Surah: Suratud Dukhan

Ayah : 28

كَذَٰلِكَۖ وَأَوۡرَثۡنَٰهَا قَوۡمًا ءَاخَرِينَ

Kamar haka ne; sai Muka kuma gadar da su ga wasu mutane daban (su ne Banu Isra’ila)



Surah: Suratud Dukhan

Ayah : 29

فَمَا بَكَتۡ عَلَيۡهِمُ ٱلسَّمَآءُ وَٱلۡأَرۡضُ وَمَا كَانُواْ مُنظَرِينَ

Sannan (halittun) sama da na qasa ba su yi alhininsu ba, ba su kuma kasance ababen saurara wa ba



Surah: Suratud Dukhan

Ayah : 30

وَلَقَدۡ نَجَّيۡنَا بَنِيٓ إِسۡرَـٰٓءِيلَ مِنَ ٱلۡعَذَابِ ٱلۡمُهِينِ

Haqiqa kuma Mun tserar da Banu Isra’ila daga azabar wulaqanci



Surah: Suratud Dukhan

Ayah : 31

مِن فِرۡعَوۡنَۚ إِنَّهُۥ كَانَ عَالِيٗا مِّنَ ٱلۡمُسۡرِفِينَ

Daga Fir’auna. Lalle shi ya kasance mai girman kai daga mavarnata



Surah: Suratud Dukhan

Ayah : 32

وَلَقَدِ ٱخۡتَرۡنَٰهُمۡ عَلَىٰ عِلۡمٍ عَلَى ٱلۡعَٰلَمِينَ

Kuma haqiqa Mun fifita su (Banu Isra’ila) bisa saninmu a kan (sauran) talikai



Surah: Suratud Dukhan

Ayah : 33

وَءَاتَيۡنَٰهُم مِّنَ ٱلۡأٓيَٰتِ مَا فِيهِ بَلَـٰٓؤٞاْ مُّبِينٌ

Muka kuma ba su wasu ayoyinmu waxanda a cikinsa akwai jarrabawa mabayyaniya



Surah: Suratul Jasiya

Ayah : 16

وَلَقَدۡ ءَاتَيۡنَا بَنِيٓ إِسۡرَـٰٓءِيلَ ٱلۡكِتَٰبَ وَٱلۡحُكۡمَ وَٱلنُّبُوَّةَ وَرَزَقۡنَٰهُم مِّنَ ٱلطَّيِّبَٰتِ وَفَضَّلۡنَٰهُمۡ عَلَى ٱلۡعَٰلَمِينَ

Haqiqa kuma Mun bai wa Banu Isra’ila littafin (Attaura) da hukunci da annabta. Muka kuma arzuta su da tsarkakan (abubuwa), kuma Muka fifita su a kan talikai



Surah: Suratul Jasiya

Ayah : 17

وَءَاتَيۡنَٰهُم بَيِّنَٰتٖ مِّنَ ٱلۡأَمۡرِۖ فَمَا ٱخۡتَلَفُوٓاْ إِلَّا مِنۢ بَعۡدِ مَا جَآءَهُمُ ٱلۡعِلۡمُ بَغۡيَۢا بَيۡنَهُمۡۚ إِنَّ رَبَّكَ يَقۡضِي بَيۡنَهُمۡ يَوۡمَ ٱلۡقِيَٰمَةِ فِيمَا كَانُواْ فِيهِ يَخۡتَلِفُونَ

Muka kuma kawo musu (hujjoji) mabayyana na addini; to ba su sassava ba, sai bayan da ilimi ya zo musu don hassada a tsakaninsu. Lalle Ubangijinka zai yi hukunci a tsakaninsu a ranar alqiyama game da abin da suka kasance suna yin savani cikinsa



Surah: Suratul Ahqaf 

Ayah : 10

قُلۡ أَرَءَيۡتُمۡ إِن كَانَ مِنۡ عِندِ ٱللَّهِ وَكَفَرۡتُم بِهِۦ وَشَهِدَ شَاهِدٞ مِّنۢ بَنِيٓ إِسۡرَـٰٓءِيلَ عَلَىٰ مِثۡلِهِۦ فَـَٔامَنَ وَٱسۡتَكۡبَرۡتُمۡۚ إِنَّ ٱللَّهَ لَا يَهۡدِي ٱلۡقَوۡمَ ٱلظَّـٰلِمِينَ

Ka ce: “Ku ba ni labari, idan (Alqur’ani) ya kasance daga wurin Allah yake, kuka kuma kafirce masa, kuma wani mai shaida daga Banu Isra’ila ya ba da shaida a kan irinsa[1], sai ya yi imani (da shi) ku kuma kuka yi girman kai; to lalle Allah ba Ya shiryar da mutane azzalumai.”


1- Watau ya shaida da ingancinsa, duba da abin da ya zo na bayaninsa a cikin littafin Attaura.


Surah: Suratus Saff 

Ayah : 5

وَإِذۡ قَالَ مُوسَىٰ لِقَوۡمِهِۦ يَٰقَوۡمِ لِمَ تُؤۡذُونَنِي وَقَد تَّعۡلَمُونَ أَنِّي رَسُولُ ٱللَّهِ إِلَيۡكُمۡۖ فَلَمَّا زَاغُوٓاْ أَزَاغَ ٱللَّهُ قُلُوبَهُمۡۚ وَٱللَّهُ لَا يَهۡدِي ٱلۡقَوۡمَ ٱلۡفَٰسِقِينَ

Kuma (ka tuna) lokacin da Musa ya ce da mutanensa: “Ya ku mutanena, don me kuke cuta ta, alhali kuma kun san cewa lalle ni Manzon Allah ne zuwa gare ku?” To lokacin da suka kauce sai Allah ya kautar da zukatansu. Allah kuma ba ya shiryar da mutane fasiqai



Surah: Suratus Saff 

Ayah : 6

وَإِذۡ قَالَ عِيسَى ٱبۡنُ مَرۡيَمَ يَٰبَنِيٓ إِسۡرَـٰٓءِيلَ إِنِّي رَسُولُ ٱللَّهِ إِلَيۡكُم مُّصَدِّقٗا لِّمَا بَيۡنَ يَدَيَّ مِنَ ٱلتَّوۡرَىٰةِ وَمُبَشِّرَۢا بِرَسُولٖ يَأۡتِي مِنۢ بَعۡدِي ٱسۡمُهُۥٓ أَحۡمَدُۖ فَلَمَّا جَآءَهُم بِٱلۡبَيِّنَٰتِ قَالُواْ هَٰذَا سِحۡرٞ مُّبِينٞ

Kuma (ka tuna) lokacin da Isa xan Maryamu ya ce: “Ya ku ‘ya’yan Isra’ila, lalle ni Manzon Allah ne zuwa gare ku, mai gaskata abin da yake gabanina na Attaura, kuma mai albishir da wani manzo da zai zo bayana, sunansa Ahmadu[1].” To lokacin da ya zo musu da (ayoyi) bayyanannu sai suka ce: “Wannan sihiri ne mabayyani.”


1- Ahmad, xaya ne daga cikin sunayen Annabi Muhammad ().