Capítulo: Suratur Rum

Verso : 31

۞مُنِيبِينَ إِلَيۡهِ وَٱتَّقُوهُ وَأَقِيمُواْ ٱلصَّلَوٰةَ وَلَا تَكُونُواْ مِنَ ٱلۡمُشۡرِكِينَ

(Kuma) kuna masu komawa zuwa gare Shi (wato Allah) kuma ku kiyaye dokokinsa ku kuma tsai da salla kuma kada ku zamanto cikin mushirikai



Capítulo: Suratur Rum

Verso : 32

مِنَ ٱلَّذِينَ فَرَّقُواْ دِينَهُمۡ وَكَانُواْ شِيَعٗاۖ كُلُّ حِزۡبِۭ بِمَا لَدَيۡهِمۡ فَرِحُونَ

Irin waxanda suka rarraba addininsu suka kuma zamanto qungiya-qungiya; kowacce qungiya tana mai farin ciki da abin da yake nata



Capítulo: Suratur Rum

Verso : 33

وَإِذَا مَسَّ ٱلنَّاسَ ضُرّٞ دَعَوۡاْ رَبَّهُم مُّنِيبِينَ إِلَيۡهِ ثُمَّ إِذَآ أَذَاقَهُم مِّنۡهُ رَحۡمَةً إِذَا فَرِيقٞ مِّنۡهُم بِرَبِّهِمۡ يُشۡرِكُونَ

Idan kuma wani matsi ya sami mutane sai su roqi Ubangijinsu suna masu komawa gare Shi, sannan kuma idan Ya xanxana musu rahama daga gare Shi sai ka ga wata qungiyar daga cikinsu suna tarayya da Ubangijinsu



Capítulo: Suratur Rum

Verso : 34

لِيَكۡفُرُواْ بِمَآ ءَاتَيۡنَٰهُمۡۚ فَتَمَتَّعُواْ فَسَوۡفَ تَعۡلَمُونَ

Don su kafirce wa abin da Muka ba su. To ku ji daxi, da sannu za ku sani



Capítulo: Suratur Rum

Verso : 35

أَمۡ أَنزَلۡنَا عَلَيۡهِمۡ سُلۡطَٰنٗا فَهُوَ يَتَكَلَّمُ بِمَا كَانُواْ بِهِۦ يُشۡرِكُونَ

Ko kuma Mun saukar musu da wani littafi ne wanda shi ne yake magana da abin da suka kasance suna shirka da shi?



Capítulo: Suratur Rum

Verso : 36

وَإِذَآ أَذَقۡنَا ٱلنَّاسَ رَحۡمَةٗ فَرِحُواْ بِهَاۖ وَإِن تُصِبۡهُمۡ سَيِّئَةُۢ بِمَا قَدَّمَتۡ أَيۡدِيهِمۡ إِذَا هُمۡ يَقۡنَطُونَ

Idan kuma Muka xanxana wa mutane rahama sai su yi farin ciki da ita; idan kuwa wata masifa ta same su saboda abin da hannayensu suka gabatar sai ka gan su suna xebe qauna



Capítulo: Suratur Rum

Verso : 37

أَوَلَمۡ يَرَوۡاْ أَنَّ ٱللَّهَ يَبۡسُطُ ٱلرِّزۡقَ لِمَن يَشَآءُ وَيَقۡدِرُۚ إِنَّ فِي ذَٰلِكَ لَأٓيَٰتٖ لِّقَوۡمٖ يُؤۡمِنُونَ

Yanzu ba su gani ba cewa Allah Yana shimfixa arziki ga wanda Ya ga dama, Yana kuma quntatawa (ga wanda ya ga dama)? Lalle a game da wannan tabbas akwai ayoyi ga mutanen da suke yin imani



Capítulo: Suratur Rum

Verso : 38

فَـَٔاتِ ذَا ٱلۡقُرۡبَىٰ حَقَّهُۥ وَٱلۡمِسۡكِينَ وَٱبۡنَ ٱلسَّبِيلِۚ ذَٰلِكَ خَيۡرٞ لِّلَّذِينَ يُرِيدُونَ وَجۡهَ ٱللَّهِۖ وَأُوْلَـٰٓئِكَ هُمُ ٱلۡمُفۡلِحُونَ

Sannan ka bai wa (xan’uwa) makusanci haqqinsa da miskini da matafiyi. Wannan shi ya fi alheri ga waxanda suke nufin Fuskar Allah; kuma waxannan su ne masu rabauta



Capítulo: Suratur Rum

Verso : 39

وَمَآ ءَاتَيۡتُم مِّن رِّبٗا لِّيَرۡبُوَاْ فِيٓ أَمۡوَٰلِ ٱلنَّاسِ فَلَا يَرۡبُواْ عِندَ ٱللَّهِۖ وَمَآ ءَاتَيۡتُم مِّن زَكَوٰةٖ تُرِيدُونَ وَجۡهَ ٱللَّهِ فَأُوْلَـٰٓئِكَ هُمُ ٱلۡمُضۡعِفُونَ

Kuma abin da kuka bayar na riba don ya qaru a cikin dukiyoyin mutane, to ba ya qaruwa a wurin Allah[1]; abin kuma da kuka bayar na zakka kuna masu nufin Fuskar Allah, to waxannan su ne masu ninninka (ladansu)


1- Da yawa daga cikin malamai sun fassara wannan gavar da cewa, ana nufin wanda zai bayar da kyauta yana nufin a mayar masa da fiye da abin da ya bayar, to ba shi da lada a wurin Allah.


Capítulo: Suratur Rum

Verso : 40

ٱللَّهُ ٱلَّذِي خَلَقَكُمۡ ثُمَّ رَزَقَكُمۡ ثُمَّ يُمِيتُكُمۡ ثُمَّ يُحۡيِيكُمۡۖ هَلۡ مِن شُرَكَآئِكُم مَّن يَفۡعَلُ مِن ذَٰلِكُم مِّن شَيۡءٖۚ سُبۡحَٰنَهُۥ وَتَعَٰلَىٰ عَمَّا يُشۡرِكُونَ

Allah (Shi ne) Wanda Ya halicce ku sannan Ya arzuta ku sannan Shi zai kashe ku sannan Ya raya ku; shin a cikin abokan tarayyarku akwai wanda zai aikata wani abu daga wannan? Tsarki ya tabbata a gare Shi, Ya kuma xaukaka daga abin da suke tarawa (da Shi)



Capítulo: Suratur Rum

Verso : 41

ظَهَرَ ٱلۡفَسَادُ فِي ٱلۡبَرِّ وَٱلۡبَحۡرِ بِمَا كَسَبَتۡ أَيۡدِي ٱلنَّاسِ لِيُذِيقَهُم بَعۡضَ ٱلَّذِي عَمِلُواْ لَعَلَّهُمۡ يَرۡجِعُونَ

Varna ta bayyana a kan tudu da kuma (cikin) ruwa saboda abubuwan da hannayen mutane suka aikata don a xanxana musu sashin abin da suka aikata, ko wataqila sa juyo



Capítulo: Suratur Rum

Verso : 42

قُلۡ سِيرُواْ فِي ٱلۡأَرۡضِ فَٱنظُرُواْ كَيۡفَ كَانَ عَٰقِبَةُ ٱلَّذِينَ مِن قَبۡلُۚ كَانَ أَكۡثَرُهُم مُّشۡرِكِينَ

Ka ce (da su): “Ku yi tafiya mana a bayan qasa sannan ku duba ku ga yadda qarshen waxanda suke gabaninku ya zama. Yawancinsu sun kasance mushirikai



Capítulo: Suratur Rum

Verso : 43

فَأَقِمۡ وَجۡهَكَ لِلدِّينِ ٱلۡقَيِّمِ مِن قَبۡلِ أَن يَأۡتِيَ يَوۡمٞ لَّا مَرَدَّ لَهُۥ مِنَ ٱللَّهِۖ يَوۡمَئِذٖ يَصَّدَّعُونَ

To sai ka tsai da fuskarka ga addini madaidaici tun kafin ranar nan da ba ta da makawa ta zo daga Allah; a wannan ranar ne (mutane) za su rarraba[1]


1- Watau wasu su tafi gidan Aljanna, wasu kuma su nufi wutar jahannama.


Capítulo: Suratur Rum

Verso : 44

مَن كَفَرَ فَعَلَيۡهِ كُفۡرُهُۥۖ وَمَنۡ عَمِلَ صَٰلِحٗا فَلِأَنفُسِهِمۡ يَمۡهَدُونَ

Wanda ya kafirta to zunubin kafircinsa yana kansa; waxanda kuwa suka yi aiki kyakkyawa, to kansu suke yi wa shimfixa (ta alheri)



Capítulo: Suratur Rum

Verso : 45

لِيَجۡزِيَ ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ وَعَمِلُواْ ٱلصَّـٰلِحَٰتِ مِن فَضۡلِهِۦٓۚ إِنَّهُۥ لَا يُحِبُّ ٱلۡكَٰفِرِينَ

Don (Allah) Ya saka wa waxanda suka yi imani suka yi ayyuka nagari daga falalarsa. Lalle Shi (Allah) ba Ya son kafirai



Capítulo: Suratur Rum

Verso : 46

وَمِنۡ ءَايَٰتِهِۦٓ أَن يُرۡسِلَ ٱلرِّيَاحَ مُبَشِّرَٰتٖ وَلِيُذِيقَكُم مِّن رَّحۡمَتِهِۦ وَلِتَجۡرِيَ ٱلۡفُلۡكُ بِأَمۡرِهِۦ وَلِتَبۡتَغُواْ مِن فَضۡلِهِۦ وَلَعَلَّكُمۡ تَشۡكُرُونَ

Yana kuma daga ayoyinsa cewa Yana aiko iska tana mai yin albishir (da ruwa) kuma don Ya xanxana muku rahamarsa, don kuma jiragen ruwa su riqa gudana da umarninsa, kuma don ku nema daga falalarsa ko kwa gode



Capítulo: Suratur Rum

Verso : 47

وَلَقَدۡ أَرۡسَلۡنَا مِن قَبۡلِكَ رُسُلًا إِلَىٰ قَوۡمِهِمۡ فَجَآءُوهُم بِٱلۡبَيِّنَٰتِ فَٱنتَقَمۡنَا مِنَ ٱلَّذِينَ أَجۡرَمُواْۖ وَكَانَ حَقًّا عَلَيۡنَا نَصۡرُ ٱلۡمُؤۡمِنِينَ

Haqiqa kuma Mun aiko wasu manzanni gabaninka zuwa ga mutanensu, sai suka zo musu da hujjoji bayyanannu, sai Muka azabtar da waxanda suka kafirce, kuma taimakon muminai ya zama haqqi ne a kanmu



Capítulo: Suratur Rum

Verso : 48

ٱللَّهُ ٱلَّذِي يُرۡسِلُ ٱلرِّيَٰحَ فَتُثِيرُ سَحَابٗا فَيَبۡسُطُهُۥ فِي ٱلسَّمَآءِ كَيۡفَ يَشَآءُ وَيَجۡعَلُهُۥ كِسَفٗا فَتَرَى ٱلۡوَدۡقَ يَخۡرُجُ مِنۡ خِلَٰلِهِۦۖ فَإِذَآ أَصَابَ بِهِۦ مَن يَشَآءُ مِنۡ عِبَادِهِۦٓ إِذَا هُمۡ يَسۡتَبۡشِرُونَ

Allah (Shi ne) wanda Yake aiko da iska sai ta motsa girgije, sai Ya shimfixa shi a (sararin) sama yadda Ya ga dama, Ya kuma sanya shi yanki-yanki, sai ka ga ruwa yana fitowa ta tsakaninsa, to idan Ya saukar da shi ga waxanda Ya ga dama daga bayinsa sai ka gan su suna ta murna



Capítulo: Suratur Rum

Verso : 49

وَإِن كَانُواْ مِن قَبۡلِ أَن يُنَزَّلَ عَلَيۡهِم مِّن قَبۡلِهِۦ لَمُبۡلِسِينَ

Ko da yake da can kafin a saukar musu shi tabbas sun kasance masu xebe qauna



Capítulo: Suratur Rum

Verso : 50

فَٱنظُرۡ إِلَىٰٓ ءَاثَٰرِ رَحۡمَتِ ٱللَّهِ كَيۡفَ يُحۡيِ ٱلۡأَرۡضَ بَعۡدَ مَوۡتِهَآۚ إِنَّ ذَٰلِكَ لَمُحۡيِ ٱلۡمَوۡتَىٰۖ وَهُوَ عَلَىٰ كُلِّ شَيۡءٖ قَدِيرٞ

To sai ka yi duba ga guraben rahamar Allah (ka ga) yadda Yake raya qasa bayan mutuwarta. Lalle wannan tabbas Mai raya matattu ne, kuma Mai iko ne a kan komai



Capítulo: Suratur Rum

Verso : 51

وَلَئِنۡ أَرۡسَلۡنَا رِيحٗا فَرَأَوۡهُ مُصۡفَرّٗا لَّظَلُّواْ مِنۢ بَعۡدِهِۦ يَكۡفُرُونَ

Tabbas kuma in da za Mu aiko da iska su gan shi (wato amfanin gonarsu) ya yi fatsi-fatsi da sai sun ci gaba da kafirce wa (Allah) bayan haka



Capítulo: Suratur Rum

Verso : 52

فَإِنَّكَ لَا تُسۡمِعُ ٱلۡمَوۡتَىٰ وَلَا تُسۡمِعُ ٱلصُّمَّ ٱلدُّعَآءَ إِذَا وَلَّوۡاْ مُدۡبِرِينَ

To lalle kai ba ka iya jiyar da matattu, kuma ba ka iya jiyar da kurame kira lokacin da suka juya suna masu ba da baya



Capítulo: Suratur Rum

Verso : 53

وَمَآ أَنتَ بِهَٰدِ ٱلۡعُمۡيِ عَن ضَلَٰلَتِهِمۡۖ إِن تُسۡمِعُ إِلَّا مَن يُؤۡمِنُ بِـَٔايَٰتِنَا فَهُم مُّسۡلِمُونَ

Kuma kai ba mai iya shiryar da makafi (wato vatattu) ba ne daga vatansu; ba waxanda kake iya jiyarwa sai waxanda suka yi imani da ayoyinmu don haka suna masu miqa wuya



Capítulo: Suratur Rum

Verso : 54

۞ٱللَّهُ ٱلَّذِي خَلَقَكُم مِّن ضَعۡفٖ ثُمَّ جَعَلَ مِنۢ بَعۡدِ ضَعۡفٖ قُوَّةٗ ثُمَّ جَعَلَ مِنۢ بَعۡدِ قُوَّةٖ ضَعۡفٗا وَشَيۡبَةٗۚ يَخۡلُقُ مَا يَشَآءُۚ وَهُوَ ٱلۡعَلِيمُ ٱلۡقَدِيرُ

Allah (Shi ne) Wanda Ya halicce ku daga rauni, sannan kuma Ya sanya qarfi bayan raunin, sannan kuma Ya sanya rauni da furfura bayan qarfi. Yana halittar abin da Ya ga dama; Shi ne kuwa Masani, Mai iko



Capítulo: Suratur Rum

Verso : 55

وَيَوۡمَ تَقُومُ ٱلسَّاعَةُ يُقۡسِمُ ٱلۡمُجۡرِمُونَ مَا لَبِثُواْ غَيۡرَ سَاعَةٖۚ كَذَٰلِكَ كَانُواْ يُؤۡفَكُونَ

Kuma a ranar da alqiyama za ta tashi masu manyan laifuka za su rantse (kan) ba su zauna ba (a qaburburansu) fiye da sa’a xaya. Kamar haka suka kasance ana karkatar da su (daga gaskiya)



Capítulo: Suratur Rum

Verso : 56

وَقَالَ ٱلَّذِينَ أُوتُواْ ٱلۡعِلۡمَ وَٱلۡإِيمَٰنَ لَقَدۡ لَبِثۡتُمۡ فِي كِتَٰبِ ٱللَّهِ إِلَىٰ يَوۡمِ ٱلۡبَعۡثِۖ فَهَٰذَا يَوۡمُ ٱلۡبَعۡثِ وَلَٰكِنَّكُمۡ كُنتُمۡ لَا تَعۡلَمُونَ

Waxanda kuwa aka bai wa ilimi da imani sai suka ce: “Haqiqa kun zauna ne gwargwadon yadda Allah Ya rubuta muku a littafinsa har zuwa ranar tashi; to wannan kuma ita ce ranar tashin, sai dai kuma ku kun kasance ba ku san (haka) ba.”



Capítulo: Suratur Rum

Verso : 57

فَيَوۡمَئِذٖ لَّا يَنفَعُ ٱلَّذِينَ ظَلَمُواْ مَعۡذِرَتُهُمۡ وَلَا هُمۡ يُسۡتَعۡتَبُونَ

To a wannan ranar waxanda suka yi zalunci hanzarinsu ba zai amfane su ba, kuma ba za a nemi su kawo wani uzuri ba



Capítulo: Suratur Rum

Verso : 58

وَلَقَدۡ ضَرَبۡنَا لِلنَّاسِ فِي هَٰذَا ٱلۡقُرۡءَانِ مِن كُلِّ مَثَلٖۚ وَلَئِن جِئۡتَهُم بِـَٔايَةٖ لَّيَقُولَنَّ ٱلَّذِينَ كَفَرُوٓاْ إِنۡ أَنتُمۡ إِلَّا مُبۡطِلُونَ

Kuma haqiqa Mun ba wa mutane kowane irin misali a cikin wannan Alqur’anin. Kuma tabbas idan da za ka zo musu da wata aya lallai da waxanda suka kafirce sun ce: “Ai ku mavarnata ne kawai.”



Capítulo: Suratur Rum

Verso : 59

كَذَٰلِكَ يَطۡبَعُ ٱللَّهُ عَلَىٰ قُلُوبِ ٱلَّذِينَ لَا يَعۡلَمُونَ

Kamar haka ne Allah Yake toshe zukatan waxanda ba sa sanin (gaskiya)



Capítulo: Suratur Rum

Verso : 60

فَٱصۡبِرۡ إِنَّ وَعۡدَ ٱللَّهِ حَقّٞۖ وَلَا يَسۡتَخِفَّنَّكَ ٱلَّذِينَ لَا يُوقِنُونَ

Sai ka yi haquri, lalle alqawarin Allah gaskiya ne; kada kuma waxanda ba sa sakankancewa (da alqiyama) su ingiza ka (har ka kasa haquri)