ءَاخِذِينَ مَآ ءَاتَىٰهُمۡ رَبُّهُمۡۚ إِنَّهُمۡ كَانُواْ قَبۡلَ ذَٰلِكَ مُحۡسِنِينَ
Suna masu kwasar abin da Ubangijinsu Ya ba su. Lalle su sun zamanto kafin wannan (ranar) masu kyautata ayyuka ne
Compartir :
كَانُواْ قَلِيلٗا مِّنَ ٱلَّيۡلِ مَا يَهۡجَعُونَ
Sun kasance kaxan ne na dare suke bacci[1]
1- Watau sun kasance masu yawaita sallar dare.
وَبِٱلۡأَسۡحَارِ هُمۡ يَسۡتَغۡفِرُونَ
A gefin asuba kuma su suna neman gafara
وَفِيٓ أَمۡوَٰلِهِمۡ حَقّٞ لِّلسَّآئِلِ وَٱلۡمَحۡرُومِ
A cikin dukiyoyinsu kuma akwai wani haqqi na mai bara da mai kamewa daga yin ta
وَفِي ٱلۡأَرۡضِ ءَايَٰتٞ لِّلۡمُوقِنِينَ
A cikin qasa kuma akwai ayoyi ga masu sakankancewa
وَفِيٓ أَنفُسِكُمۡۚ أَفَلَا تُبۡصِرُونَ
Da kuma cikin kawunanku. Yanzu ba kwa lura ba?
وَفِي ٱلسَّمَآءِ رِزۡقُكُمۡ وَمَا تُوعَدُونَ
A cikin sammai kuma akwai arzikinku da kuma abin da aka yi muku alkawarinsa
فَوَرَبِّ ٱلسَّمَآءِ وَٱلۡأَرۡضِ إِنَّهُۥ لَحَقّٞ مِّثۡلَ مَآ أَنَّكُمۡ تَنطِقُونَ
To na rantse da Ubangijin sammai da qasa, lalle shi (abin da ake yi muku gargaxinsa) tabbas gaskiya ne kamar dai yadda kuke yin magana
هَلۡ أَتَىٰكَ حَدِيثُ ضَيۡفِ إِبۡرَٰهِيمَ ٱلۡمُكۡرَمِينَ
Shin labarin baqin Ibrahimu masu girma[1] ya zo maka?
1- Su ne mala’iku da Allah ya aiko.
إِذۡ دَخَلُواْ عَلَيۡهِ فَقَالُواْ سَلَٰمٗاۖ قَالَ سَلَٰمٞ قَوۡمٞ مُّنكَرُونَ
Lokacin da suka shiga wurinsa sai suka ce: “Muna maka sallama;” ya ce: “Aminci ya tabbata gare ku, (ku) mutane ne da ba sanannu ba.”
فَرَاغَ إِلَىٰٓ أَهۡلِهِۦ فَجَآءَ بِعِجۡلٖ سَمِينٖ
Sai ya saxaxa da sauri zuwa ga iyalinsa, sai ya zo da wani xan maraqi mai mai
فَقَرَّبَهُۥٓ إِلَيۡهِمۡ قَالَ أَلَا تَأۡكُلُونَ
Sai ya kusanta shi gare su, ya ce: “Yanzu ba za ku ci ba?”
فَأَوۡجَسَ مِنۡهُمۡ خِيفَةٗۖ قَالُواْ لَا تَخَفۡۖ وَبَشَّرُوهُ بِغُلَٰمٍ عَلِيمٖ
(Da suka qi ci) sai ya tsorata da su, suka ce: “Kada ka tsorata;” suka kuma yi masa albishir da samun yaro mai ilimi[1]
1- Watau Annabi Ishaq ().
فَأَقۡبَلَتِ ٱمۡرَأَتُهُۥ فِي صَرَّةٖ فَصَكَّتۡ وَجۡهَهَا وَقَالَتۡ عَجُوزٌ عَقِيمٞ
Sannan sai matarsa ta gabato su cikin wata qara, sai ta mari fuskarta ta ce: “Yanzu tsohuwa bakarara (ita ce za ta haihu?)”
قَالُواْ كَذَٰلِكِ قَالَ رَبُّكِۖ إِنَّهُۥ هُوَ ٱلۡحَكِيمُ ٱلۡعَلِيمُ
Suka ce, “Kamar haka Ubangijinki Ya ce, lalle Shi Mai hikima ne, Masani.”