَارَهَاۚ ذَٰلِكَۖ وَلَوۡ يَشَآءُ ٱللَّهُ لَٱنتَصَرَ مِنۡهُمۡ وَلَٰكِن لِّيَبۡلُوَاْ بَعۡضَكُم بِبَعۡضٖۗ وَٱلَّذِينَ قُتِلُواْ فِي سَبِيلِ ٱللَّهِ فَلَن يُضِلَّ أَعۡمَٰلَهُمۡ

To idan kuka haxu da waxanda suka kafirta sai ku sare wuyoyinsu har lokacin da kuka yi musu jina-jina, sai ku tsananta xauri[1]; to bayan nan ko dai yafewa su tafi bayan (kun ribace su), ko kuma karvar fansa har sai yaqi ya lafa. Wannan abu haka yake, da kuma Allah Ya ga dama da Ya yi nasara a kansu (ko da ba yaqi), sai dai kuma (Ya yi haka ne) don Ya jarrabi shashinku da shashi. Waxanda kuwa aka kashe su a hanyar Allah, to ba zai tava lalata ayyukansa ba


1- Watau Musulmi su kama su a matsayin ribatattun yaqi.


Surah: Suratul Hadid

Ayah : 19

وَٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ بِٱللَّهِ وَرُسُلِهِۦٓ أُوْلَـٰٓئِكَ هُمُ ٱلصِّدِّيقُونَۖ وَٱلشُّهَدَآءُ عِندَ رَبِّهِمۡ لَهُمۡ أَجۡرُهُمۡ وَنُورُهُمۡۖ وَٱلَّذِينَ كَفَرُواْ وَكَذَّبُواْ بِـَٔايَٰتِنَآ أُوْلَـٰٓئِكَ أَصۡحَٰبُ ٱلۡجَحِيمِ

Waxanda kuma suka yi imani da Allah da manzanninsa, waxannan su ne siddiqai; shahidai kuma suna da ladansu da haskensu a wurin Ubangijinsu; waxanda kuwa suka kafirta suke kuma qaryata ayoyinmu, to waxannan su ne ‘yan (wutar) Jahimu