Capítulo: Suratu Yusuf 

Verso : 31

فَلَمَّا سَمِعَتۡ بِمَكۡرِهِنَّ أَرۡسَلَتۡ إِلَيۡهِنَّ وَأَعۡتَدَتۡ لَهُنَّ مُتَّكَـٔٗا وَءَاتَتۡ كُلَّ وَٰحِدَةٖ مِّنۡهُنَّ سِكِّينٗا وَقَالَتِ ٱخۡرُجۡ عَلَيۡهِنَّۖ فَلَمَّا رَأَيۡنَهُۥٓ أَكۡبَرۡنَهُۥ وَقَطَّعۡنَ أَيۡدِيَهُنَّ وَقُلۡنَ حَٰشَ لِلَّهِ مَا هَٰذَا بَشَرًا إِنۡ هَٰذَآ إِلَّا مَلَكٞ كَرِيمٞ

Lokacin da ta ji irin tsegungumansu, sai ta aika musu (da gayyata), ta kuma tanadar musu wurin zaman cin abinci, kuma ta bai wa kowacce xayarsu wuqa, ta kuma ce (da Annabi Yusufu): “Fita ka gilma ta gabansu.” Lokacin da suka gan shi sai suka girmama shi suka yanyanke hannayensu, suka kuma ce: “Tsarki ya tabbata ga Allah; ai wannan ba mutum ba ne; wannan babban mala’ika ne kawai!”



Capítulo: Suratu Yusuf 

Verso : 32

قَالَتۡ فَذَٰلِكُنَّ ٱلَّذِي لُمۡتُنَّنِي فِيهِۖ وَلَقَدۡ رَٰوَدتُّهُۥ عَن نَّفۡسِهِۦ فَٱسۡتَعۡصَمَۖ وَلَئِن لَّمۡ يَفۡعَلۡ مَآ ءَامُرُهُۥ لَيُسۡجَنَنَّ وَلَيَكُونٗا مِّنَ ٱلصَّـٰغِرِينَ

Ta ce: “To wannan shi ne wanda kuka zarge ni a kansa. Haqiqa kuma na neme shi sai ya qi yarda; Wallahi kuwa in bai aikata abin da na umarce shi ba, to za a sa shi kurkuku, kuma lalle zai zamanto cikin wulaqantattu.”



Capítulo: Suratu Yusuf 

Verso : 33

قَالَ رَبِّ ٱلسِّجۡنُ أَحَبُّ إِلَيَّ مِمَّا يَدۡعُونَنِيٓ إِلَيۡهِۖ وَإِلَّا تَصۡرِفۡ عَنِّي كَيۡدَهُنَّ أَصۡبُ إِلَيۡهِنَّ وَأَكُن مِّنَ ٱلۡجَٰهِلِينَ

(Annabi Yusufu) Ya ce: “Ya Ubangijina, kurkuku shi ya fi soyuwa a gare ni kan abin da suke nema na da shi. Idan kuwa ba Ka ije mini makircinsu ba, to zan karkata gare su kuma in zama cikin jahilai.”



Capítulo: Suratu Yusuf 

Verso : 34

فَٱسۡتَجَابَ لَهُۥ رَبُّهُۥ فَصَرَفَ عَنۡهُ كَيۡدَهُنَّۚ إِنَّهُۥ هُوَ ٱلسَّمِيعُ ٱلۡعَلِيمُ

To sai Ubangijinsa Ya amsa masa, sai Ya ije masa makircin nasu. Lalle Shi ne Mai ji kuma Masani



Capítulo: Suratu Yusuf 

Verso : 35

ثُمَّ بَدَا لَهُم مِّنۢ بَعۡدِ مَا رَأَوُاْ ٱلۡأٓيَٰتِ لَيَسۡجُنُنَّهُۥ حَتَّىٰ حِينٖ

Sannan bayan duk sun ga ayoyin (da suke wanke Yusufu daga zargi) sai suka ga dai cewa lalle gara su xaure shi har zuwa wani lokaci



Capítulo: Suratu Yusuf 

Verso : 36

وَدَخَلَ مَعَهُ ٱلسِّجۡنَ فَتَيَانِۖ قَالَ أَحَدُهُمَآ إِنِّيٓ أَرَىٰنِيٓ أَعۡصِرُ خَمۡرٗاۖ وَقَالَ ٱلۡأٓخَرُ إِنِّيٓ أَرَىٰنِيٓ أَحۡمِلُ فَوۡقَ رَأۡسِي خُبۡزٗا تَأۡكُلُ ٱلطَّيۡرُ مِنۡهُۖ نَبِّئۡنَا بِتَأۡوِيلِهِۦٓۖ إِنَّا نَرَىٰكَ مِنَ ٱلۡمُحۡسِنِينَ

Wasu samari su biyu kuma suka shiga kurkukun tare da shi; xaya daga cikinsu ya ce: “Lalle na yi mafarki ina matsar giya.” Xayan kuma ya ce: “Lalle na yi mafarki ina xauke da gurasa a kaina, tsuntsaye suna caccakar ta. Ba mu labarin fassararsa; lalle muna ganin ka kana cikin mutane nagari.”



Capítulo: Suratu Yusuf 

Verso : 37

قَالَ لَا يَأۡتِيكُمَا طَعَامٞ تُرۡزَقَانِهِۦٓ إِلَّا نَبَّأۡتُكُمَا بِتَأۡوِيلِهِۦ قَبۡلَ أَن يَأۡتِيَكُمَاۚ ذَٰلِكُمَا مِمَّا عَلَّمَنِي رَبِّيٓۚ إِنِّي تَرَكۡتُ مِلَّةَ قَوۡمٖ لَّا يُؤۡمِنُونَ بِٱللَّهِ وَهُم بِٱلۡأٓخِرَةِ هُمۡ كَٰفِرُونَ

Ya ce: “Babu wani abinci da za a kawo muku sai na iya ba ku labarinsa tun ma kafin a kawo muku shi. Wannan yana daga abin da Ubangijina Ya sanar da ni; lalle ni na bar hanyar mutanen da ba sa ba da gaskiya da Allah, su kuma suna masu kafircewa da ranar lahira



Capítulo: Suratu Yusuf 

Verso : 38

وَٱتَّبَعۡتُ مِلَّةَ ءَابَآءِيٓ إِبۡرَٰهِيمَ وَإِسۡحَٰقَ وَيَعۡقُوبَۚ مَا كَانَ لَنَآ أَن نُّشۡرِكَ بِٱللَّهِ مِن شَيۡءٖۚ ذَٰلِكَ مِن فَضۡلِ ٱللَّهِ عَلَيۡنَا وَعَلَى ٱلنَّاسِ وَلَٰكِنَّ أَكۡثَرَ ٱلنَّاسِ لَا يَشۡكُرُونَ

“Na kuma bi hanyar iyayena Ibrahimu da Is’haqa da kuma Yaqubu. Bai kamace mu ba a ce mu tara wani abu da Allah. Wannan yana daga falalar Allah a gare mu da kuma sauran mutane, sai dai kuma yawancin mutane ba sa godewa



Capítulo: Suratu Yusuf 

Verso : 39

يَٰصَٰحِبَيِ ٱلسِّجۡنِ ءَأَرۡبَابٞ مُّتَفَرِّقُونَ خَيۡرٌ أَمِ ٱللَّهُ ٱلۡوَٰحِدُ ٱلۡقَهَّارُ

“Ya abokaina na kurkuku, yanzu iyayen giji barkatai su suka fi, ko kuwa Allah Xaya Mai rinjaye?



Capítulo: Suratu Yusuf 

Verso : 40

مَا تَعۡبُدُونَ مِن دُونِهِۦٓ إِلَّآ أَسۡمَآءٗ سَمَّيۡتُمُوهَآ أَنتُمۡ وَءَابَآؤُكُم مَّآ أَنزَلَ ٱللَّهُ بِهَا مِن سُلۡطَٰنٍۚ إِنِ ٱلۡحُكۡمُ إِلَّا لِلَّهِ أَمَرَ أَلَّا تَعۡبُدُوٓاْ إِلَّآ إِيَّاهُۚ ذَٰلِكَ ٱلدِّينُ ٱلۡقَيِّمُ وَلَٰكِنَّ أَكۡثَرَ ٱلنَّاسِ لَا يَعۡلَمُونَ

“Ba komai kuke bauta wa ba- bayan Allah- sai wasu sunaye da kuka qaga ku da iyayenku, waxanda Allah bai saukar da wata hujja game da su ba. Hukunci na Allah ne kawai; Ya yi umarni cewa kada ku bauta wa kowa sai Shi kaxai. Wannan shi ne addini miqaqqe, sai dai yawancin mutane ba sa sanin (haka)



Capítulo: Suratu Yusuf 

Verso : 41

يَٰصَٰحِبَيِ ٱلسِّجۡنِ أَمَّآ أَحَدُكُمَا فَيَسۡقِي رَبَّهُۥ خَمۡرٗاۖ وَأَمَّا ٱلۡأٓخَرُ فَيُصۡلَبُ فَتَأۡكُلُ ٱلطَّيۡرُ مِن رَّأۡسِهِۦۚ قُضِيَ ٱلۡأَمۡرُ ٱلَّذِي فِيهِ تَسۡتَفۡتِيَانِ

“Ya abokaina na kurkuku, amma xaya daga cikinku zai riqa shayar da mai gidansa giya ne; amma xaya kuwa za a tsire shi ne, sannan tsuntsaye su zo su riqa cakar kansa. An zartar da al’amarin da kuke fatawa game da shi.”



Capítulo: Suratu Yusuf 

Verso : 42

وَقَالَ لِلَّذِي ظَنَّ أَنَّهُۥ نَاجٖ مِّنۡهُمَا ٱذۡكُرۡنِي عِندَ رَبِّكَ فَأَنسَىٰهُ ٱلشَّيۡطَٰنُ ذِكۡرَ رَبِّهِۦ فَلَبِثَ فِي ٱلسِّجۡنِ بِضۡعَ سِنِينَ

Kuma ya ce wa wanda ya tabbatar da cewa shi zai tsira daga cikinsu: “Ka tuna wa mai gidanka ni;” sai Shaixan ya mantar da shi tuna wa mai gidan nasa, sai ya zauna a kurkuku ‘yan shekaru



Capítulo: Suratu Yusuf 

Verso : 43

وَقَالَ ٱلۡمَلِكُ إِنِّيٓ أَرَىٰ سَبۡعَ بَقَرَٰتٖ سِمَانٖ يَأۡكُلُهُنَّ سَبۡعٌ عِجَافٞ وَسَبۡعَ سُنۢبُلَٰتٍ خُضۡرٖ وَأُخَرَ يَابِسَٰتٖۖ يَـٰٓأَيُّهَا ٱلۡمَلَأُ أَفۡتُونِي فِي رُءۡيَٰيَ إِن كُنتُمۡ لِلرُّءۡيَا تَعۡبُرُونَ

Sarki kuma ya ce (da jama’arsa): “Lalle na yi mafarkin shanu guda bakwai masu qiba da wasu bakwan qanjamammu suna cinye su da kuma zangarnu guda bakwai koraye da wasu bakwai busassu. Ya ku manyan malamai, ku sanar da ni fassarar mafarkin nan nawa in kun iya fassara mafarki.”



Capítulo: Suratu Yusuf 

Verso : 44

قَالُوٓاْ أَضۡغَٰثُ أَحۡلَٰمٖۖ وَمَا نَحۡنُ بِتَأۡوِيلِ ٱلۡأَحۡلَٰمِ بِعَٰلِمِينَ

Suka ce: “Ai (wannan) kwashe-kwashen mafarki ne (kawai); mu kuma ba masana fassarar mafarki ne ba.”



Capítulo: Suratu Yusuf 

Verso : 45

وَقَالَ ٱلَّذِي نَجَا مِنۡهُمَا وَٱدَّكَرَ بَعۡدَ أُمَّةٍ أَنَا۠ أُنَبِّئُكُم بِتَأۡوِيلِهِۦ فَأَرۡسِلُونِ

Wanda kuwa ya tsiran nan daga cikinsu, ya kuma tuna bayan zamani mai tsawo, ya ce: “Ni zan ba ku labarin fassararsa; to ku aike ni.”



Capítulo: Suratu Yusuf 

Verso : 46

يُوسُفُ أَيُّهَا ٱلصِّدِّيقُ أَفۡتِنَا فِي سَبۡعِ بَقَرَٰتٖ سِمَانٖ يَأۡكُلُهُنَّ سَبۡعٌ عِجَافٞ وَسَبۡعِ سُنۢبُلَٰتٍ خُضۡرٖ وَأُخَرَ يَابِسَٰتٖ لَّعَلِّيٓ أَرۡجِعُ إِلَى ٱلنَّاسِ لَعَلَّهُمۡ يَعۡلَمُونَ

(Ya zo kurkuku ya ce): “Ya Yusufu, ya mai riqon gaskiya, ka ba mu fatawar (mafarki) game da shanu bakwai masu qiba ga wasu bakwan qanjamammu suna cinye su, da kuma zangarnu guda bakwai korayr da wasu bakwai busassu, don in koma wajen mutanen (da suka turo ni) saboda su sani.”



Capítulo: Suratu Yusuf 

Verso : 47

قَالَ تَزۡرَعُونَ سَبۡعَ سِنِينَ دَأَبٗا فَمَا حَصَدتُّمۡ فَذَرُوهُ فِي سُنۢبُلِهِۦٓ إِلَّا قَلِيلٗا مِّمَّا تَأۡكُلُونَ

(Annabi Yusufu) ya ce: “Za ku yi noma shekara bakwai a jere; to abin da kuka girba sai ku bar shi a zangarniyarsa, sai kaxan daga abin da za ku ci



Capítulo: Suratu Yusuf 

Verso : 48

ثُمَّ يَأۡتِي مِنۢ بَعۡدِ ذَٰلِكَ سَبۡعٞ شِدَادٞ يَأۡكُلۡنَ مَا قَدَّمۡتُمۡ لَهُنَّ إِلَّا قَلِيلٗا مِّمَّا تُحۡصِنُونَ

“Sannan bayan wannan wasu (shekarun) bakwai masu tsanani za su zo su cinye abin da kuka tanada a cikinsu, sai xan kaxan daga abin da kuke adanawa



Capítulo: Suratu Yusuf 

Verso : 49

ثُمَّ يَأۡتِي مِنۢ بَعۡدِ ذَٰلِكَ عَامٞ فِيهِ يُغَاثُ ٱلنَّاسُ وَفِيهِ يَعۡصِرُونَ

“Sannan kuma wata shekara za ta zo wadda a cikinta ne mutane za su sami ruwa, a cikinta ne kuma za su tatsi (abubuwan sha).”



Capítulo: Suratu Yusuf 

Verso : 50

وَقَالَ ٱلۡمَلِكُ ٱئۡتُونِي بِهِۦۖ فَلَمَّا جَآءَهُ ٱلرَّسُولُ قَالَ ٱرۡجِعۡ إِلَىٰ رَبِّكَ فَسۡـَٔلۡهُ مَا بَالُ ٱلنِّسۡوَةِ ٱلَّـٰتِي قَطَّعۡنَ أَيۡدِيَهُنَّۚ إِنَّ رَبِّي بِكَيۡدِهِنَّ عَلِيمٞ

Sarki kuwa ya ce: “Ku zo min da shi.” Lokacin da xan aiken ya zo masa (ya ce Sarki na kira), sai ya ce: “Koma wurin mai gidanka ka tambaye shi, mene ne halin matan da suka yanyanke hannayensu? Lalle Ubangijina Yana sane da makircinsu.”



Capítulo: Suratu Yusuf 

Verso : 51

قَالَ مَا خَطۡبُكُنَّ إِذۡ رَٰوَدتُّنَّ يُوسُفَ عَن نَّفۡسِهِۦۚ قُلۡنَ حَٰشَ لِلَّهِ مَا عَلِمۡنَا عَلَيۡهِ مِن سُوٓءٖۚ قَالَتِ ٱمۡرَأَتُ ٱلۡعَزِيزِ ٱلۡـَٰٔنَ حَصۡحَصَ ٱلۡحَقُّ أَنَا۠ رَٰوَدتُّهُۥ عَن نَّفۡسِهِۦ وَإِنَّهُۥ لَمِنَ ٱلصَّـٰدِقِينَ

(Sarki) ya ce: “Mene ne labarinku lokacin da kuka nemi Yusufu da lalata?” Suka ce: “Tsarki ya tabbata ga Allah; ba mu san wani mummunan abu game da shi ba.” Matar Azizu ta ce: “Yanzu kam gaskiya ta bayyana; ni ce da kaina na nemi lalata da shi; lalle kuma shi yana cikin masu gaskiya



Capítulo: Suratu Yusuf 

Verso : 52

ذَٰلِكَ لِيَعۡلَمَ أَنِّي لَمۡ أَخُنۡهُ بِٱلۡغَيۡبِ وَأَنَّ ٱللَّهَ لَا يَهۡدِي كَيۡدَ ٱلۡخَآئِنِينَ

“Wannan kuwa don ya san cewa ni ban ha’ince shi a bayan idonsa ba, kuma lalle Allah ba Ya shiryar da makircin masu ha’inci



Capítulo: Suratu Yusuf 

Verso : 53

۞وَمَآ أُبَرِّئُ نَفۡسِيٓۚ إِنَّ ٱلنَّفۡسَ لَأَمَّارَةُۢ بِٱلسُّوٓءِ إِلَّا مَا رَحِمَ رَبِّيٓۚ إِنَّ رَبِّي غَفُورٞ رَّحِيمٞ

“Ba kuma wai ina wanke kaina ba ne. Babu shakka xabi’ar rai ce ta umarci mutum da yin mummunan abu, sai fa wanda Ubangijina Ya yi wa jin qai. Lalle Ubangijina Mai gafara ne Mai jin qai.”



Capítulo: Suratu Yusuf 

Verso : 54

وَقَالَ ٱلۡمَلِكُ ٱئۡتُونِي بِهِۦٓ أَسۡتَخۡلِصۡهُ لِنَفۡسِيۖ فَلَمَّا كَلَّمَهُۥ قَالَ إِنَّكَ ٱلۡيَوۡمَ لَدَيۡنَا مَكِينٌ أَمِينٞ

Sarki kuma ya ce: “Ku zo min da shi in mai da shi xan-gaban-goshina.” Lokacin da ya yi magana da shi sai ya ce: “Lalle kai kam a yau kana da matsayi (babba, kuma kai) amintacce ne a wurinmu!”



Capítulo: Suratu Yusuf 

Verso : 55

قَالَ ٱجۡعَلۡنِي عَلَىٰ خَزَآئِنِ ٱلۡأَرۡضِۖ إِنِّي حَفِيظٌ عَلِيمٞ

(Yusufu) Ya ce: “Ka naxa ni mai kula da taskokin qasa, lalle ni mai kiyaye (amana) ne, masani.”



Capítulo: Suratu Yusuf 

Verso : 56

وَكَذَٰلِكَ مَكَّنَّا لِيُوسُفَ فِي ٱلۡأَرۡضِ يَتَبَوَّأُ مِنۡهَا حَيۡثُ يَشَآءُۚ نُصِيبُ بِرَحۡمَتِنَا مَن نَّشَآءُۖ وَلَا نُضِيعُ أَجۡرَ ٱلۡمُحۡسِنِينَ

Kamar haka ne Muka kafa Yusufu a bayan qasa; yana zama a cikinta inda ya ga dama. Muna bayar da rahamarmu ga wanda Muka ga dama, ba kuwa za Mu tozarta ladan masu kyautatawa ba



Capítulo: Suratu Yusuf 

Verso : 57

وَلَأَجۡرُ ٱلۡأٓخِرَةِ خَيۡرٞ لِّلَّذِينَ ءَامَنُواْ وَكَانُواْ يَتَّقُونَ

Kuma lalle ladan lahira shi ya fi ga waxanda suka yi imani kuma suka zamanto suna kiyaye dokokin (Allah)



Capítulo: Suratu Yusuf 

Verso : 58

وَجَآءَ إِخۡوَةُ يُوسُفَ فَدَخَلُواْ عَلَيۡهِ فَعَرَفَهُمۡ وَهُمۡ لَهُۥ مُنكِرُونَ

‘Yan’uwan Yusufu kuma suka zo suka shiga wurinsa sai ya gane su, sai dai su ba su shaida shi ba[1]


1- Saboda kamanninsa sun canza bayan shekaru da ya kwashe ba ya tare da su.


Capítulo: Suratu Yusuf 

Verso : 59

وَلَمَّا جَهَّزَهُم بِجَهَازِهِمۡ قَالَ ٱئۡتُونِي بِأَخٖ لَّكُم مِّنۡ أَبِيكُمۡۚ أَلَا تَرَوۡنَ أَنِّيٓ أُوفِي ٱلۡكَيۡلَ وَأَنَا۠ خَيۡرُ ٱلۡمُنزِلِينَ

Lokacin da ya haxa musu kayan abincinsu, sai ya ce: “Ku zo min da xan’uwanku na wajen uba[1]. Ashe ba kwa ganin irin yadda nake cika mudu, kuma ni ne mafi kyautata wa baqi?


1- Shi ne shaqiqinsa Binyaminu.


Capítulo: Suratu Yusuf 

Verso : 60

فَإِن لَّمۡ تَأۡتُونِي بِهِۦ فَلَا كَيۡلَ لَكُمۡ عِندِي وَلَا تَقۡرَبُونِ

“To idan ba ku zo min da shi ba to fa ba ku da wani awo ke nan a wurina (nan gaba), kuma kada ma ku kusanto ni!”