Capítulo: Suratul Ma’arij

Verso : 31

فَمَنِ ٱبۡتَغَىٰ وَرَآءَ ذَٰلِكَ فَأُوْلَـٰٓئِكَ هُمُ ٱلۡعَادُونَ

To duk wanda ya nemi (wani abu) bayan wannan, to waxannan su ne masu qetare iyaka



Capítulo: Suratul Ma’arij

Verso : 32

وَٱلَّذِينَ هُمۡ لِأَمَٰنَٰتِهِمۡ وَعَهۡدِهِمۡ رَٰعُونَ

Waxanda kuma suke kiyaye amanoninsu da alqawuransu



Capítulo: Suratul Ma’arij

Verso : 33

وَٱلَّذِينَ هُم بِشَهَٰدَٰتِهِمۡ قَآئِمُونَ

Waxanda kuma suke tsai da shaidarsu



Capítulo: Suratul Ma’arij

Verso : 34

وَٱلَّذِينَ هُمۡ عَلَىٰ صَلَاتِهِمۡ يُحَافِظُونَ

Waxanda kuma suke kiyaye sallolinsu



Capítulo: Suratul Ma’arij

Verso : 35

أُوْلَـٰٓئِكَ فِي جَنَّـٰتٖ مُّكۡرَمُونَ

Waxannan su ne waxanda ake girmamawa cikin gidajen Aljanna



Capítulo: Suratul Ma’arij

Verso : 36

فَمَالِ ٱلَّذِينَ كَفَرُواْ قِبَلَكَ مُهۡطِعِينَ

To me ya sami waxanda suka kafirta suke gaggawa zuwa gare ka?



Capítulo: Suratul Ma’arij

Verso : 37

عَنِ ٱلۡيَمِينِ وَعَنِ ٱلشِّمَالِ عِزِينَ

Qungiya-qungiya, ta damanka da ta hagunka



Capítulo: Suratul Ma’arij

Verso : 38

أَيَطۡمَعُ كُلُّ ٱمۡرِيٕٖ مِّنۡهُمۡ أَن يُدۡخَلَ جَنَّةَ نَعِيمٖ

Yanzu ashe kowane mutum daga cikinsu yana kwaxayin a shigar da shi Aljannar ni’ima?



Capítulo: Suratul Ma’arij

Verso : 39

كَلَّآۖ إِنَّا خَلَقۡنَٰهُم مِّمَّا يَعۡلَمُونَ

Faufau! Lalle Mu Mun halitta su daga abin da suka sani.[1]


1- Watau wulaqantaccen ruwa na maniyyi.


Capítulo: Suratul Ma’arij

Verso : 40

فَلَآ أُقۡسِمُ بِرَبِّ ٱلۡمَشَٰرِقِ وَٱلۡمَغَٰرِبِ إِنَّا لَقَٰدِرُونَ

To, ina yin rantsuwa da Ubangijin wuraren hudowar rana da wuraren faxuwarta, lalle Mu Masu iko ne



Capítulo: Suratul Ma’arij

Verso : 41

عَلَىٰٓ أَن نُّبَدِّلَ خَيۡرٗا مِّنۡهُمۡ وَمَا نَحۡنُ بِمَسۡبُوقِينَ

A kan Mu musanya wasu fiye da su, kuma Mu ba Masu kasawa ba ne



Capítulo: Suratul Ma’arij

Verso : 42

فَذَرۡهُمۡ يَخُوضُواْ وَيَلۡعَبُواْ حَتَّىٰ يُلَٰقُواْ يَوۡمَهُمُ ٱلَّذِي يُوعَدُونَ

To ka qyale su su kutsa su yi wasa har sai sun haxu da ranarsu wadda ake yi musu alqawarinta



Capítulo: Suratul Ma’arij

Verso : 43

يَوۡمَ يَخۡرُجُونَ مِنَ ٱلۡأَجۡدَاثِ سِرَاعٗا كَأَنَّهُمۡ إِلَىٰ نُصُبٖ يُوفِضُونَ

A ranar da za su fito daga qaburbura a gurguje, kai ka ce su suna gaggawa ne zuwa ga wata tuta (ta matattara)



Capítulo: Suratul Ma’arij

Verso : 44

خَٰشِعَةً أَبۡصَٰرُهُمۡ تَرۡهَقُهُمۡ ذِلَّةٞۚ ذَٰلِكَ ٱلۡيَوۡمُ ٱلَّذِي كَانُواْ يُوعَدُونَ

Idanuwansu a qasqance, wulaqanci ya lulluve su. Wannan ne ranar da ake yi musu alqawarinta