فَأَخَذَتۡهُمُ ٱلصَّيۡحَةُ مُشۡرِقِينَ
Sai tsawa ta auka musu lokacin hudowar rana
فَجَعَلۡنَا عَٰلِيَهَا سَافِلَهَا وَأَمۡطَرۡنَا عَلَيۡهِمۡ حِجَارَةٗ مِّن سِجِّيلٍ
Sai Muka mayar da samanta ya koma qasa, Muka kuma yi musu ruwan duwatsu soyayyu
إِنَّ فِي ذَٰلِكَ لَأٓيَٰتٖ لِّلۡمُتَوَسِّمِينَ
Lalle a game da wannan tabbas akwai ayoyi ga masu hangen nesa
وَإِنَّهَا لَبِسَبِيلٖ مُّقِيمٍ
Lalle kuma ita (alqaryar) tabbas tana kan wani gwadabe ne miqaqqe
إِنَّ فِي ذَٰلِكَ لَأٓيَةٗ لِّلۡمُؤۡمِنِينَ
Lalle a game da wannan tabbas akwai izina ga muminai
وَلُوطًا ءَاتَيۡنَٰهُ حُكۡمٗا وَعِلۡمٗا وَنَجَّيۡنَٰهُ مِنَ ٱلۡقَرۡيَةِ ٱلَّتِي كَانَت تَّعۡمَلُ ٱلۡخَبَـٰٓئِثَۚ إِنَّهُمۡ كَانُواْ قَوۡمَ سَوۡءٖ فَٰسِقِينَ
Luxu kuma Muka ba shi hukunci da ilimi, Muka kuma tserar da shi daga alqaryar nan da (mutanenta) suka zamanto suna aikata munanan ayyuka. Lallai su sun kasance mutanen banza ne fasiqai
وَأَدۡخَلۡنَٰهُ فِي رَحۡمَتِنَآۖ إِنَّهُۥ مِنَ ٱلصَّـٰلِحِينَ
Muka kuma shigar da shi cikin rahamarmu; lallai shi yana daga (cikin) mutane na gari
كَذَّبَتۡ قَوۡمُ لُوطٍ ٱلۡمُرۡسَلِينَ
Mutanen Luxu sun qaryata manzanni
إِذۡ قَالَ لَهُمۡ أَخُوهُمۡ لُوطٌ أَلَا تَتَّقُونَ
Lokacin da xan’uwansu Luxu ya ce da su: “Yanzu ba kwa kiyaye dokokin Allah ba?
إِنِّي لَكُمۡ رَسُولٌ أَمِينٞ
“Lalle ni Manzo ne amintacce gare ku
فَٱتَّقُواْ ٱللَّهَ وَأَطِيعُونِ
“To ku kiyaye dokokin Allah kuma ku bi ni
وَمَآ أَسۡـَٔلُكُمۡ عَلَيۡهِ مِنۡ أَجۡرٍۖ إِنۡ أَجۡرِيَ إِلَّا عَلَىٰ رَبِّ ٱلۡعَٰلَمِينَ
“Kuma ba na tambayar ku wani lada game da shi (isar da manzancin); ladana yana wajen Ubangijin talikai kawai
أَتَأۡتُونَ ٱلذُّكۡرَانَ مِنَ ٱلۡعَٰلَمِينَ
“Yanzu kwa riqa zaike wa maza daga halittu?
وَتَذَرُونَ مَا خَلَقَ لَكُمۡ رَبُّكُم مِّنۡ أَزۡوَٰجِكُمۚ بَلۡ أَنتُمۡ قَوۡمٌ عَادُونَ
“Kuma ku bar abin da Ubangijinku Ya halitta na matanku dominku? A’a, ku dai mutane ne masu qetare iyaka.”
قَالُواْ لَئِن لَّمۡ تَنتَهِ يَٰلُوطُ لَتَكُونَنَّ مِنَ ٱلۡمُخۡرَجِينَ
Suka ce: “Tabbas Luxu idan ba ka bar (faxar abin da kake faxa ba) haqiqa za ka kasance daga korarru (daga garin nan).”
قَالَ إِنِّي لِعَمَلِكُم مِّنَ ٱلۡقَالِينَ
(Luxu) ya ce: “Lalle ni ina cikin masu qyamar aikin nan naku
رَبِّ نَجِّنِي وَأَهۡلِي مِمَّا يَعۡمَلُونَ
“Ya Ubangijina, Ka tserar da ni da iyalina daga (sakamakon) abin da suke aikatawa.”
فَنَجَّيۡنَٰهُ وَأَهۡلَهُۥٓ أَجۡمَعِينَ
Sai Muka tserar da shi da iyalinsa gaba xaya
إِلَّا عَجُوزٗا فِي ٱلۡغَٰبِرِينَ
Sai fa wata tsohuwa (watau matarsa) da ta (kasance tana) cikin hallakakku
ثُمَّ دَمَّرۡنَا ٱلۡأٓخَرِينَ
Sannan Muka hallaka sauran
وَأَمۡطَرۡنَا عَلَيۡهِم مَّطَرٗاۖ فَسَآءَ مَطَرُ ٱلۡمُنذَرِينَ
Muka kuma saukar musu da ruwa na azaba; to ruwan azabar waxanda aka yi wa gargaxi ya munana
إِنَّ فِي ذَٰلِكَ لَأٓيَةٗۖ وَمَا كَانَ أَكۡثَرُهُم مُّؤۡمِنِينَ
Lalle a game da wannan tabbas akwai aya; yawancinsu kuwa ba su zamanto muminai ba
وَإِنَّ رَبَّكَ لَهُوَ ٱلۡعَزِيزُ ٱلرَّحِيمُ
Kuma lalle Ubangiijnka tabbas Shi ne Mabuwayi, Mai jin qai
وَلُوطًا إِذۡ قَالَ لِقَوۡمِهِۦٓ أَتَأۡتُونَ ٱلۡفَٰحِشَةَ وَأَنتُمۡ تُبۡصِرُونَ
Kuma ka (ambaci) Luxu lokacin da ya ce da mutanensa: “Yanzu kwa riqa zaike wa alfasha alhali kuwa kuna gani?
أَئِنَّكُمۡ لَتَأۡتُونَ ٱلرِّجَالَ شَهۡوَةٗ مِّن دُونِ ٱلنِّسَآءِۚ بَلۡ أَنتُمۡ قَوۡمٞ تَجۡهَلُونَ
“Yanzu kwa riqa zaike wa maza don sha’awa ba mata ba? A’a, ku dai wasu irin mutane ne da kuke da jahilci”
۞فَمَا كَانَ جَوَابَ قَوۡمِهِۦٓ إِلَّآ أَن قَالُوٓاْ أَخۡرِجُوٓاْ ءَالَ لُوطٖ مِّن قَرۡيَتِكُمۡۖ إِنَّهُمۡ أُنَاسٞ يَتَطَهَّرُونَ
To babu wata amsa da ta fito daga bakin mutanensa sai kawai suka ce: “Ku fitar da Luxu shi da iyalinsa daga alqaryarku; lalle su mutane ne da suke nuna su masu tsarki ne.”
فَأَنجَيۡنَٰهُ وَأَهۡلَهُۥٓ إِلَّا ٱمۡرَأَتَهُۥ قَدَّرۡنَٰهَا مِنَ ٱلۡغَٰبِرِينَ
Sai Muka tserar da shi tare da iyalinsa in ban da matarsa da Muka qaddara ta cikin hallakakku
وَأَمۡطَرۡنَا عَلَيۡهِم مَّطَرٗاۖ فَسَآءَ مَطَرُ ٱلۡمُنذَرِينَ
Muka kuma yi musu ruwan azaba; to ruwan azabar waxanda aka yi wa gargaxi ya munana
۞فَـَٔامَنَ لَهُۥ لُوطٞۘ وَقَالَ إِنِّي مُهَاجِرٌ إِلَىٰ رَبِّيٓۖ إِنَّهُۥ هُوَ ٱلۡعَزِيزُ ٱلۡحَكِيمُ
Sai Luxu ya yi imani da shi. (Sai Ibrahimu) kuma ya ce: “Lalle ni mai yin hijira ne zuwa ga Ubangijina; lalle Shi Mabuwayi ne, Mai hikima.”
وَلَمَّا جَآءَتۡ رُسُلُنَآ إِبۡرَٰهِيمَ بِٱلۡبُشۡرَىٰ قَالُوٓاْ إِنَّا مُهۡلِكُوٓاْ أَهۡلِ هَٰذِهِ ٱلۡقَرۡيَةِۖ إِنَّ أَهۡلَهَا كَانُواْ ظَٰلِمِينَ
Lokacin kuwa da manzanninmu suka zo wa Ibrahimu da albishir[1], sai suka ce: “Lalle mu masu hallaka mutanen wannan alqaryar ne, lalle mutanenta sun kasance azzalumai.”
1- Albishir na samun haihuwar xansa Ishaq () da kuma jikansa Ya’aqub ().