Surah: Suratus Shu’ara

Ayah : 134

وَجَنَّـٰتٖ وَعُيُونٍ

“Da kuma gonakai da idanuwan ruwa



Surah: Suratus Shu’ara

Ayah : 135

إِنِّيٓ أَخَافُ عَلَيۡكُمۡ عَذَابَ يَوۡمٍ عَظِيمٖ

“Lalle ni ina jiye muku tsoron azabar wani yini mai girma.”



Surah: Suratus Shu’ara

Ayah : 136

قَالُواْ سَوَآءٌ عَلَيۡنَآ أَوَعَظۡتَ أَمۡ لَمۡ تَكُن مِّنَ ٱلۡوَٰعِظِينَ

Suka ce: “Mu duk xaya ne a wajenmu; ko ka yi wa’azi ko kuwa kada ka zamanto daga masu wa’azi



Surah: Suratus Shu’ara

Ayah : 137

إِنۡ هَٰذَآ إِلَّا خُلُقُ ٱلۡأَوَّلِينَ

“Wannan ba wani abu ba ne in ban da halayyar mutanen farko



Surah: Suratus Shu’ara

Ayah : 138

وَمَا نَحۡنُ بِمُعَذَّبِينَ

“Mu kuma ba waxanda za a yi wa azaba ba ne.”



Surah: Suratus Shu’ara

Ayah : 139

فَكَذَّبُوهُ فَأَهۡلَكۡنَٰهُمۡۚ إِنَّ فِي ذَٰلِكَ لَأٓيَةٗۖ وَمَا كَانَ أَكۡثَرُهُم مُّؤۡمِنِينَ

Sai suka qaryata shi, sannan Muka hallaka su. Lalle a game da wannan tabbas akwai aya; kuma yawancinsu ba su zamanto muminai ba



Surah: Suratus Shu’ara

Ayah : 140

وَإِنَّ رَبَّكَ لَهُوَ ٱلۡعَزِيزُ ٱلرَّحِيمُ

Kuma lalle Ubangijinka tabbas Shi ne Mabuwayi, Mai jin qai



Surah: Suratul Ankabut

Ayah : 38

وَعَادٗا وَثَمُودَاْ وَقَد تَّبَيَّنَ لَكُم مِّن مَّسَٰكِنِهِمۡۖ وَزَيَّنَ لَهُمُ ٱلشَّيۡطَٰنُ أَعۡمَٰلَهُمۡ فَصَدَّهُمۡ عَنِ ٱلسَّبِيلِ وَكَانُواْ مُسۡتَبۡصِرِينَ

Kuma (Mun hallaka) Adawa da Samudawa, haqiqa (abin da ya faru a gare su) ya bayyana gare ku a fili a gidajensu; kuma Shaixan ya qawata musu ayyukansu, sai ya kange su daga hanya (madaidaiciya), sun kuma kasance masu gani da basirarsu (amma suka zavi vata)



Surah: Suratu Fussilat

Ayah : 15

فَأَمَّا عَادٞ فَٱسۡتَكۡبَرُواْ فِي ٱلۡأَرۡضِ بِغَيۡرِ ٱلۡحَقِّ وَقَالُواْ مَنۡ أَشَدُّ مِنَّا قُوَّةًۖ أَوَلَمۡ يَرَوۡاْ أَنَّ ٱللَّهَ ٱلَّذِي خَلَقَهُمۡ هُوَ أَشَدُّ مِنۡهُمۡ قُوَّةٗۖ وَكَانُواْ بِـَٔايَٰتِنَا يَجۡحَدُونَ

Amma Adawa sai suka yi girman kai a bayan qasa ba a kan gaskiya ba, suka kuma ce: “Wane ne ya fi mu tsananin qarfi?” Yanzu ba su ga cewa lalle Allah wanda Ya halicce su Ya fi su tsananin qarfi ba? Sun kuma kasance suna musanta ayoyinmu



Surah: Suratu Fussilat

Ayah : 16

فَأَرۡسَلۡنَا عَلَيۡهِمۡ رِيحٗا صَرۡصَرٗا فِيٓ أَيَّامٖ نَّحِسَاتٖ لِّنُذِيقَهُمۡ عَذَابَ ٱلۡخِزۡيِ فِي ٱلۡحَيَوٰةِ ٱلدُّنۡيَاۖ وَلَعَذَابُ ٱلۡأٓخِرَةِ أَخۡزَىٰۖ وَهُمۡ لَا يُنصَرُونَ

Sai Muka aiko musu da wata iska mai qara a wasu kwanaki masu cike da shu’umci don Mu xanxana musu azabar kunyata a rayuwar duniya; azabar lahira kuma ta fi kunyatarwa; alhalin su ba za a taimake su ba



Surah: Suratul Ahqaf 

Ayah : 21

۞وَٱذۡكُرۡ أَخَا عَادٍ إِذۡ أَنذَرَ قَوۡمَهُۥ بِٱلۡأَحۡقَافِ وَقَدۡ خَلَتِ ٱلنُّذُرُ مِنۢ بَيۡنِ يَدَيۡهِ وَمِنۡ خَلۡفِهِۦٓ أَلَّا تَعۡبُدُوٓاْ إِلَّا ٱللَّهَ إِنِّيٓ أَخَافُ عَلَيۡكُمۡ عَذَابَ يَوۡمٍ عَظِيمٖ

Ka kuma tuna xan’uwan Adawa (watau Hudu) lokacin da ya gargaxi mutanensa a al‑Ahqafu, alhali haqiqa masu gargaxi sun shuxe a gabaninsa da kuma a bayansa (suna cewa:) “Kada ku bauta wa (kowa) sai Allah, lalle ni ina jiye muku tsoron azabar wani yini mai girma.”



Surah: Suratul Ahqaf 

Ayah : 22

قَالُوٓاْ أَجِئۡتَنَا لِتَأۡفِكَنَا عَنۡ ءَالِهَتِنَا فَأۡتِنَا بِمَا تَعِدُنَآ إِن كُنتَ مِنَ ٱلصَّـٰدِقِينَ

Sai suka ce: “Yanzu ka zo ne don ka kawar da mu daga ababen bautarmu? To ka zo mana da abin da kake yi mana alqawarin narko (da shi) idan ka kasance cikin masu gaskiya.”



Surah: Suratul Ahqaf 

Ayah : 23

قَالَ إِنَّمَا ٱلۡعِلۡمُ عِندَ ٱللَّهِ وَأُبَلِّغُكُم مَّآ أُرۡسِلۡتُ بِهِۦ وَلَٰكِنِّيٓ أَرَىٰكُمۡ قَوۡمٗا تَجۡهَلُونَ

Sai ya ce: “Lalle sani yana wurin Allah kawai, ni kuma ina isar muku abin da aka aiko ni da shi ne, sai dai kuma ni ina ganin ku mutane ne masu wauta.”



Surah: Suratul Ahqaf 

Ayah : 24

فَلَمَّا رَأَوۡهُ عَارِضٗا مُّسۡتَقۡبِلَ أَوۡدِيَتِهِمۡ قَالُواْ هَٰذَا عَارِضٞ مُّمۡطِرُنَاۚ بَلۡ هُوَ مَا ٱسۡتَعۡجَلۡتُم بِهِۦۖ رِيحٞ فِيهَا عَذَابٌ أَلِيمٞ

To lokacin da suka gan ta (azabar) wani hadari ne mai gindayawa, ya doso wa kwarurukansu sai suka ce: “Wannan hadari ne mai ba mu ruwa!” A’a, (ba ku sani ba) shi ne abin da kuke neman gaggautowarsa, watau iska da take cike da azaba mai raxaxi



Surah: Suratul Ahqaf 

Ayah : 25

تُدَمِّرُ كُلَّ شَيۡءِۭ بِأَمۡرِ رَبِّهَا فَأَصۡبَحُواْ لَا يُرَىٰٓ إِلَّا مَسَٰكِنُهُمۡۚ كَذَٰلِكَ نَجۡزِي ٱلۡقَوۡمَ ٱلۡمُجۡرِمِينَ

Tana ruguza kowane irin abu da umarnin Ubangijinta, sai suka wayi gari ba abin da ake gani sai (kufaifan) gidajensu. Kamar haka Muke saka wa mutane masu manyan laifuka



Surah: Suratul Ahqaf 

Ayah : 26

وَلَقَدۡ مَكَّنَّـٰهُمۡ فِيمَآ إِن مَّكَّنَّـٰكُمۡ فِيهِ وَجَعَلۡنَا لَهُمۡ سَمۡعٗا وَأَبۡصَٰرٗا وَأَفۡـِٔدَةٗ فَمَآ أَغۡنَىٰ عَنۡهُمۡ سَمۡعُهُمۡ وَلَآ أَبۡصَٰرُهُمۡ وَلَآ أَفۡـِٔدَتُهُم مِّن شَيۡءٍ إِذۡ كَانُواْ يَجۡحَدُونَ بِـَٔايَٰتِ ٱللَّهِ وَحَاقَ بِهِم مَّا كَانُواْ بِهِۦ يَسۡتَهۡزِءُونَ

Haqiqa Mun kafa su (a bayan qasa) kafawar da ba Mu yi muku irinta ba, Muka kuma sanya musu ji da gani da tunani, sai jin nasu da ganinsu da tunaninsu ba su amfana musu komai ba, tunda sun kasance suna musanta ayoyin Allah, abin da kuma suka kasance suna yi wa izgili ya auka musu



Surah: Suratuz Zariyat

Ayah : 41

وَفِي عَادٍ إِذۡ أَرۡسَلۡنَا عَلَيۡهِمُ ٱلرِّيحَ ٱلۡعَقِيمَ

Kuma game da Adawa (akwai aya), lokacin da Muka aiko musu da iska marar alhairi



Surah: Suratuz Zariyat

Ayah : 42

مَا تَذَرُ مِن شَيۡءٍ أَتَتۡ عَلَيۡهِ إِلَّا جَعَلَتۡهُ كَٱلرَّمِيمِ

Ba ta barin wani abu idan ta biyo ta kansa sai ta mayar da shi kamar daddagagge qashi



Surah: Suratul Qamar

Ayah : 18

كَذَّبَتۡ عَادٞ فَكَيۡفَ كَانَ عَذَابِي وَنُذُرِ

Adawa sun qaryata (Annabinsu), to qaqa azabata da gargaxina suka kasance?



Surah: Suratul Qamar

Ayah : 19

إِنَّآ أَرۡسَلۡنَا عَلَيۡهِمۡ رِيحٗا صَرۡصَرٗا فِي يَوۡمِ نَحۡسٖ مُّسۡتَمِرّٖ

Lalle Mu Mun aiko musu da iska mai qarfi a ranar shu’umci mai zarcewa



Surah: Suratul Qamar

Ayah : 20

تَنزِعُ ٱلنَّاسَ كَأَنَّهُمۡ أَعۡجَازُ نَخۡلٖ مُّنقَعِرٖ

Tana tumvuko mutane[1] ta kayar su, kai ka ce su kututturan dabinai ne da aka tuttunvuke


1- Watau daga doron qasa ta yi sama da su sannan ta kifo da su ta kawunansu su faxo qasa a mace.


Surah: Suratul Qamar

Ayah : 21

فَكَيۡفَ كَانَ عَذَابِي وَنُذُرِ

To qaqa azabata da gargaxina suka kasance?



Surah: Suratul Haqqa

Ayah : 4

كَذَّبَتۡ ثَمُودُ وَعَادُۢ بِٱلۡقَارِعَةِ

Samudawa da Adawa sun qaryata mai qwanqwasa (zukata da tsoro)



Surah: Suratul Haqqa

Ayah : 6

وَأَمَّا عَادٞ فَأُهۡلِكُواْ بِرِيحٖ صَرۡصَرٍ عَاتِيَةٖ

Adawa kuma sai aka hallaka su da iska mai tsananin sanyi mai qarfi



Surah: Suratul Fajr

Ayah : 6

أَلَمۡ تَرَ كَيۡفَ فَعَلَ رَبُّكَ بِعَادٍ

Shin ba ka ga yadda Ubangijinka Ya aikata ba ga Adawa?



Surah: Suratul Fajr

Ayah : 7

إِرَمَ ذَاتِ ٱلۡعِمَادِ

(Watau qabilar) Iramu ma’abociyar tsawo



Surah: Suratul Fajr

Ayah : 8

ٱلَّتِي لَمۡ يُخۡلَقۡ مِثۡلُهَا فِي ٱلۡبِلَٰدِ

Wadda ba a halicci irinta ba a cikin garuruwa (a tsananin qarfi)