Surah: Suratul A’araf

Ayah : 65

۞وَإِلَىٰ عَادٍ أَخَاهُمۡ هُودٗاۚ قَالَ يَٰقَوۡمِ ٱعۡبُدُواْ ٱللَّهَ مَا لَكُم مِّنۡ إِلَٰهٍ غَيۡرُهُۥٓۚ أَفَلَا تَتَّقُونَ

Kuma Mun aika wa Adawa xan’uwansu Hudu. Ya ce: “Ya ku mutanena, ku bautata wa Allah, ba ku da wani abin bauta wa da gaskiya sai Shi. Shin ba za ku kiyaye dokokin Allah ba?”



Surah: Suratul A’araf

Ayah : 66

قَالَ ٱلۡمَلَأُ ٱلَّذِينَ كَفَرُواْ مِن قَوۡمِهِۦٓ إِنَّا لَنَرَىٰكَ فِي سَفَاهَةٖ وَإِنَّا لَنَظُنُّكَ مِنَ ٱلۡكَٰذِبِينَ

Sai manyan gari waxanda suka kafirce cikin mutanensa suka ce: “Lalle mu tabbas muna ganin ka kana cikin wauta, kuma lalle mu tabbas muna zaton kai kana cikin maqaryata



Surah: Suratul A’araf

Ayah : 67

قَالَ يَٰقَوۡمِ لَيۡسَ بِي سَفَاهَةٞ وَلَٰكِنِّي رَسُولٞ مِّن رَّبِّ ٱلۡعَٰلَمِينَ

Sai ya ce: “Ya ku mutanena, babu wata wauta a tare da ni, sai dai ni kawai Manzo ne daga Ubangijin talikai



Surah: Suratul A’araf

Ayah : 68

أُبَلِّغُكُمۡ رِسَٰلَٰتِ رَبِّي وَأَنَا۠ لَكُمۡ نَاصِحٌ أَمِينٌ

“Ina isar muku da saqonnin Ubangijina, kuma ni mai nasiha ne a gare ku, amintacce



Surah: Suratul A’araf

Ayah : 69

أَوَعَجِبۡتُمۡ أَن جَآءَكُمۡ ذِكۡرٞ مِّن رَّبِّكُمۡ عَلَىٰ رَجُلٖ مِّنكُمۡ لِيُنذِرَكُمۡۚ وَٱذۡكُرُوٓاْ إِذۡ جَعَلَكُمۡ خُلَفَآءَ مِنۢ بَعۡدِ قَوۡمِ نُوحٖ وَزَادَكُمۡ فِي ٱلۡخَلۡقِ بَصۜۡطَةٗۖ فَٱذۡكُرُوٓاْ ءَالَآءَ ٱللَّهِ لَعَلَّكُمۡ تُفۡلِحُونَ

“Shin mamaki kuke yi wa’azi ya zo muku daga Ubangijinku a kan (harshen) wani mutum daga cikinku don ya gargaxe ku? Kuma ku tuna yayin da Ya sa kuka zama masu maye gurbi bayan wucewar mutanen Nuhu, kuma Ya qara muku girman halitta; don haka ku tuna ni’imomin Allah, don ku rabauta.”



Surah: Suratul A’araf

Ayah : 70

قَالُوٓاْ أَجِئۡتَنَا لِنَعۡبُدَ ٱللَّهَ وَحۡدَهُۥ وَنَذَرَ مَا كَانَ يَعۡبُدُ ءَابَآؤُنَا فَأۡتِنَا بِمَا تَعِدُنَآ إِن كُنتَ مِنَ ٱلصَّـٰدِقِينَ

Sai suka ce: “Yanzu ka zo mana ne don mu bauta wa Allah Shi kaxai, kuma mu qyale abin da iyayenmu suka kasance suna bautata wa? To ka kawo mana abin da kake yi mana alqawarinsa[1] idan ka kasance cikin masu gaskiya.”


1- Watau azabar Allah ().


Surah: Suratul A’araf

Ayah : 71

قَالَ قَدۡ وَقَعَ عَلَيۡكُم مِّن رَّبِّكُمۡ رِجۡسٞ وَغَضَبٌۖ أَتُجَٰدِلُونَنِي فِيٓ أَسۡمَآءٖ سَمَّيۡتُمُوهَآ أَنتُمۡ وَءَابَآؤُكُم مَّا نَزَّلَ ٱللَّهُ بِهَا مِن سُلۡطَٰنٖۚ فَٱنتَظِرُوٓاْ إِنِّي مَعَكُم مِّنَ ٱلۡمُنتَظِرِينَ

Sai ya ce: “Haqiqa azaba da fushi daga Ubangijinku sun faxa a kanku. Yanzu kwa riqa jayayya da ni a kan waxansu sunaye da ku ne kuka qago su da iyayenku[1], alhalin Allah bai saukar da wata hujja a kansu ba? To ku jira (ku gani), lalle ni ma ina nan cikin masu jira tare da ku.”


1- Watau gumakan da suke bauta wa ba Allah ba.


Surah: Suratul A’araf

Ayah : 72

فَأَنجَيۡنَٰهُ وَٱلَّذِينَ مَعَهُۥ بِرَحۡمَةٖ مِّنَّا وَقَطَعۡنَا دَابِرَ ٱلَّذِينَ كَذَّبُواْ بِـَٔايَٰتِنَاۖ وَمَا كَانُواْ مُؤۡمِنِينَ

Sai Muka tserar da shi, da waxanda suke tare da shi da rahamarmu, Muka kuma tumvuke tushen waxanda suka qaryata ayoyinmu; kuma ba su kasance muminai ba



Surah: Suratu Hud

Ayah : 50

وَإِلَىٰ عَادٍ أَخَاهُمۡ هُودٗاۚ قَالَ يَٰقَوۡمِ ٱعۡبُدُواْ ٱللَّهَ مَا لَكُم مِّنۡ إِلَٰهٍ غَيۡرُهُۥٓۖ إِنۡ أَنتُمۡ إِلَّا مُفۡتَرُونَ

Kuma (Mun aiko wa) Adawa xan’uwansu Hudu, ya ce: “Ya ku mutanena, ku bauta wa Allah, ba ku da wani abin bauta da gaskiya sai shi; ku ba wasu ne ba face masu qaga wa (Allah) qarya



Surah: Suratu Hud

Ayah : 51

يَٰقَوۡمِ لَآ أَسۡـَٔلُكُمۡ عَلَيۡهِ أَجۡرًاۖ إِنۡ أَجۡرِيَ إِلَّا عَلَى ٱلَّذِي فَطَرَنِيٓۚ أَفَلَا تَعۡقِلُونَ

“Ya ku mutanena, ba na tambayar ku wani lada game da shi (wannan saqo); ladana dai yana ga wanda ya qagi halittata. Yanzu ba za ku hankalta ba?



Surah: Suratu Hud

Ayah : 52

وَيَٰقَوۡمِ ٱسۡتَغۡفِرُواْ رَبَّكُمۡ ثُمَّ تُوبُوٓاْ إِلَيۡهِ يُرۡسِلِ ٱلسَّمَآءَ عَلَيۡكُم مِّدۡرَارٗا وَيَزِدۡكُمۡ قُوَّةً إِلَىٰ قُوَّتِكُمۡ وَلَا تَتَوَلَّوۡاْ مُجۡرِمِينَ

“Kuma ya ku mutanena, ku nemi gafarar Ubangijinku sannan ku tuba gare Shi, zai sauko muku da mamakon ruwan sama, zai kuma qara muku qarfi a kan qarfinku, kada kuma ku ba da baya kuna masu aikata laifi.”



Surah: Suratu Hud

Ayah : 53

قَالُواْ يَٰهُودُ مَا جِئۡتَنَا بِبَيِّنَةٖ وَمَا نَحۡنُ بِتَارِكِيٓ ءَالِهَتِنَا عَن قَوۡلِكَ وَمَا نَحۡنُ لَكَ بِمُؤۡمِنِينَ

Suka ce: “Ya kai Hudu ba ka zo mana da wata hujja ba, kuma ba za mu bar abubuwan da muke bauta ba saboda maganarka, ba kuma za mu yi imani da kai ba



Surah: Suratu Hud

Ayah : 54

إِن نَّقُولُ إِلَّا ٱعۡتَرَىٰكَ بَعۡضُ ءَالِهَتِنَا بِسُوٓءٖۗ قَالَ إِنِّيٓ أُشۡهِدُ ٱللَّهَ وَٱشۡهَدُوٓاْ أَنِّي بَرِيٓءٞ مِّمَّا تُشۡرِكُونَ

“Ba abin da za mu faxa sai dai kawai (mu ce) wasu abubuwan bautarmu ne suka sa maka tavuwa.” Ya ce: “Ni lalle ina shaidar da Allah, ku ma kuma ku shaida cewa ni lalle ba ruwana da abin da kuke haxa (Allah) da shi



Surah: Suratu Hud

Ayah : 55

مِن دُونِهِۦۖ فَكِيدُونِي جَمِيعٗا ثُمَّ لَا تُنظِرُونِ

“Wanda ba Shi (Allah) ba; to sai ku shirya min makirci gaba xayanku, kar kuma ku saurara mini



Surah: Suratu Hud

Ayah : 56

إِنِّي تَوَكَّلۡتُ عَلَى ٱللَّهِ رَبِّي وَرَبِّكُمۚ مَّا مِن دَآبَّةٍ إِلَّا هُوَ ءَاخِذُۢ بِنَاصِيَتِهَآۚ إِنَّ رَبِّي عَلَىٰ صِرَٰطٖ مُّسۡتَقِيمٖ

“Lalle ni na dogara ga Allah, Ubangijina kuma Ubangijinku. Babu wata dabba face Shi ne Yake riqe da makwarkwaxarta. Lalle Ubangijina a kan tafarki madaidaici Yake



Surah: Suratu Hud

Ayah : 57

فَإِن تَوَلَّوۡاْ فَقَدۡ أَبۡلَغۡتُكُم مَّآ أُرۡسِلۡتُ بِهِۦٓ إِلَيۡكُمۡۚ وَيَسۡتَخۡلِفُ رَبِّي قَوۡمًا غَيۡرَكُمۡ وَلَا تَضُرُّونَهُۥ شَيۡـًٔاۚ إِنَّ رَبِّي عَلَىٰ كُلِّ شَيۡءٍ حَفِيظٞ

“To idan kuka ba da baya, haqiqa na isar muku abin da aka aiko ni da shi zuwa gare ku. Kuma Ubangijina zai iya musanya wasu mutanen ba ku ba, kuma ba za ku cutar da Shi da komai ba. Lalle Ubangijina Mai kula da komai ne.”



Surah: Suratu Hud

Ayah : 58

وَلَمَّا جَآءَ أَمۡرُنَا نَجَّيۡنَا هُودٗا وَٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ مَعَهُۥ بِرَحۡمَةٖ مِّنَّا وَنَجَّيۡنَٰهُم مِّنۡ عَذَابٍ غَلِيظٖ

Lokacin kuwa da umarninmu ya zo sai Muka tserar da Hudu shi da waxanda suka ba da gaskiya da shi, saboda wata rahama daga gare mu, Muka kuma tserar da su daga azaba mai gwavi



Surah: Suratu Hud

Ayah : 59

وَتِلۡكَ عَادٞۖ جَحَدُواْ بِـَٔايَٰتِ رَبِّهِمۡ وَعَصَوۡاْ رُسُلَهُۥ وَٱتَّبَعُوٓاْ أَمۡرَ كُلِّ جَبَّارٍ عَنِيدٖ

Waxancan kuwa su ne Adawa, da suka musanta ayoyin Ubangijinsu, suka kuma sava wa manzanninsa, kuma suka bi umarnin duk wani mai girman kai taqadari



Surah: Suratu Hud

Ayah : 60

وَأُتۡبِعُواْ فِي هَٰذِهِ ٱلدُّنۡيَا لَعۡنَةٗ وَيَوۡمَ ٱلۡقِيَٰمَةِۗ أَلَآ إِنَّ عَادٗا كَفَرُواْ رَبَّهُمۡۗ أَلَا بُعۡدٗا لِّعَادٖ قَوۡمِ هُودٖ

Aka kuma biyar musu da la’ana a duniya, haka kuma a ranar alqiyama. Ku saurara! Lalle Adawa kam sun kafirce wa Ubangijinsu. Ku saurara! Halaka ta tabbata ga Adawa mutanen Hudu



Surah: Suratus Shu’ara

Ayah : 123

كَذَّبَتۡ عَادٌ ٱلۡمُرۡسَلِينَ

Adawa (ma) sun qaryata manzanni[1]


1- Domin qaryata Annabi Hudu () daidai yake da qaryata duk manzannin Allah, saboda saqo iri xaya suke xauke da shi.


Surah: Suratus Shu’ara

Ayah : 124

إِذۡ قَالَ لَهُمۡ أَخُوهُمۡ هُودٌ أَلَا تَتَّقُونَ

Lokacin da xan’uwansu Hudu ya ce da su: “Yanzu ba kwa riqa kiyaye dokokin (Allah) ba?



Surah: Suratus Shu’ara

Ayah : 125

إِنِّي لَكُمۡ رَسُولٌ أَمِينٞ

“Lalle ni Manzo ne amintacce gare ku



Surah: Suratus Shu’ara

Ayah : 126

فَٱتَّقُواْ ٱللَّهَ وَأَطِيعُونِ

“To ku kiyaye dokokin Allah kuma ku bi ni



Surah: Suratus Shu’ara

Ayah : 127

وَمَآ أَسۡـَٔلُكُمۡ عَلَيۡهِ مِنۡ أَجۡرٍۖ إِنۡ أَجۡرِيَ إِلَّا عَلَىٰ رَبِّ ٱلۡعَٰلَمِينَ

“Kuma ba na tambayar ku wani lada game da shi (isar da manzancin); ladana yana wajen Ubangijin talikai kawai



Surah: Suratus Shu’ara

Ayah : 128

أَتَبۡنُونَ بِكُلِّ رِيعٍ ءَايَةٗ تَعۡبَثُونَ

“Yanzu kwa riqa yin dogayen gine-gine a kan tuddai kuna sharholiya?



Surah: Suratus Shu’ara

Ayah : 129

وَتَتَّخِذُونَ مَصَانِعَ لَعَلَّكُمۡ تَخۡلُدُونَ

“Kuma ku riqa gina ganuwoyi da maka-makan gidaje kamar za ku dawwama?



Surah: Suratus Shu’ara

Ayah : 130

وَإِذَا بَطَشۡتُم بَطَشۡتُمۡ جَبَّارِينَ

“Idan kuma kuka yi damqa sai kukan yi damqa da tsanani



Surah: Suratus Shu’ara

Ayah : 131

فَٱتَّقُواْ ٱللَّهَ وَأَطِيعُونِ

“To ku kiyaye dokokin Allah kuma ku bi ni



Surah: Suratus Shu’ara

Ayah : 132

وَٱتَّقُواْ ٱلَّذِيٓ أَمَدَّكُم بِمَا تَعۡلَمُونَ

“Kuma ku kiyaye dokokin (Allah) wanda Ya ni’imta ku da abin da kuka sani



Surah: Suratus Shu’ara

Ayah : 133

أَمَدَّكُم بِأَنۡعَٰمٖ وَبَنِينَ

“Ya ni’imta ku da dabbobin ni’ima da ‘ya’ya