Surah: Suratu Ali-Imran

Ayah : 3

نَزَّلَ عَلَيۡكَ ٱلۡكِتَٰبَ بِٱلۡحَقِّ مُصَدِّقٗا لِّمَا بَيۡنَ يَدَيۡهِ وَأَنزَلَ ٱلتَّوۡرَىٰةَ وَٱلۡإِنجِيلَ

Ya saukar maka da Littafi da gaskiya, yana mai gaskata abin da ya gabace shi, kuma Ya saukar da Attaura da Linjila



Surah: Suratu Ali-Imran

Ayah : 4

مِن قَبۡلُ هُدٗى لِّلنَّاسِ وَأَنزَلَ ٱلۡفُرۡقَانَۗ إِنَّ ٱلَّذِينَ كَفَرُواْ بِـَٔايَٰتِ ٱللَّهِ لَهُمۡ عَذَابٞ شَدِيدٞۗ وَٱللَّهُ عَزِيزٞ ذُو ٱنتِقَامٍ

Tun kafin (Alqur’ani), (don su zama) shiriya ga mutane, kuma Ya saukar da mai rarrabewa (tsakanin qarya da gaskiya). Lalle waxanda suka kafirce wa ayoyin Allah, suna da azaba mai tsanani, kuma Allah Mabuwayi ne, Ma’abocin xaukar fansa



Surah: Suratu Ali-Imran

Ayah : 48

وَيُعَلِّمُهُ ٱلۡكِتَٰبَ وَٱلۡحِكۡمَةَ وَٱلتَّوۡرَىٰةَ وَٱلۡإِنجِيلَ

“Kuma zai sanar da shi rubutu da hikima da Attaura da Linjila



Surah: Suratu Ali-Imran

Ayah : 65

يَـٰٓأَهۡلَ ٱلۡكِتَٰبِ لِمَ تُحَآجُّونَ فِيٓ إِبۡرَٰهِيمَ وَمَآ أُنزِلَتِ ٱلتَّوۡرَىٰةُ وَٱلۡإِنجِيلُ إِلَّا مِنۢ بَعۡدِهِۦٓۚ أَفَلَا تَعۡقِلُونَ

Ya ku Ma’abota Littafi, don me kuke yin jayayya game da Ibrahimu, alhalin ba a saukar da Attaura da Linjila ba sai bayan shuxewarsa? Yanzu ba za ku hankalta ba?



Surah: Suratul Ma’ida

Ayah : 47

وَلۡيَحۡكُمۡ أَهۡلُ ٱلۡإِنجِيلِ بِمَآ أَنزَلَ ٱللَّهُ فِيهِۚ وَمَن لَّمۡ يَحۡكُم بِمَآ أَنزَلَ ٱللَّهُ فَأُوْلَـٰٓئِكَ هُمُ ٱلۡفَٰسِقُونَ

Lalle kuma ma’abota Linjila su yi hukunci da abin da Allah Ya saukar a cikinsa. Duk wanda bai yi hukunci da abin da Allah Ya saukar ba kuwa, to waxannan su ne fasiqai



Surah: Suratul Ma’ida

Ayah : 66

وَلَوۡ أَنَّهُمۡ أَقَامُواْ ٱلتَّوۡرَىٰةَ وَٱلۡإِنجِيلَ وَمَآ أُنزِلَ إِلَيۡهِم مِّن رَّبِّهِمۡ لَأَكَلُواْ مِن فَوۡقِهِمۡ وَمِن تَحۡتِ أَرۡجُلِهِمۚ مِّنۡهُمۡ أُمَّةٞ مُّقۡتَصِدَةٞۖ وَكَثِيرٞ مِّنۡهُمۡ سَآءَ مَا يَعۡمَلُونَ

Kuma da a ce sun tsaya a kan aiki da Attaura da Linjila da kuma abin da aka saukar musu daga Ubangijinsu, lalle da sun ci daga samansu da kuma qarqashin qafafunsu. Daga cikinsu akwai wata al’umma madaidaiciya, (amma) kuma mafi yawa daga cikinsu, irin abin da suke aikatawa ya munana (matuqa)



Surah: Suratul Ma’ida

Ayah : 68

قُلۡ يَـٰٓأَهۡلَ ٱلۡكِتَٰبِ لَسۡتُمۡ عَلَىٰ شَيۡءٍ حَتَّىٰ تُقِيمُواْ ٱلتَّوۡرَىٰةَ وَٱلۡإِنجِيلَ وَمَآ أُنزِلَ إِلَيۡكُم مِّن رَّبِّكُمۡۗ وَلَيَزِيدَنَّ كَثِيرٗا مِّنۡهُم مَّآ أُنزِلَ إِلَيۡكَ مِن رَّبِّكَ طُغۡيَٰنٗا وَكُفۡرٗاۖ فَلَا تَأۡسَ عَلَى ٱلۡقَوۡمِ ٱلۡكَٰفِرِينَ

Ka ce: “Ya ku Ma’abota Littafi, ba kwa kan wani abu (na addinin gaskiya), har sai kun tsaya a kan yin aiki da Attaura da Linjila da kuma abin da aka saukar muku daga wajen Ubangijinku.” Kuma abin da ake saukar maka daga Ubangijinka tabbas yana qara wa yawancinsu shisshigi da kafirci. Don haka kada ka yi baqin ciki dangane da (abin da yake samun) mutane kafirai



Surah: Suratul Ma’ida

Ayah : 110

إِذۡ قَالَ ٱللَّهُ يَٰعِيسَى ٱبۡنَ مَرۡيَمَ ٱذۡكُرۡ نِعۡمَتِي عَلَيۡكَ وَعَلَىٰ وَٰلِدَتِكَ إِذۡ أَيَّدتُّكَ بِرُوحِ ٱلۡقُدُسِ تُكَلِّمُ ٱلنَّاسَ فِي ٱلۡمَهۡدِ وَكَهۡلٗاۖ وَإِذۡ عَلَّمۡتُكَ ٱلۡكِتَٰبَ وَٱلۡحِكۡمَةَ وَٱلتَّوۡرَىٰةَ وَٱلۡإِنجِيلَۖ وَإِذۡ تَخۡلُقُ مِنَ ٱلطِّينِ كَهَيۡـَٔةِ ٱلطَّيۡرِ بِإِذۡنِي فَتَنفُخُ فِيهَا فَتَكُونُ طَيۡرَۢا بِإِذۡنِيۖ وَتُبۡرِئُ ٱلۡأَكۡمَهَ وَٱلۡأَبۡرَصَ بِإِذۡنِيۖ وَإِذۡ تُخۡرِجُ ٱلۡمَوۡتَىٰ بِإِذۡنِيۖ وَإِذۡ كَفَفۡتُ بَنِيٓ إِسۡرَـٰٓءِيلَ عَنكَ إِذۡ جِئۡتَهُم بِٱلۡبَيِّنَٰتِ فَقَالَ ٱلَّذِينَ كَفَرُواْ مِنۡهُمۡ إِنۡ هَٰذَآ إِلَّا سِحۡرٞ مُّبِينٞ

(Ka tuna) lokacin da Allah zai ce: “Ya kai Isa xan Maryamu, ka tuna ni’imata da Na yi maka kai da mahaifiyarka, yayin da Na qarfafe ka da Ruhi mai tsarki, kana yi wa mutane magana lokacin kana cikin zanin goyo, da kuma lokacin da kake dattijo, kuma ka tuna lokacin da Na koyar da kai rubutu da hikima da Attaura da Linjila. Kuma ka tuna lokacin da kake qirqirar (wani abu) kamar tsuntsu da tavo da izinina, sai ka yi busa a cikinsa, sai ya zamo tsuntsu da izinina; kuma kake warkar da wanda aka haifa da makanta da mai albaras da izinina; kuma ka tuna lokacin da kake fito da matattu (daga cikin qaburburansu) da izinina; kuma ka tuna lokacin da Na kare ka (daga cutar) Bani Isra’ila yayin da ka zo musu da hujjoji bayyanannu, sai waxanda suka kafirta daga cikinsu suka ce: “Ai wannan ba komai ba ne face sihiri mabayyani.”



Surah: Suratul A’araf

Ayah : 157

ٱلَّذِينَ يَتَّبِعُونَ ٱلرَّسُولَ ٱلنَّبِيَّ ٱلۡأُمِّيَّ ٱلَّذِي يَجِدُونَهُۥ مَكۡتُوبًا عِندَهُمۡ فِي ٱلتَّوۡرَىٰةِ وَٱلۡإِنجِيلِ يَأۡمُرُهُم بِٱلۡمَعۡرُوفِ وَيَنۡهَىٰهُمۡ عَنِ ٱلۡمُنكَرِ وَيُحِلُّ لَهُمُ ٱلطَّيِّبَٰتِ وَيُحَرِّمُ عَلَيۡهِمُ ٱلۡخَبَـٰٓئِثَ وَيَضَعُ عَنۡهُمۡ إِصۡرَهُمۡ وَٱلۡأَغۡلَٰلَ ٱلَّتِي كَانَتۡ عَلَيۡهِمۡۚ فَٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ بِهِۦ وَعَزَّرُوهُ وَنَصَرُوهُ وَٱتَّبَعُواْ ٱلنُّورَ ٱلَّذِيٓ أُنزِلَ مَعَهُۥٓ أُوْلَـٰٓئِكَ هُمُ ٱلۡمُفۡلِحُونَ

“(Su ne) waxanda suke bin Manzo Annabi Ummiyyi, wanda suke samun sa a rubuce a wurinsu a cikin Attaura da Linjila, yana umartar su da kyakkyawan abu, kuma yana hana su mummuna, kuma yana halatta musu daxaxan abubuwa, yana kuma haramta musu qazantattu, kuma yana sauke musu nauyaye-nauyayensu da ququmce-ququmcen da suka kasance a kansu[1]. Don haka waxanda suka yi imani da shi, kuma suka qarfafe shi, suka kuma taimake shi, suka bi hasken da aka saukar tare da shi, waxannan su ne masu rabauta.”


1- Nauyaye-nauyayensu su ne abubuwa masu wuya da aka wajabta musu aiki da su a littafin Attaura. Ququmce-ququmcensu kuwa su ne abubuwan da aka tsananta musu haramcinsu masu kama da ququmi.


Surah: Suratut Tauba

Ayah : 111

۞إِنَّ ٱللَّهَ ٱشۡتَرَىٰ مِنَ ٱلۡمُؤۡمِنِينَ أَنفُسَهُمۡ وَأَمۡوَٰلَهُم بِأَنَّ لَهُمُ ٱلۡجَنَّةَۚ يُقَٰتِلُونَ فِي سَبِيلِ ٱللَّهِ فَيَقۡتُلُونَ وَيُقۡتَلُونَۖ وَعۡدًا عَلَيۡهِ حَقّٗا فِي ٱلتَّوۡرَىٰةِ وَٱلۡإِنجِيلِ وَٱلۡقُرۡءَانِۚ وَمَنۡ أَوۡفَىٰ بِعَهۡدِهِۦ مِنَ ٱللَّهِۚ فَٱسۡتَبۡشِرُواْ بِبَيۡعِكُمُ ٱلَّذِي بَايَعۡتُم بِهِۦۚ وَذَٰلِكَ هُوَ ٱلۡفَوۡزُ ٱلۡعَظِيمُ

Lalle Allah Ya sayi rayuka da dukiyoyin muminai daga wurinsu cewa suna da Aljanna: Za su yi yaqi saboda Allah, sai su kashe su ma kuma a kashe su. Alqawari ne na gaskiya da Ya xaukar wa kansa a cikin Attaura da Linjila da Alqur’ani. Wane ne ya fi Allah cika alqawarinsa? Saboda haka sai ku yi farin ciki da cinikin nan naku da kuka yi da Shi. Wannan kuwa shi ne rabo mai girma



Surah: Suratul Fat’h

Ayah : 29

مُّحَمَّدٞ رَّسُولُ ٱللَّهِۚ وَٱلَّذِينَ مَعَهُۥٓ أَشِدَّآءُ عَلَى ٱلۡكُفَّارِ رُحَمَآءُ بَيۡنَهُمۡۖ تَرَىٰهُمۡ رُكَّعٗا سُجَّدٗا يَبۡتَغُونَ فَضۡلٗا مِّنَ ٱللَّهِ وَرِضۡوَٰنٗاۖ سِيمَاهُمۡ فِي وُجُوهِهِم مِّنۡ أَثَرِ ٱلسُّجُودِۚ ذَٰلِكَ مَثَلُهُمۡ فِي ٱلتَّوۡرَىٰةِۚ وَمَثَلُهُمۡ فِي ٱلۡإِنجِيلِ كَزَرۡعٍ أَخۡرَجَ شَطۡـَٔهُۥ فَـَٔازَرَهُۥ فَٱسۡتَغۡلَظَ فَٱسۡتَوَىٰ عَلَىٰ سُوقِهِۦ يُعۡجِبُ ٱلزُّرَّاعَ لِيَغِيظَ بِهِمُ ٱلۡكُفَّارَۗ وَعَدَ ٱللَّهُ ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ وَعَمِلُواْ ٱلصَّـٰلِحَٰتِ مِنۡهُم مَّغۡفِرَةٗ وَأَجۡرًا عَظِيمَۢا

Muhammadu Manzon Allah ne. Waxanda kuma suke tare da shi masu tsanani ne a kan kafirai, kuma masu tausayin junansu ne; za ka gan su suna ruku’i suna sujjada suna neman falala daga Allah da yardarsa; alamominsu na gurbin sujjada suna bayyana a fuskokinsu. Wannan shi ne misalinsu a cikin Attaura. Misalinsu kuwa a cikin Linjila kamar shuka ce da ta fitar da reshenta sai ya qarfafe ta, sannan ta yi kauri sai ta daidaita a kan tushiyarta ta riqa qayatar da manoma, don Ya cusa wa kafirai haushi. Allah Ya yi wa waxanda suka yi imani suka kuma yi ayyuka nagari daga cikinsu alqawarin gafara da lada mai girma



Surah: Suratul Hadid

Ayah : 27

ثُمَّ قَفَّيۡنَا عَلَىٰٓ ءَاثَٰرِهِم بِرُسُلِنَا وَقَفَّيۡنَا بِعِيسَى ٱبۡنِ مَرۡيَمَ وَءَاتَيۡنَٰهُ ٱلۡإِنجِيلَۖ وَجَعَلۡنَا فِي قُلُوبِ ٱلَّذِينَ ٱتَّبَعُوهُ رَأۡفَةٗ وَرَحۡمَةٗۚ وَرَهۡبَانِيَّةً ٱبۡتَدَعُوهَا مَا كَتَبۡنَٰهَا عَلَيۡهِمۡ إِلَّا ٱبۡتِغَآءَ رِضۡوَٰنِ ٱللَّهِ فَمَا رَعَوۡهَا حَقَّ رِعَايَتِهَاۖ فَـَٔاتَيۡنَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ مِنۡهُمۡ أَجۡرَهُمۡۖ وَكَثِيرٞ مِّنۡهُمۡ فَٰسِقُونَ

Sannan a bayansu Muka biyar da manzanninmu, Muka kuma biyar da Isa xan Maryamu Muka kuma ba shi Linjila, kuma Muka sanya jin qai da rahama a cikin zukatan waxanda suka bi shi. Rahbaniyanci[1] kuma su ne suka qago shi, ba Mu wajabta musu shi ba, sai dai (Mun wajabta musu) neman yardar Allah, amma ba su kiyaye shi ba kamar yadda ya kamata; sai Muka bai wa waxanda suka yi imani daga cikinsu ladansu; da yawa kuwa fasiqai ne


1- Bidi’ar Rahbaniyanci ita ce, qaurace wa aure da barin cin daxaxan abubuwa na halal da haramta wa kai wasu abubuwa da Allah ya halatta.