Surah: Suratul A’araf

Ayah : 83

فَأَنجَيۡنَٰهُ وَأَهۡلَهُۥٓ إِلَّا ٱمۡرَأَتَهُۥ كَانَتۡ مِنَ ٱلۡغَٰبِرِينَ

Sai Muka tserar da shi da iyalansa, in ban da matarsa, ita ta kasance cikin waxanda suka rage (a cikin azaba)



Surah: Suratu Hud

Ayah : 81

قَالُواْ يَٰلُوطُ إِنَّا رُسُلُ رَبِّكَ لَن يَصِلُوٓاْ إِلَيۡكَۖ فَأَسۡرِ بِأَهۡلِكَ بِقِطۡعٖ مِّنَ ٱلَّيۡلِ وَلَا يَلۡتَفِتۡ مِنكُمۡ أَحَدٌ إِلَّا ٱمۡرَأَتَكَۖ إِنَّهُۥ مُصِيبُهَا مَآ أَصَابَهُمۡۚ إِنَّ مَوۡعِدَهُمُ ٱلصُّبۡحُۚ أَلَيۡسَ ٱلصُّبۡحُ بِقَرِيبٖ

(Baqin) suka ce: “Ya Luxu, lalle mu manzannin Ubangijinka ne; ba za su iya isowa gare ka ba; don haka sai ka tafi kai da iyalanka cikin wani yanki na dare, kada kuwa xaya daga cikinku ya waiwaya, sai matarka kawai. Lalle ita kam abin da ya same su zai same ta. Lalle lokacin da aka xebar musu asuba ne kawai; shin asuba ba kurkusa take ba?



Surah: Suratul Hijr

Ayah : 60

إِلَّا ٱمۡرَأَتَهُۥ قَدَّرۡنَآ إِنَّهَا لَمِنَ ٱلۡغَٰبِرِينَ

“Sai fa matarsa ita kam mun qaddara cewa tabbas za ta zama cikin halakakku.”



Surah: Suratus Shu’ara

Ayah : 171

إِلَّا عَجُوزٗا فِي ٱلۡغَٰبِرِينَ

Sai fa wata tsohuwa (watau matarsa) da ta (kasance tana) cikin hallakakku



Surah: Suratun Namli

Ayah : 57

فَأَنجَيۡنَٰهُ وَأَهۡلَهُۥٓ إِلَّا ٱمۡرَأَتَهُۥ قَدَّرۡنَٰهَا مِنَ ٱلۡغَٰبِرِينَ

Sai Muka tserar da shi tare da iyalinsa in ban da matarsa da Muka qaddara ta cikin hallakakku



Surah: Suratul Ankabut

Ayah : 32

قَالَ إِنَّ فِيهَا لُوطٗاۚ قَالُواْ نَحۡنُ أَعۡلَمُ بِمَن فِيهَاۖ لَنُنَجِّيَنَّهُۥ وَأَهۡلَهُۥٓ إِلَّا ٱمۡرَأَتَهُۥ كَانَتۡ مِنَ ٱلۡغَٰبِرِينَ

Sai (Ibrahimu) ya ce: “Lalle Luxu yana cikinta”. Sai suka ce: “Mu muka fi sanin waxanda suke cikinta; tabbas za mu tserar da shi tare da iyalinsa, sai matarsa kawai da ta kasance cikin waxanda za su yi saura (a hallaka su tare)”



Surah: Suratul Ankabut

Ayah : 33

وَلَمَّآ أَن جَآءَتۡ رُسُلُنَا لُوطٗا سِيٓءَ بِهِمۡ وَضَاقَ بِهِمۡ ذَرۡعٗاۖ وَقَالُواْ لَا تَخَفۡ وَلَا تَحۡزَنۡ إِنَّا مُنَجُّوكَ وَأَهۡلَكَ إِلَّا ٱمۡرَأَتَكَ كَانَتۡ مِنَ ٱلۡغَٰبِرِينَ

Lokacin kuma da manzanninmu suka zo wa Luxu, sai ya yi baqin ciki da zuwansu, zuciyarsa kuma ta quntata saboda su[1], sai suka ce da shi: “Kada ka ji tsoro, kuma kada ka damu; lalle mu masu tserar da kai ne tare da iyalinka, sai matarka kawai da ta kasance cikin waxanda za su yi saura (a hallaka su tare)


1- Domin jiye musu tsoron mugun halin mutanensa musamman saboda mala’ikun sun zo a cikin kamanni na mutane maza.


Surah: Suratus Saffat

Ayah : 135

إِلَّا عَجُوزٗا فِي ٱلۡغَٰبِرِينَ

Sai dai wata tsohuwa (wato matarsa) da take cikin halakakku



Surah: Suratut Tahrim

Ayah : 10

ضَرَبَ ٱللَّهُ مَثَلٗا لِّلَّذِينَ كَفَرُواْ ٱمۡرَأَتَ نُوحٖ وَٱمۡرَأَتَ لُوطٖۖ كَانَتَا تَحۡتَ عَبۡدَيۡنِ مِنۡ عِبَادِنَا صَٰلِحَيۡنِ فَخَانَتَاهُمَا فَلَمۡ يُغۡنِيَا عَنۡهُمَا مِنَ ٱللَّهِ شَيۡـٔٗا وَقِيلَ ٱدۡخُلَا ٱلنَّارَ مَعَ ٱلدَّـٰخِلِينَ

Allah Ya ba da wani misali ga waxanda suka kafirta da matar Nuhu da matar Luxu; sun kasance qarqashin (igiyar auren) wasu bayi su biyu salihai daga bayinmu, sai suka ha’ince su[1], saboda haka ba su wadatar musu komai ba (daga azabar) Allah, aka kuma ce: “Ku shiga wuta tare da masu shiga.”


1- Watau suka kafirce musu, suka riqa hana mutane bin addinin Allah, suka kuma riqa goyon bayan kafirai.