وَلَقَدِ ٱسۡتُهۡزِئَ بِرُسُلٖ مِّن قَبۡلِكَ فَأَمۡلَيۡتُ لِلَّذِينَ كَفَرُواْ ثُمَّ أَخَذۡتُهُمۡۖ فَكَيۡفَ كَانَ عِقَابِ
Haqiqa an yi wa manzannin da suka gabace ka izgili, sai Na yi wa waxanda suka kafirta talala, sannan Na damqe su. To yaya uqubata ta kasance (a gare su)?
أَفَمَنۡ هُوَ قَآئِمٌ عَلَىٰ كُلِّ نَفۡسِۭ بِمَا كَسَبَتۡۗ وَجَعَلُواْ لِلَّهِ شُرَكَآءَ قُلۡ سَمُّوهُمۡۚ أَمۡ تُنَبِّـُٔونَهُۥ بِمَا لَا يَعۡلَمُ فِي ٱلۡأَرۡضِ أَم بِظَٰهِرٖ مِّنَ ٱلۡقَوۡلِۗ بَلۡ زُيِّنَ لِلَّذِينَ كَفَرُواْ مَكۡرُهُمۡ وَصُدُّواْ عَنِ ٱلسَّبِيلِۗ وَمَن يُضۡلِلِ ٱللَّهُ فَمَا لَهُۥ مِنۡ هَادٖ
Yanzu wanda Yake tsaye a kan kula da kowane rai game da abin da ya aikata, (zai zama daidai da wanda ba haka ba?) Sun kuma sanya wa Allah abokan tarayya. Ka ce: (da su) “Ku faxa min sunayensu. Ko kuwa kuna ba Shi labarin abin da bai sani ba ne a bayan qasa, ko kuma dai kun riqe wata vatacciyar magana ce?” Bari dai; an dai qawata wa kafirai makircinsu ne kawai, aka kuma toshe musu hanyar (Allah). Wanda kuwa Allah Ya vatar to ba shi da wani mai shiryarwa
لَّهُمۡ عَذَابٞ فِي ٱلۡحَيَوٰةِ ٱلدُّنۡيَاۖ وَلَعَذَابُ ٱلۡأٓخِرَةِ أَشَقُّۖ وَمَا لَهُم مِّنَ ٱللَّهِ مِن وَاقٖ
Suna da wata azaba a rayuwar duniya; kuma lalle azabar lahira ita ta fi tsanani; ba su kuwa da wani mai kare su daga (azabar) Allah
۞مَّثَلُ ٱلۡجَنَّةِ ٱلَّتِي وُعِدَ ٱلۡمُتَّقُونَۖ تَجۡرِي مِن تَحۡتِهَا ٱلۡأَنۡهَٰرُۖ أُكُلُهَا دَآئِمٞ وَظِلُّهَاۚ تِلۡكَ عُقۡبَى ٱلَّذِينَ ٱتَّقَواْۚ وَّعُقۡبَى ٱلۡكَٰفِرِينَ ٱلنَّارُ
Misalin Aljannar nan da aka yi wa masu taqawa alqawari da ita; qoramu ne suke gudana ta qarqashinta; abincinta kuma mai dawwama ne da kuma inuwarta. Wannan shi ne makomar waxanda suka kiyaye dokokin Allah; makomar kafirai kuma ita ce wuta
وَٱلَّذِينَ ءَاتَيۡنَٰهُمُ ٱلۡكِتَٰبَ يَفۡرَحُونَ بِمَآ أُنزِلَ إِلَيۡكَۖ وَمِنَ ٱلۡأَحۡزَابِ مَن يُنكِرُ بَعۡضَهُۥۚ قُلۡ إِنَّمَآ أُمِرۡتُ أَنۡ أَعۡبُدَ ٱللَّهَ وَلَآ أُشۡرِكَ بِهِۦٓۚ إِلَيۡهِ أَدۡعُواْ وَإِلَيۡهِ مَـَٔابِ
Waxanda kuwa Muka bai wa littafi (muminansu) suna farin ciki da abin da aka saukar maka; akwai kuma wasu daga qungiyoyi waxanda suke musun wani sashi nasa. Ka ce: “Ni dai an umarce ni ne kawai da in bauta wa Allah, kada kuma in tara wani abu da Shi. Kuma zuwa gare Shi kawai nake kira, wurinsa ne kawai kuma makomata.”
وَكَذَٰلِكَ أَنزَلۡنَٰهُ حُكۡمًا عَرَبِيّٗاۚ وَلَئِنِ ٱتَّبَعۡتَ أَهۡوَآءَهُم بَعۡدَ مَا جَآءَكَ مِنَ ٱلۡعِلۡمِ مَا لَكَ مِنَ ٱللَّهِ مِن وَلِيّٖ وَلَا وَاقٖ
Kamar haka Muka saukar da shi (Alqur’ani), ya zama hukunci, da harshen Larabci. Lalle kuma idan ka bi son ransu bayan abin da ya zo maka na ilimi, to ba ka da wani majivinci ko mai kariya daga (azabar) Allah
وَلَقَدۡ أَرۡسَلۡنَا رُسُلٗا مِّن قَبۡلِكَ وَجَعَلۡنَا لَهُمۡ أَزۡوَٰجٗا وَذُرِّيَّةٗۚ وَمَا كَانَ لِرَسُولٍ أَن يَأۡتِيَ بِـَٔايَةٍ إِلَّا بِإِذۡنِ ٱللَّهِۗ لِكُلِّ أَجَلٖ كِتَابٞ
Haqiqa kuma Mun aiko manzanni a gabaninka, Muka kuma ba su matan aure da zurriya. Bai kuma kamata ba ga wani annabi ya zo da wata aya (da za a neme shi da ya kawo ta) sai da izinin Allah. Kuma kowane lokaci yana nan a rubuce
يَمۡحُواْ ٱللَّهُ مَا يَشَآءُ وَيُثۡبِتُۖ وَعِندَهُۥٓ أُمُّ ٱلۡكِتَٰبِ
Allah Yana shafe abin da ya ga dama, Yana kuma tabbatar (da abin da ya ga dama); kuma a wurinsa asalin littafi yake[1]
1- Watau Lauhul Mahfuzu, littafin da Allah ya rubuta komai a cikinsa.
وَإِن مَّا نُرِيَنَّكَ بَعۡضَ ٱلَّذِي نَعِدُهُمۡ أَوۡ نَتَوَفَّيَنَّكَ فَإِنَّمَا عَلَيۡكَ ٱلۡبَلَٰغُ وَعَلَيۡنَا ٱلۡحِسَابُ
Ko dai Mu nuna maka irin sashin abin da Muke yi musu gargaxi da aukuwarsa, ko kuma Mu karvi ranka (kafin lokacin), abin da yake kanka kawai shi ne isar da aike, Mu kuma hisabi yana a kanmu
أَوَلَمۡ يَرَوۡاْ أَنَّا نَأۡتِي ٱلۡأَرۡضَ نَنقُصُهَا مِنۡ أَطۡرَافِهَاۚ وَٱللَّهُ يَحۡكُمُ لَا مُعَقِّبَ لِحُكۡمِهِۦۚ وَهُوَ سَرِيعُ ٱلۡحِسَابِ
Yanzu ba sa ganin cewa Muna zaike wa qasa Muna ta cinye iyakokinta[1]? Allah ne Mai yin hukunci, babu kuma mai yin gyara ga hukuncinsa. Shi ne kuma Mai saurin yin hisabi
1- Watau Musulmi suna ta samun nasara a kansu, suna ta cinye garuruwansu da yaqi.
وَقَدۡ مَكَرَ ٱلَّذِينَ مِن قَبۡلِهِمۡ فَلِلَّهِ ٱلۡمَكۡرُ جَمِيعٗاۖ يَعۡلَمُ مَا تَكۡسِبُ كُلُّ نَفۡسٖۗ وَسَيَعۡلَمُ ٱلۡكُفَّـٰرُ لِمَنۡ عُقۡبَى ٱلدَّارِ
Haqiqa kuma waxanda suke gabaninsu sun qulla makirci, (sakamakon) qulle-qulle dukkaninsa ga Allah yake; Yana sane da abin da kowane rai yake aikatawa. Ba da daxewa ba kuma kafirai za su san wane ne mai kyakkyawan gidan (qarshe)
وَيَقُولُ ٱلَّذِينَ كَفَرُواْ لَسۡتَ مُرۡسَلٗاۚ قُلۡ كَفَىٰ بِٱللَّهِ شَهِيدَۢا بَيۡنِي وَبَيۡنَكُمۡ وَمَنۡ عِندَهُۥ عِلۡمُ ٱلۡكِتَٰبِ
Kafirai kuma suna cewa: “Kai ba manzo ba ne.” Ka ce (da su): “Allah Ya isa shaida tsakanina da ku, da kuma wanda yake da ilimin Littafi[1].”
1- Watau malaman Ahlulkitabi waxanda suka musulunta suka shaida da manzancinsa, suka yi imani da shi.
الٓرۚ كِتَٰبٌ أَنزَلۡنَٰهُ إِلَيۡكَ لِتُخۡرِجَ ٱلنَّاسَ مِنَ ٱلظُّلُمَٰتِ إِلَى ٱلنُّورِ بِإِذۡنِ رَبِّهِمۡ إِلَىٰ صِرَٰطِ ٱلۡعَزِيزِ ٱلۡحَمِيدِ
ALIF LAM RA[1]. Littafi ne da Muka saukar maka da shi, don ka fitar da mutane daga duffai zuwa ga haske, da izinin Ubangijinsu zuwa ga tafarkin (Allah) Mabuwayi, Abin godiya
1- Duba Suratul Baqara aya ta 1, hashiya ta 8.
ٱللَّهِ ٱلَّذِي لَهُۥ مَا فِي ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَمَا فِي ٱلۡأَرۡضِۗ وَوَيۡلٞ لِّلۡكَٰفِرِينَ مِنۡ عَذَابٖ شَدِيدٍ
(Watau) Allah, Wanda abin da yake cikin sammai da na cikin qasa duka nasa ne. Bone na wata azaba mai tsanani kuma ya tabbatta ga kafirai
ٱلَّذِينَ يَسۡتَحِبُّونَ ٱلۡحَيَوٰةَ ٱلدُّنۡيَا عَلَى ٱلۡأٓخِرَةِ وَيَصُدُّونَ عَن سَبِيلِ ٱللَّهِ وَيَبۡغُونَهَا عِوَجًاۚ أُوْلَـٰٓئِكَ فِي ضَلَٰلِۭ بَعِيدٖ
Waxanda suke fifita son rayuwar duniya a kan lahira, suke kuma hanawa (a bi) hanyar Allah, kuma suke neman ta zama karkatacciya. To waxannan suna cikin vata mai nisa
وَمَآ أَرۡسَلۡنَا مِن رَّسُولٍ إِلَّا بِلِسَانِ قَوۡمِهِۦ لِيُبَيِّنَ لَهُمۡۖ فَيُضِلُّ ٱللَّهُ مَن يَشَآءُ وَيَهۡدِي مَن يَشَآءُۚ وَهُوَ ٱلۡعَزِيزُ ٱلۡحَكِيمُ
Ba Mu tava aiko wani manzo ba kuwa sai da harshen mutanensa don ya yi musu bayani; sannan Allah Yana vatar da wanda ya ga dama, ya kuma shiryar da wanda ya ga dama. Shi ne kuwa Mabuwayi, Mai hikima
وَلَقَدۡ أَرۡسَلۡنَا مُوسَىٰ بِـَٔايَٰتِنَآ أَنۡ أَخۡرِجۡ قَوۡمَكَ مِنَ ٱلظُّلُمَٰتِ إِلَى ٱلنُّورِ وَذَكِّرۡهُم بِأَيَّىٰمِ ٱللَّهِۚ إِنَّ فِي ذَٰلِكَ لَأٓيَٰتٖ لِّكُلِّ صَبَّارٖ شَكُورٖ
Haqiqa kuma Mun aiko Musa da ayoyinmu cewa: “Ka fitar da mutananka daga duffai zuwa ga haske, kuma ka tunatar da su ni’imomin Allah (da ya yi musu).” Lalle game da wannan da akwai ayoyi ga duk wani mai yawan haquri, mai yawan godiya
وَإِذۡ قَالَ مُوسَىٰ لِقَوۡمِهِ ٱذۡكُرُواْ نِعۡمَةَ ٱللَّهِ عَلَيۡكُمۡ إِذۡ أَنجَىٰكُم مِّنۡ ءَالِ فِرۡعَوۡنَ يَسُومُونَكُمۡ سُوٓءَ ٱلۡعَذَابِ وَيُذَبِّحُونَ أَبۡنَآءَكُمۡ وَيَسۡتَحۡيُونَ نِسَآءَكُمۡۚ وَفِي ذَٰلِكُم بَلَآءٞ مِّن رَّبِّكُمۡ عَظِيمٞ
Kuma (ka tuna) lokacin da Musa ya ce da mutanensa: “Ku tuna ni’imar Allah a gare ku lokacin da Ya tserar da ku daga mutanen Fir’auna, suna gana muku azaba, suna kuma yanyanka ‘ya’yanku, kuma suna raya matayenku. A game da wannan da akwai bala’i mai girma daga Ubangijinku
وَإِذۡ تَأَذَّنَ رَبُّكُمۡ لَئِن شَكَرۡتُمۡ لَأَزِيدَنَّكُمۡۖ وَلَئِن كَفَرۡتُمۡ إِنَّ عَذَابِي لَشَدِيدٞ
“Kuma (ku tuna) lokacin da Ubangijinku ya sanar da ku: “Lalle idan kuka gode wa (ni’imata) tabbas zan qara muku; idan kuwa kuka butulce, to lalle azabata tabbas mai tsanani ce.”
وَقَالَ مُوسَىٰٓ إِن تَكۡفُرُوٓاْ أَنتُمۡ وَمَن فِي ٱلۡأَرۡضِ جَمِيعٗا فَإِنَّ ٱللَّهَ لَغَنِيٌّ حَمِيدٌ
Musa kuma ya ce: “Idan kuka kafirce, ku da waxanda suke a bayan qasa baki xaya, to lalle Allah tabbas Mawadaci ne, Sha-yabo.”
أَلَمۡ يَأۡتِكُمۡ نَبَؤُاْ ٱلَّذِينَ مِن قَبۡلِكُمۡ قَوۡمِ نُوحٖ وَعَادٖ وَثَمُودَ وَٱلَّذِينَ مِنۢ بَعۡدِهِمۡ لَا يَعۡلَمُهُمۡ إِلَّا ٱللَّهُۚ جَآءَتۡهُمۡ رُسُلُهُم بِٱلۡبَيِّنَٰتِ فَرَدُّوٓاْ أَيۡدِيَهُمۡ فِيٓ أَفۡوَٰهِهِمۡ وَقَالُوٓاْ إِنَّا كَفَرۡنَا بِمَآ أُرۡسِلۡتُم بِهِۦ وَإِنَّا لَفِي شَكّٖ مِّمَّا تَدۡعُونَنَآ إِلَيۡهِ مُرِيبٖ
Wai yanzu labarin waxanda suka gabace ku bai zo muku ba na mutanen Nuhu da Adawa da Samudawa da waxanda (suka zo) daga bayansu? Ba wanda ya san iyakarsu sai Allah. Manzanninsu sun zo musu da hujjoji bayyanannu, amma sai suka riqa cizon hannayensu (saboda haushi), suka kuma ce: “Lalle mu kam mun kafirta da abin da aka aiko ku da shi, lalle kuma muna cikin matuqar shakka game abin da kuke kiran mu zuwa gare shi.”
۞قَالَتۡ رُسُلُهُمۡ أَفِي ٱللَّهِ شَكّٞ فَاطِرِ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِۖ يَدۡعُوكُمۡ لِيَغۡفِرَ لَكُم مِّن ذُنُوبِكُمۡ وَيُؤَخِّرَكُمۡ إِلَىٰٓ أَجَلٖ مُّسَمّٗىۚ قَالُوٓاْ إِنۡ أَنتُمۡ إِلَّا بَشَرٞ مِّثۡلُنَا تُرِيدُونَ أَن تَصُدُّونَا عَمَّا كَانَ يَعۡبُدُ ءَابَآؤُنَا فَأۡتُونَا بِسُلۡطَٰنٖ مُّبِينٖ
Mazanninsu suka ce: “Yanzu kuwa ashe akwai wata shakka game da Allah, Maqagin sammai da qasa? Yana kiran ku ne don ya gafarta muku zunubanku kuma ya saurara muku har zuwa wani lokaci qayyadajje.” Suka ce: “Ku ba wasu ba ne daban in ban da mutane kamar mu, kuna so ne ku hana mu bin abin da iyanenmu suka kasance suna bauta wa, to sai ku kawo mana hujjoji bayyanannu.”
قَالَتۡ لَهُمۡ رُسُلُهُمۡ إِن نَّحۡنُ إِلَّا بَشَرٞ مِّثۡلُكُمۡ وَلَٰكِنَّ ٱللَّهَ يَمُنُّ عَلَىٰ مَن يَشَآءُ مِنۡ عِبَادِهِۦۖ وَمَا كَانَ لَنَآ أَن نَّأۡتِيَكُم بِسُلۡطَٰنٍ إِلَّا بِإِذۡنِ ٱللَّهِۚ وَعَلَى ٱللَّهِ فَلۡيَتَوَكَّلِ ٱلۡمُؤۡمِنُونَ
Manzanninsu suka ce: “Mu ba kowa ba ne in ban da mutane kamarku, sai dai Allah Yana yin baiwa ga wanda Ya ga dama ne daga bayinsa, kuma ba zai yiwu ba a gare mu mu zo muku da wata hujja sai dai da izinin Allah. Muminai kuwa lalle su dogara ga Allah kawai
وَمَا لَنَآ أَلَّا نَتَوَكَّلَ عَلَى ٱللَّهِ وَقَدۡ هَدَىٰنَا سُبُلَنَاۚ وَلَنَصۡبِرَنَّ عَلَىٰ مَآ ءَاذَيۡتُمُونَاۚ وَعَلَى ٱللَّهِ فَلۡيَتَوَكَّلِ ٱلۡمُتَوَكِّلُونَ
“Kuma me zai hana mu mu dogara ga Allah, alhali kuwa haqiqa Ya shiryar da mu hanyoyinmu? Lalle kuwa tabbas za mu yi haquri bisa irin cutar mu da kuka yi. Masu dogaro kuma sai su dogara ga Allah kaxai.”
وَقَالَ ٱلَّذِينَ كَفَرُواْ لِرُسُلِهِمۡ لَنُخۡرِجَنَّكُم مِّنۡ أَرۡضِنَآ أَوۡ لَتَعُودُنَّ فِي مِلَّتِنَاۖ فَأَوۡحَىٰٓ إِلَيۡهِمۡ رَبُّهُمۡ لَنُهۡلِكَنَّ ٱلظَّـٰلِمِينَ
Waxanda suka kafirta kuma suka ce da manzanninsu: “Lalle ba makawa za mu fitar da ku daga qasarmu, ko kuwa lalle ku komo cikin addininmu. Sai Ubangijinsu ya aiko musu cewa: “Lalle za Mu hallaka azzalumai
وَلَنُسۡكِنَنَّكُمُ ٱلۡأَرۡضَ مِنۢ بَعۡدِهِمۡۚ ذَٰلِكَ لِمَنۡ خَافَ مَقَامِي وَخَافَ وَعِيدِ
“Kuma tabbas za mu zaunar da ku qasar (tasu) a bayansu. Wannan kuwa sai ga wanda ya ji tsoron tsayuwa a gabana ya kuma ji tsoron narkona.”
وَٱسۡتَفۡتَحُواْ وَخَابَ كُلُّ جَبَّارٍ عَنِيدٖ
Sai kuma (manzannin) suka nemi nasarar (Allah), kuma (a qarshenta) duk wani mai nuna isa mai taurin kai ya hallaka
مِّن وَرَآئِهِۦ جَهَنَّمُ وَيُسۡقَىٰ مِن مَّآءٖ صَدِيدٖ
A gabansa Jahannama ce (take jiran sa), za a kuma shayar da shi ruwan mugunya
يَتَجَرَّعُهُۥ وَلَا يَكَادُ يُسِيغُهُۥ وَيَأۡتِيهِ ٱلۡمَوۡتُ مِن كُلِّ مَكَانٖ وَمَا هُوَ بِمَيِّتٖۖ وَمِن وَرَآئِهِۦ عَذَابٌ غَلِيظٞ
Yana kwankwaxar sa, ba kuwa zai ji daxin haxiyarsa ba, mutuwa kuma za ta zo masa ko ta ina, ba kuwa zai mutu ba; kuma a gabansa ga azaba mai kauri
مَّثَلُ ٱلَّذِينَ كَفَرُواْ بِرَبِّهِمۡۖ أَعۡمَٰلُهُمۡ كَرَمَادٍ ٱشۡتَدَّتۡ بِهِ ٱلرِّيحُ فِي يَوۡمٍ عَاصِفٖۖ لَّا يَقۡدِرُونَ مِمَّا كَسَبُواْ عَلَىٰ شَيۡءٖۚ ذَٰلِكَ هُوَ ٱلضَّلَٰلُ ٱلۡبَعِيدُ
Misalin waxanda suka kafirce wa Ubangijnsu; ayyukansu sun yi kama da toka wadda iska mai tsananin qarfi ta kwasa a wata rana mai guguwa; ba za su sami iko a kan komai ba dangane da abin da suka aikata (na kirki). Wannan shi ne vata mai nisa