Surah: Suratul Baqara

Ayah : 39

وَٱلَّذِينَ كَفَرُواْ وَكَذَّبُواْ بِـَٔايَٰتِنَآ أُوْلَـٰٓئِكَ أَصۡحَٰبُ ٱلنَّارِۖ هُمۡ فِيهَا خَٰلِدُونَ

Kuma waxanda suka kafirta suka kuma qaryata ayoyinmu, waxannan su ne ‘yan wuta, su masu dawwama ne a cikinta



Surah: Suratul Baqara

Ayah : 86

أُوْلَـٰٓئِكَ ٱلَّذِينَ ٱشۡتَرَوُاْ ٱلۡحَيَوٰةَ ٱلدُّنۡيَا بِٱلۡأٓخِرَةِۖ فَلَا يُخَفَّفُ عَنۡهُمُ ٱلۡعَذَابُ وَلَا هُمۡ يُنصَرُونَ

Waxannan su ne waxanda suka musanya rayuwar duniya da ta lahira, kuma ba za a sassauta musu azaba ba, kuma ba za a taimaka musu ba



Surah: Suratul Baqara

Ayah : 161

إِنَّ ٱلَّذِينَ كَفَرُواْ وَمَاتُواْ وَهُمۡ كُفَّارٌ أُوْلَـٰٓئِكَ عَلَيۡهِمۡ لَعۡنَةُ ٱللَّهِ وَٱلۡمَلَـٰٓئِكَةِ وَٱلنَّاسِ أَجۡمَعِينَ

Lalle waxanda suka kafirta kuma suka mutu suna kafirai, to waxannan la’anar Allah ta tabbata a kansu da ta mala’iku da mutane gaba xaya



Surah: Suratul Baqara

Ayah : 162

خَٰلِدِينَ فِيهَا لَا يُخَفَّفُ عَنۡهُمُ ٱلۡعَذَابُ وَلَا هُمۡ يُنظَرُونَ

Suna masu dawwama a cikinta, ba za a sassauta masu azaba ba kuma ba za a saurara musu ba



Surah: Suratun Nisa’i

Ayah : 10

إِنَّ ٱلَّذِينَ يَأۡكُلُونَ أَمۡوَٰلَ ٱلۡيَتَٰمَىٰ ظُلۡمًا إِنَّمَا يَأۡكُلُونَ فِي بُطُونِهِمۡ نَارٗاۖ وَسَيَصۡلَوۡنَ سَعِيرٗا

Lalle waxanda suke cin dukiyar marayu bisa zalunci, wuta ce kawai suke ci a cikkunansu; kuma da sannu za su shiga wuta mai tsananin quna



Surah: Suratun Nisa’i

Ayah : 93

وَمَن يَقۡتُلۡ مُؤۡمِنٗا مُّتَعَمِّدٗا فَجَزَآؤُهُۥ جَهَنَّمُ خَٰلِدٗا فِيهَا وَغَضِبَ ٱللَّهُ عَلَيۡهِ وَلَعَنَهُۥ وَأَعَدَّ لَهُۥ عَذَابًا عَظِيمٗا

Duk kuwa wanda ya kashe mumini da gangan, to sakamakonsa wutar Jahannama ce, yana mai dawwama a cikinta, kuma Allah Ya yi fushi da shi, kuma Ya la’ance shi, kuma Ya yi masa tanadin azaba mai girma



Surah: Suratun Nisa’i

Ayah : 140

وَقَدۡ نَزَّلَ عَلَيۡكُمۡ فِي ٱلۡكِتَٰبِ أَنۡ إِذَا سَمِعۡتُمۡ ءَايَٰتِ ٱللَّهِ يُكۡفَرُ بِهَا وَيُسۡتَهۡزَأُ بِهَا فَلَا تَقۡعُدُواْ مَعَهُمۡ حَتَّىٰ يَخُوضُواْ فِي حَدِيثٍ غَيۡرِهِۦٓ إِنَّكُمۡ إِذٗا مِّثۡلُهُمۡۗ إِنَّ ٱللَّهَ جَامِعُ ٱلۡمُنَٰفِقِينَ وَٱلۡكَٰفِرِينَ فِي جَهَنَّمَ جَمِيعًا

Kuma haqiqa Ya saukar muku a cikin littafi[1] cewa, idan kuka ji ayoyin Allah ana kafirce musu, ana izgili da su, to kar ku zauna tare da su har sai sun shiga cikin wani zancen daban ba wannan ba. Lalle in har kuka zauna tare da su, to kun zama kamarsu. Lalle Allah Mai tattara munafuqai ne da kafirai cikin wutar Jahannama gaba xaya


1- Watau a cikin Alqur’ani a Suratul An’am, aya ta 68 inda Allah ya haramta wa muminai zama a inda ake yi wa shari’ar Allah izgili da rashin kunya.


Surah: Suratun Nisa’i

Ayah : 145

إِنَّ ٱلۡمُنَٰفِقِينَ فِي ٱلدَّرۡكِ ٱلۡأَسۡفَلِ مِنَ ٱلنَّارِ وَلَن تَجِدَ لَهُمۡ نَصِيرًا

Lalle munafuqai suna cikin matakin qarshe na can qarqashin wuta, kuma ba za ka tava sama musu wani mataimaki ba



Surah: Suratul Ma’ida

Ayah : 10

وَٱلَّذِينَ كَفَرُواْ وَكَذَّبُواْ بِـَٔايَٰتِنَآ أُوْلَـٰٓئِكَ أَصۡحَٰبُ ٱلۡجَحِيمِ

Kuma waxanda suka kafirta, suka kuma qaryata ayoyinmu, waxannan su ne ‘yan wuta



Surah: Suratul Ma’ida

Ayah : 72

لَقَدۡ كَفَرَ ٱلَّذِينَ قَالُوٓاْ إِنَّ ٱللَّهَ هُوَ ٱلۡمَسِيحُ ٱبۡنُ مَرۡيَمَۖ وَقَالَ ٱلۡمَسِيحُ يَٰبَنِيٓ إِسۡرَـٰٓءِيلَ ٱعۡبُدُواْ ٱللَّهَ رَبِّي وَرَبَّكُمۡۖ إِنَّهُۥ مَن يُشۡرِكۡ بِٱللَّهِ فَقَدۡ حَرَّمَ ٱللَّهُ عَلَيۡهِ ٱلۡجَنَّةَ وَمَأۡوَىٰهُ ٱلنَّارُۖ وَمَا لِلظَّـٰلِمِينَ مِنۡ أَنصَارٖ

Lalle haqiqa waxanda suka ce: “Lalle Allah Shi ne Almasihu xan Maryamu” sun kafirta. Shi kuwa Almasihu cewa ya yi: “Ya ku Bani-Isra’ila, ku bauta wa Allah Ubangijina kuma Ubangijinku. Lalle yadda al’amarin yake, duk wanda ya yi shirka da Allah, to haqiqa Allah Ya haramta masa shiga Aljanna, kuma makomarsa ita ce wuta, kuma azzalumai ba su da wasu mataimaka.”



Surah: Suratul A’araf

Ayah : 18

قَالَ ٱخۡرُجۡ مِنۡهَا مَذۡءُومٗا مَّدۡحُورٗاۖ لَّمَن تَبِعَكَ مِنۡهُمۡ لَأَمۡلَأَنَّ جَهَنَّمَ مِنكُمۡ أَجۡمَعِينَ

Ya ce: “Ka fita daga cikinta kana abin aibatawa, korarre (daga rahama); Na rantse duk wanda ya bi ka daga cikinsu, lalle zan cika Jahannama da ku gaba xaya.”



Surah: Suratul A’araf

Ayah : 36

وَٱلَّذِينَ كَذَّبُواْ بِـَٔايَٰتِنَا وَٱسۡتَكۡبَرُواْ عَنۡهَآ أُوْلَـٰٓئِكَ أَصۡحَٰبُ ٱلنَّارِۖ هُمۡ فِيهَا خَٰلِدُونَ

Waxanda kuwa suka qaryata ayoyinmu, kuma suka yi girman kai gare su, waxannan su ne ma’abota wuta; suna masu dawwama a cikinta



Surah: Suratul A’araf

Ayah : 38

قَالَ ٱدۡخُلُواْ فِيٓ أُمَمٖ قَدۡ خَلَتۡ مِن قَبۡلِكُم مِّنَ ٱلۡجِنِّ وَٱلۡإِنسِ فِي ٱلنَّارِۖ كُلَّمَا دَخَلَتۡ أُمَّةٞ لَّعَنَتۡ أُخۡتَهَاۖ حَتَّىٰٓ إِذَا ٱدَّارَكُواْ فِيهَا جَمِيعٗا قَالَتۡ أُخۡرَىٰهُمۡ لِأُولَىٰهُمۡ رَبَّنَا هَـٰٓؤُلَآءِ أَضَلُّونَا فَـَٔاتِهِمۡ عَذَابٗا ضِعۡفٗا مِّنَ ٱلنَّارِۖ قَالَ لِكُلّٖ ضِعۡفٞ وَلَٰكِن لَّا تَعۡلَمُونَ

Sai Ya ce: “Ku shiga cikin jerin al’ummomin da suka shuxe kafinku na aljannu da mutane a cikin wuta.” Ko da yaushe wata al’umma ta shiga (wutar) sai ta la’anci ‘yar’uwarta; har sai lokacin da suka haxu a cikinta gaba xaya, sai na qarshensu su ce wa na farkonsu: “Ya Ubangijinmu, waxannan ne suka vatar da mu, don haka Ka ninka musu azabar wuta.” Sai Ya ce: “Kowanne yana da ninki, sai dai ku ba ku sani ba ne.”



Surah: Suratul A’araf

Ayah : 39

وَقَالَتۡ أُولَىٰهُمۡ لِأُخۡرَىٰهُمۡ فَمَا كَانَ لَكُمۡ عَلَيۡنَا مِن فَضۡلٖ فَذُوقُواْ ٱلۡعَذَابَ بِمَا كُنتُمۡ تَكۡسِبُونَ

Sai kuma na farkonsu su ce wa na qarshensu: “Ai ba ku da wani fifiko a kanmu; to ku xanxani azaba saboda abin da kuka kasance kuna aikatawa.”



Surah: Suratut Tauba

Ayah : 63

أَلَمۡ يَعۡلَمُوٓاْ أَنَّهُۥ مَن يُحَادِدِ ٱللَّهَ وَرَسُولَهُۥ فَأَنَّ لَهُۥ نَارَ جَهَنَّمَ خَٰلِدٗا فِيهَاۚ ذَٰلِكَ ٱلۡخِزۡيُ ٱلۡعَظِيمُ

Yanzu ba su sani ba cewa, wanda yake jayayya da Allah da Manzonsa, to lalle yana da wutar Jahannama da zai dawwama a cikinta? Wannan kuwa kunyata ce mai girma



Surah: Suratut Tauba

Ayah : 68

وَعَدَ ٱللَّهُ ٱلۡمُنَٰفِقِينَ وَٱلۡمُنَٰفِقَٰتِ وَٱلۡكُفَّارَ نَارَ جَهَنَّمَ خَٰلِدِينَ فِيهَاۚ هِيَ حَسۡبُهُمۡۚ وَلَعَنَهُمُ ٱللَّهُۖ وَلَهُمۡ عَذَابٞ مُّقِيمٞ

Allah kuwa Ya yi wa munafukai maza da mata da kuma kafirai alqawarin wutar Jahannama wadda za su dawwama a cikinta. Ita ta ishe su. Allah kuma Ya tsine musu, suna kuma da azaba mai xorewa



Surah: Suratu Hud

Ayah : 119

إِلَّا مَن رَّحِمَ رَبُّكَۚ وَلِذَٰلِكَ خَلَقَهُمۡۗ وَتَمَّتۡ كَلِمَةُ رَبِّكَ لَأَمۡلَأَنَّ جَهَنَّمَ مِنَ ٱلۡجِنَّةِ وَٱلنَّاسِ أَجۡمَعِينَ

Sai wanda Ubangijinka Ya yi wa rahama. A kan haka kuwa Ya halicce su; kuma Kalmar Ubangijinka ta tabbata (cewa): Lalle zan cika Jahannama da aljannu da mutane baki xaya



Surah: Suratul Isra’i

Ayah : 18

مَّن كَانَ يُرِيدُ ٱلۡعَاجِلَةَ عَجَّلۡنَا لَهُۥ فِيهَا مَا نَشَآءُ لِمَن نُّرِيدُ ثُمَّ جَعَلۡنَا لَهُۥ جَهَنَّمَ يَصۡلَىٰهَا مَذۡمُومٗا مَّدۡحُورٗا

Wanda ya kasance yana nufin duniya ne (kawai) to za Mu gaggauto masa a cikinta abin da Muka ga dama ga wanda Muka yi nufi; sannan Mu sanya masa Jahannama, ya shige ta (a lahira) yana abin zargi, korarre (daga rahamar Allah)



Surah: Suratu Maryam

Ayah : 72

ثُمَّ نُنَجِّي ٱلَّذِينَ ٱتَّقَواْ وَّنَذَرُ ٱلظَّـٰلِمِينَ فِيهَا جِثِيّٗا

Sannan kuma za Mu tserar da waxanda suka kiyaye dokokin Allah Mu kuma bar kafirai a duddurqushe cikinta



Surah: Suratu Xa Ha

Ayah : 74

إِنَّهُۥ مَن يَأۡتِ رَبَّهُۥ مُجۡرِمٗا فَإِنَّ لَهُۥ جَهَنَّمَ لَا يَمُوتُ فِيهَا وَلَا يَحۡيَىٰ

Lalle duk wanda ya zo wa Ubangijinsa yana mai babban laifi[1] to lalle yana da (sakamakon) Jahannama, ba zai mutu a cikinta ba, ba kuma zai rayu ba (rayuwa mai daxi)


1- Watau kafirce wa Allah da haxa wani da shi a wajen bauta.


Surah: Suratul Anbiya

Ayah : 29

۞وَمَن يَقُلۡ مِنۡهُمۡ إِنِّيٓ إِلَٰهٞ مِّن دُونِهِۦ فَذَٰلِكَ نَجۡزِيهِ جَهَنَّمَۚ كَذَٰلِكَ نَجۡزِي ٱلظَّـٰلِمِينَ

Daga cikinsu kuwa duk wanda ya ce: “Ni abin bauta ne ba shi (Allah) ba,” to wannan za Mu saka masa da (wutar) Jahannama. Kamar haka kuwa Muke saka wa azzalumai



Surah: Suratul Anbiya

Ayah : 98

إِنَّكُمۡ وَمَا تَعۡبُدُونَ مِن دُونِ ٱللَّهِ حَصَبُ جَهَنَّمَ أَنتُمۡ لَهَا وَٰرِدُونَ

(Sai a ce da su): “Lallai ku da abin da kuke bauta wa ba Allah ba, (duka) makamashin Jahannama ne, kuma ku masu shigar ta ne.”



Surah: Suratul Anbiya

Ayah : 99

لَوۡ كَانَ هَـٰٓؤُلَآءِ ءَالِهَةٗ مَّا وَرَدُوهَاۖ وَكُلّٞ فِيهَا خَٰلِدُونَ

Da waxancan (gumakan) sun kasance alloli (na gaske) da ba su shiga cikinta ba, dukkaninsu kuwa madawwama ne a cikinta



Surah: Suratul Hajji

Ayah : 51

وَٱلَّذِينَ سَعَوۡاْ فِيٓ ءَايَٰتِنَا مُعَٰجِزِينَ أُوْلَـٰٓئِكَ أَصۡحَٰبُ ٱلۡجَحِيمِ

Waxanda kuwa suka yi iya qoqarinsu game da vata ayoyinmu suna ganin za su gagare Mu, to waxannan su ne ma’abota (wutar) Jahima



Surah: Suratus Shu’ara

Ayah : 94

فَكُبۡكِبُواْ فِيهَا هُمۡ وَٱلۡغَاوُۥنَ

Sai aka kikkifa su cikinta (wutar) su da vatattu



Surah: Suratus Shu’ara

Ayah : 95

وَجُنُودُ إِبۡلِيسَ أَجۡمَعُونَ

Da kuma rundunar Iblis gaba xaya



Surah: Suratul Ahzab

Ayah : 64

إِنَّ ٱللَّهَ لَعَنَ ٱلۡكَٰفِرِينَ وَأَعَدَّ لَهُمۡ سَعِيرًا

Lalle Allah Ya la’anci kafirai Ya kuma tanadar musu da (wutar) Sa’ira



Surah: Suratul Ahzab

Ayah : 65

خَٰلِدِينَ فِيهَآ أَبَدٗاۖ لَّا يَجِدُونَ وَلِيّٗا وَلَا نَصِيرٗا

Masu dawwama ne a cikinta har abada; ba kuma za su sami wani majivinci ko mataimaki ba



Surah: Suratu Sad

Ayah : 55

هَٰذَاۚ وَإِنَّ لِلطَّـٰغِينَ لَشَرَّ مَـَٔابٖ

Wannan (shi ne sakamakon masu taqawa). Kuma lalle masu xagawa tabbas suna da mummunar makoma



Surah: Suratu Sad

Ayah : 56

جَهَنَّمَ يَصۡلَوۡنَهَا فَبِئۡسَ ٱلۡمِهَادُ

(Wato) Jahannama wadda za su shige ta, to wannan shimfixar zama ta munana