Surah: Suratul An’am

Ayah : 84

وَوَهَبۡنَا لَهُۥٓ إِسۡحَٰقَ وَيَعۡقُوبَۚ كُلًّا هَدَيۡنَاۚ وَنُوحًا هَدَيۡنَا مِن قَبۡلُۖ وَمِن ذُرِّيَّتِهِۦ دَاوُۥدَ وَسُلَيۡمَٰنَ وَأَيُّوبَ وَيُوسُفَ وَمُوسَىٰ وَهَٰرُونَۚ وَكَذَٰلِكَ نَجۡزِي ٱلۡمُحۡسِنِينَ

Kuma Muka ba shi Ishaqa da Ya’aqubu. Kowanne daga cikinsu Mun shiryar da shi, kuma Mun shiryar da Nuhu tun gabaninsu. Kuma daga cikin zurriyarsa akwai Dawudu da Sulaimanu da Ayyuba da Yusufu da Musa da Haruna. Kuma kamar haka ne Muke saka wa masu kyautata (ayyukansu)



Surah: Suratu Hud

Ayah : 71

وَٱمۡرَأَتُهُۥ قَآئِمَةٞ فَضَحِكَتۡ فَبَشَّرۡنَٰهَا بِإِسۡحَٰقَ وَمِن وَرَآءِ إِسۡحَٰقَ يَعۡقُوبَ

Matarsa kuwa tana tsaye sai ta yi dariya, sai Muka yi mata albishir da Is’haqa, bayan kuma Is’haqa (sai) Yakubu



Surah: Suratu Ibrahim

Ayah : 39

ٱلۡحَمۡدُ لِلَّهِ ٱلَّذِي وَهَبَ لِي عَلَى ٱلۡكِبَرِ إِسۡمَٰعِيلَ وَإِسۡحَٰقَۚ إِنَّ رَبِّي لَسَمِيعُ ٱلدُّعَآءِ

“Dukkan yabo ya tabbata ga Allah wanda Ya ba ni Isma’ila da Is’haqa a cikin halin tsufa. Lalle Ubangijina tabbas Mai jin roqo ne



Surah: Suratu Maryam

Ayah : 49

فَلَمَّا ٱعۡتَزَلَهُمۡ وَمَا يَعۡبُدُونَ مِن دُونِ ٱللَّهِ وَهَبۡنَا لَهُۥٓ إِسۡحَٰقَ وَيَعۡقُوبَۖ وَكُلّٗا جَعَلۡنَا نَبِيّٗا

To lokacin da ya qaurace musu tare da abin da suke bauta wa wanda ba Allah ba, sai Muka yi masa baiwa da Is’haqa da Ya’aqubu; kowannensu kuma Muka ba shi annabta



Surah: Suratul Anbiya

Ayah : 72

وَوَهَبۡنَا لَهُۥٓ إِسۡحَٰقَ وَيَعۡقُوبَ نَافِلَةٗۖ وَكُلّٗا جَعَلۡنَا صَٰلِحِينَ

Muka kuma ba shi Is’haqa da kuma Ya’aqubu qari (wato jika). Dukkanninsu kuma Mun sanya su salihai



Surah: Suratus Saffat

Ayah : 112

وَبَشَّرۡنَٰهُ بِإِسۡحَٰقَ نَبِيّٗا مِّنَ ٱلصَّـٰلِحِينَ

Muka kuma yi masa albishir da Is’haqa a matsayin Annabi daga salihai



Surah: Suratus Saffat

Ayah : 113

وَبَٰرَكۡنَا عَلَيۡهِ وَعَلَىٰٓ إِسۡحَٰقَۚ وَمِن ذُرِّيَّتِهِمَا مُحۡسِنٞ وَظَالِمٞ لِّنَفۡسِهِۦ مُبِينٞ

Muka kuma yi masa albarka, da kuma Is’haqa. Daga zuriyarsu kuma akwai mai kyautatawa akwai kuma mai zaluntar kansa a fili (wato kafiri)



Surah: Suratu Sad

Ayah : 45

وَٱذۡكُرۡ عِبَٰدَنَآ إِبۡرَٰهِيمَ وَإِسۡحَٰقَ وَيَعۡقُوبَ أُوْلِي ٱلۡأَيۡدِي وَٱلۡأَبۡصَٰرِ

Ka kuma tuna bayinmu Ibrahimu da Is’haqa da Yaqubu ma’abota qarfi da basira