Capítulo: Suratut Tahrim

Verso : 9

يَـٰٓأَيُّهَا ٱلنَّبِيُّ جَٰهِدِ ٱلۡكُفَّارَ وَٱلۡمُنَٰفِقِينَ وَٱغۡلُظۡ عَلَيۡهِمۡۚ وَمَأۡوَىٰهُمۡ جَهَنَّمُۖ وَبِئۡسَ ٱلۡمَصِيرُ

Ya kai wannan Annabi, ka yaqi kafirai da munafukai, ka kuma tsananta musu. Makomarsu kuma Jahannama ce; makoma kuwa ta munana



Capítulo: Suratut Tahrim

Verso : 10

ضَرَبَ ٱللَّهُ مَثَلٗا لِّلَّذِينَ كَفَرُواْ ٱمۡرَأَتَ نُوحٖ وَٱمۡرَأَتَ لُوطٖۖ كَانَتَا تَحۡتَ عَبۡدَيۡنِ مِنۡ عِبَادِنَا صَٰلِحَيۡنِ فَخَانَتَاهُمَا فَلَمۡ يُغۡنِيَا عَنۡهُمَا مِنَ ٱللَّهِ شَيۡـٔٗا وَقِيلَ ٱدۡخُلَا ٱلنَّارَ مَعَ ٱلدَّـٰخِلِينَ

Allah Ya ba da wani misali ga waxanda suka kafirta da matar Nuhu da matar Luxu; sun kasance qarqashin (igiyar auren) wasu bayi su biyu salihai daga bayinmu, sai suka ha’ince su[1], saboda haka ba su wadatar musu komai ba (daga azabar) Allah, aka kuma ce: “Ku shiga wuta tare da masu shiga.”


1- Watau suka kafirce musu, suka riqa hana mutane bin addinin Allah, suka kuma riqa goyon bayan kafirai.


Capítulo: Suratut Tahrim

Verso : 11

وَضَرَبَ ٱللَّهُ مَثَلٗا لِّلَّذِينَ ءَامَنُواْ ٱمۡرَأَتَ فِرۡعَوۡنَ إِذۡ قَالَتۡ رَبِّ ٱبۡنِ لِي عِندَكَ بَيۡتٗا فِي ٱلۡجَنَّةِ وَنَجِّنِي مِن فِرۡعَوۡنَ وَعَمَلِهِۦ وَنَجِّنِي مِنَ ٱلۡقَوۡمِ ٱلظَّـٰلِمِينَ

Allah kuma Ya ba da wani misali ga waxanda suka yi imani da matar Fir’auna lokacin da ta ce: “Ya Ubangijina, Ka gina min gida a wurinka cikin Aljanna, Ka kuma tserar da ni daga Fir’auna da aikinsa, kuma Ka tserar da ni daga azzaluman mutane.”



Capítulo: Suratut Tahrim

Verso : 12

وَمَرۡيَمَ ٱبۡنَتَ عِمۡرَٰنَ ٱلَّتِيٓ أَحۡصَنَتۡ فَرۡجَهَا فَنَفَخۡنَا فِيهِ مِن رُّوحِنَا وَصَدَّقَتۡ بِكَلِمَٰتِ رَبِّهَا وَكُتُبِهِۦ وَكَانَتۡ مِنَ ٱلۡقَٰنِتِينَ

Da kuma Maryamu ‘yar Imrana wadda ta kiyaye matuncinta, sai Muka masa busa daga Ruhinmu[1], ta kuma gaskata ayoyin Ubangijinta da littattafansa, ta kuma kasance daga masu biyayya ga Allah


1- Watau Allah ya umarci Mala’ika Jibrilu () ya yi busa a gare ta.