Ana xaukar gaskiya a matsayin xaya daga cikin turakun da suke ba da gudunmawa wurin rabautar mutum da kuma samun dacewa. A kanta ne kai-komon alaqar mutane ta aminci take qulluwa, kuma ita ce tushen yarda tsakanin xaixaikun mutane. Gaskiya ita ce tufar cin nasara da kuma ruhinsa, yayin da qarya kuma ta zama babban tushen faxuwa da tavewa. Dukkanin al’ummu da addinai sun haxu a kan ganin darajar gaskiya da muhimmancinta yayin gina al’ummomi da tabbatar da zaman lafiya a tsakanin al’umma.
Dabi'u a cikin Alqur'ani
Ana xaukar gaskiya a matsayin xaya daga cikin turakun da suke ba da gudunmawa wurin rabautar mutum da kuma samun dacewa. A kanta ne kai-komon alaqar mutane ta aminci take qulluwa, kuma ita ce tushen yarda tsakanin xaixaikun mutane. Gaskiya ita ce tufar cin nasara da kuma ruhinsa, yayin da qarya kuma ta zama babban tushen faxuwa da tavewa. Dukkanin al’ummu da addinai sun haxu a kan ganin darajar gaskiya da muhimmancinta yayin gina al’ummomi da tabbatar da zaman lafiya a tsakanin al’umma.
Gaskiya ita ce ginshiqin kyawawan xabi’u, kuma gaskiya tana cikin mafi muhimmancin siffofin Musulmi na gaskiya. Kuma gaskiya ta qunshi vangarori da dama, daga cikinsu akwai:
Gaskiya a magana: Dole ne Musulmi ya zamo mai gaskiya a dukkan abin da zai faxa, saboda yin gaskiya dalili ne da yake nuna imani mutum, yin qarya kuma dalili ne da yake nuna munafuncin mutum.
Gaskiya a ayyuka: Ya kamata ayyukan Musulmi su dace da maganganunsa, kuma ya zamana baxininsa ya yi daidai da zahirinsa.
Gaskiya a niyya da nufi: Dole ne niyyar Musulmi ta zamo an tsantsantata ga Allah Ta’ala, ba tare da an gaurayata da wani abu na riya ko neman duniya ba.
Gaskiya a qudiri: Ya wajaba a kan Musulmi ya kasance mai tabbatuwa a kan qudirinsa, kada ya canja shi ko ya musanya shi bayan ya yi wa Allah alqawari a kan wannan qudirin. Allah Ta’ala yana cewa a cikin mabuwayin littafinsa: (Daga cikinsu kuma akwai waxanda suka yi wa Allah alqawarin cewa: “Idan Ya arzuta mu daga falalarsa, to lalle tabbas za mu riqa ba da sadaka, kuma lalle tabbas za mu zama cikin mutane salihai.”. To lokacin da Ya arzuta su xin sai suka yi rowa da ita (sadakar) suka kuma ba da baya suna masu bijirewa. Sai Ya gadar musu da munafunci a cikin zukatansu har zuwa ranar da za su gamu da Shi, saboda sava wa alqawarin da suka yi wa Allah da kuma qaryatawar da suka zamanto suna yi). [Tauba: 75-77]
Gaskiya a matakan addini: Dole ne Musulmi ya kiyaye matsayin imaninsa, ya kums kasance mai gaskiya a dogaronsa da tsoronsa ga Allah.
Gaskiya a tsoro: Ya kamata tsoron Allahn Musulmi ya zamo na gaskiya, kuma hakan ya bayyana ta fuskar nisantar laifuffuka da abubuwan da suka sava wa shari’a.
Gaskiya a ayyukan zuciyoyi: Dole ne zuciyar Musulmi ta zamo mai fuskantar Allah da gaskiya da ikhlasi a yayin dukkan ibadu da dukkan yanayi.
Ta dalilin yin kwalliya da waxannan siffofi ne, Musulmi zai rayu irin rayuwar da take cike da nutsuwa da kwanciyar hankali, ya kuma zama abin buga misali ga mumini na gaskiya wanda aikinsa yake dacewa da maganarsa, ya kuma zamo a mafi darajojin imani da taqawa.
Ana xaukar gaskiya a matsayin mabuxin tsira da rabauta a duniya da lahira, hakan kuma yana bayyana a vangarori uku manya:
Gaskiya tare Allah: Wannan tana samuwa ta hanyar yin ikhlasi a imani da aiki na gari da xabi’un sam-barka. Hakanan ta haxa da gaskiya a yaqini da niyya da tsoron Allah. Ana iya yin gane wannan gaskiyar ta hanyar lizimtar ayyukan xa’a da nisantar laifuffuka, da yin kwalliya da siffofin muminai masu gaskiya kamar yadda ya zo a cikin Alqur’ani.
Gaskiya a karan-kan mutum: Ana so mutum ya zamo mai faxa wa kansa gaskiya, mai yi wa kansa hisabi, mai gyara aibukan da yake tattare dasu. Hakanan wajibi ne mutum ya nisanci faxawa tarkon burace-burace na qarya da soye-soyen zuciya, ya kuma zamo mai faxakuwa game da haxarin zuciya da makircinta, ya yi aiki tuquru don tsarkaketa da miqar da ita ta yi daidai da koyarwar addini.
Ya kamata mu zamo masu faxa wa kanmu gaskiya, mu kalli aibukanmu mu tsayu mu gyara su. Yi wa kai hisabi hanya ce da muminai suke bi, kuma alama ce ta masu kaxaita Allah da bauta, kuma adireshi ne na masu tsoron Allah. Shi mumimi mutum ne mai kiyaye dokokin Ubangijinsa, mai kuma yi wa kansa hisabi ne, mai kuma neman gafarar zunubansa ne, yana sane da cewa, haxarin zuciya abu ne mai girma, kuma cutarta aba ce mai cutarwa, makircinta kuma babba ne, sharrinta kuma mai yaxuwa ne. Lalle ita rai mai yawan umarni da mummunan aiki ce, kuma mai yawan karkata ce zuwa ga son zuciya, kuma mai kira ce zuwa jahilci, kuma mai yin jagora ce zuwa ga halaka, mai kuma karkata zuwa ga wargi ce, sai fa ga wanda Allah ya yi wa rahama. Don haka kada a qyaleta da abin da take so, domin ita mai kira ce zuwa ga xagawa. Duk wanda ya yi mata biyayya, to za ta ja shi zuwa ga munanan ayyuka, ta kuma kira shi zuwa ga abubuwan qi, ta kuma kutsa da shi cikin abubuwan da ba a so, musibunta ababen mamaki ne, abubuwan da suke fizgarta ababen tsoro ne, sharrikanta masu yawa ne, duk wanda ya bar ragamar ransa ta yi xagawa, to wutar jahimu ita ce makomarsa a ranar alqiyama. (To (a wannan ranar) duk wanda ya yi xagawa. Ya kuma fifita rayuwar duniya. To lalle (wutar) jahimu ita ce makomarsa). [Nazi’at: 37-39]. Akasinsa kuma shi ne (Duk wanda kuma ya ji tsoron tsayuwa gaban Ubangijinsa, ya kuma hana zuciya bin abin da take so. To lalle Aljanna ita ce makoma.) [Nazi’at: 40-41]
Gaskiya ga mutane: Wannan ya qunshi gaskiya a maganganu da ayyuka da halaye. Ana xaukar mu’amalantar mutane da gaskiya a matsayin dalili a kan gaskiyar imanin mutum, ita kuma qarya a matsayin dalili a kan munafuncin mutum. Wajibi ne Musulmi ya kasance mai nasiha ga ‘yan’uwansa Musulmi, mai kiyaye amana da yarjejeniya, ya kuma yi qawa da kyawawan xabi’u a yayin mu’amalarsa da wasu.
Dole ne gaskiya ta zama siffa mai lizimtar Musulmi a dukkan vangarorin rayuwarsa, kuma yin hakan yakan zama hanyar rabauta da tsira a duniya da lahira.
Ana xaukar gaskiya a matsayin xaya daga cikin turakun da suke ba da gudunmawa wurin rabautar mutum da kuma samun dacewa. A kanta ne kai-komon alaqar mutane ta aminci take qulluwa, kuma ita ce tushen yarda tsakanin xaixaikun mutane. Gaskiya ita ce tufar cin nasara da kuma ruhinsa, yayin da qarya kuma ta zama babban tushen faxuwa da tavewa. Dukkanin al’ummu da addinai sun haxu a kan ganin darajar gaskiya da muhimmancinta yayin gina al’ummomi da tabbatar da zaman lafiya a tsakanin al’umma.
Dukkan addinai musamman Musulunci sun ba da babbar kulawa game da sha’anin gaskiya, sun kuma sanya ta daga cikin xabi’u da ake so, wanda ya wajaba ga duk wani mumini ya yi kwalliya da ita. A Musulunci, gaskiya tana cikin tushen addini, kuma tana cikin turakun addini. Tana xaya daga cikin siffofin da suke bambance tsakanin mumini na gaskiya da kuma munafuki. Manzon Allah Annabi Muhammadu, salatin Allah da amincinsa su tabbata a gare shi, ya tabbatar da cewa, lalle yin gaskiya yana bayuwa zuwa ga samun nutsuwa da hutun rai, a yayin da yin qarya yake bayuwa zuwa ga samun kokwanto da tababa.
Gaskiya ita ce ma’aunin sauran kyawawan xabi’u, kuma ita ce hanya mafi dacewa da za a bi don a isa zuwa ga maxaukakan matsayai. Duk wanda ya yi qawa da gaskiya, to za a iya azurta shi da hangen nesa na gaskiya da kuma hanya mai qarfin gaske. Gaskiya wata takobi ce da take sare kan varna, kuma hanya ce ta tsira daga wahalhalu da abubuwan tashin hankali.
Annabi salatin Allah da amincinsa su tabbata a gare shi ya bayyana cewa, lalle mumini zai iya zamowa matsoraci ko marowaci, amma ba zai yiwu ya zamo maqaryaci ba. Wannan yake nuni zuwa ga cewa, gaskiya wani vangare ne na imanin mumini wanda ba a iya rabata da shi. Gaskiya sababi ce ta rabauta da tsira a duniya da lahira, kuma tana daga cikin abubuwan da ake kimsa wa masu gaskiya a maganganunsu da ayyukansu.
Saboda kyawun gaskiya hankali ma yana kira zuwa gareta, kamar yadda yake qin kishiyarta. Addini ma ya yi umarni da a yi gaskiya ya kuma kwaxaitar da yinta. Annabi salatin Allah da amincinsa su tabbata a gare shi yana cewa: “Wasu mutane daga cikin waxanda suka gabaceku suna tsaka da tafiya, sai kwatsam ruwan sama ya sauko, sai suka shiga wani kogo suka fake, sai wani dutse ya gangaro ya rufe su. Sai sashinsu ya ce da sashi, lalle fa ku sani wallahi babu abin da zai tserar da ku in ba gaskiya ba, don haka kowane mutum daga cikinku ya yi addu’a da abin da ya san ya yi gaskiya yayin da ya aiwatar dashi”. Har zuwa qarshen hadisin. Sai ya zamana dalilin tsiransu shi ne gaskiyar da suka yi wa Allah. Mutuntuka aba ce da ke bayuwa zuwa aikata gaskiya kuma tana zaburarwa zuwa ga aikata gaskiya. Labarawa sun kasance ba sa son su ga an samu qarya daga wajensu, suna son su ga sun shahara da gaskiya. Hakanan kuma ana lissafa qarya daga cikin alamomin munafunci.
Download
Amana a Musulunci
Amana babban nauyi ce a Musulunci kuma kayan xauka ne masu nauyi. Abin da ake nufi da amana shi ne, bayar da haqqin Allah ta hanyar bauta masa da tsantsanta addini gare shi, da tsayuwa da haqqoqin halittu ba tare da tawaya ba. A Musulunci amana tana xaya daga cikin manyan turaku na gyaran xabi’a. Annabi salatin Allah da amincinsa su tabbata a gare shi, ya qulla alaqa tsakanin amana da imani. Amana ta qunshi dukkan vangarorin rayuwar Musulmi na duniya da na lahira, tun daga abin da ya shafi ibadu, misali salla da azumi da zakka, zuwa abin da abin da ya shafi ayyukan gavovi, kamar ji da gani da zuciya. Hakanan ta qunshi rayuwa da dukiya da mace da ‘ya’ya da iyaye da maqota da cinikayya da wasiyoyi da shaidu da ayyukan qwadago da abin da ya shafi al’umma da ilimi. Allah Ta’ala yana cewa: “Lalle ji da gani da kuma tunani duk waxannan sun zama abin tambaya ne game da su”. [Isra’i: 36]
Amana ta qunshi kiyaye addini da yaxa shi, da aiwatar da ibadu da ikhlasi da bin shari’a, da ba wa rai kulawa da tsarkaketa, da amfani da gavovi cikin abin da zai yardar da Allah. Kamar yadda kuma amana ta qunshi amfanar rayuwa cikin ayyukan xa’a, da yin mu’amala ingantacciya da kudi da tsayuwa da haqqoqin mace da ‘ya’ya da iyaye da maqota. Hakanan amana tana tsanantawa game da abin da ya shafi wajabcin cika alqawarin da aka yi wanda ya shafi cinikayya da yarjeniyoyi da zartar da wasiyoyi da adalci, da bayar da shaida da amana da tsayuwa da ayyukan da aka xora wa mutum da ikhlasi, da ba da kariya ga wurin da al’ummar Musulmi suke rayuwa da qarfafarsa, da xaukar ilimi da gaskiya da tsare sirrikan majalisa.
Kowane Musulmi yana xaukar nauyin amanar abin da aka amince masa a kansa, kuma da sannu Allah zai tambaye shi game da wannan amanar ranar alqiyama. Haqiqa Annabi salatin Allah da amincinsa su tabbata a gare shi, ya tsoratar game da yin algus da ha’inci a amana, ya qarfafa zancensa da cewa, duk wanda bai kewaye abin da aka bashi kiwo da nasiharsa ba ba zai shaqi qamshin Aljanna ba. Amana ta tattaro kowane irin abu a rayuwa. Amana wani nauyi ne mai girma da Allah ya bijirar dashi ga sammai da qasa da duwatsu amma suka qi xauka, shi kuma mutum ya xauka.
Muhimmancin kyawawan halaye da tadoji masu girma wurin samar da nutsuwa da dacewa ga mutum da kuma al’umma. Kuma yana qarfafa cewa, wajibi ne a riqa aiwatar da waxannan xabi’un a kowane hali da kowane yanayi. Xabi’ar amana tana daga cikin mafi muhimmancin waxannan xabi’un. Kuma ita amana ba ta taqaita a kan kiyaye dukiya ba kawai, a’a ta haxa da kiyaye magana da aiki da mu’amalolin yau da gobe da ibadu da alqawurra da abubuwan da aka lizimta wa mutum da abin da ya shafi lafiya da kafafen isar da saqo da ke jikin mutum da wasunsu.
Amana wani vangare ne kuma jigo na halittar dan’adam da kuma addini. A bisa xabi’ar mutane sukan so su karkata zuwa ga amintaccen mutum su kuma aminta dashi. Nassoshi sun zo da suke kwaxaitar da Musulmi a kan koyon xabi’ar amana daga Musulunci da yin qawa da ita a dukkan vangarorin rayuwa, suna masu tabbatar da cewa, dukkan wanda zai yi qawa da riqon amana, to zai mai yarda da kansa kuma mutane da za su karve shi, kuma zai shiga cikin rahamar Allah da ihsaninsa.
An wayi gari amana ta yi qaranci saboda gafala game da abin da ya shafi lahira da son duniya da nisantar koyarwar addini. Don haka ake gargaxin dukkan al’ummar da aka rasa amana a cikinta da cewa, tana cikin al’umma mafi lalacewa. Hakanan kuma ana cewa, gushewar amana zai faru ne a sannu-a sannu tare da munanan ayyuka da ake yi, wanda hakan zai bayu ga canja abubawan da suke sune gaskiya, da yin qarya game da abubuwan da suka faru. Akwai nassin hadisin Annabi da ya zo yake nuni da gargaxi game da wani zamani da zai zo wanda za a riqa gaskata maqaryaci a riqa qaryata mai gaskiya, a aminta da maha’inci, amintacce kuma a mayar da shi maha’inci.
Tawaya a amana yana bayuwa zuwa ga tawaya a imani. Hadisin Annabi ya zo da siffar yadda za a cire amana daga zukata, amana ta zama wata aba ce ‘yar kaxan har ya zamana ana yabon wanda babu wani alheri ko imani a tattare dashi.