Surah: Suratu Ali-Imran

Ayah : 39

فَنَادَتۡهُ ٱلۡمَلَـٰٓئِكَةُ وَهُوَ قَآئِمٞ يُصَلِّي فِي ٱلۡمِحۡرَابِ أَنَّ ٱللَّهَ يُبَشِّرُكَ بِيَحۡيَىٰ مُصَدِّقَۢا بِكَلِمَةٖ مِّنَ ٱللَّهِ وَسَيِّدٗا وَحَصُورٗا وَنَبِيّٗا مِّنَ ٱلصَّـٰلِحِينَ

Sai mala’iku suka kira shi, lokacin yana tsaye yana salla a cikin xakin ibada, (suka ce): “Lalle Allah Yana yi maka albishir da Yahya, wanda yake mai gaskatawa da wata kalma daga Allah, kuma zai zama shugaba, kuma mai tsare kansa daga mata, kuma Annabi daga cikin salihan bayi.”



Surah: Suratul An’am

Ayah : 85

وَزَكَرِيَّا وَيَحۡيَىٰ وَعِيسَىٰ وَإِلۡيَاسَۖ كُلّٞ مِّنَ ٱلصَّـٰلِحِينَ

Da Zakariyya da Yahaya da Isa da Iliyasu; kowanne daga cikinsu yana cikin salihan bayi



Surah: Suratu Maryam

Ayah : 7

يَٰزَكَرِيَّآ إِنَّا نُبَشِّرُكَ بِغُلَٰمٍ ٱسۡمُهُۥ يَحۡيَىٰ لَمۡ نَجۡعَل لَّهُۥ مِن قَبۡلُ سَمِيّٗا

(Aka ce): Ya Zakariyya, lalle Muna yi maka albishir da samun xa, sunansa Yahya, ba Mu kuwa sanya wa wani sunan ba gabaninsa



Surah: Suratu Maryam

Ayah : 12

يَٰيَحۡيَىٰ خُذِ ٱلۡكِتَٰبَ بِقُوَّةٖۖ وَءَاتَيۡنَٰهُ ٱلۡحُكۡمَ صَبِيّٗا

(Allah ya ce): “Ya Yahaya, ka riqi littafin (Attaura) da qarfi”; Muka kuma ba shi annabci tun yana qarami



Surah: Suratu Maryam

Ayah : 13

وَحَنَانٗا مِّن لَّدُنَّا وَزَكَوٰةٗۖ وَكَانَ تَقِيّٗا

Kuma (Muka hore masa) tausayi daga gare Mu da tsarkin (zuciya), ya kuma kasance mai kiyaye dokokin Allah ne



Surah: Suratu Maryam

Ayah : 14

وَبَرَّۢا بِوَٰلِدَيۡهِ وَلَمۡ يَكُن جَبَّارًا عَصِيّٗا

Kuma mai biyayya ga mahaifansa, bai kuma zamanto mai taurin kai mai sava wa (umarnin Allah) ba



Surah: Suratu Maryam

Ayah : 15

وَسَلَٰمٌ عَلَيۡهِ يَوۡمَ وُلِدَ وَيَوۡمَ يَمُوتُ وَيَوۡمَ يُبۡعَثُ حَيّٗا

Kuma aminci ya tabbata a gare shi ranar da aka haife shi da kuma ranar da zai mutu da kuma ranar da za a tashe shi rayayye



Surah: Suratul Anbiya

Ayah : 89

وَزَكَرِيَّآ إِذۡ نَادَىٰ رَبَّهُۥ رَبِّ لَا تَذَرۡنِي فَرۡدٗا وَأَنتَ خَيۡرُ ٱلۡوَٰرِثِينَ

(Ka tuna) kuma Zakariya’u lokacin da ya roqi Ubangijinsa (cewa): “Ya Ubangijina, kada Ka bar ni ni kaxai (ba magaji), Kai ne kuwa Fiyayyen magada.”



Surah: Suratul Anbiya

Ayah : 90

فَٱسۡتَجَبۡنَا لَهُۥ وَوَهَبۡنَا لَهُۥ يَحۡيَىٰ وَأَصۡلَحۡنَا لَهُۥ زَوۡجَهُۥٓۚ إِنَّهُمۡ كَانُواْ يُسَٰرِعُونَ فِي ٱلۡخَيۡرَٰتِ وَيَدۡعُونَنَا رَغَبٗا وَرَهَبٗاۖ وَكَانُواْ لَنَا خَٰشِعِينَ

Sai Muka amsa masa Muka ba shi Yahya, Muka kuma gyara masa (mahaifar) matarsa. Lallai su sun kasance suna gaggawa wajen yin alherai, suna kuma roqon Mu suna masu kwaxayin (rahamarmu) masu kuma tsoron (azabarmu), sun kuma zamanto masu qasqantar da kai gare Mu