Surah: Suratul Ma’ida

Ayah : 115

قَالَ ٱللَّهُ إِنِّي مُنَزِّلُهَا عَلَيۡكُمۡۖ فَمَن يَكۡفُرۡ بَعۡدُ مِنكُمۡ فَإِنِّيٓ أُعَذِّبُهُۥ عَذَابٗا لَّآ أُعَذِّبُهُۥٓ أَحَدٗا مِّنَ ٱلۡعَٰلَمِينَ

Allah Ya ce: “Lalle Ni Mai saukar muku da shi (kavakin) ne; amma duk wanda ya kafirta daga baya cikinku, to lalle Ni zan yi masa wata irin azaba wadda ba zan tava azabtar da wani daga cikin halittu irinta ba.”



Surah: Suratul Ma’ida

Ayah : 116

وَإِذۡ قَالَ ٱللَّهُ يَٰعِيسَى ٱبۡنَ مَرۡيَمَ ءَأَنتَ قُلۡتَ لِلنَّاسِ ٱتَّخِذُونِي وَأُمِّيَ إِلَٰهَيۡنِ مِن دُونِ ٱللَّهِۖ قَالَ سُبۡحَٰنَكَ مَا يَكُونُ لِيٓ أَنۡ أَقُولَ مَا لَيۡسَ لِي بِحَقٍّۚ إِن كُنتُ قُلۡتُهُۥ فَقَدۡ عَلِمۡتَهُۥۚ تَعۡلَمُ مَا فِي نَفۡسِي وَلَآ أَعۡلَمُ مَا فِي نَفۡسِكَۚ إِنَّكَ أَنتَ عَلَّـٰمُ ٱلۡغُيُوبِ

Kuma (ka tuna) lokacin da Allah zai ce: “Ya kai Isa xan Maryamu, shin kai ne ka ce da mutane: ‘Ku riqe ni, ni da mahaifiyata a matsayin alloli biyu ban da Allah?’” Sai ya ce: “Tsarki ya tabbata gare Ka, bai dace ba a gare ni in faxi wani abu wanda ba ni da haqqin (faxar sa). Idan har na faxe shi, to haqiqa Ka riga Ka sani, Ka san abin da yake cikin raina, amma ni ban san abin da yake ranka ba. Lalle Kai ne Masanin abubuwan da suke voye



Surah: Suratul Ma’ida

Ayah : 117

مَا قُلۡتُ لَهُمۡ إِلَّا مَآ أَمَرۡتَنِي بِهِۦٓ أَنِ ٱعۡبُدُواْ ٱللَّهَ رَبِّي وَرَبَّكُمۡۚ وَكُنتُ عَلَيۡهِمۡ شَهِيدٗا مَّا دُمۡتُ فِيهِمۡۖ فَلَمَّا تَوَفَّيۡتَنِي كُنتَ أَنتَ ٱلرَّقِيبَ عَلَيۡهِمۡۚ وَأَنتَ عَلَىٰ كُلِّ شَيۡءٖ شَهِيدٌ

“Ban faxa musu komai ba sai abin da Ka umarce ni da shi, cewa: ‘Ku bauta wa Allah Ubangijina, kuma Ubangijinku.’ Kuma na kasance mai sa ido a kansu lokacin da nake cikinsu. Amma yayin da Ka karvi rayuwata, Ka zama Kai ne Mai kula da su. Kuma lalle Kai Mai kula ne a kan komai



Surah: Suratul Ma’ida

Ayah : 118

إِن تُعَذِّبۡهُمۡ فَإِنَّهُمۡ عِبَادُكَۖ وَإِن تَغۡفِرۡ لَهُمۡ فَإِنَّكَ أَنتَ ٱلۡعَزِيزُ ٱلۡحَكِيمُ

“Idan har Ka azabtar da su, haqiqa su bayinka ne; idan kuwa Ka yafe musu, to lalle Kai Mabuwayi ne, Mai hikima.”



Surah: Suratu Maryam

Ayah : 19

قَالَ إِنَّمَآ أَنَا۠ رَسُولُ رَبِّكِ لِأَهَبَ لَكِ غُلَٰمٗا زَكِيّٗا

Ya ce: “Ni manzo ne kawai na Ubangijinki na zo don in yi miki baiwar xa tsarkakakke.”



Surah: Suratu Maryam

Ayah : 20

قَالَتۡ أَنَّىٰ يَكُونُ لِي غُلَٰمٞ وَلَمۡ يَمۡسَسۡنِي بَشَرٞ وَلَمۡ أَكُ بَغِيّٗا

Ta ce: “Ta qaqa zan samu xa, alhalin kuwa wani namiji bai tava shafa ta ba, kuma ni ban zamanto mazinaciya ba?”



Surah: Suratu Maryam

Ayah : 21

قَالَ كَذَٰلِكِ قَالَ رَبُّكِ هُوَ عَلَيَّ هَيِّنٞۖ وَلِنَجۡعَلَهُۥٓ ءَايَةٗ لِّلنَّاسِ وَرَحۡمَةٗ مِّنَّاۚ وَكَانَ أَمۡرٗا مَّقۡضِيّٗا

(Mala’ika) ya ce: “Kamar haka ne Ubangijinki Ya faxa (cewa): “Shi (wannan) mai sauqi ne a wurina, kuma don Mu mayar da shi aya ga mutane da kuma rahama daga gare Mu, kuma (yin haka) ya zamanto al’amari ne tabbatacce (rubuce a Lauhul-Mahafuzu).”



Surah: Suratu Maryam

Ayah : 22

۞فَحَمَلَتۡهُ فَٱنتَبَذَتۡ بِهِۦ مَكَانٗا قَصِيّٗا

Sai ta xauki cikinsa sannan ta (tafi) da shi wani wuri mai nisa



Surah: Suratu Maryam

Ayah : 23

فَأَجَآءَهَا ٱلۡمَخَاضُ إِلَىٰ جِذۡعِ ٱلنَّخۡلَةِ قَالَتۡ يَٰلَيۡتَنِي مِتُّ قَبۡلَ هَٰذَا وَكُنتُ نَسۡيٗا مَّنسِيّٗا

Sai ciwon naquda ya tilasta mata zuwa ga kututturen dabino, ta ce: “Ina ma na mutu tun kafin wannan (abu ya faru), na kuma kasance yasasshiya, mantacciya!”



Surah: Suratu Maryam

Ayah : 24

فَنَادَىٰهَا مِن تَحۡتِهَآ أَلَّا تَحۡزَنِي قَدۡ جَعَلَ رَبُّكِ تَحۡتَكِ سَرِيّٗا

Sai ya kira ta daga qarqashinta[1] cewa: “Kada ki yi baqin ciki, haqiqa Ubangijinki Ya sanya qorama a qarqashinki


1- Watau Annabi Isa ().


Surah: Suratu Maryam

Ayah : 25

وَهُزِّيٓ إِلَيۡكِ بِجِذۡعِ ٱلنَّخۡلَةِ تُسَٰقِطۡ عَلَيۡكِ رُطَبٗا جَنِيّٗا

“Ki kuma girgiza kututturen dabinon nan zai zubo miki da lubiyar dabino nunanniya



Surah: Suratu Maryam

Ayah : 26

فَكُلِي وَٱشۡرَبِي وَقَرِّي عَيۡنٗاۖ فَإِمَّا تَرَيِنَّ مِنَ ٱلۡبَشَرِ أَحَدٗا فَقُولِيٓ إِنِّي نَذَرۡتُ لِلرَّحۡمَٰنِ صَوۡمٗا فَلَنۡ أُكَلِّمَ ٱلۡيَوۡمَ إِنسِيّٗا

“Don haka ki ci, ki sha, kuma ki kwantar da hankalinki; kuma duk mutumin da kika gani (ya yi magana da ke), sai ki yi nuni da cewa: “Na xauki alqawari ga Allah na kame bakina, ba zan yi magana da wani mutum ba yau.”



Surah: Suratu Maryam

Ayah : 27

فَأَتَتۡ بِهِۦ قَوۡمَهَا تَحۡمِلُهُۥۖ قَالُواْ يَٰمَرۡيَمُ لَقَدۡ جِئۡتِ شَيۡـٔٗا فَرِيّٗا

Sai ta zo wa mutanenta da shi tana xauke da shi; suka ce: “Ya Maryamu, haqiqa kin zo da babban abu!



Surah: Suratu Maryam

Ayah : 28

يَـٰٓأُخۡتَ هَٰرُونَ مَا كَانَ أَبُوكِ ٱمۡرَأَ سَوۡءٖ وَمَا كَانَتۡ أُمُّكِ بَغِيّٗا

“Ya ke ‘yar’uwar Haruna[1], mahaifinki bai kasance lalataccen mutum ba, mahaifiyarki ma ba mazinaciya ba.”


1- Wani mutum ne mai ibada da kamun kai, ana ce masa Haruna. Wasu malaman sun ce xan’uwanta ne.


Surah: Suratu Maryam

Ayah : 29

فَأَشَارَتۡ إِلَيۡهِۖ قَالُواْ كَيۡفَ نُكَلِّمُ مَن كَانَ فِي ٱلۡمَهۡدِ صَبِيّٗا

Sai ta nuna shi; (sai) suka ce: “Ta qaqa za mu yi magana da wanda yake xan jariri cikin shimfixar jego?”



Surah: Suratu Maryam

Ayah : 30

قَالَ إِنِّي عَبۡدُ ٱللَّهِ ءَاتَىٰنِيَ ٱلۡكِتَٰبَ وَجَعَلَنِي نَبِيّٗا

(Isa) ya ce (da su): “Lalle ni bawan Allah ne, Ya ba ni littafi Ya kuma sanya ni Annabi



Surah: Suratu Maryam

Ayah : 31

وَجَعَلَنِي مُبَارَكًا أَيۡنَ مَا كُنتُ وَأَوۡصَٰنِي بِٱلصَّلَوٰةِ وَٱلزَّكَوٰةِ مَا دُمۡتُ حَيّٗا

“Ya kuma sanya ni mai albarka a duk inda nake, kuma Ya umarce ni da yin salla da kuma ba da zakka matuqar ina raye



Surah: Suratu Maryam

Ayah : 32

وَبَرَّۢا بِوَٰلِدَتِي وَلَمۡ يَجۡعَلۡنِي جَبَّارٗا شَقِيّٗا

“Kuma mai biyayya ga mahaifiyata, bai kuma sanya ni mai girman kai mai savo ba



Surah: Suratu Maryam

Ayah : 33

وَٱلسَّلَٰمُ عَلَيَّ يَوۡمَ وُلِدتُّ وَيَوۡمَ أَمُوتُ وَيَوۡمَ أُبۡعَثُ حَيّٗا

“Amincin (Allah) kuma ya tabbata a gare ni ranar da aka haife ni da ranar da zan mutu da kuma ranar da za a tashe ni rayayye.”



Surah: Suratu Maryam

Ayah : 34

ذَٰلِكَ عِيسَى ٱبۡنُ مَرۡيَمَۖ قَوۡلَ ٱلۡحَقِّ ٱلَّذِي فِيهِ يَمۡتَرُونَ

Wannan shi ne Isa xan Maryamu. Zance na gaskiya wanda a kansa ne suke ta shakka suna jayayya (da junansu)



Surah: Suratu Maryam

Ayah : 35

مَا كَانَ لِلَّهِ أَن يَتَّخِذَ مِن وَلَدٖۖ سُبۡحَٰنَهُۥٓۚ إِذَا قَضَىٰٓ أَمۡرٗا فَإِنَّمَا يَقُولُ لَهُۥ كُن فَيَكُونُ

Ba zai yiwu a ce Allah yana da xa ba; tsarki ya tabbata a gare Shi. Idan Ya nufi zartar da wani lamari sai kawai Ya ce masa: “Kasance”, sai ko ya kasance



Surah: Suratu Maryam

Ayah : 36

وَإِنَّ ٱللَّهَ رَبِّي وَرَبُّكُمۡ فَٱعۡبُدُوهُۚ هَٰذَا صِرَٰطٞ مُّسۡتَقِيمٞ

“Lalle kuma Allah shi ne Ubangijina kuma Ubangijinku, sai ku bauta masa. Wannan ita ce hanya madaidaiciya.”



Surah: Suratu Maryam

Ayah : 37

فَٱخۡتَلَفَ ٱلۡأَحۡزَابُ مِنۢ بَيۡنِهِمۡۖ فَوَيۡلٞ لِّلَّذِينَ كَفَرُواْ مِن مَّشۡهَدِ يَوۡمٍ عَظِيمٍ

Sai qungiyoyin suka sassava a tsakaninsu; to bone ya tabbata ga waxanda suka kafirta daga halartar rana mai girma (ita ce alqiyama)



Surah: Suratul Mu’uminun

Ayah : 50

وَجَعَلۡنَا ٱبۡنَ مَرۡيَمَ وَأُمَّهُۥٓ ءَايَةٗ وَءَاوَيۡنَٰهُمَآ إِلَىٰ رَبۡوَةٖ ذَاتِ قَرَارٖ وَمَعِينٖ

Muka kuma sanya Xan Maryamu da mahaifiyarsa (don su zama) aya, Muka kuma zaunar da su a wata jigawa ta hutawa da kuma ruwa mai gudana



Surah: Suratuz Zukhruf 

Ayah : 57

۞وَلَمَّا ضُرِبَ ٱبۡنُ مَرۡيَمَ مَثَلًا إِذَا قَوۡمُكَ مِنۡهُ يَصِدُّونَ

Lokacin da kuwa aka buga misali da (Isa) xan Maryamu, sai ga mutanenka suna ta annashawa game da shi[1]


1- Watau lokacin da Abdullahi xan Az-Ziba’ara ya ji faxar Allah cewa, waxanda aka bautawa ba Allah ba za su shiga wuta tare da masu bautarsu, sai ya ce, to idan haka ne Annabi Isa ma zai shiga wuta, wannan magana tasa ta faranta wa mushirikai rai sosai.


Surah: Suratuz Zukhruf 

Ayah : 58

وَقَالُوٓاْ ءَأَٰلِهَتُنَا خَيۡرٌ أَمۡ هُوَۚ مَا ضَرَبُوهُ لَكَ إِلَّا جَدَلَۢاۚ بَلۡ هُمۡ قَوۡمٌ خَصِمُونَ

Suka kuma ce: “Yanzu ababen bautar mu ne suka fi ko kuwa shi (Isa)?” Ba su buga maka misali da shi ba sai don son jayayya. Ba shakka su dai mutane ne masu tsananin jayayya



Surah: Suratuz Zukhruf 

Ayah : 59

إِنۡ هُوَ إِلَّا عَبۡدٌ أَنۡعَمۡنَا عَلَيۡهِ وَجَعَلۡنَٰهُ مَثَلٗا لِّبَنِيٓ إِسۡرَـٰٓءِيلَ

Shi (Isa) ba wani ba ne face bawa ne da Muka yi masa ni’ima, Muka kuma sanya shi abin buga misali ga Bani-Isra’ila



Surah: Suratuz Zukhruf 

Ayah : 60

وَلَوۡ نَشَآءُ لَجَعَلۡنَا مِنكُم مَّلَـٰٓئِكَةٗ فِي ٱلۡأَرۡضِ يَخۡلُفُونَ

Da kuma za Mu ga dama tabbas da Mun sanya mala’iku ne za su maye gurbinku a bayan qasa



Surah: Suratuz Zukhruf 

Ayah : 61

وَإِنَّهُۥ لَعِلۡمٞ لِّلسَّاعَةِ فَلَا تَمۡتَرُنَّ بِهَا وَٱتَّبِعُونِۚ هَٰذَا صِرَٰطٞ مُّسۡتَقِيمٞ

Lalle kuma shi (Isa) alama ce ta zuwan alqiyama[1], kada ku yi shakka game da ita, kuma ku bi Ni. Wannan ita ce hanya madaidaiciya


1- Watau lokacin da zai sauko daga sama ta biyu a qarshen zamani, kamar yadda tarin hadisan Annabi () suka tabbatar.


Surah: Suratuz Zukhruf 

Ayah : 62

وَلَا يَصُدَّنَّكُمُ ٱلشَّيۡطَٰنُۖ إِنَّهُۥ لَكُمۡ عَدُوّٞ مُّبِينٞ

Kada kuma Shaixan ya kange ku; lalle shi maqiyi ne mai bayyana (qiyyaya) a gare ku