Surah: Suratul Ma’ida

Ayah : 27

۞وَٱتۡلُ عَلَيۡهِمۡ نَبَأَ ٱبۡنَيۡ ءَادَمَ بِٱلۡحَقِّ إِذۡ قَرَّبَا قُرۡبَانٗا فَتُقُبِّلَ مِنۡ أَحَدِهِمَا وَلَمۡ يُتَقَبَّلۡ مِنَ ٱلۡأٓخَرِ قَالَ لَأَقۡتُلَنَّكَۖ قَالَ إِنَّمَا يَتَقَبَّلُ ٱللَّهُ مِنَ ٱلۡمُتَّقِينَ

Kuma ka karanta musu labarin gaskiya na ‘ya’yan Adamu su biyu, yayin da suka gabatar da wani abin neman lada, sai aka karvi na xaya daga cikinsu, xayan kuma ba a karvi nasa ba, sai ya ce: “Wallahi, sai na kashe ka!” Sai ya ce: “Allah Yana karvar aiki ne kawai daga masu taqawa



Surah: Suratul Ma’ida

Ayah : 28

لَئِنۢ بَسَطتَ إِلَيَّ يَدَكَ لِتَقۡتُلَنِي مَآ أَنَا۠ بِبَاسِطٖ يَدِيَ إِلَيۡكَ لِأَقۡتُلَكَۖ إِنِّيٓ أَخَافُ ٱللَّهَ رَبَّ ٱلۡعَٰلَمِينَ

“Wallahi, idan har ka miqa hannunka gare ni domin ka kashe ni, ni kam ba zan miqa hannuna gare ka don in kashe ka ba; lalle ni ina jin tsoron Allah Ubangijin talikai



Surah: Suratul Ma’ida

Ayah : 29

إِنِّيٓ أُرِيدُ أَن تَبُوٓأَ بِإِثۡمِي وَإِثۡمِكَ فَتَكُونَ مِنۡ أَصۡحَٰبِ ٱلنَّارِۚ وَذَٰلِكَ جَزَـٰٓؤُاْ ٱلظَّـٰلِمِينَ

“Lalle ni ina son ka xauki zunubina da zunubinka, sai ka kasance daga cikin ‘yan wuta. Kuma wannan shi ne sakamakon azzalumai.”



Surah: Suratul Ma’ida

Ayah : 30

فَطَوَّعَتۡ لَهُۥ نَفۡسُهُۥ قَتۡلَ أَخِيهِ فَقَتَلَهُۥ فَأَصۡبَحَ مِنَ ٱلۡخَٰسِرِينَ

Sai zuciyarsa ta qawata masa ya kashe xan’uwansa, sai ya kashe shi, sai ya zama cikin hasararru[1]


1- Wannan shi ne xan’adam na farko da ya fara kisan kai a duniya, don haka yana da kamasho a cikin kowane jini da za a zubar har zuwa tashin alqiyam..


Surah: Suratul Ma’ida

Ayah : 31

فَبَعَثَ ٱللَّهُ غُرَابٗا يَبۡحَثُ فِي ٱلۡأَرۡضِ لِيُرِيَهُۥ كَيۡفَ يُوَٰرِي سَوۡءَةَ أَخِيهِۚ قَالَ يَٰوَيۡلَتَىٰٓ أَعَجَزۡتُ أَنۡ أَكُونَ مِثۡلَ هَٰذَا ٱلۡغُرَابِ فَأُوَٰرِيَ سَوۡءَةَ أَخِيۖ فَأَصۡبَحَ مِنَ ٱلنَّـٰدِمِينَ

Sai Allah Ya aiko da wani hankaka ya riqa tona qasa don ya nuna masa yadda zai binne gawar xan’uwansa. Sai ya ce: “Kaicona! Yanzu na kasa zama kamar wannan hankakan, in je in binne gawar xan’uwana?” Sai ya wayi gari cikin masu nadama