Capítulo: Suratun Nisa’i

Verso : 84

فَقَٰتِلۡ فِي سَبِيلِ ٱللَّهِ لَا تُكَلَّفُ إِلَّا نَفۡسَكَۚ وَحَرِّضِ ٱلۡمُؤۡمِنِينَۖ عَسَى ٱللَّهُ أَن يَكُفَّ بَأۡسَ ٱلَّذِينَ كَفَرُواْۚ وَٱللَّهُ أَشَدُّ بَأۡسٗا وَأَشَدُّ تَنكِيلٗا

To ka yi yaqi domin xaukaka kalmar Allah, ba a xora maka nauyin tilasta kowa ba sai kanka. Kuma ka zaburar da muminai; Allah zai dankwafe qarfin waxanda suka kafirta; kuma Allah Shi ne Mafi tsananin qarfi, kuma Mafi tsananin uquba



Capítulo: Suratun Nisa’i

Verso : 85

مَّن يَشۡفَعۡ شَفَٰعَةً حَسَنَةٗ يَكُن لَّهُۥ نَصِيبٞ مِّنۡهَاۖ وَمَن يَشۡفَعۡ شَفَٰعَةٗ سَيِّئَةٗ يَكُن لَّهُۥ كِفۡلٞ مِّنۡهَاۗ وَكَانَ ٱللَّهُ عَلَىٰ كُلِّ شَيۡءٖ مُّقِيتٗا

Duk wanda ya yi (ma wani) kyakkyawar alfarma, zai samu rabonsa na lada daga gare ta; kuma duk wanda ya yi wa wani mummunar alfarma, zai samu rabonsa na zunubi daga gare ta. Kuma Allah Ya kasance Mai kiyaye komai ne[1]


1- Watau zai yi wa kowa sakamako gwargwadon aikinsa mai kyau ko mummuna.


Capítulo: Suratun Nisa’i

Verso : 86

وَإِذَا حُيِّيتُم بِتَحِيَّةٖ فَحَيُّواْ بِأَحۡسَنَ مِنۡهَآ أَوۡ رُدُّوهَآۗ إِنَّ ٱللَّهَ كَانَ عَلَىٰ كُلِّ شَيۡءٍ حَسِيبًا

Kuma idan an gaishe ku da wata gaisuwa, to ku amsa da gaisuwar da ta fi wadda aka yi muku kyau, ko ku mayar da irinta. Lalle Allah Ya kasance Mai hisabi ne a kan kowane abu



Capítulo: Suratun Nisa’i

Verso : 87

ٱللَّهُ لَآ إِلَٰهَ إِلَّا هُوَۚ لَيَجۡمَعَنَّكُمۡ إِلَىٰ يَوۡمِ ٱلۡقِيَٰمَةِ لَا رَيۡبَ فِيهِۗ وَمَنۡ أَصۡدَقُ مِنَ ٱللَّهِ حَدِيثٗا

Allah, babu wani abin bauta wa da gaskiya sai Shi. Lalle zai tattara ku a ranar alqiyama, wadda babu kokwanto a cikinsa. Kuma wane ne ya fi Allah gaskiyar zance?