إِذِ ٱلۡأَغۡلَٰلُ فِيٓ أَعۡنَٰقِهِمۡ وَٱلسَّلَٰسِلُ يُسۡحَبُونَ
A yayin da ququmai suke a wuyoyinsu, da kuma sarqoqi ana jan su
فِي ٱلۡحَمِيمِ ثُمَّ فِي ٱلنَّارِ يُسۡجَرُونَ
A cikin tafasasshen ruwan, sannan kuma ana qona su a cikin wuta
ثُمَّ قِيلَ لَهُمۡ أَيۡنَ مَا كُنتُمۡ تُشۡرِكُونَ
Sannan kuma a ce da su: “Ina abin da kuka kasance kuna shirka da shi?
مِن دُونِ ٱللَّهِۖ قَالُواْ ضَلُّواْ عَنَّا بَل لَّمۡ نَكُن نَّدۡعُواْ مِن قَبۡلُ شَيۡـٔٗاۚ كَذَٰلِكَ يُضِلُّ ٱللَّهُ ٱلۡكَٰفِرِينَ
“Wanda ba Allah ba?” Suka ce: “Sun vace mana; ai ba mu kasance muna bauta wa wani abu ba a da”. Kamar haka ne Allah Yake vatar da kafirai
ذَٰلِكُم بِمَا كُنتُمۡ تَفۡرَحُونَ فِي ٱلۡأَرۡضِ بِغَيۡرِ ٱلۡحَقِّ وَبِمَا كُنتُمۡ تَمۡرَحُونَ
Wannan fa (ya same ku ne) saboda abin da kuka kasance kuna yin girman kai da shi a bayan qasa ba da wata hujja ba, da kuma abin da kuka kasance kuna yin walwala da shi
ٱدۡخُلُوٓاْ أَبۡوَٰبَ جَهَنَّمَ خَٰلِدِينَ فِيهَاۖ فَبِئۡسَ مَثۡوَى ٱلۡمُتَكَبِّرِينَ
(Za a ce da su): “Ku shiga qofofin Jahannama kuna masu dawwama a cikinta”; to makomar masu girman kai ta munana
فَٱصۡبِرۡ إِنَّ وَعۡدَ ٱللَّهِ حَقّٞۚ فَإِمَّا نُرِيَنَّكَ بَعۡضَ ٱلَّذِي نَعِدُهُمۡ أَوۡ نَتَوَفَّيَنَّكَ فَإِلَيۡنَا يُرۡجَعُونَ
Sai ka yi haquri, lalle alqawarin Allah gaskiya ne. To idan Mun nuna maka sashin abin da Muke yi musu alqawari da shi na narko; ko kuma Mun karvi ranka, to zuwa gare Mu dai za a dawo da su
وَلَقَدۡ أَرۡسَلۡنَا رُسُلٗا مِّن قَبۡلِكَ مِنۡهُم مَّن قَصَصۡنَا عَلَيۡكَ وَمِنۡهُم مَّن لَّمۡ نَقۡصُصۡ عَلَيۡكَۗ وَمَا كَانَ لِرَسُولٍ أَن يَأۡتِيَ بِـَٔايَةٍ إِلَّا بِإِذۡنِ ٱللَّهِۚ فَإِذَا جَآءَ أَمۡرُ ٱللَّهِ قُضِيَ بِٱلۡحَقِّ وَخَسِرَ هُنَالِكَ ٱلۡمُبۡطِلُونَ
Haqiqa Mun aiko manzanni a gabaninka, daga cikinsu akwai waxanda Muka labarta maka akwai kuma daga cikinsu waxanda ba Mu labarta maka ba. Ba zai yiwu ba ga wani manzo ya zo da wata aya sai da izinin Allah. Sannan idan al’amarin Allah ya zo, to sai a yi hukunci da gaskiya, kuma a nan ne mavarnata za su yi asara
ٱللَّهُ ٱلَّذِي جَعَلَ لَكُمُ ٱلۡأَنۡعَٰمَ لِتَرۡكَبُواْ مِنۡهَا وَمِنۡهَا تَأۡكُلُونَ
Allah ne wanda Ya halitta muku dabbobin ni’ima don ku hau wasu daga cikinsu, kuma daga cikinsu kuke ci
وَلَكُمۡ فِيهَا مَنَٰفِعُ وَلِتَبۡلُغُواْ عَلَيۡهَا حَاجَةٗ فِي صُدُورِكُمۡ وَعَلَيۡهَا وَعَلَى ٱلۡفُلۡكِ تُحۡمَلُونَ
Kuna kuma da wasu abubuwan amfani game da su, don kuma ku isa (wurin) da kuke da buqatar isa a cikin zukatanku a kansu, kuma a kansu ne da kuma a kan jiragen ruwa ake xaukar ku
وَيُرِيكُمۡ ءَايَٰتِهِۦ فَأَيَّ ءَايَٰتِ ٱللَّهِ تُنكِرُونَ
Yana kuma nuna muku ayoyinsa, to wacce (aya) ce (daga) ayoyin Allah kuke musawa?
أَفَلَمۡ يَسِيرُواْ فِي ٱلۡأَرۡضِ فَيَنظُرُواْ كَيۡفَ كَانَ عَٰقِبَةُ ٱلَّذِينَ مِن قَبۡلِهِمۡۚ كَانُوٓاْ أَكۡثَرَ مِنۡهُمۡ وَأَشَدَّ قُوَّةٗ وَءَاثَارٗا فِي ٱلۡأَرۡضِ فَمَآ أَغۡنَىٰ عَنۡهُم مَّا كَانُواْ يَكۡسِبُونَ
Shin ba za su yi tafiya ba a bayan qasa sannan su duba yadda qarshen waxanda suke gabaninsu ya zama? Sun zamanto sun fi su yawa, sun kuma fi su tsananin qarfi da barin gurabe a bayan qasa; to abin da suka kasance suna aikatawa bai wadatar musu da komai ba
فَلَمَّا جَآءَتۡهُمۡ رُسُلُهُم بِٱلۡبَيِّنَٰتِ فَرِحُواْ بِمَا عِندَهُم مِّنَ ٱلۡعِلۡمِ وَحَاقَ بِهِم مَّا كَانُواْ بِهِۦ يَسۡتَهۡزِءُونَ
Sannan lokacin da manzanninsu suka zo musu da (ayoyi) bayyanannu, sai suka nuna farin ciki da ilimin da ke gare su, abin kuma da suka kasance suna yi wa izgili ya saukar musu
فَلَمَّا رَأَوۡاْ بَأۡسَنَا قَالُوٓاْ ءَامَنَّا بِٱللَّهِ وَحۡدَهُۥ وَكَفَرۡنَا بِمَا كُنَّا بِهِۦ مُشۡرِكِينَ
To lokacin da suka ga azabarmu sai suka ce: “Mun yi imani da Allah Shi kaxai, mun kuma kafirce wa abin da muka kasance muna yin shirka da shi.”
فَلَمۡ يَكُ يَنفَعُهُمۡ إِيمَٰنُهُمۡ لَمَّا رَأَوۡاْ بَأۡسَنَاۖ سُنَّتَ ٱللَّهِ ٱلَّتِي قَدۡ خَلَتۡ فِي عِبَادِهِۦۖ وَخَسِرَ هُنَالِكَ ٱلۡكَٰفِرُونَ
To imaninsu bai zamanto zai amfane su ba yayin da suka ga azabarmu; wannan sunna ce ta Allah wadda ta shuxe a kan bayinsa. Kafirai kuma sun yi asara a nan
حمٓ
HA MIM[1]
1- Duba Suratul Baqara, aya ta 1, hashiya ta 8.
تَنزِيلٞ مِّنَ ٱلرَّحۡمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ
(Alqur’ani) saukakke ne daga (Allah) Mai rahama, Mai jin qai
كِتَٰبٞ فُصِّلَتۡ ءَايَٰتُهُۥ قُرۡءَانًا عَرَبِيّٗا لِّقَوۡمٖ يَعۡلَمُونَ
(Shi) Littafi ne Alqur’ani Balarabe da aka rarrabe ayoyinsa ga mutanen da suke sanin (ma’anarsa)
بَشِيرٗا وَنَذِيرٗا فَأَعۡرَضَ أَكۡثَرُهُمۡ فَهُمۡ لَا يَسۡمَعُونَ
Mai albishir ne kuma mai gargaxi, sai yawancinsu suka bijire, don haka su ba sa jin (kira)
وَقَالُواْ قُلُوبُنَا فِيٓ أَكِنَّةٖ مِّمَّا تَدۡعُونَآ إِلَيۡهِ وَفِيٓ ءَاذَانِنَا وَقۡرٞ وَمِنۢ بَيۡنِنَا وَبَيۡنِكَ حِجَابٞ فَٱعۡمَلۡ إِنَّنَا عَٰمِلُونَ
Suka kuma ce: “Zukatanmu suna cikin rufi game da abin da kuke kiran mu zuwa gare shi; a cikin kunnuwanmu kuma akwai nauyi[1], kuma tsakaninmu da kai akwai shamaki[2], sai ka yi aiki da (addininka), lalle mu ma masu yin aiki ne (da namu).”
1- Watau akwai kurumta tare da kunnuwansu, don haka ba sa jin duk wani kira da ake yi musu.
2- Wanda yake hana muryarsa isa zuwa inda suke.
قُلۡ إِنَّمَآ أَنَا۠ بَشَرٞ مِّثۡلُكُمۡ يُوحَىٰٓ إِلَيَّ أَنَّمَآ إِلَٰهُكُمۡ إِلَٰهٞ وَٰحِدٞ فَٱسۡتَقِيمُوٓاْ إِلَيۡهِ وَٱسۡتَغۡفِرُوهُۗ وَوَيۡلٞ لِّلۡمُشۡرِكِينَ
Ka ce: “Ni ba wani ba ne sai mutum kamarku, ana yiwo min wahayin cewa, abin bautarku abin bauta ne Guda Xaya, sai ku miqe kyam zuwa gare Shi, kuma ku nemi gafararsa. Tsananin azaba kuma ya tabbata ga mushirikai
ٱلَّذِينَ لَا يُؤۡتُونَ ٱلزَّكَوٰةَ وَهُم بِٱلۡأٓخِرَةِ هُمۡ كَٰفِرُونَ
“Waxanda ba sa ba da zakka, kuma su masu kafircewa ne da (ranar) lahira.”
إِنَّ ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ وَعَمِلُواْ ٱلصَّـٰلِحَٰتِ لَهُمۡ أَجۡرٌ غَيۡرُ مَمۡنُونٖ
Lalle waxanda suka yi imani kuma suka yi aiki nagari suna da lada marar yankewa
۞قُلۡ أَئِنَّكُمۡ لَتَكۡفُرُونَ بِٱلَّذِي خَلَقَ ٱلۡأَرۡضَ فِي يَوۡمَيۡنِ وَتَجۡعَلُونَ لَهُۥٓ أَندَادٗاۚ ذَٰلِكَ رَبُّ ٱلۡعَٰلَمِينَ
Ka ce: “Yanzu kwa riqa kafircewa da wanda Ya halicci qasa a cikin (gwargwadon) kwana biyu, kuna kuma sanya masa kishiyoyi? Wannan fa Shi ne Ubangijin talikai!
وَجَعَلَ فِيهَا رَوَٰسِيَ مِن فَوۡقِهَا وَبَٰرَكَ فِيهَا وَقَدَّرَ فِيهَآ أَقۡوَٰتَهَا فِيٓ أَرۡبَعَةِ أَيَّامٖ سَوَآءٗ لِّلسَّآئِلِينَ
“Ya kuma sanya kafaffun duwatsu a cikinta daga samanta, Ya kuma yi albarka a cikinta, Ya kuma qaddara dangogin abincinta a cikin kwana huxu (tare da kwanaki biyu na halittar qasa) daidai da daidai ga masu tambaya
ثُمَّ ٱسۡتَوَىٰٓ إِلَى ٱلسَّمَآءِ وَهِيَ دُخَانٞ فَقَالَ لَهَا وَلِلۡأَرۡضِ ٱئۡتِيَا طَوۡعًا أَوۡ كَرۡهٗا قَالَتَآ أَتَيۡنَا طَآئِعِينَ
“Sannan Ya nufi zuwa sama, (a sannan) ita kuma hayaqi ce, sai Ya ce da ita da kuma qasa: “Ku zo cikin biyayya ko kuma bisa tilas.” Suka ce: ‘Mun zo muna masu biyayya’
فَقَضَىٰهُنَّ سَبۡعَ سَمَٰوَاتٖ فِي يَوۡمَيۡنِ وَأَوۡحَىٰ فِي كُلِّ سَمَآءٍ أَمۡرَهَاۚ وَزَيَّنَّا ٱلسَّمَآءَ ٱلدُّنۡيَا بِمَصَٰبِيحَ وَحِفۡظٗاۚ ذَٰلِكَ تَقۡدِيرُ ٱلۡعَزِيزِ ٱلۡعَلِيمِ
“Sai Ya mayar da su sammai bakwai a cikin kwana biyu, Ya kuma yi wa kowacce sama wahayin umarninta. Muka kuma qawata saman duniya da taurari da kuma tsaro[1]. Wannan tsari ne na Allah Mabuwayi, Masani.”
1- Watau daga aljannu masu qoqarin satar sauraro.
فَإِنۡ أَعۡرَضُواْ فَقُلۡ أَنذَرۡتُكُمۡ صَٰعِقَةٗ مِّثۡلَ صَٰعِقَةِ عَادٖ وَثَمُودَ
To idan suka bijire sai ka ce: “Na tsoratar da ku da tsawa irin tsawar Adawa da Samudawa
إِذۡ جَآءَتۡهُمُ ٱلرُّسُلُ مِنۢ بَيۡنِ أَيۡدِيهِمۡ وَمِنۡ خَلۡفِهِمۡ أَلَّا تَعۡبُدُوٓاْ إِلَّا ٱللَّهَۖ قَالُواْ لَوۡ شَآءَ رَبُّنَا لَأَنزَلَ مَلَـٰٓئِكَةٗ فَإِنَّا بِمَآ أُرۡسِلۡتُم بِهِۦ كَٰفِرُونَ
“Lokacin da manzanninsu suka zo musu ta gabansu da ta bayansu[1] cewa: ‘Kada ku bauta wa komai sai Allah.’” Suka ce: “Da Ubangijinmu Ya ga dama, da Ya saukar da mala’iku, saboda haka mu lalle masu kafirce wa abin da aka aiko ku da shi ne.’”
1- Watau suka yi amfani da hanyoyi daban-daban domin isar musu da saqon Allah.
فَأَمَّا عَادٞ فَٱسۡتَكۡبَرُواْ فِي ٱلۡأَرۡضِ بِغَيۡرِ ٱلۡحَقِّ وَقَالُواْ مَنۡ أَشَدُّ مِنَّا قُوَّةًۖ أَوَلَمۡ يَرَوۡاْ أَنَّ ٱللَّهَ ٱلَّذِي خَلَقَهُمۡ هُوَ أَشَدُّ مِنۡهُمۡ قُوَّةٗۖ وَكَانُواْ بِـَٔايَٰتِنَا يَجۡحَدُونَ
Amma Adawa sai suka yi girman kai a bayan qasa ba a kan gaskiya ba, suka kuma ce: “Wane ne ya fi mu tsananin qarfi?” Yanzu ba su ga cewa lalle Allah wanda Ya halicce su Ya fi su tsananin qarfi ba? Sun kuma kasance suna musanta ayoyinmu