Surah: Suratul Ma’arij

Ayah : 29

وَٱلَّذِينَ هُمۡ لِفُرُوجِهِمۡ حَٰفِظُونَ

Waxanda kuma suke kiyaye al’aurarsu (daga yin zina)



Surah: Suratul Ma’arij

Ayah : 30

إِلَّا عَلَىٰٓ أَزۡوَٰجِهِمۡ أَوۡ مَا مَلَكَتۡ أَيۡمَٰنُهُمۡ فَإِنَّهُمۡ غَيۡرُ مَلُومِينَ

Sai a wajan matayensu ko kuma qwarqarorinsu; to su a nan ba ababen zargi ba ne



Surah: Suratul Ma’arij

Ayah : 31

فَمَنِ ٱبۡتَغَىٰ وَرَآءَ ذَٰلِكَ فَأُوْلَـٰٓئِكَ هُمُ ٱلۡعَادُونَ

To duk wanda ya nemi (wani abu) bayan wannan, to waxannan su ne masu qetare iyaka