Surata: Suratul A’araf

O versículo : 91

فَأَخَذَتۡهُمُ ٱلرَّجۡفَةُ فَأَصۡبَحُواْ فِي دَارِهِمۡ جَٰثِمِينَ

Sai girgizar qasa ta kama su, suka wayi gari a gidajensu gurfane a kan gwiwoyinsu (matattu)



Surata: Suratul A’araf

O versículo : 92

ٱلَّذِينَ كَذَّبُواْ شُعَيۡبٗا كَأَن لَّمۡ يَغۡنَوۡاْ فِيهَاۚ ٱلَّذِينَ كَذَّبُواْ شُعَيۡبٗا كَانُواْ هُمُ ٱلۡخَٰسِرِينَ

Waxanda suka qaryata Shu’aibu, kai ka ce ba su tava zama a cikinsu (gidajensu) ba, lalle waxanda suka qaryata Shu’aibu sun kasance su ne hasararru



Surata: Suratul A’araf

O versículo : 93

فَتَوَلَّىٰ عَنۡهُمۡ وَقَالَ يَٰقَوۡمِ لَقَدۡ أَبۡلَغۡتُكُمۡ رِسَٰلَٰتِ رَبِّي وَنَصَحۡتُ لَكُمۡۖ فَكَيۡفَ ءَاسَىٰ عَلَىٰ قَوۡمٖ كَٰفِرِينَ

Sai ya juya ya bar su, kuma ya ce: “Ya ku mutanena, lalle haqiqa na isar muku da saqonnin Ubangijina, na kuma yi muku nasiha; to saboda me zan ji takaici a kan mutane kafirai?”



Surata: Suratul A’araf

O versículo : 94

وَمَآ أَرۡسَلۡنَا فِي قَرۡيَةٖ مِّن نَّبِيٍّ إِلَّآ أَخَذۡنَآ أَهۡلَهَا بِٱلۡبَأۡسَآءِ وَٱلضَّرَّآءِ لَعَلَّهُمۡ يَضَّرَّعُونَ

Kuma ba Mu tava aiko wani annabi cikin wata alqarya ba, (mutanensa suka qaryata shi) sai Mun kama su da tsananin talauci da cututtuka, ko sa qasqantar da kai



Surata: Suratul A’araf

O versículo : 95

ثُمَّ بَدَّلۡنَا مَكَانَ ٱلسَّيِّئَةِ ٱلۡحَسَنَةَ حَتَّىٰ عَفَواْ وَّقَالُواْ قَدۡ مَسَّ ءَابَآءَنَا ٱلضَّرَّآءُ وَٱلسَّرَّآءُ فَأَخَذۡنَٰهُم بَغۡتَةٗ وَهُمۡ لَا يَشۡعُرُونَ

Sannan sai Muka musanya mahallin tsanani da jin daxi, har dai suka yawaita, suka ce: “Haqiqa da can cututtuka da kuma wadata sun samu iyayenmu.” Sai kawai Muka damqe su (da azaba) ba zato ba tsammani alhalin ba sa jin (hakan zai faru)



Surata: Suratul A’araf

O versículo : 96

وَلَوۡ أَنَّ أَهۡلَ ٱلۡقُرَىٰٓ ءَامَنُواْ وَٱتَّقَوۡاْ لَفَتَحۡنَا عَلَيۡهِم بَرَكَٰتٖ مِّنَ ٱلسَّمَآءِ وَٱلۡأَرۡضِ وَلَٰكِن كَذَّبُواْ فَأَخَذۡنَٰهُم بِمَا كَانُواْ يَكۡسِبُونَ

Kuma in da a ce mutanen alqaryu sun yi imani kuma sun tsare dokokin Allah, to lalle da Mun buxe musu albarkatu daga sama da kuma qasa, sai dai sun qaryata, Mu kuwa sai Muka kama su da abin da suka kasance suna aikatawa



Surata: Suratul A’araf

O versículo : 97

أَفَأَمِنَ أَهۡلُ ٱلۡقُرَىٰٓ أَن يَأۡتِيَهُم بَأۡسُنَا بَيَٰتٗا وَهُمۡ نَآئِمُونَ

Yanzu mutanen alqaryu sun amince azabarmu ta zo musu cikin dare alhali suna bacci?



Surata: Suratul A’araf

O versículo : 98

أَوَأَمِنَ أَهۡلُ ٱلۡقُرَىٰٓ أَن يَأۡتِيَهُم بَأۡسُنَا ضُحٗى وَهُمۡ يَلۡعَبُونَ

Ko kuma mutanen alqaryun sun amince azabarmu ta zo musu da hantsi suna tsakiyar wasanni?



Surata: Suratul A’araf

O versículo : 99

أَفَأَمِنُواْ مَكۡرَ ٱللَّهِۚ فَلَا يَأۡمَنُ مَكۡرَ ٱللَّهِ إِلَّا ٱلۡقَوۡمُ ٱلۡخَٰسِرُونَ

Yanzu sun amince da makarun Allah ne? To kuwa ba mai amince wa makarun Allah sai mutanen da suke asararru[1]


1- A nan Allah () ya ambaci makarunsa shi kaxai bai ambaci makarun bawansa ba. To amma a cikin Suratul Anfal aya ta 30 Allah () ya ambaci makarunsa da na bayinsa.


Surata: Suratul A’araf

O versículo : 100

أَوَلَمۡ يَهۡدِ لِلَّذِينَ يَرِثُونَ ٱلۡأَرۡضَ مِنۢ بَعۡدِ أَهۡلِهَآ أَن لَّوۡ نَشَآءُ أَصَبۡنَٰهُم بِذُنُوبِهِمۡۚ وَنَطۡبَعُ عَلَىٰ قُلُوبِهِمۡ فَهُمۡ لَا يَسۡمَعُونَ

Ko kuwa bai bayyana ba ga waxanda suke gaje qasa bayan gushewar mutanenta (na farko) cewa, idan da Mun ga dama da Mun kama su da zunubansu. Kuma da Mun rufe zukatansu don haka ba za su iya ji ba?



Surata: Suratul A’araf

O versículo : 101

تِلۡكَ ٱلۡقُرَىٰ نَقُصُّ عَلَيۡكَ مِنۡ أَنۢبَآئِهَاۚ وَلَقَدۡ جَآءَتۡهُمۡ رُسُلُهُم بِٱلۡبَيِّنَٰتِ فَمَا كَانُواْ لِيُؤۡمِنُواْ بِمَا كَذَّبُواْ مِن قَبۡلُۚ كَذَٰلِكَ يَطۡبَعُ ٱللَّهُ عَلَىٰ قُلُوبِ ٱلۡكَٰفِرِينَ

Waxancan alqaryun Muna ba ka labarinsu ne. Kuma lalle haqiqa manzanninsu sun zo musu da hujjoji bayyanannu, amma ba su kasance masu yin imani ba, saboda qaryatawar da suka yi a da. Kamar haka ne Allah Yake rufe zukatan kafirai



Surata: Suratul A’araf

O versículo : 102

وَمَا وَجَدۡنَا لِأَكۡثَرِهِم مِّنۡ عَهۡدٖۖ وَإِن وَجَدۡنَآ أَكۡثَرَهُمۡ لَفَٰسِقِينَ

Kuma yawancinsu ba Mu same su da riqe wani alqawari ba; haqiqa kuma Mun samu yawancinsu fasiqai ne



Surata: Suratul A’araf

O versículo : 103

ثُمَّ بَعَثۡنَا مِنۢ بَعۡدِهِم مُّوسَىٰ بِـَٔايَٰتِنَآ إِلَىٰ فِرۡعَوۡنَ وَمَلَإِيْهِۦ فَظَلَمُواْ بِهَاۖ فَٱنظُرۡ كَيۡفَ كَانَ عَٰقِبَةُ ٱلۡمُفۡسِدِينَ

Sannan sai Muka aika Musa a bayansu da ayoyinmu, zuwa Fir’auna da manyan mutanensa, sai suka zalunci (kansu) da su; to duba ka ga, yaya qarshen mavarnata ya kasance?



Surata: Suratul A’araf

O versículo : 104

وَقَالَ مُوسَىٰ يَٰفِرۡعَوۡنُ إِنِّي رَسُولٞ مِّن رَّبِّ ٱلۡعَٰلَمِينَ

Kuma Musa ya ce: “Ya kai Fir’auna, lalle ni Manzo ne daga Ubangijin talikai



Surata: Suratul A’araf

O versículo : 105

حَقِيقٌ عَلَىٰٓ أَن لَّآ أَقُولَ عَلَى ٱللَّهِ إِلَّا ٱلۡحَقَّۚ قَدۡ جِئۡتُكُم بِبَيِّنَةٖ مِّن رَّبِّكُمۡ فَأَرۡسِلۡ مَعِيَ بَنِيٓ إِسۡرَـٰٓءِيلَ

“Wajibi ne a kaina cewa ba zan faxi wata magana game da Allah ba sai ta gaskiya. Haqiqa na zo muku da hujja bayyananniya daga Ubangijinku, don haka ka sakar min Banu Isra’ila.”



Surata: Suratul A’araf

O versículo : 106

قَالَ إِن كُنتَ جِئۡتَ بِـَٔايَةٖ فَأۡتِ بِهَآ إِن كُنتَ مِنَ ٱلصَّـٰدِقِينَ

Sai ya ce: “Idan har kana da wata alama, to ka zo da ita, idan har kana cikin masu gaskiya.[1]”


1- A al’adar annabawa ba su ne suke fara bayyana mu’ujizarsu ba, har sai an qalubalance su, sai Allah () ya bayyana ta, don kiyaye martabar annabci kada a yi saurin qaryata su.


Surata: Suratul A’araf

O versículo : 107

فَأَلۡقَىٰ عَصَاهُ فَإِذَا هِيَ ثُعۡبَانٞ مُّبِينٞ

Sai ya jefar da sandarsa, sai ga shi ta zama wani irin qaton kumurci a fili



Surata: Suratul A’araf

O versículo : 108

وَنَزَعَ يَدَهُۥ فَإِذَا هِيَ بَيۡضَآءُ لِلنَّـٰظِرِينَ

Kuma ya zaro hannunsa, sai ga shi fari qal ga masu kallo



Surata: Suratul A’araf

O versículo : 109

قَالَ ٱلۡمَلَأُ مِن قَوۡمِ فِرۡعَوۡنَ إِنَّ هَٰذَا لَسَٰحِرٌ عَلِيمٞ

Sai manyan gari daga cikin mutanen Fir’auna suka ce: “Lalle wannan tabbas mai sihiri ne, masani



Surata: Suratul A’araf

O versículo : 110

يُرِيدُ أَن يُخۡرِجَكُم مِّنۡ أَرۡضِكُمۡۖ فَمَاذَا تَأۡمُرُونَ

“Yana nufi ne ya fitar da ku daga qasarku, don haka me kuke yin umarni (da a yi)?”



Surata: Suratul A’araf

O versículo : 111

قَالُوٓاْ أَرۡجِهۡ وَأَخَاهُ وَأَرۡسِلۡ فِي ٱلۡمَدَآئِنِ حَٰشِرِينَ

Sai suka ce: “Ka dakatar da shi da xan’uwansa, ka kuma tura masu yin gangami cikin birane



Surata: Suratul A’araf

O versículo : 112

يَأۡتُوكَ بِكُلِّ سَٰحِرٍ عَلِيمٖ

“Za su zo maka da duk wani qwararren matsafi.”



Surata: Suratul A’araf

O versículo : 113

وَجَآءَ ٱلسَّحَرَةُ فِرۡعَوۡنَ قَالُوٓاْ إِنَّ لَنَا لَأَجۡرًا إِن كُنَّا نَحۡنُ ٱلۡغَٰلِبِينَ

Matsafan kuwa suka zo wa Fir’auna suka ce: “Shin tabbas muna da wani lada idan muka kasance masu rinjaye?”



Surata: Suratul A’araf

O versículo : 114

قَالَ نَعَمۡ وَإِنَّكُمۡ لَمِنَ ٱلۡمُقَرَّبِينَ

Ya ce, “E, kuma ma tabbas kuna cikin makusanta.”



Surata: Suratul A’araf

O versículo : 115

قَالُواْ يَٰمُوسَىٰٓ إِمَّآ أَن تُلۡقِيَ وَإِمَّآ أَن نَّكُونَ نَحۡنُ ٱلۡمُلۡقِينَ

Sai suka ce: “Ya kai Musa, ko dai ka (fara) jefawa, ko kuwa mu mu kasance mu ne masu (fara) jefawa.”



Surata: Suratul A’araf

O versículo : 116

قَالَ أَلۡقُواْۖ فَلَمَّآ أَلۡقَوۡاْ سَحَرُوٓاْ أَعۡيُنَ ٱلنَّاسِ وَٱسۡتَرۡهَبُوهُمۡ وَجَآءُو بِسِحۡرٍ عَظِيمٖ

Ya ce: “Ku jefa”. To yayin da suka jefa (sandunansu) sai suka sihirce idon mutane[1], kuma suka gigita su, suka zo da wani tsafi babba


1- Sihiri ba ya canza haqiqanin abu zuwa wani abu daban sai dai ya zama rufa ido kawai.


Surata: Suratul A’araf

O versículo : 117

۞وَأَوۡحَيۡنَآ إِلَىٰ مُوسَىٰٓ أَنۡ أَلۡقِ عَصَاكَۖ فَإِذَا هِيَ تَلۡقَفُ مَا يَأۡفِكُونَ

Muka kuma yi wahayi ga Musa cewa: “Jefa sandarka.” Sai ga shi nan take tana haxiye abin da suke qagowa



Surata: Suratul A’araf

O versículo : 118

فَوَقَعَ ٱلۡحَقُّ وَبَطَلَ مَا كَانُواْ يَعۡمَلُونَ

Sai gaskiya ta tabbata, abin da kuma suka kasance suna aikatawa sai ya lalace



Surata: Suratul A’araf

O versículo : 119

فَغُلِبُواْ هُنَالِكَ وَٱنقَلَبُواْ صَٰغِرِينَ

Sai aka rinjaye su a nan, suka kuma juya a qasqance



Surata: Suratul A’araf

O versículo : 120

وَأُلۡقِيَ ٱلسَّحَرَةُ سَٰجِدِينَ

Matsafa kuwa suka faxi suna masu sujjada