Capítulo: Suratul Qasas

Verso : 64

وَقِيلَ ٱدۡعُواْ شُرَكَآءَكُمۡ فَدَعَوۡهُمۡ فَلَمۡ يَسۡتَجِيبُواْ لَهُمۡ وَرَأَوُاْ ٱلۡعَذَابَۚ لَوۡ أَنَّهُمۡ كَانُواْ يَهۡتَدُونَ

Kuma aka ce: “Ku kirawo abokan tarayyar naku”, sannan suka kirawo su, sai ba su amsa musu ba, suka kuma ga azaba. (Suka riqa burin) ina ma sun kasance shiryayyu!



Capítulo: Suratul Ankabut

Verso : 17

إِنَّمَا تَعۡبُدُونَ مِن دُونِ ٱللَّهِ أَوۡثَٰنٗا وَتَخۡلُقُونَ إِفۡكًاۚ إِنَّ ٱلَّذِينَ تَعۡبُدُونَ مِن دُونِ ٱللَّهِ لَا يَمۡلِكُونَ لَكُمۡ رِزۡقٗا فَٱبۡتَغُواْ عِندَ ٱللَّهِ ٱلرِّزۡقَ وَٱعۡبُدُوهُ وَٱشۡكُرُواْ لَهُۥٓۖ إِلَيۡهِ تُرۡجَعُونَ

Lalle abin da kuke bauta wa ba Allah ba gumaka ne kawai, kuna kuma qirqirar qarya ne[1]. Lalle waxanda kuke bauta wa ba Allah ba, ba su mallaki wani arziki ba gare ku, sai ku nemi arziki a wurin Allah, kuma ku bauta masa, ku kuma gode masa; gare Shi ne kawai za a mayar da ku


1- Domin su ne suke sassaqa su da hannayensu suke kuma sanya musu sunaye sannan su bauta musu.


Capítulo: Suratul Ankabut

Verso : 25

وَقَالَ إِنَّمَا ٱتَّخَذۡتُم مِّن دُونِ ٱللَّهِ أَوۡثَٰنٗا مَّوَدَّةَ بَيۡنِكُمۡ فِي ٱلۡحَيَوٰةِ ٱلدُّنۡيَاۖ ثُمَّ يَوۡمَ ٱلۡقِيَٰمَةِ يَكۡفُرُ بَعۡضُكُم بِبَعۡضٖ وَيَلۡعَنُ بَعۡضُكُم بَعۡضٗا وَمَأۡوَىٰكُمُ ٱلنَّارُ وَمَا لَكُم مِّن نَّـٰصِرِينَ

Kuma ya ce (da su): “Lalle ba abin da kuka riqa wanin Allah sai gumaka kawai don qauna da take tsakaninku a rayuwar duniya; sannan ranar alqiyama wasunku za su kafirce wa wasu, kuma wasunku za su la’anci wasu, makomarku kuma wuta ce, ba ku da kuwa wasu mataimaka.”



Capítulo: Suratul Ankabut

Verso : 52

قُلۡ كَفَىٰ بِٱللَّهِ بَيۡنِي وَبَيۡنَكُمۡ شَهِيدٗاۖ يَعۡلَمُ مَا فِي ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِۗ وَٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ بِٱلۡبَٰطِلِ وَكَفَرُواْ بِٱللَّهِ أُوْلَـٰٓئِكَ هُمُ ٱلۡخَٰسِرُونَ

Ka ce (da su): “Allah Ya isa shaida tsakanina da ku; Yana sane da abin da yake cikin sammai da qasa. Waxanda kuwa suka yi imani da qarya suka kuma kafirce wa Allah, waxannan su ne asararru.”



Capítulo: Suratu Luqman

Verso : 30

ذَٰلِكَ بِأَنَّ ٱللَّهَ هُوَ ٱلۡحَقُّ وَأَنَّ مَا يَدۡعُونَ مِن دُونِهِ ٱلۡبَٰطِلُ وَأَنَّ ٱللَّهَ هُوَ ٱلۡعَلِيُّ ٱلۡكَبِيرُ

Wannan kuwa (suna samuwa ne) saboda Allah Shi ne Gaskiya, lalle kuma abin da suke bauta wa ba Shi ba qarya ne, lalle kuma Shi Allah Maxaukaki ne, Mai girma



Capítulo: Suratu Saba’i

Verso : 22

قُلِ ٱدۡعُواْ ٱلَّذِينَ زَعَمۡتُم مِّن دُونِ ٱللَّهِ لَا يَمۡلِكُونَ مِثۡقَالَ ذَرَّةٖ فِي ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَلَا فِي ٱلۡأَرۡضِ وَمَا لَهُمۡ فِيهِمَا مِن شِرۡكٖ وَمَا لَهُۥ مِنۡهُم مِّن ظَهِيرٖ

Ka ce: “Ku kirawo waxanda kuka riya (cewa su ne iyayen giji) ba Allah ba;” ba sa mallakar wani abu daidai da qwayar zarra a cikin sammai ko a cikin qasa, ba kuma su da wata tarayya a cikinsu, ba Shi kuma da wani mataimaki daga cikinsu



Capítulo: Suratu Saba’i

Verso : 49

قُلۡ جَآءَ ٱلۡحَقُّ وَمَا يُبۡدِئُ ٱلۡبَٰطِلُ وَمَا يُعِيدُ

Ka ce: “Gaskiya ta zo qarya kuma ba za ta sake faruwa ba, ba kuma za ta dawo ba.”



Capítulo: Suratu Faxir

Verso : 14

إِن تَدۡعُوهُمۡ لَا يَسۡمَعُواْ دُعَآءَكُمۡ وَلَوۡ سَمِعُواْ مَا ٱسۡتَجَابُواْ لَكُمۡۖ وَيَوۡمَ ٱلۡقِيَٰمَةِ يَكۡفُرُونَ بِشِرۡكِكُمۡۚ وَلَا يُنَبِّئُكَ مِثۡلُ خَبِيرٖ

Idan kuna kiran su, ba sa jin kiranku, ko da ma sun ji, ba za su amsa muku ba; a ranar alqiyama kuma za su butulce wa shirkarku. Ba kuwa mai ba ka labari kamar cikakken Masani



Capítulo: Suratu Faxir

Verso : 40

قُلۡ أَرَءَيۡتُمۡ شُرَكَآءَكُمُ ٱلَّذِينَ تَدۡعُونَ مِن دُونِ ٱللَّهِ أَرُونِي مَاذَا خَلَقُواْ مِنَ ٱلۡأَرۡضِ أَمۡ لَهُمۡ شِرۡكٞ فِي ٱلسَّمَٰوَٰتِ أَمۡ ءَاتَيۡنَٰهُمۡ كِتَٰبٗا فَهُمۡ عَلَىٰ بَيِّنَتٖ مِّنۡهُۚ بَلۡ إِن يَعِدُ ٱلظَّـٰلِمُونَ بَعۡضُهُم بَعۡضًا إِلَّا غُرُورًا

Ka ce: “Ku ba ni labarin abokan tarayyar naku da kuke bauta wa ba Allah ba, ku nuna min abin da suka halitta daga qasa, ko kuma suna da wata tarayya ne a cikin (halittar) sammai, ko kuma Mun ba su wani littafi ne, saboda haka suke da wata hujja daga wajensa?” Ba haka ba ne, ba dai abin da azzalumai suke wa juna alqawari da shi in ban da ruxi



Capítulo: Suratu Yasin

Verso : 22

وَمَالِيَ لَآ أَعۡبُدُ ٱلَّذِي فَطَرَنِي وَإِلَيۡهِ تُرۡجَعُونَ

“Ni kuma me zai hana ni in bauta wa wanda Ya halicce ni, kuma gare Shi ne za a komar da ku?



Capítulo: Suratu Yasin

Verso : 23

ءَأَتَّخِذُ مِن دُونِهِۦٓ ءَالِهَةً إِن يُرِدۡنِ ٱلرَّحۡمَٰنُ بِضُرّٖ لَّا تُغۡنِ عَنِّي شَفَٰعَتُهُمۡ شَيۡـٔٗا وَلَا يُنقِذُونِ

“Yanzu na riqi wasu ababen bauta ba Shi ba, alhali kuwa idan (Allah) Mai rahama Ya nufe ni da wata cuta, cetonsu ba zai amfana min komai ba, kuma ba za su iya tsamo ni ba?



Capítulo: Suratu Yasin

Verso : 24

إِنِّيٓ إِذٗا لَّفِي ضَلَٰلٖ مُّبِينٍ

“Lalle ni idan na yi haka to tabbas na zama cikin vata mabayyani



Capítulo: Suratu Yasin

Verso : 74

وَٱتَّخَذُواْ مِن دُونِ ٱللَّهِ ءَالِهَةٗ لَّعَلَّهُمۡ يُنصَرُونَ

Suka kuma riqi wasu ababen bauta ba Allah ba, don a taimaka musu



Capítulo: Suratu Yasin

Verso : 75

لَا يَسۡتَطِيعُونَ نَصۡرَهُمۡ وَهُمۡ لَهُمۡ جُندٞ مُّحۡضَرُونَ

Ba za su iya taimakon su ba, su da gumakan nasu duka ababen tattarawa ne (cikin wuta)



Capítulo: Suratus Saffat

Verso : 22

۞ٱحۡشُرُواْ ٱلَّذِينَ ظَلَمُواْ وَأَزۡوَٰجَهُمۡ وَمَا كَانُواْ يَعۡبُدُونَ

(Za a ce da mala’iku): “Ku tattaro waxanda suka yi zalunci su da abokan haxinsu (shaixanu) da kuma abin da suka kasance suna bauta wa



Capítulo: Suratus Saffat

Verso : 23

مِن دُونِ ٱللَّهِ فَٱهۡدُوهُمۡ إِلَىٰ صِرَٰطِ ٱلۡجَحِيمِ

Waxanda ba Allah ba, sai ku nuna musu hanyar zuwa wutar Jahima



Capítulo: Suratus Saffat

Verso : 125

أَتَدۡعُونَ بَعۡلٗا وَتَذَرُونَ أَحۡسَنَ ٱلۡخَٰلِقِينَ

“Yanzu kwa riqa bauta wa (gunkin) Ba’alu ku riqa barin Mafi iya kyautata halitta?



Capítulo: Suratu Ghafir

Verso : 5

كَذَّبَتۡ قَبۡلَهُمۡ قَوۡمُ نُوحٖ وَٱلۡأَحۡزَابُ مِنۢ بَعۡدِهِمۡۖ وَهَمَّتۡ كُلُّ أُمَّةِۭ بِرَسُولِهِمۡ لِيَأۡخُذُوهُۖ وَجَٰدَلُواْ بِٱلۡبَٰطِلِ لِيُدۡحِضُواْ بِهِ ٱلۡحَقَّ فَأَخَذۡتُهُمۡۖ فَكَيۡفَ كَانَ عِقَابِ

Mutanen Nuhu sun qaryata kafin su, da kuma qungiyoyi (na kafirai) bayansu; kowace al’umma kuma sun yi mummunan nufi da manzonsu don su kama shi (su cutar da shi); suka kuma yi jayayya da (hujja ta) qarya don su rusa gaskiya da ita, sai Na kama su; to yaya uqubata ta kasance?



Capítulo: Suratu Ghafir

Verso : 20

وَٱللَّهُ يَقۡضِي بِٱلۡحَقِّۖ وَٱلَّذِينَ يَدۡعُونَ مِن دُونِهِۦ لَا يَقۡضُونَ بِشَيۡءٍۗ إِنَّ ٱللَّهَ هُوَ ٱلسَّمِيعُ ٱلۡبَصِيرُ

Allah Yana hukunci da gaskiya; waxanda kuwa suke bauta wa wanda ba Shi ba, ba sa hukunta komai. Haqiqa Allah Shi ne Mai ji, Mai gani



Capítulo: Suratu Ghafir

Verso : 43

لَا جَرَمَ أَنَّمَا تَدۡعُونَنِيٓ إِلَيۡهِ لَيۡسَ لَهُۥ دَعۡوَةٞ فِي ٱلدُّنۡيَا وَلَا فِي ٱلۡأٓخِرَةِ وَأَنَّ مَرَدَّنَآ إِلَى ٱللَّهِ وَأَنَّ ٱلۡمُسۡرِفِينَ هُمۡ أَصۡحَٰبُ ٱلنَّارِ

“Ba shakka abin da kuke kira na zuwa gare shi ba shi da wani kira karvavve a duniya ko a lahira, kuma lalle makomarmu zuwa ga Allah ne, mavarnata kuma tabbas su ne ‘yan wuta



Capítulo: Suratus Shura

Verso : 24

أَمۡ يَقُولُونَ ٱفۡتَرَىٰ عَلَى ٱللَّهِ كَذِبٗاۖ فَإِن يَشَإِ ٱللَّهُ يَخۡتِمۡ عَلَىٰ قَلۡبِكَۗ وَيَمۡحُ ٱللَّهُ ٱلۡبَٰطِلَ وَيُحِقُّ ٱلۡحَقَّ بِكَلِمَٰتِهِۦٓۚ إِنَّهُۥ عَلِيمُۢ بِذَاتِ ٱلصُّدُورِ

A’a, suna dai cewa ya qaga wa Allah qarya ne; to da Allah Ya ga dama da sai Ya rufe zuciyarka[1]. Allah kuma Yana shafe qarya Yana kuma tabbatar da gaskiya da kalmominsa. Lalle Shi Masanin abubuwan da suke cikin zukata ne


1- Watau da a ce zuciyarsa ta riya masa ya qirqiri Alqur’ani da kansa ya jingina wa Allah, to da Allah ya toshe masa zuciyarsa yadda ba zai qara fahimtar komai ba.


Capítulo: Suratul Jasiya

Verso : 23

أَفَرَءَيۡتَ مَنِ ٱتَّخَذَ إِلَٰهَهُۥ هَوَىٰهُ وَأَضَلَّهُ ٱللَّهُ عَلَىٰ عِلۡمٖ وَخَتَمَ عَلَىٰ سَمۡعِهِۦ وَقَلۡبِهِۦ وَجَعَلَ عَلَىٰ بَصَرِهِۦ غِشَٰوَةٗ فَمَن يَهۡدِيهِ مِنۢ بَعۡدِ ٱللَّهِۚ أَفَلَا تَذَكَّرُونَ

Shin kuwa ka ga wanda ya xauki son zuciyarsa (shi ne) abin bautarsa, Allah kuwa Ya vatar da shi a kan yana sane[1], Ya kuma rufe jinsa da zuciyarsa, kuma Ya sanya yana a kan ganinsa, to wane ne zai shiryar da shi in ba Allah ba? Me ya sa ba kwa wa’azantuwa?


1- Watau ya vatar da shi bayan ilimi ya zo masa, saboda Allah ya san cewa ya cancanci vata.


Capítulo: Suratul Ahqaf 

Verso : 4

قُلۡ أَرَءَيۡتُم مَّا تَدۡعُونَ مِن دُونِ ٱللَّهِ أَرُونِي مَاذَا خَلَقُواْ مِنَ ٱلۡأَرۡضِ أَمۡ لَهُمۡ شِرۡكٞ فِي ٱلسَّمَٰوَٰتِۖ ٱئۡتُونِي بِكِتَٰبٖ مِّن قَبۡلِ هَٰذَآ أَوۡ أَثَٰرَةٖ مِّنۡ عِلۡمٍ إِن كُنتُمۡ صَٰدِقِينَ

Ka ce: “Shin kun ga abin da kuke bauta wa ba Allah ba, ku nuna min abin da suka halitta na qasa, ko kuwa suna da tarayya ne a (halittar) sammai; ku kawo mini wani littafi da yake gabanin wannan (Alqur’anin), ko kuma wani virvishi na ilimi idan kun kasance masu gaskiya.”



Capítulo: Suratul Ahqaf 

Verso : 5

وَمَنۡ أَضَلُّ مِمَّن يَدۡعُواْ مِن دُونِ ٱللَّهِ مَن لَّا يَسۡتَجِيبُ لَهُۥٓ إِلَىٰ يَوۡمِ ٱلۡقِيَٰمَةِ وَهُمۡ عَن دُعَآئِهِمۡ غَٰفِلُونَ

Wane ne ya fi vata fiye da wanda yake bauta wa wani ba Allah ba, wanda ba zai amsa masa ba har zuwa ranar alqiyama, kuma su (ababen bautar) rafkanannu ne game da bautar da suke yi musu?



Capítulo: Suratul Ahqaf 

Verso : 6

وَإِذَا حُشِرَ ٱلنَّاسُ كَانُواْ لَهُمۡ أَعۡدَآءٗ وَكَانُواْ بِعِبَادَتِهِمۡ كَٰفِرِينَ

Idan kuma aka tashi mutane (ababen bautar) za su kasance abokan gabarsu, kuma su zamo masu musanta bautar tasu



Capítulo: Suratul Ahqaf 

Verso : 28

فَلَوۡلَا نَصَرَهُمُ ٱلَّذِينَ ٱتَّخَذُواْ مِن دُونِ ٱللَّهِ قُرۡبَانًا ءَالِهَةَۢۖ بَلۡ ضَلُّواْ عَنۡهُمۡۚ وَذَٰلِكَ إِفۡكُهُمۡ وَمَا كَانُواْ يَفۡتَرُونَ

To me ya hana allolin da suka riqe suna bautar su ba Allah ba, su taimake su? A’a, sun dai vace musu ne. Wannan kuma da man qaryarsu ce da kuma abin da suka kasance suna qagawa



Capítulo: Suratun Najm

Verso : 19

أَفَرَءَيۡتُمُ ٱللَّـٰتَ وَٱلۡعُزَّىٰ

Ku ba ni labarin (gumakan) Lata da Uzza



Capítulo: Suratun Najm

Verso : 20

وَمَنَوٰةَ ٱلثَّالِثَةَ ٱلۡأُخۡرَىٰٓ

Da Manata cikon ta ukunsu



Capítulo: Suratun Najm

Verso : 21

أَلَكُمُ ٱلذَّكَرُ وَلَهُ ٱلۡأُنثَىٰ

Yanzu xa namiji zai zama naku, Shi kuma Ya tashi da ‘ya mace?



Capítulo: Suratun Najm

Verso : 22

تِلۡكَ إِذٗا قِسۡمَةٞ ضِيزَىٰٓ

Idan haka ne wannan rabon na zalunci ne[1]


1- Domin ya qunshi Fifita mahaluki a kan Mahalicci.