وَٱلضُّحَىٰ
Na rantse da lokacin hantsi
Compartir :
وَٱلَّيۡلِ إِذَا سَجَىٰ
Da kuma dare idan ya yi tsit[1]
1- Watau ya lulluve komai da duhunsa, mutane su shiga mazaunansu don su yi barci.
مَا وَدَّعَكَ رَبُّكَ وَمَا قَلَىٰ
Ubangijinka bai bar ka ba, kuma bai qi ka ba
وَلَلۡأٓخِرَةُ خَيۡرٞ لَّكَ مِنَ ٱلۡأُولَىٰ
Kuma lalle lahira ta fi maka alheri a kan duniya
وَلَسَوۡفَ يُعۡطِيكَ رَبُّكَ فَتَرۡضَىٰٓ
Kuma lalle Ubangijinka zai ba ka har sai ka yarda (da abin da Ya ba ka)
أَلَمۡ يَجِدۡكَ يَتِيمٗا فَـَٔاوَىٰ
Shin bai same ka maraya ba sai Ya haxa ka (da mai kula da kai)?
وَوَجَدَكَ ضَآلّٗا فَهَدَىٰ
Ya kuma same ka marashin shiriya Ya shiryar (da kai)?
وَوَجَدَكَ عَآئِلٗا فَأَغۡنَىٰ
Ya kuma same ka matalauci Ya wadata (ka)?
فَأَمَّا ٱلۡيَتِيمَ فَلَا تَقۡهَرۡ
Don haka maraya fa kada ka yi masa fin qarfi
وَأَمَّا ٱلسَّآئِلَ فَلَا تَنۡهَرۡ
Mai tambaya[1] kuma kada ka daka masa tsawa
1- Watau mai neman taimako saboda buqata, ko mai tambaya don neman sani.
وَأَمَّا بِنِعۡمَةِ رَبِّكَ فَحَدِّثۡ
Amma kuma game da ni’imar Ubangijinka sai ka ba da labari