لَّا ظَلِيلٖ وَلَا يُغۡنِي مِنَ ٱللَّهَبِ
Ba mai ba da inuwa ba kuma ba mai karewa daga harshen wuta ba
Compartir :
إِنَّهَا تَرۡمِي بِشَرَرٖ كَٱلۡقَصۡرِ
Haqiqa ita tana jefa tartsatsi kamar qaton gini
كَأَنَّهُۥ جِمَٰلَتٞ صُفۡرٞ
Kai ka ce su raquma ne baqaqe
وَيۡلٞ يَوۡمَئِذٖ لِّلۡمُكَذِّبِينَ
Tsananin azaba ya tabbata a wannan ranar ga masu qaryatawa
هَٰذَا يَوۡمُ لَا يَنطِقُونَ
Wannan ita ce ranar da ba sa magana
وَلَا يُؤۡذَنُ لَهُمۡ فَيَعۡتَذِرُونَ
Kuma ba za a yi musu izini ba balle su kawo hanzari
هَٰذَا يَوۡمُ ٱلۡفَصۡلِۖ جَمَعۡنَٰكُمۡ وَٱلۡأَوَّلِينَ
Wannan ita ce rana ta yin hukunci da Muka tara ku da na farko
فَإِن كَانَ لَكُمۡ كَيۡدٞ فَكِيدُونِ
To idan kuna da wani tanadi na makirci sai ku qulla Mini
إِنَّ ٱلۡمُتَّقِينَ فِي ظِلَٰلٖ وَعُيُونٖ
Lalle masu taqawa suna cikin inuwoyi da idanuwan ruwa
وَفَوَٰكِهَ مِمَّا يَشۡتَهُونَ
Da kuma ababan marmari daga abin da suke sha’awa
كُلُواْ وَٱشۡرَبُواْ هَنِيٓـَٔۢا بِمَا كُنتُمۡ تَعۡمَلُونَ
Ku ci kuma ku sha kuna masu farin ciki saboda abin da kuka kasance kuna aikatawa
إِنَّا كَذَٰلِكَ نَجۡزِي ٱلۡمُحۡسِنِينَ
Lalle Mu kamar haka Muke saka wa masu kyautatawa
كُلُواْ وَتَمَتَّعُواْ قَلِيلًا إِنَّكُم مُّجۡرِمُونَ
Ku ci kuma ku ji daxi kaxan (a duniya), lalle ku kun tabbata manyan masu laifi
وَإِذَا قِيلَ لَهُمُ ٱرۡكَعُواْ لَا يَرۡكَعُونَ
Idan kuma aka ce da su: “Ku yi ruku’u”, to ba za su yi ruku’u ba
فَبِأَيِّ حَدِيثِۭ بَعۡدَهُۥ يُؤۡمِنُونَ
To da wane irin zance ne bayansa (Alqur’ani) za su yi imani?