قَالُواْ سَنُرَٰوِدُ عَنۡهُ أَبَاهُ وَإِنَّا لَفَٰعِلُونَ
Suka ce: “To za mu rarrashi babansa game da shi, kuma lalle tabbas za mu aikata (haka).”
وَقَالَ لِفِتۡيَٰنِهِ ٱجۡعَلُواْ بِضَٰعَتَهُمۡ فِي رِحَالِهِمۡ لَعَلَّهُمۡ يَعۡرِفُونَهَآ إِذَا ٱنقَلَبُوٓاْ إِلَىٰٓ أَهۡلِهِمۡ لَعَلَّهُمۡ يَرۡجِعُونَ
(Yusufu) Ya ce da yaransa: “Ku sanya hajarsu[1] cikin jakunkunansu don su gan ta lokacin da suka koma ga iyalinsu wataqila za su dawo.”
1- Watau kayansu da suka zo da shi domin furfure, domin idan sun gan su za su fahimci ba ciniki ya yi da su ba, wannan zai sa su dawo tare da xan’uwansa.
فَلَمَّا رَجَعُوٓاْ إِلَىٰٓ أَبِيهِمۡ قَالُواْ يَـٰٓأَبَانَا مُنِعَ مِنَّا ٱلۡكَيۡلُ فَأَرۡسِلۡ مَعَنَآ أَخَانَا نَكۡتَلۡ وَإِنَّا لَهُۥ لَحَٰفِظُونَ
Lokacin da suka dawo wurin babansu sai suka ce: “Ya babanmu, an hana mu yin awo (nan gaba), sai ka aika mu tare da xan’uwanmu mu yiwo awo, lalle kuma mu tabbas za mu kula da shi.”
قَالَ هَلۡ ءَامَنُكُمۡ عَلَيۡهِ إِلَّا كَمَآ أَمِنتُكُمۡ عَلَىٰٓ أَخِيهِ مِن قَبۡلُ فَٱللَّهُ خَيۡرٌ حَٰفِظٗاۖ وَهُوَ أَرۡحَمُ ٱلرَّـٰحِمِينَ
Ya ce: “Yanzu anya kuwa na amince muku game da shi, ai sai dai kawai kamar yadda na amince muku game da xan’uwansa tun tuni; sai dai Allah ne Fiyayen Mai kiyayewa, kuma Shi ne Fiyayyen masu rahama.”
وَلَمَّا فَتَحُواْ مَتَٰعَهُمۡ وَجَدُواْ بِضَٰعَتَهُمۡ رُدَّتۡ إِلَيۡهِمۡۖ قَالُواْ يَـٰٓأَبَانَا مَا نَبۡغِيۖ هَٰذِهِۦ بِضَٰعَتُنَا رُدَّتۡ إِلَيۡنَاۖ وَنَمِيرُ أَهۡلَنَا وَنَحۡفَظُ أَخَانَا وَنَزۡدَادُ كَيۡلَ بَعِيرٖۖ ذَٰلِكَ كَيۡلٞ يَسِيرٞ
Lokacin kuma da suka buxe jakunkunansu sai suka samu hajarsu an mayar musu da ita, suka ce: “Ya babanmu, me kuma muke nema? Ai wannan hajarmu ce aka dawo mana da ita; (idan muka koma) ai za mu nemo wa iyalinmu abinci kuma mu kula da xan’uwanmu, kuma mu qara kayan raqumi (xaya). Wannan (kuwa) kaya ne sassauqa.”
قَالَ لَنۡ أُرۡسِلَهُۥ مَعَكُمۡ حَتَّىٰ تُؤۡتُونِ مَوۡثِقٗا مِّنَ ٱللَّهِ لَتَأۡتُنَّنِي بِهِۦٓ إِلَّآ أَن يُحَاطَ بِكُمۡۖ فَلَمَّآ ءَاتَوۡهُ مَوۡثِقَهُمۡ قَالَ ٱللَّهُ عَلَىٰ مَا نَقُولُ وَكِيلٞ
(Babansu) Ya ce: “Ba zan aika ku tare da shi ba, har sai kun yi min alqawari tsakaninku da Allah lalle za ku dawo min da shi, sai dai in wata masifa ta rutsa da ku.” Lokacin da suka yi masa alqawari sai ya ce: “Allah ne Wakili a kan abin da muke faxa.”
وَقَالَ يَٰبَنِيَّ لَا تَدۡخُلُواْ مِنۢ بَابٖ وَٰحِدٖ وَٱدۡخُلُواْ مِنۡ أَبۡوَٰبٖ مُّتَفَرِّقَةٖۖ وَمَآ أُغۡنِي عَنكُم مِّنَ ٱللَّهِ مِن شَيۡءٍۖ إِنِ ٱلۡحُكۡمُ إِلَّا لِلَّهِۖ عَلَيۡهِ تَوَكَّلۡتُۖ وَعَلَيۡهِ فَلۡيَتَوَكَّلِ ٱلۡمُتَوَكِّلُونَ
Ya kuma ce: “Ya ‘ya’yana, kada ku shiga (Masar) ta qofa guda; ku shiga ta qofofi daban-daban[1]. Ba zan kare muku komai daga Allah ba; ba wani hukunci sai na Allah; a gare Shi na dogara, kuma a gare Shi ne masu dogaro ya wajaba su dogara.”
1- Domi kauce wa wata cutarwa da za ta iya fuskantar su, don kada ta same su gaba xayansu a lokaci guda.
وَلَمَّا دَخَلُواْ مِنۡ حَيۡثُ أَمَرَهُمۡ أَبُوهُم مَّا كَانَ يُغۡنِي عَنۡهُم مِّنَ ٱللَّهِ مِن شَيۡءٍ إِلَّا حَاجَةٗ فِي نَفۡسِ يَعۡقُوبَ قَضَىٰهَاۚ وَإِنَّهُۥ لَذُو عِلۡمٖ لِّمَا عَلَّمۡنَٰهُ وَلَٰكِنَّ أَكۡثَرَ ٱلنَّاسِ لَا يَعۡلَمُونَ
To lokacin da suka shiga ta inda babansu ya umarce su, (wannan) ba zai maganta musu komai ba daga Allah, sai dai wata buqata ce a zuciyar Yakubu da ya samu biyanta. Lalle kuma shi tabbas mai ilimi ne na abin da Muka sanar da shi, sai dai yawancin mutane ba su sani ba
وَلَمَّا دَخَلُواْ عَلَىٰ يُوسُفَ ءَاوَىٰٓ إِلَيۡهِ أَخَاهُۖ قَالَ إِنِّيٓ أَنَا۠ أَخُوكَ فَلَا تَبۡتَئِسۡ بِمَا كَانُواْ يَعۡمَلُونَ
Lokacin kuma da suka shiga wurin Yusufu sai ya janye xan’uwansa wajensa ya ce: “Ni fa lalle xan’uwanka ne; saboda haka kada ka damu da abin da suke aikatawa.”
فَلَمَّا جَهَّزَهُم بِجَهَازِهِمۡ جَعَلَ ٱلسِّقَايَةَ فِي رَحۡلِ أَخِيهِ ثُمَّ أَذَّنَ مُؤَذِّنٌ أَيَّتُهَا ٱلۡعِيرُ إِنَّكُمۡ لَسَٰرِقُونَ
To lokacin da (Azizu) ya haxa musu kayayyakinsu sai ya sanya ma’aunin a cikin kayan xan’uwansa, sannan mai shela ya yi yekuwa da cewa: “Ya ku waxannan ayari, lalle ku fa tabbas varayi ne!”
قَالُواْ وَأَقۡبَلُواْ عَلَيۡهِم مَّاذَا تَفۡقِدُونَ
Suka ce: (yayin da) suka juyo wajensu: “Wane abu ne ya vace muku?”
قَالُواْ نَفۡقِدُ صُوَاعَ ٱلۡمَلِكِ وَلِمَن جَآءَ بِهِۦ حِمۡلُ بَعِيرٖ وَأَنَا۠ بِهِۦ زَعِيمٞ
Suka ce: “Ma’aunin Sarki ne ba mu gani ba, kuma duk wanda ya zo da shi yana da ladan kayan raqumi guda, kuma ni ne mai lamuninsa.”
قَالُواْ تَٱللَّهِ لَقَدۡ عَلِمۡتُم مَّا جِئۡنَا لِنُفۡسِدَ فِي ٱلۡأَرۡضِ وَمَا كُنَّا سَٰرِقِينَ
Suka ce: “Wallahi haqiqa kun sani ba mu zo don mu yi varna a bayan qasa ba, kuma mu ba mu tava zama varayi ba.”
قَالُواْ فَمَا جَزَـٰٓؤُهُۥٓ إِن كُنتُمۡ كَٰذِبِينَ
(Mutanen Sarki) suka ce: “Mene ne horon da za a yi masa (varawon) idan qarya kuke yi?”
قَالُواْ جَزَـٰٓؤُهُۥ مَن وُجِدَ فِي رَحۡلِهِۦ فَهُوَ جَزَـٰٓؤُهُۥۚ كَذَٰلِكَ نَجۡزِي ٱلظَّـٰلِمِينَ
Suka ce: “Horonsa shi ne, wanda aka same shi a cikin kayansa, to shi ne horonsa (watau a riqe shi)[1]. Kamar haka muke saka wa azzalumai.”
1- A shari’ance duk wanda ya yi sata ana miqa shi ga wanda ya yi wa satar ya mayar da shi bawansa.
فَبَدَأَ بِأَوۡعِيَتِهِمۡ قَبۡلَ وِعَآءِ أَخِيهِ ثُمَّ ٱسۡتَخۡرَجَهَا مِن وِعَآءِ أَخِيهِۚ كَذَٰلِكَ كِدۡنَا لِيُوسُفَۖ مَا كَانَ لِيَأۡخُذَ أَخَاهُ فِي دِينِ ٱلۡمَلِكِ إِلَّآ أَن يَشَآءَ ٱللَّهُۚ نَرۡفَعُ دَرَجَٰتٖ مَّن نَّشَآءُۗ وَفَوۡقَ كُلِّ ذِي عِلۡمٍ عَلِيمٞ
Sai ya fara da (binciken) jakunkunansu kafin jakar xan’uwansa; sannan ya fito da shi (mudun) daga jakar xan’uwansa. Kamar haka Muka shirya wa Yusufu; ba zai yiwu ya riqe xan’uwansa ba a shari’ar Sarkin (Masar), sai dai idan Allah Ya ga dama. Muna xaukaka darajojin waxanda Muka ga dama ne. Kuma duk wani mai ilimi akwai wanda yake samansa a ilimi
۞قَالُوٓاْ إِن يَسۡرِقۡ فَقَدۡ سَرَقَ أَخٞ لَّهُۥ مِن قَبۡلُۚ فَأَسَرَّهَا يُوسُفُ فِي نَفۡسِهِۦ وَلَمۡ يُبۡدِهَا لَهُمۡۚ قَالَ أَنتُمۡ شَرّٞ مَّكَانٗاۖ وَٱللَّهُ أَعۡلَمُ بِمَا تَصِفُونَ
Suka ce: “Idan har ya yi sata, to haqiqa xan’uwansa ma a da can ya tava yin sata.” Sai Yusufu ya voye wannan (maganar) a ransa bai kuma bayyana musu ita ba, yana mai cewa (a ransa): “Ku ne dai masu mummunan matsayi (a wurin Allah). Allah kuwa Shi ne Mafi sanin abin da kuke sifantawa.”
قَالُواْ يَـٰٓأَيُّهَا ٱلۡعَزِيزُ إِنَّ لَهُۥٓ أَبٗا شَيۡخٗا كَبِيرٗا فَخُذۡ أَحَدَنَا مَكَانَهُۥٓۖ إِنَّا نَرَىٰكَ مِنَ ٱلۡمُحۡسِنِينَ
Suka ce: “Ya kai wannan Azizu, lalle yana da mahaifi tsoho tukuf, sai ka riqe xayanmu a madadinsa; lalle kuwa muna ganin kana daga masu kyautatawa.”
قَالَ مَعَاذَ ٱللَّهِ أَن نَّأۡخُذَ إِلَّا مَن وَجَدۡنَا مَتَٰعَنَا عِندَهُۥٓ إِنَّآ إِذٗا لَّظَٰلِمُونَ
Ya ce: “Allah Ya kiyaye mu da riqe wani ba wanda muka sami kayanmu a wurinsa ba; idan kuwa muka yi haka to lalle mun zama azzalumai.”
فَلَمَّا ٱسۡتَيۡـَٔسُواْ مِنۡهُ خَلَصُواْ نَجِيّٗاۖ قَالَ كَبِيرُهُمۡ أَلَمۡ تَعۡلَمُوٓاْ أَنَّ أَبَاكُمۡ قَدۡ أَخَذَ عَلَيۡكُم مَّوۡثِقٗا مِّنَ ٱللَّهِ وَمِن قَبۡلُ مَا فَرَّطتُمۡ فِي يُوسُفَۖ فَلَنۡ أَبۡرَحَ ٱلۡأَرۡضَ حَتَّىٰ يَأۡذَنَ لِيٓ أَبِيٓ أَوۡ يَحۡكُمَ ٱللَّهُ لِيۖ وَهُوَ خَيۡرُ ٱلۡحَٰكِمِينَ
To lokacin da suka fitar da rai daga gare shi, sai suka keve suna ganawa. Babbansu ya ce: “Ba ku san cewa babanku ya xauki alqawari daga gare ku tsakaninku da Allah ba, kuma a da can ga irin sakacin da kuka yi game da Yusufu? To ni dai ba zan bar qasar (Masar) ba har sai babana ya yi min izini (da komawa), ko kuwa Allah Ya hukunta (abin da Ya ga dama) da ni; Shi ne kuwa Fiyayyen masu hukunci
ٱرۡجِعُوٓاْ إِلَىٰٓ أَبِيكُمۡ فَقُولُواْ يَـٰٓأَبَانَآ إِنَّ ٱبۡنَكَ سَرَقَ وَمَا شَهِدۡنَآ إِلَّا بِمَا عَلِمۡنَا وَمَا كُنَّا لِلۡغَيۡبِ حَٰفِظِينَ
“Sai ku koma wurin babanku ku ce da shi: “Ya babanmu, lalle xanka ya yi sata! Ba mu kuwa ba da shaida ba sai da abin da muka sani, ba mu kuma zamanto masu kiyaye gaibu ba[1]
1- Watau ba mu san yana sata ba, domin da a ce mun sani, to ba za mu xaukar maka alqawarin za mu zo maka da shi ba.
وَسۡـَٔلِ ٱلۡقَرۡيَةَ ٱلَّتِي كُنَّا فِيهَا وَٱلۡعِيرَ ٱلَّتِيٓ أَقۡبَلۡنَا فِيهَاۖ وَإِنَّا لَصَٰدِقُونَ
“Kuma ka tambayi mutanen alqaryar da muka kasance a cikinta (watau Masar) da kuma ayarin da muka zo cikinsu. Wallahi mu kam lalle masu gaskiya ne.”
قَالَ بَلۡ سَوَّلَتۡ لَكُمۡ أَنفُسُكُمۡ أَمۡرٗاۖ فَصَبۡرٞ جَمِيلٌۖ عَسَى ٱللَّهُ أَن يَأۡتِيَنِي بِهِمۡ جَمِيعًاۚ إِنَّهُۥ هُوَ ٱلۡعَلِيمُ ٱلۡحَكِيمُ
Ya ce: “Ba haka ba ne, zuciyarku dai ta shirya muku wani abu. Haquri kawai shi ya fi kyau (gare ni). Ina sa tsammani Allah Ya kawo min su gaba xaya. Lalle Shi ne Masani, Mai hikima.”
وَتَوَلَّىٰ عَنۡهُمۡ وَقَالَ يَـٰٓأَسَفَىٰ عَلَىٰ يُوسُفَ وَٱبۡيَضَّتۡ عَيۡنَاهُ مِنَ ٱلۡحُزۡنِ فَهُوَ كَظِيمٞ
Sai ya kau da kai daga gare su, ya kuma ce: “Wayyo baqin cikina game da Yusufu!” Idanuwansa kuwa suka yi fari[1] don baqin ciki, yana cike da vacin rai
1- Watau ya makance ya daina gani.
قَالُواْ تَٱللَّهِ تَفۡتَؤُاْ تَذۡكُرُ يُوسُفَ حَتَّىٰ تَكُونَ حَرَضًا أَوۡ تَكُونَ مِنَ ٱلۡهَٰلِكِينَ
Suka ce: “Wallahi ba za ka bar tuna Yusufu ba har sai ka tasam ma mutuwa ko sai ka zamanto cikin matattu!”
قَالَ إِنَّمَآ أَشۡكُواْ بَثِّي وَحُزۡنِيٓ إِلَى ٱللَّهِ وَأَعۡلَمُ مِنَ ٱللَّهِ مَا لَا تَعۡلَمُونَ
Ya ce: “Ni fa kawai ina bayyana tsananin damuwata ne da baqin cikina ga Allah, kuma ina sane da abin da ba ku sani ba game da Allah
يَٰبَنِيَّ ٱذۡهَبُواْ فَتَحَسَّسُواْ مِن يُوسُفَ وَأَخِيهِ وَلَا تَاْيۡـَٔسُواْ مِن رَّوۡحِ ٱللَّهِۖ إِنَّهُۥ لَا يَاْيۡـَٔسُ مِن رَّوۡحِ ٱللَّهِ إِلَّا ٱلۡقَوۡمُ ٱلۡكَٰفِرُونَ
“Ya ku ‘ya’yana, ku tafi ku lalubo labarin Yusufu shi da xan’uwansa, kada ku xebe qauna daga rahamar Allah. Lalle ba mai xebe qauna daga rahamar Allah sai mutane kafirai.”
فَلَمَّا دَخَلُواْ عَلَيۡهِ قَالُواْ يَـٰٓأَيُّهَا ٱلۡعَزِيزُ مَسَّنَا وَأَهۡلَنَا ٱلضُّرُّ وَجِئۡنَا بِبِضَٰعَةٖ مُّزۡجَىٰةٖ فَأَوۡفِ لَنَا ٱلۡكَيۡلَ وَتَصَدَّقۡ عَلَيۡنَآۖ إِنَّ ٱللَّهَ يَجۡزِي ٱلۡمُتَصَدِّقِينَ
Lokacin da suka shiga wurinsa (Annabi Yusufu) sai suka ce: “Ya Azizu, muna fama da yunwa mu da iyalanmu, kuma mun zo maka da wata haja marar daraja; to ka cika mana mudu, ka kuma kyautata mana; lalle Allah Yana saka wa masu kyautatawa.”
قَالَ هَلۡ عَلِمۡتُم مَّا فَعَلۡتُم بِيُوسُفَ وَأَخِيهِ إِذۡ أَنتُمۡ جَٰهِلُونَ
Ya ce: “Shin kun kuwa san abin da kuka aikata wa Yusufu shi da xan’uwansa a lokacin da kuke jahilai?”
قَالُوٓاْ أَءِنَّكَ لَأَنتَ يُوسُفُۖ قَالَ أَنَا۠ يُوسُفُ وَهَٰذَآ أَخِيۖ قَدۡ مَنَّ ٱللَّهُ عَلَيۡنَآۖ إِنَّهُۥ مَن يَتَّقِ وَيَصۡبِرۡ فَإِنَّ ٱللَّهَ لَا يُضِيعُ أَجۡرَ ٱلۡمُحۡسِنِينَ
Suka ce: “Shin kuwa tabbas ko kai ne Yusufu ne?” Ya ce: “Ni ne Yusufu, wannan kuma xan’uwana ne; haqiqa Allah Ya yi mana baiwa; lalle wanda ya kiyaye dokokin (Allah) ya kuma yi haquri, to tabbas Allah ba Ya tozarta sakamakon masu kyautatawa.”