Haquri mai kyau shi ne haqurin da babu raki a cikinsa, haqurin da yake xaukaka ran mai shi sama da raxaxin da take ji, ya gina mata wasu gadoji na fata a saman kogunan xebe qauna. Irin wannan haqurin ba jira ne marar kyau ba, a’a haquri ne na aiki da imani da kuma fatan cewa lokacin yaye damuwa a kusa yake
A yayin da ake cikin ruxanin rayuwa da jujjuyawarta, haquri yana kasancewa kamar haske da zai haskaka hanya mai duhu, kamar yadda Allah Ta’ala ya faxa a cikin Suratul Ma’arij: “Ka yi haquri, haquri mai kyau”.
Haquri mai kyau shi ne haqurin da babu raki a cikinsa, haqurin da yake xaukaka ran mai shi sama da raxaxin da take ji, ya gina mata wasu gadoji na fata a saman kogunan xebe qauna. Irin wannan haqurin ba jira ne marar kyau ba, a’a haquri ne na aiki da imani da kuma fatan cewa lokacin yaye damuwa a kusa yake.
A yayin da ake tafiya a zangon rayuwa, haquri yana zama wani mabuxi da ake cin galaba a kan qalubale da tsananin da ake fuskanta.
“Ka yi haquri haquri mai kyau”. Suratul Ma’arij, Aya ta 5.
Kalmomi ne da suke vuvvugowa daga hikimar Ubangiji a cikin Suratul Ma’arij, waxanda suke kiranmu zuwa ga yin haqurin da ba a cakuxa shi da raki ba.
Haquri mai kyau shi ne haqurin da ya siffantu da yarda da kuma kyakkyawan fata, ta yadda mai haquri zai kalli sama yana mai imani cewa, kowane baqin girgije, to qarqashinsa akwai rana mai haske.
Kuma kamar yadda Allah ya yi alqawari a cikin Suratuz Zumar inda yake cewa, “Kaxai ana cika wa masu haquri ladansu ba tare da lissafi ba”. Don haka lallai ladan da yake jiran masu haquri ba shi da iyaka, ya wuce duk wani tunani, da kuma kishiyantar girman sakamakon da za a samu daga Allah Ta’ala.
“Matakanka Na Samun Nasara: Ka sanya haquri ya zama abokin tafiyarka”
Rayuwa ba ta rabuwa da jarrabawoyi da ibtila’oi, sai dai haquri yakan bamu qarfin da za mu fuskance su ta hanyar tabbatuwa da kyakkyawan fata. Haquri yayin fuskantar tsanani yana bukatar qarfin imani da qaqqarfan qudiri ba sakwa-sakwa ba. Don haka yayin da za mu yi haquri za mu tsinci kanmu muna qaruwa da ci gaba ta hanyoyin da ba mu tava tsammani ba.
Haquri yana buxe qofofin yaye damuwa, yana kuma kawo hutun da amincin rai. Mutum mai haquri ya san cewa, akwai yalwa bayan tsanani, kuma Allah ba ya tozarta ladan waxanda suka kyautata aiki.
Haquri mabuxin yaye damuwa ne, kuma dashi ne hikimar Allah mahalicci take bayyana game da sanar da xan’adam matsayin yin dako da kuma kyakkyawan fata, kuma kamar faxin Allah, “Kaxai ana cika wa masu haquri ladansu ba tare da lissafi ba”. Suratuz Zumar.
Kamar yadda Allah Ta’ala ya bamu labari a cikin Suratuz Zumar aya ta 10. Haquri ba samun falala ba ce kawai, a’a hanya ce ta samun babban lada, ladan da ba shi da iyaka ko qididdiga. Masu haquri suna tafiya a natse a cikin harkokin rayuwa, suna sane da cewa, duk wani jinkiri akwai alheri a cikinsa, kuma sakamakon haqurinsu zai wuce a kwatance.
Yin haquri bai taqaita a kan juriya yayin tsanani ba kawai, a’a ya haxa da yin ado da qawa da kyawawan xabi’u waxanda ake yaba yayin mu’amalantar sauran mutane.
Yin haquri a bisa cutarwa da yin afuwa yayin da ake da ikon ramawa, siffofi ne da Allah yake sonsu, yake kuma ba da kyakkyawan sakamako idan an yi su.
Haquri yana koyar da mu ya ya za mu yafe qullacin da ke cikin zuciya, don akwai hutun zuciya a cikin kawar da kai, kuma yana gina gadojin soyayya da ‘yan’uwantaka a tsakanin mutane.
Haquri yana bayyana a mafi kyawun siffarsa yayin da ya kasance ya haxu da aiki na gari. Mai haquri ba ya wadatuwa da zaman jira, yana yin aiki yana qoqari da kai-kawo a bayan qasa yana mai kuma dogaro da Allah, yana mai imani cewa qoqarinsa ba zai tafi a banza ba.
Haquri da aiki na gari ‘yan biyu ba sa rabuwa, kowane xaya daga cikinsu yana cika xayan, kuma suna haskaka hanya don cimma manufar da aka sa a gaba.
Dukkan wata manufa da take da muhimmanci ana buqatar haquri da dagewa don a cimmata, wannan ya haxa da abin da yake da alaqa da yin zarra a sha’anin karatu, ko gina wani babban aiki ake so ya yi nasara, ko abin da ya shafi bunqasa kai, to lalle ana xaukar haquri a matsayin abokin tafiya a irin wannan tafiyar yayin da muke fuskantar rashin cin nasara.
A tsarin tafiyar da rayuwa, haquri shi ne abokin da yake shiryar da mu zuwa ga cin nasara. Kowace manufa tana da buqatar a jajirce a kuma ba ta lokaci. In ba a yi haquri ba, to nan da nan za a juya da baya a kauce hanya. Haquri yana koyar da mu ya ya za mu fuskanci qalubale ba tare da mun rasa fatan mu na tabbatar da mafarkinmu ba. Lalle haquri yana tunatar da mu cewa, a haqiqanin lamari dukkan wani jinkiri mataki ne na havaka da bunqasa da kuma ci gaba.
Haquri yana haska kyawun ruhin xan’adamtakar mutum da kuma ikonsa a kan tsallake qalubale ta hanyar imani da kyakkyawan fata.
Haquri a haqiqaninsa yana nuna irin qarfin da ke taskace a cikin ran mutum, wanda yake ba shi dama na fuskantar qalubalen rayuwa ta hanyar tabbatuwa da samun nutsuwa. Domin yana nufin wanzuwar ruhin mutum yana rataye da irin mafarkinta da kuma fatanta, har a cikin lokuta mafiya tsananin duhu da wahala.
Haquri shi ne kafaffen imani da cewa, lallai bayan kowane tsanani akwai sauqi, kuma kowane tsanani yana da mafita, kuma komai nisan dare gari zai waye.
Haquri sakamako ne na Ubangiji ba tare da iyaka ba
“Kaxai ana cika wa masu haquri ladansu ne ba tare da lissafi ba”.
Waxannan kalmomi da suke daga sama da suke a farko-farkon Alqur’ani mai girma suna xauke da girman lada ga wanda ya yi haquri yayin masifu da jarrabawoyi.
Kira ne don a tabbata da ci gaba wurin kafewa, bisa hasken sanin Allah da abin da ke cikin zukata, da kuma hisabinsa na adalci ga dukkan wani aiki da magana.
Masu haquri su suke mallakar qarfi na haqiqa, ba tare da makamai da ake gani ba, a’a da tabbatuwar imani da kuma taqawarsu, domin suna fuskantar yanayiyyika da tsanani, suna masu imani cewa, duk irin tsayin da dare zai yi, jarrabawoyi su qaru, lallai Allah zai saka musu da abin da yake mafi alheri kuma mafi kyau a tattare da su.
A duniyar yau muna ganin yadda qalubalantar haquri yake a koda yaushe, ladan masu haquri yana kasancewa ne a cikin qarfin ransu da ikon su wurin juriya da qalubalantar tsanani da kowace irin tabbatuwa da imani, mun koyi yadda za mu iya ci gana da kiyayewa a kan tabbatuwarmu duk da irin tsanin da ya ke fizgar mu.
Mu za mo cikin masu haquri, mu gina gabanmu da amintuwa da tabbatuwa, mu aminta da cewa Allah ba zai tava tozarta ladan wanda ya kyautata aiki ba. Koda yaushe mu riqa tuna cewa: “Kaxai ana cika wa waxanda suka yi haquri ladansu ne ba tare da lissafi ba”.