Capítulo: Suratul Ahzab

Verso : 18

۞قَدۡ يَعۡلَمُ ٱللَّهُ ٱلۡمُعَوِّقِينَ مِنكُمۡ وَٱلۡقَآئِلِينَ لِإِخۡوَٰنِهِمۡ هَلُمَّ إِلَيۡنَاۖ وَلَا يَأۡتُونَ ٱلۡبَأۡسَ إِلَّا قَلِيلًا

Haqiqa Allah Yana sane da masu hana ruwa gudu[1] daga cikinku, da masu ce wa ‘yan’uwansu: “Ku zo wurinmu,” kuma ba sa zuwa yaqi sai kaxan


1- Su ne munafukai masu daqile Musulmi da karya musu gwiwa wajen fita yaqi.


Capítulo: Suratul Ahzab

Verso : 19

أَشِحَّةً عَلَيۡكُمۡۖ فَإِذَا جَآءَ ٱلۡخَوۡفُ رَأَيۡتَهُمۡ يَنظُرُونَ إِلَيۡكَ تَدُورُ أَعۡيُنُهُمۡ كَٱلَّذِي يُغۡشَىٰ عَلَيۡهِ مِنَ ٱلۡمَوۡتِۖ فَإِذَا ذَهَبَ ٱلۡخَوۡفُ سَلَقُوكُم بِأَلۡسِنَةٍ حِدَادٍ أَشِحَّةً عَلَى ٱلۡخَيۡرِۚ أُوْلَـٰٓئِكَ لَمۡ يُؤۡمِنُواْ فَأَحۡبَطَ ٱللَّهُ أَعۡمَٰلَهُمۡۚ وَكَانَ ذَٰلِكَ عَلَى ٱللَّهِ يَسِيرٗا

(Su ne) masu yi muku rowar (taimako); sannan idan (abin) tsoro ya zo, sai ka gan su suna duban ka idanuwansu suna jujjuyawa kamar wanda yake suman mutuwa; sannan idan tsoron ya yaye, sai su riqa cutar da ku da harsuna kaifafa, suna masu rowar alheri. Waxannan ba su yi imani ba, don haka Allah Ya lalata ayyukansu. Wannan kuwa ya kasance abu ne mai sauqi a wurin Allah



Capítulo: Suratul Ahzab

Verso : 20

يَحۡسَبُونَ ٱلۡأَحۡزَابَ لَمۡ يَذۡهَبُواْۖ وَإِن يَأۡتِ ٱلۡأَحۡزَابُ يَوَدُّواْ لَوۡ أَنَّهُم بَادُونَ فِي ٱلۡأَعۡرَابِ يَسۡـَٔلُونَ عَنۡ أَنۢبَآئِكُمۡۖ وَلَوۡ كَانُواْ فِيكُم مَّا قَٰتَلُوٓاْ إِلَّا قَلِيلٗا

Suna zaton rundunonin gangami ba su tafi ba; da a ce kuwa rundunonin na gangami za su sake dawowa to da sai su riqa burin ina ma suna can tare da mutanen qauye suna tambayar labaranku; ko ma da za su kasance a cikinku to da ba za su yi yaqi ba sai xan kaxan



Capítulo: Suratul Ahzab

Verso : 21

لَّقَدۡ كَانَ لَكُمۡ فِي رَسُولِ ٱللَّهِ أُسۡوَةٌ حَسَنَةٞ لِّمَن كَانَ يَرۡجُواْ ٱللَّهَ وَٱلۡيَوۡمَ ٱلۡأٓخِرَ وَذَكَرَ ٱللَّهَ كَثِيرٗا

Haqiqa kuna da kyakkyawan abin koyi tare da Manzon Allah, ga wanda yake yin kyakkyawan fata game da Allah da ranar lahira, ya kuma ambaci Allah da yawa



Capítulo: Suratul Ahzab

Verso : 22

وَلَمَّا رَءَا ٱلۡمُؤۡمِنُونَ ٱلۡأَحۡزَابَ قَالُواْ هَٰذَا مَا وَعَدَنَا ٱللَّهُ وَرَسُولُهُۥ وَصَدَقَ ٱللَّهُ وَرَسُولُهُۥۚ وَمَا زَادَهُمۡ إِلَّآ إِيمَٰنٗا وَتَسۡلِيمٗا

Lokacin kuwa da muminai suka ga rundunonin gangami sai suka ce: “Wannan shi ne abin da Allah da Manzonsa suka yi mana alqawari, Allah kuwa da Manzonsa sun yi gaskiya. Ba kuwa abin da (wannan) ya qara musu sai imani da miqa wuya



Capítulo: Suratul Ahzab

Verso : 23

مِّنَ ٱلۡمُؤۡمِنِينَ رِجَالٞ صَدَقُواْ مَا عَٰهَدُواْ ٱللَّهَ عَلَيۡهِۖ فَمِنۡهُم مَّن قَضَىٰ نَحۡبَهُۥ وَمِنۡهُم مَّن يَنتَظِرُۖ وَمَا بَدَّلُواْ تَبۡدِيلٗا

Akwai wasu mazaje daga muminai da suka cika abin da suka yi wa Allah alqawari da shi; akwai daga cikinsu wanda ya haxu da ajalinsa, akwai kuma daga cikinsu wanda yake sauraron (ajalin); kuma ba su yi kowace irin savawa ba (game da alqawarin)



Capítulo: Suratul Ahzab

Verso : 24

لِّيَجۡزِيَ ٱللَّهُ ٱلصَّـٰدِقِينَ بِصِدۡقِهِمۡ وَيُعَذِّبَ ٱلۡمُنَٰفِقِينَ إِن شَآءَ أَوۡ يَتُوبَ عَلَيۡهِمۡۚ إِنَّ ٱللَّهَ كَانَ غَفُورٗا رَّحِيمٗا

Don Allah Ya saka wa masu gaskiya a kan gaskiyarsu, Ya kuma azabtar da munafukai idan Ya ga dama, ko kuma Ya karvi tubarsu. Lalle Allah Ya kasance Mai gafara ne, Mai jin qai



Capítulo: Suratul Ahzab

Verso : 25

وَرَدَّ ٱللَّهُ ٱلَّذِينَ كَفَرُواْ بِغَيۡظِهِمۡ لَمۡ يَنَالُواْ خَيۡرٗاۚ وَكَفَى ٱللَّهُ ٱلۡمُؤۡمِنِينَ ٱلۡقِتَالَۚ وَكَانَ ٱللَّهُ قَوِيًّا عَزِيزٗا

Allah kuma Ya komar da waxanda suka kafirta da fushinsu ba su sami wani alheri ba. Allah kuma Ya xauke wa muminai yin yaqi. Domin kuwa Allah Ya kasance Mai qarfi ne, Mabuwayi



Capítulo: Suratul Ahzab

Verso : 26

وَأَنزَلَ ٱلَّذِينَ ظَٰهَرُوهُم مِّنۡ أَهۡلِ ٱلۡكِتَٰبِ مِن صَيَاصِيهِمۡ وَقَذَفَ فِي قُلُوبِهِمُ ٱلرُّعۡبَ فَرِيقٗا تَقۡتُلُونَ وَتَأۡسِرُونَ فَرِيقٗا

Ya kuma sauko da waxanda suka taimake su daga ma’abota littafi[1] daga ganuwoyinsu Ya kuma jefa tsoro a zukatansu, wasu jama’ar kuke kashe su kuna kuma ribace wasu jama’ar


1- Watau Yahudawan Banu Quraiza. Ya sauko da su daga ganuwoyinsu da suka tanada don kare kansu.


Capítulo: Suratul Ahzab

Verso : 27

وَأَوۡرَثَكُمۡ أَرۡضَهُمۡ وَدِيَٰرَهُمۡ وَأَمۡوَٰلَهُمۡ وَأَرۡضٗا لَّمۡ تَطَـُٔوهَاۚ وَكَانَ ٱللَّهُ عَلَىٰ كُلِّ شَيۡءٖ قَدِيرٗا

Ya kuma gadar muku qasarsu da gidajensu da dukiyoyinsu, da kuma wata qasa ma da ba ku tava taka ta ba[1]. Allah kuwa Ya kasance Mai iko ne a kan komai


1- Watau ita ce qasar Khaibar wadda Musulmi suka samu bayan shekara ta biyu da gama yaqin Ahzab.


Capítulo: Suratul Ahzab

Verso : 28

يَـٰٓأَيُّهَا ٱلنَّبِيُّ قُل لِّأَزۡوَٰجِكَ إِن كُنتُنَّ تُرِدۡنَ ٱلۡحَيَوٰةَ ٱلدُّنۡيَا وَزِينَتَهَا فَتَعَالَيۡنَ أُمَتِّعۡكُنَّ وَأُسَرِّحۡكُنَّ سَرَاحٗا جَمِيلٗا

Ya kai wannan Annabi, ka gaya wa matanka: “Idan kun kasance kuna son rayuwar duniya ne da kuma adonta, to sai ku zo in jiyar da ku daxi, in kuma sake ku kyakkyawan saki



Capítulo: Suratul Ahzab

Verso : 29

وَإِن كُنتُنَّ تُرِدۡنَ ٱللَّهَ وَرَسُولَهُۥ وَٱلدَّارَ ٱلۡأٓخِرَةَ فَإِنَّ ٱللَّهَ أَعَدَّ لِلۡمُحۡسِنَٰتِ مِنكُنَّ أَجۡرًا عَظِيمٗا

“Idan kuwa kun kasance kuna qaunar Allah ne da Manzonsa da kuma ranar lahira, to haqiqa Allah Ya tanadi lada mai girma ga masu kyautatawa daga cikinku



Capítulo: Suratul Ahzab

Verso : 30

يَٰنِسَآءَ ٱلنَّبِيِّ مَن يَأۡتِ مِنكُنَّ بِفَٰحِشَةٖ مُّبَيِّنَةٖ يُضَٰعَفۡ لَهَا ٱلۡعَذَابُ ضِعۡفَيۡنِۚ وَكَانَ ذَٰلِكَ عَلَى ٱللَّهِ يَسِيرٗا

Ya ku matan Annabi, duk wadda ta zo da wani abin qi na sarari daga cikinku to za a ninninka mata azaba ninki biyu. Yin wannan kuma ya kasance abu ne mai sauqi ga Allah