وَٱلتِّينِ وَٱلزَّيۡتُونِ
Na rantse da vaure da zaitun[1]
1- Watau wuraren tsirowarsu, watau Sham, ko kuma su kansu waxanan bishiyoyin.
Compartir :
وَطُورِ سِينِينَ
Da (dutsen) Xuri Sinina
وَهَٰذَا ٱلۡبَلَدِ ٱلۡأَمِينِ
Da wannan garin amintacce (watau Makka)
لَقَدۡ خَلَقۡنَا ٱلۡإِنسَٰنَ فِيٓ أَحۡسَنِ تَقۡوِيمٖ
Haqiqa Mun halicci mutum a kan mafi kyan diri
ثُمَّ رَدَدۡنَٰهُ أَسۡفَلَ سَٰفِلِينَ
Sannan Muka mayar da shi mafi qasqancin qasqantattu[1]
1- Watau ya mayar da shi tsoho tukuf a duniya, ko kuma a lahira ya zamanto xan wuta.
إِلَّا ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ وَعَمِلُواْ ٱلصَّـٰلِحَٰتِ فَلَهُمۡ أَجۡرٌ غَيۡرُ مَمۡنُونٖ
Sai fa waxanda suka yi imani suka kuma yi ayyuka nagari, to su kam suna da lada ba mai yankewa ba
فَمَا يُكَذِّبُكَ بَعۡدُ بِٱلدِّينِ
To (kai kafiri) me ya sa kake qaryata ranar sakamako bayan haka?
أَلَيۡسَ ٱللَّهُ بِأَحۡكَمِ ٱلۡحَٰكِمِينَ
Ashe Allah ba Shi ne Mafi iya hukuncin masu hukunci ba?