يَـٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ لِمَ تَقُولُونَ مَا لَا تَفۡعَلُونَ
Ya ku waxanda suka yi imani, don me kuke faxar abin da ba kwa aikatawa?
كَبُرَ مَقۡتًا عِندَ ٱللَّهِ أَن تَقُولُواْ مَا لَا تَفۡعَلُونَ
Ya isa babban abin qi a wurin Allah, ku riqa faxin abin da ba kwa aikatawa
إِنَّ ٱللَّهَ يُحِبُّ ٱلَّذِينَ يُقَٰتِلُونَ فِي سَبِيلِهِۦ صَفّٗا كَأَنَّهُم بُنۡيَٰنٞ مَّرۡصُوصٞ
Lalle Allah Yana son waxanda suke yin yaqi dominsa sahu-sahu kai ka ce su gini ne wanda yake xamfare da juna
وَإِذۡ قَالَ مُوسَىٰ لِقَوۡمِهِۦ يَٰقَوۡمِ لِمَ تُؤۡذُونَنِي وَقَد تَّعۡلَمُونَ أَنِّي رَسُولُ ٱللَّهِ إِلَيۡكُمۡۖ فَلَمَّا زَاغُوٓاْ أَزَاغَ ٱللَّهُ قُلُوبَهُمۡۚ وَٱللَّهُ لَا يَهۡدِي ٱلۡقَوۡمَ ٱلۡفَٰسِقِينَ
Kuma (ka tuna) lokacin da Musa ya ce da mutanensa: “Ya ku mutanena, don me kuke cuta ta, alhali kuma kun san cewa lalle ni Manzon Allah ne zuwa gare ku?” To lokacin da suka kauce sai Allah ya kautar da zukatansu. Allah kuma ba ya shiryar da mutane fasiqai
وَإِذۡ قَالَ عِيسَى ٱبۡنُ مَرۡيَمَ يَٰبَنِيٓ إِسۡرَـٰٓءِيلَ إِنِّي رَسُولُ ٱللَّهِ إِلَيۡكُم مُّصَدِّقٗا لِّمَا بَيۡنَ يَدَيَّ مِنَ ٱلتَّوۡرَىٰةِ وَمُبَشِّرَۢا بِرَسُولٖ يَأۡتِي مِنۢ بَعۡدِي ٱسۡمُهُۥٓ أَحۡمَدُۖ فَلَمَّا جَآءَهُم بِٱلۡبَيِّنَٰتِ قَالُواْ هَٰذَا سِحۡرٞ مُّبِينٞ
Kuma (ka tuna) lokacin da Isa xan Maryamu ya ce: “Ya ku ‘ya’yan Isra’ila, lalle ni Manzon Allah ne zuwa gare ku, mai gaskata abin da yake gabanina na Attaura, kuma mai albishir da wani manzo da zai zo bayana, sunansa Ahmadu[1].” To lokacin da ya zo musu da (ayoyi) bayyanannu sai suka ce: “Wannan sihiri ne mabayyani.”
1- Ahmad, xaya ne daga cikin sunayen Annabi Muhammad ().
وَمَنۡ أَظۡلَمُ مِمَّنِ ٱفۡتَرَىٰ عَلَى ٱللَّهِ ٱلۡكَذِبَ وَهُوَ يُدۡعَىٰٓ إِلَى ٱلۡإِسۡلَٰمِۚ وَٱللَّهُ لَا يَهۡدِي ٱلۡقَوۡمَ ٱلظَّـٰلِمِينَ
Ba wanda kuma ya fi zalunci kamar wanda ya qaga wa Allah qarya, alhali kuwa shi ana kiran sa zuwa Musulunci. Allah kuma ba Ya shiryar da mutane azzalumai
يُرِيدُونَ لِيُطۡفِـُٔواْ نُورَ ٱللَّهِ بِأَفۡوَٰهِهِمۡ وَٱللَّهُ مُتِمُّ نُورِهِۦ وَلَوۡ كَرِهَ ٱلۡكَٰفِرُونَ
Suna nufin su dusashe hasken Allah da bakunansu, Allah kuwa Mai cika haskensa ne ko da kafirai sun qi
هُوَ ٱلَّذِيٓ أَرۡسَلَ رَسُولَهُۥ بِٱلۡهُدَىٰ وَدِينِ ٱلۡحَقِّ لِيُظۡهِرَهُۥ عَلَى ٱلدِّينِ كُلِّهِۦ وَلَوۡ كَرِهَ ٱلۡمُشۡرِكُونَ
Shi ne Wanda Ya aiko Manzonsa da shiriya da kuma addinin gaskiya don Ya xora shi a kan kowane addini, ko da kuwa mushirikai sun qi
يَـٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ هَلۡ أَدُلُّكُمۡ عَلَىٰ تِجَٰرَةٖ تُنجِيكُم مِّنۡ عَذَابٍ أَلِيمٖ
Ya ku waxanda suka yi imani, yanzu ba Na nuna muku ku wani ciniki da zai tserar da ku daga azaba mai raxaxi ba?
تُؤۡمِنُونَ بِٱللَّهِ وَرَسُولِهِۦ وَتُجَٰهِدُونَ فِي سَبِيلِ ٱللَّهِ بِأَمۡوَٰلِكُمۡ وَأَنفُسِكُمۡۚ ذَٰلِكُمۡ خَيۡرٞ لَّكُمۡ إِن كُنتُمۡ تَعۡلَمُونَ
(Shi ne) ku yi imani da Allah da Manzonsa ku kuma yi jihadi don Allah da dukiyoyinku da rayukanku. Wannan shi ne ya fiye muku alheri, idan kun kasance kuna sane (da haka)
يَغۡفِرۡ لَكُمۡ ذُنُوبَكُمۡ وَيُدۡخِلۡكُمۡ جَنَّـٰتٖ تَجۡرِي مِن تَحۡتِهَا ٱلۡأَنۡهَٰرُ وَمَسَٰكِنَ طَيِّبَةٗ فِي جَنَّـٰتِ عَدۡنٖۚ ذَٰلِكَ ٱلۡفَوۡزُ ٱلۡعَظِيمُ
(Idan kun yi haka) zai gafarta muku zunubanku Ya kuma shigar da ku gidajen Aljanna (waxanda) qoramu suke gudana ta qarqashinsu da kuma wuraren zama masu kyau, a cikin gidajen Aljanna na dawwama. Wannan shi ne babban rabo
وَأُخۡرَىٰ تُحِبُّونَهَاۖ نَصۡرٞ مِّنَ ٱللَّهِ وَفَتۡحٞ قَرِيبٞۗ وَبَشِّرِ ٱلۡمُؤۡمِنِينَ
Da kuma wata xayar da kuke so; (watau) nasara daga Allah da kuma buxi a kusa. Ka kuma yi wa muminai albishir
يَـٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ كُونُوٓاْ أَنصَارَ ٱللَّهِ كَمَا قَالَ عِيسَى ٱبۡنُ مَرۡيَمَ لِلۡحَوَارِيِّـۧنَ مَنۡ أَنصَارِيٓ إِلَى ٱللَّهِۖ قَالَ ٱلۡحَوَارِيُّونَ نَحۡنُ أَنصَارُ ٱللَّهِۖ فَـَٔامَنَت طَّآئِفَةٞ مِّنۢ بَنِيٓ إِسۡرَـٰٓءِيلَ وَكَفَرَت طَّآئِفَةٞۖ فَأَيَّدۡنَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ عَلَىٰ عَدُوِّهِمۡ فَأَصۡبَحُواْ ظَٰهِرِينَ
Ya ku waxanda suka yi imani, ku zama masu taimaka wa (addinin) Allah, kamar yadda Isa xan Maryamu ya ce da Hawariyawa[1]: “Su wane ne masu taimaka mini zuwa ga Allah?” Hawariyawan suka ce: “Mu ne masu taimaka wa Allah.” Sai wata qungiya daga Bani Isra’ila suka yi imani, wata qungiya kuma ta kafirta, sai Muka qarfafa waxanda suka yi imani a kan maqiyansu, sai suka wayi gari suna masu cin nasara
1- Su ne almajiransa da suka yi imani da shi.
يُسَبِّحُ لِلَّهِ مَا فِي ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَمَا فِي ٱلۡأَرۡضِ ٱلۡمَلِكِ ٱلۡقُدُّوسِ ٱلۡعَزِيزِ ٱلۡحَكِيمِ
Duk abin da yake cikin sammai da abin da yake cikin qasa yana yin tasbihi ga Allah Sarki, Tsarkakakke, Mabuwayi, Mai hikima
هُوَ ٱلَّذِي بَعَثَ فِي ٱلۡأُمِّيِّـۧنَ رَسُولٗا مِّنۡهُمۡ يَتۡلُواْ عَلَيۡهِمۡ ءَايَٰتِهِۦ وَيُزَكِّيهِمۡ وَيُعَلِّمُهُمُ ٱلۡكِتَٰبَ وَٱلۡحِكۡمَةَ وَإِن كَانُواْ مِن قَبۡلُ لَفِي ضَلَٰلٖ مُّبِينٖ
Shi ne wanda Ya aiko wa (Larabawa) ummiyyai (watau waxanda ba sa karatu da rubutu) Manzo daga cikinsu, yana karanta musu ayoyinsa, yana kuma tsarkake su, kuma yana sanar da su Alqur’ani da hikima, ko da yake a da can sun kasance cikin vata mabayyani
وَءَاخَرِينَ مِنۡهُمۡ لَمَّا يَلۡحَقُواْ بِهِمۡۚ وَهُوَ ٱلۡعَزِيزُ ٱلۡحَكِيمُ
Da kuma wasunsu (waxanda) tukuna ba su riske su ba[1]. Shi ne kuwa Mabuwayi, Mai hikima
1- Watau wasu al’ummu daban waxanda su ma saqon zai kai gare su nan gaba.
ذَٰلِكَ فَضۡلُ ٱللَّهِ يُؤۡتِيهِ مَن يَشَآءُۚ وَٱللَّهُ ذُو ٱلۡفَضۡلِ ٱلۡعَظِيمِ
Wannan falala ce daga Allah, Yana bayar da ita ga wanda Ya ga dama. Allah kuwa Ma’abocin babbar falala ne
مَثَلُ ٱلَّذِينَ حُمِّلُواْ ٱلتَّوۡرَىٰةَ ثُمَّ لَمۡ يَحۡمِلُوهَا كَمَثَلِ ٱلۡحِمَارِ يَحۡمِلُ أَسۡفَارَۢاۚ بِئۡسَ مَثَلُ ٱلۡقَوۡمِ ٱلَّذِينَ كَذَّبُواْ بِـَٔايَٰتِ ٱللَّهِۚ وَٱللَّهُ لَا يَهۡدِي ٱلۡقَوۡمَ ٱلظَّـٰلِمِينَ
Misalin waxanda aka xora wa Attaura[1] sannan ba su xauke ta ba, kamar misalin jaki ne da yake xauke da wagagen littattafai. Misalin mutanen da suka qaryata ayoyin Allah ya munana. Allah kuwa ba Ya shiryar da mutane azzalumai
1- Su ne malaman Yahudawa da Allah ya sanar da su Attaura; ya umarce su su yi aiki da ita.
قُلۡ يَـٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ هَادُوٓاْ إِن زَعَمۡتُمۡ أَنَّكُمۡ أَوۡلِيَآءُ لِلَّهِ مِن دُونِ ٱلنَّاسِ فَتَمَنَّوُاْ ٱلۡمَوۡتَ إِن كُنتُمۡ صَٰدِقِينَ
Ka ce: “Ya ku waxanda suka zama Yahudawa, idan kun riya cewa ku ne masoyan Allah ban da sauran mutane, to ku yi burin mutuwa, idan kun kasance masu gaskiya ne.”
وَلَا يَتَمَنَّوۡنَهُۥٓ أَبَدَۢا بِمَا قَدَّمَتۡ أَيۡدِيهِمۡۚ وَٱللَّهُ عَلِيمُۢ بِٱلظَّـٰلِمِينَ
Ba za su yi burin ta ba har abada saboda abin da hannayensu suka gabatar. Allah kuwa Masanin azzalumai ne
قُلۡ إِنَّ ٱلۡمَوۡتَ ٱلَّذِي تَفِرُّونَ مِنۡهُ فَإِنَّهُۥ مُلَٰقِيكُمۡۖ ثُمَّ تُرَدُّونَ إِلَىٰ عَٰلِمِ ٱلۡغَيۡبِ وَٱلشَّهَٰدَةِ فَيُنَبِّئُكُم بِمَا كُنتُمۡ تَعۡمَلُونَ
Ka ce (da su): “Lalle ita mutuwar da kuke gudun ta, lalle za ta haxu da ku; sannan za a mayar da ku wurin Masanin voye da sarari, sannan Ya ba ku labarin abin da kuka kasance kuna aikatawa.”
يَـٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوٓاْ إِذَا نُودِيَ لِلصَّلَوٰةِ مِن يَوۡمِ ٱلۡجُمُعَةِ فَٱسۡعَوۡاْ إِلَىٰ ذِكۡرِ ٱللَّهِ وَذَرُواْ ٱلۡبَيۡعَۚ ذَٰلِكُمۡ خَيۡرٞ لَّكُمۡ إِن كُنتُمۡ تَعۡلَمُونَ
Ya ku waxanda suka yi imani, idan aka kira salla ranar Juma’a[1] sai ku tafi zuwa zikirin Allah, kuma ku bar ciniki. Wannan (shi) ya fi muku alheri, idan kun kasance kuna sane (da haka)
1- Watau kiran salla bayan liman ya hau kan mimbari. Wajibi a lokacin duk wani Musulmi ya bar duk wata sabga ta saye da sayarwa.
فَإِذَا قُضِيَتِ ٱلصَّلَوٰةُ فَٱنتَشِرُواْ فِي ٱلۡأَرۡضِ وَٱبۡتَغُواْ مِن فَضۡلِ ٱللَّهِ وَٱذۡكُرُواْ ٱللَّهَ كَثِيرٗا لَّعَلَّكُمۡ تُفۡلِحُونَ
Sannan idan aka gama salla sai ku bazu a bayan qasa ku kuma nema daga falalar Allah, kuma ku ambaci Allah da yawa don ku rabauta
وَإِذَا رَأَوۡاْ تِجَٰرَةً أَوۡ لَهۡوًا ٱنفَضُّوٓاْ إِلَيۡهَا وَتَرَكُوكَ قَآئِمٗاۚ قُلۡ مَا عِندَ ٱللَّهِ خَيۡرٞ مِّنَ ٱللَّهۡوِ وَمِنَ ٱلتِّجَٰرَةِۚ وَٱللَّهُ خَيۡرُ ٱلرَّـٰزِقِينَ
Idan kuma suka ga kasuwanci ko wasa sai su watse zuwa gare su, su bar ka a tsaye (kana huxuba). Ka ce: “Abin da yake wurin Allah ya fi wasa da ciniki. Kuma Allah Fiyayyen masu arzutawa ne.”
إِذَا جَآءَكَ ٱلۡمُنَٰفِقُونَ قَالُواْ نَشۡهَدُ إِنَّكَ لَرَسُولُ ٱللَّهِۗ وَٱللَّهُ يَعۡلَمُ إِنَّكَ لَرَسُولُهُۥ وَٱللَّهُ يَشۡهَدُ إِنَّ ٱلۡمُنَٰفِقِينَ لَكَٰذِبُونَ
Idan munafukai suka zo maka sai suka ce: “Muna shaidawa cewa lalle kai Manzon Allah ne.” Allah kuma Yana sane da cewa kai tabbas Manzonsa ne, kuma Allah Yana shaidawa cewa munafukai tabbas qarya suke yi
ٱتَّخَذُوٓاْ أَيۡمَٰنَهُمۡ جُنَّةٗ فَصَدُّواْ عَن سَبِيلِ ٱللَّهِۚ إِنَّهُمۡ سَآءَ مَا كَانُواْ يَعۡمَلُونَ
Sun xauki rantse-rantsensu garkuwa, saboda haka suka kange (mutane) daga hanyar Allah. Lalle su abin da suka kasance suna aikatawa ya munana
ذَٰلِكَ بِأَنَّهُمۡ ءَامَنُواْ ثُمَّ كَفَرُواْ فَطُبِعَ عَلَىٰ قُلُوبِهِمۡ فَهُمۡ لَا يَفۡقَهُونَ
Wannan kuwa saboda cewa sun yi imani sannan suka kafirta, sai aka rufe zukatansu, saboda haka su ba sa fahimta
۞وَإِذَا رَأَيۡتَهُمۡ تُعۡجِبُكَ أَجۡسَامُهُمۡۖ وَإِن يَقُولُواْ تَسۡمَعۡ لِقَوۡلِهِمۡۖ كَأَنَّهُمۡ خُشُبٞ مُّسَنَّدَةٞۖ يَحۡسَبُونَ كُلَّ صَيۡحَةٍ عَلَيۡهِمۡۚ هُمُ ٱلۡعَدُوُّ فَٱحۡذَرۡهُمۡۚ قَٰتَلَهُمُ ٱللَّهُۖ أَنَّىٰ يُؤۡفَكُونَ
Idan ka gan su sai jikkunansu su qayatar da kai; idan kuma suka yi magana za ka saurari maganarsu; kai ka ce su wasu gumaguman itatuwa ne a jingine[1]; suna tsammanin kowace irin kururuwa saboda su ne. Su ne maqiya, saboda haka ka yi hattara da su. Allah kuma Ya la’ance su; ta ina ne ake karkatar da su?
1- Watau dai wannan cika fuskar duka fankanfayau ne, ba sa fahimtar komai daga bayanan da Annabi () yake yi.
وَإِذَا قِيلَ لَهُمۡ تَعَالَوۡاْ يَسۡتَغۡفِرۡ لَكُمۡ رَسُولُ ٱللَّهِ لَوَّوۡاْ رُءُوسَهُمۡ وَرَأَيۡتَهُمۡ يَصُدُّونَ وَهُم مُّسۡتَكۡبِرُونَ
Idan kuma aka ce da su: “Ku zo Manzon Allah ya nema muku gafara,” sai su kau da kansu, sai ka gan su suna bijirewa, alhalin suna masu girman kai
سَوَآءٌ عَلَيۡهِمۡ أَسۡتَغۡفَرۡتَ لَهُمۡ أَمۡ لَمۡ تَسۡتَغۡفِرۡ لَهُمۡ لَن يَغۡفِرَ ٱللَّهُ لَهُمۡۚ إِنَّ ٱللَّهَ لَا يَهۡدِي ٱلۡقَوۡمَ ٱلۡفَٰسِقِينَ
Duk xaya ne game da su, ka nema musu gafara, ko ba ka nema musu gafara ba, Allah ba zai gafarta musu ba har abada. Lalle Allah ba Ya shiryar da mutane fasiqai