وَمَآ أَنتُم بِمُعۡجِزِينَ فِي ٱلۡأَرۡضِۖ وَمَا لَكُم مِّن دُونِ ٱللَّهِ مِن وَلِيّٖ وَلَا نَصِيرٖ
Kuma ku ba za ku gagara ba a bayan qasa; kuma ba ku da wani majivinci ko mataimaki in ba Allah ba
وَمِنۡ ءَايَٰتِهِ ٱلۡجَوَارِ فِي ٱلۡبَحۡرِ كَٱلۡأَعۡلَٰمِ
Daga cikin ayoyinsa kuma akwai jiragen ruwa masu gudu a cikin kogi kamar duwatsu
إِن يَشَأۡ يُسۡكِنِ ٱلرِّيحَ فَيَظۡلَلۡنَ رَوَاكِدَ عَلَىٰ ظَهۡرِهِۦٓۚ إِنَّ فِي ذَٰلِكَ لَأٓيَٰتٖ لِّكُلِّ صَبَّارٖ شَكُورٍ
Idan da Ya ga dama da sai Ya kwantar da iska sai (jiragen) su zama a tsaye cak a kan (kogin). Lalle a game da wannan tabbas akwai ayoyi ga duk wani mai yawan haquri, mai yawan godiya
أَوۡ يُوبِقۡهُنَّ بِمَا كَسَبُواْ وَيَعۡفُ عَن كَثِيرٖ
Ko kuma Ya nutsar da su saboda (munanan ayyukan) da suka aikata. Ko kuma ya yi afuwa ga wasu (laifuka) masu yawa
وَيَعۡلَمَ ٱلَّذِينَ يُجَٰدِلُونَ فِيٓ ءَايَٰتِنَا مَا لَهُم مِّن مَّحِيصٖ
Kuma waxanda suke jayayya game da ayoyinmu sun san da cewa ba su da wata matsera
فَمَآ أُوتِيتُم مِّن شَيۡءٖ فَمَتَٰعُ ٱلۡحَيَوٰةِ ٱلدُّنۡيَاۚ وَمَا عِندَ ٱللَّهِ خَيۡرٞ وَأَبۡقَىٰ لِلَّذِينَ ءَامَنُواْ وَعَلَىٰ رَبِّهِمۡ يَتَوَكَّلُونَ
Sannan duk wani abu da aka ba ku to jin daxin rayuwar duniya ne; kuma abin da yake wurin Allah shi ya fi alheri ya kuma fi wanzuwa ga waxanda suka yi imani suke kuma dogara ga Ubangijinsu
وَٱلَّذِينَ يَجۡتَنِبُونَ كَبَـٰٓئِرَ ٱلۡإِثۡمِ وَٱلۡفَوَٰحِشَ وَإِذَا مَا غَضِبُواْ هُمۡ يَغۡفِرُونَ
Waxanda kuma suke nesantar manyan zunubai da munanansu, idan kuma sun yi fushi sukan yafe
وَٱلَّذِينَ ٱسۡتَجَابُواْ لِرَبِّهِمۡ وَأَقَامُواْ ٱلصَّلَوٰةَ وَأَمۡرُهُمۡ شُورَىٰ بَيۡنَهُمۡ وَمِمَّا رَزَقۡنَٰهُمۡ يُنفِقُونَ
(Su ne) kuma waxanda suka amsa kiran Ubangijinsu suka kuma tsai da salla, al’amarinsu kuwa (suna) shawara ne a tsakaninsu, suna kuma ciyarwa daga abin da Muka arzuta su
وَٱلَّذِينَ إِذَآ أَصَابَهُمُ ٱلۡبَغۡيُ هُمۡ يَنتَصِرُونَ
(Su ne) kuma waxanda idan wani zalunci ya shafe su sukan rama[1]
1- Yayin da azzalumin ya kasance ba wanda ya cancanci afuwa ba ne, kuma babu maslaha cikin yi masa afuwar.
وَجَزَـٰٓؤُاْ سَيِّئَةٖ سَيِّئَةٞ مِّثۡلُهَاۖ فَمَنۡ عَفَا وَأَصۡلَحَ فَأَجۡرُهُۥ عَلَى ٱللَّهِۚ إِنَّهُۥ لَا يُحِبُّ ٱلظَّـٰلِمِينَ
Kuma sakamakon mummunan (abu) shi ne mayar da mummuna kamarsa; to wanda ya yi afuwa ya kuma kyautata, to ladansa yana wurin Allah. Lalle Shi ba Ya son azzalumai
وَلَمَنِ ٱنتَصَرَ بَعۡدَ ظُلۡمِهِۦ فَأُوْلَـٰٓئِكَ مَا عَلَيۡهِم مِّن سَبِيلٍ
Tabbas kuma duk wanda ya rama bayan an zalunce shi, to waxannan ba wani laifi a kansu
إِنَّمَا ٱلسَّبِيلُ عَلَى ٱلَّذِينَ يَظۡلِمُونَ ٱلنَّاسَ وَيَبۡغُونَ فِي ٱلۡأَرۡضِ بِغَيۡرِ ٱلۡحَقِّۚ أُوْلَـٰٓئِكَ لَهُمۡ عَذَابٌ أَلِيمٞ
Laifi kam yana kan waxanda suke zaluntar mutane ne suke kuma yin ta’adda a bayan qasa ba da wata hujja ba. Waxannan suna da azaba mai raxaxi
وَلَمَن صَبَرَ وَغَفَرَ إِنَّ ذَٰلِكَ لَمِنۡ عَزۡمِ ٱلۡأُمُورِ
Tabbas kuma wanda ya yi haquri ya yafe, to tabbas wannan yana daga muhimman al’amura[1]
1- Watau haqurinsa zai zame masa alheri, har ma da al’ummarsa gaba xaya.
وَمَن يُضۡلِلِ ٱللَّهُ فَمَا لَهُۥ مِن وَلِيّٖ مِّنۢ بَعۡدِهِۦۗ وَتَرَى ٱلظَّـٰلِمِينَ لَمَّا رَأَوُاْ ٱلۡعَذَابَ يَقُولُونَ هَلۡ إِلَىٰ مَرَدّٖ مِّن سَبِيلٖ
Wanda kuma Allah Ya vatar, to ba shi da wani majivinci bayanSa. Kuma za ka ga azzalumai lokacin da suka ga azabar suna cewa: “Ina ma da akwai wata damar komawa (duniya)?”
وَتَرَىٰهُمۡ يُعۡرَضُونَ عَلَيۡهَا خَٰشِعِينَ مِنَ ٱلذُّلِّ يَنظُرُونَ مِن طَرۡفٍ خَفِيّٖۗ وَقَالَ ٱلَّذِينَ ءَامَنُوٓاْ إِنَّ ٱلۡخَٰسِرِينَ ٱلَّذِينَ خَسِرُوٓاْ أَنفُسَهُمۡ وَأَهۡلِيهِمۡ يَوۡمَ ٱلۡقِيَٰمَةِۗ أَلَآ إِنَّ ٱلظَّـٰلِمِينَ فِي عَذَابٖ مُّقِيمٖ
Kuma za ka gan su ana bijiro su a kanta (wutar) suna masu qanqan da kai na wulaqanci, suna kallo a sace. Waxanda kuma suka yi imani suka ce: “Lalle asararru su ne waxanda suka yi asarar rayuwarsu da ta iyalinsu a ranar alqiyama.” Ku saurara, lalle azzalumai suna cikin azaba dawwamammiya
وَمَا كَانَ لَهُم مِّنۡ أَوۡلِيَآءَ يَنصُرُونَهُم مِّن دُونِ ٱللَّهِۗ وَمَن يُضۡلِلِ ٱللَّهُ فَمَا لَهُۥ مِن سَبِيلٍ
Kuma ba su da wasu majivinta da za su taimake su in ban da Allah. Duk wanda Allah Ya vatar, to ba shi da wata hanya daban (ta shiriya)
ٱسۡتَجِيبُواْ لِرَبِّكُم مِّن قَبۡلِ أَن يَأۡتِيَ يَوۡمٞ لَّا مَرَدَّ لَهُۥ مِنَ ٱللَّهِۚ مَا لَكُم مِّن مَّلۡجَإٖ يَوۡمَئِذٖ وَمَا لَكُم مِّن نَّكِيرٖ
Ku amsa kiran Ubangijinku tun kafin ranar da ba ta da wata makauta[1] ta zo daga Allah. Ba ku da wata mafaka a wannan ranar, kuma ba ku da damar yin musu[2]
1- Watau babu wanda ya isa ya hana zuwanta.
2- Watau ba su da damar musunta zunuban da suka aikata a duniya.
فَإِنۡ أَعۡرَضُواْ فَمَآ أَرۡسَلۡنَٰكَ عَلَيۡهِمۡ حَفِيظًاۖ إِنۡ عَلَيۡكَ إِلَّا ٱلۡبَلَٰغُۗ وَإِنَّآ إِذَآ أَذَقۡنَا ٱلۡإِنسَٰنَ مِنَّا رَحۡمَةٗ فَرِحَ بِهَاۖ وَإِن تُصِبۡهُمۡ سَيِّئَةُۢ بِمَا قَدَّمَتۡ أَيۡدِيهِمۡ فَإِنَّ ٱلۡإِنسَٰنَ كَفُورٞ
To idan sun bijire, to ba Mu aika ka don ka zama mai gadin su ba; ba abin da yake kanka sai isar da saqo. Lalle kuma Mu idan Muka xanxana wa mutum wata rahama daga gare Mu sai ya riqa tutiya da ita. Idan kuma wani mummunan abu ya same su saboda abin da hannayensu suka aikata, to lalle shi mutum butulu ne
لِّلَّهِ مُلۡكُ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِۚ يَخۡلُقُ مَا يَشَآءُۚ يَهَبُ لِمَن يَشَآءُ إِنَٰثٗا وَيَهَبُ لِمَن يَشَآءُ ٱلذُّكُورَ
Mulkin sammai da qasa na Allah ne. Yana halittar abin da Ya ga dama. Yana ba da `ya`ya mata ga wanda Ya ga dama, Yana kuma ba da `ya`ya maza ga wanda Ya ga dama
أَوۡ يُزَوِّجُهُمۡ ذُكۡرَانٗا وَإِنَٰثٗاۖ وَيَجۡعَلُ مَن يَشَآءُ عَقِيمًاۚ إِنَّهُۥ عَلِيمٞ قَدِيرٞ
Ko kuma ya haxa musu maza da mata; Yakan kuma mayar da wanda ya ga dama bakarare. Lalle Shi Masani ne, Mai iko
۞وَمَا كَانَ لِبَشَرٍ أَن يُكَلِّمَهُ ٱللَّهُ إِلَّا وَحۡيًا أَوۡ مِن وَرَآيِٕ حِجَابٍ أَوۡ يُرۡسِلَ رَسُولٗا فَيُوحِيَ بِإِذۡنِهِۦ مَا يَشَآءُۚ إِنَّهُۥ عَلِيٌّ حَكِيمٞ
Kuma zai yiwu ga wani mutum a ce Allah Ya yi magana da shi ba (baki da baki), sai dai wahayi ko kuma ta bayan wani shamaki, ko kuwa Ya aiko wani manzo (mala’ika) sai ya yi masa wahayin abin da ya ga dama da yardarsa. Lalle Shi Maxaukaki ne, Mai hikima
وَكَذَٰلِكَ أَوۡحَيۡنَآ إِلَيۡكَ رُوحٗا مِّنۡ أَمۡرِنَاۚ مَا كُنتَ تَدۡرِي مَا ٱلۡكِتَٰبُ وَلَا ٱلۡإِيمَٰنُ وَلَٰكِن جَعَلۡنَٰهُ نُورٗا نَّهۡدِي بِهِۦ مَن نَّشَآءُ مِنۡ عِبَادِنَاۚ وَإِنَّكَ لَتَهۡدِيٓ إِلَىٰ صِرَٰطٖ مُّسۡتَقِيمٖ
Kuma kamar haka ne Muka yiwo maka wahayin Ruhi (watau Alqur’ani) daga umarninmu. Ba ka zamanto ka san mene ne littafi ko kuma imani ba, sai dai kuma Mun sanya shi (Alqur’ani) haske ne da Muke shiryar da wanda Muka ga dama daga bayinmu da shi. Lalle kuma kai tabbas kana shiryarwa zuwa ga tafarki madaidaici
صِرَٰطِ ٱللَّهِ ٱلَّذِي لَهُۥ مَا فِي ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَمَا فِي ٱلۡأَرۡضِۗ أَلَآ إِلَى ٱللَّهِ تَصِيرُ ٱلۡأُمُورُ
(Watau) tafarkin Allah wanda Yake da mulkin abin da yake cikin sammai da abin da yake qasa. Ku saurara, zuwa ga Allah ne kawai al’amura suke komawa