Capítulo: Suratul Isra’i

Verso : 85

وَيَسۡـَٔلُونَكَ عَنِ ٱلرُّوحِۖ قُلِ ٱلرُّوحُ مِنۡ أَمۡرِ رَبِّي وَمَآ أُوتِيتُم مِّنَ ٱلۡعِلۡمِ إِلَّا قَلِيلٗا

Suna kuma tambayar ka game da ruhi. Ka ce da su: “Shi ruhi yana daga al’amarin Ubangijina, ba abin da aka ba ku na ilimi sai xan kaxan.”



Capítulo: Suratul Isra’i

Verso : 96

قُلۡ كَفَىٰ بِٱللَّهِ شَهِيدَۢا بَيۡنِي وَبَيۡنَكُمۡۚ إِنَّهُۥ كَانَ بِعِبَادِهِۦ خَبِيرَۢا بَصِيرٗا

Ka ce: “Allah Ya isa shaida tsakanina da ku: Lalle Shi ya zamanto Masani ne ga bayinsa, kuma Mai ganin (abin da suke aikatawa) ne.”



Capítulo: Suratul Isra’i

Verso : 99

۞أَوَلَمۡ يَرَوۡاْ أَنَّ ٱللَّهَ ٱلَّذِي خَلَقَ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضَ قَادِرٌ عَلَىٰٓ أَن يَخۡلُقَ مِثۡلَهُمۡ وَجَعَلَ لَهُمۡ أَجَلٗا لَّا رَيۡبَ فِيهِ فَأَبَى ٱلظَّـٰلِمُونَ إِلَّا كُفُورٗا

Yanzu ba sa gani cewa Allah wanda Ya halicci sammai da qasa Mai iko ne a kan Ya halicci irinsu? Ya kuma sanya musu wani lokaci wanda ba kokwanto a cikinsa, sai azzalumai suka qi (yin imani) sai kafircewa



Capítulo: Suratul Isra’i

Verso : 111

وَقُلِ ٱلۡحَمۡدُ لِلَّهِ ٱلَّذِي لَمۡ يَتَّخِذۡ وَلَدٗا وَلَمۡ يَكُن لَّهُۥ شَرِيكٞ فِي ٱلۡمُلۡكِ وَلَمۡ يَكُن لَّهُۥ وَلِيّٞ مِّنَ ٱلذُّلِّۖ وَكَبِّرۡهُ تَكۡبِيرَۢا

Kuma ka ce, “Yabo da godiya sun tabbata ga Allah wanda bai riqi xa ba, kuma ba Shi da wani abokin tarayya a cikin mulki, kuma ba Shi da wani mataimaki don kare masa qasqanci.” Kuma ka girmama shi girmamawa ta sosai



Capítulo: Suratul Kahf 

Verso : 13

نَّحۡنُ نَقُصُّ عَلَيۡكَ نَبَأَهُم بِٱلۡحَقِّۚ إِنَّهُمۡ فِتۡيَةٌ ءَامَنُواْ بِرَبِّهِمۡ وَزِدۡنَٰهُمۡ هُدٗى

Mu ne za Mu ba ka labarinsu da gaskiya. Lalle su samari ne da suka yi imani da Ubangijinsu, Muka kuwa qara musu shiriya



Capítulo: Suratul Kahf 

Verso : 14

وَرَبَطۡنَا عَلَىٰ قُلُوبِهِمۡ إِذۡ قَامُواْ فَقَالُواْ رَبُّنَا رَبُّ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِ لَن نَّدۡعُوَاْ مِن دُونِهِۦٓ إِلَٰهٗاۖ لَّقَدۡ قُلۡنَآ إِذٗا شَطَطًا

Muka kuma xaure zukatansu lokacin da suka tsaya suka ce: “Ubangijinmu Shi ne Ubangijin sammai da qasa; ba za mu bauta wa wani abin bauta ba in ban da Shi; idan muka yi haka kuwa to haqiqa mun faxi qarya



Capítulo: Suratul Kahf 

Verso : 16

وَإِذِ ٱعۡتَزَلۡتُمُوهُمۡ وَمَا يَعۡبُدُونَ إِلَّا ٱللَّهَ فَأۡوُۥٓاْ إِلَى ٱلۡكَهۡفِ يَنشُرۡ لَكُمۡ رَبُّكُم مِّن رَّحۡمَتِهِۦ وَيُهَيِّئۡ لَكُم مِّنۡ أَمۡرِكُم مِّرۡفَقٗا

“Tun da kun qaurace musu tare da abin da suke bauta wa sai Allah, to sai ku tare a kogon, Ubangijinku zai yalwata muku rahamarsa ya kuma shirya muku hanyar rayuwa mai sauqi ga al’amuranku.”



Capítulo: Suratul Kahf 

Verso : 24

إِلَّآ أَن يَشَآءَ ٱللَّهُۚ وَٱذۡكُر رَّبَّكَ إِذَا نَسِيتَ وَقُلۡ عَسَىٰٓ أَن يَهۡدِيَنِ رَبِّي لِأَقۡرَبَ مِنۡ هَٰذَا رَشَدٗا

Sai dai (tare da cewa): ‘In sha Allah’; ka kuma ambaci Ubangijinka idan ka manta, kuma ka ce: “Ina fatan Ubangijina Ya nuna mini abin da ya fi wannan zama shiriya.”



Capítulo: Suratul Kahf 

Verso : 26

قُلِ ٱللَّهُ أَعۡلَمُ بِمَا لَبِثُواْۖ لَهُۥ غَيۡبُ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِۖ أَبۡصِرۡ بِهِۦ وَأَسۡمِعۡۚ مَا لَهُم مِّن دُونِهِۦ مِن وَلِيّٖ وَلَا يُشۡرِكُ فِي حُكۡمِهِۦٓ أَحَدٗا

Ka ce: “Allah ne Mafi sanin tsawon zaman da suka yi.” Gaibun da yake sammai da qasa nasa ne. Wa ya yi gani irin nasa, wa kuma ya yi ji irin nasa (watau Allah). Ba su da wani majivinci in ban da Shi; ba Ya kuma tarayya da wani a cikin hukuncinsa



Capítulo: Suratul Kahf 

Verso : 28

وَٱصۡبِرۡ نَفۡسَكَ مَعَ ٱلَّذِينَ يَدۡعُونَ رَبَّهُم بِٱلۡغَدَوٰةِ وَٱلۡعَشِيِّ يُرِيدُونَ وَجۡهَهُۥۖ وَلَا تَعۡدُ عَيۡنَاكَ عَنۡهُمۡ تُرِيدُ زِينَةَ ٱلۡحَيَوٰةِ ٱلدُّنۡيَاۖ وَلَا تُطِعۡ مَنۡ أَغۡفَلۡنَا قَلۡبَهُۥ عَن ذِكۡرِنَا وَٱتَّبَعَ هَوَىٰهُ وَكَانَ أَمۡرُهُۥ فُرُطٗا

Ka kuma haqurqurtar da kanka (da zama) tare da waxanda suke bauta wa Ubangijinsu safe da yamma suna neman yardarsa; kar kuma ka kawar da idanuwanka daga gare su kana neman adon rayuwar duniya; kada kuma ka bi wanda Muka shagaltar da zuciyarsa daga ambatonmu ya kuma bi son ransa, wanda kuma al’amarinsa ya zama a sukurkuce



Capítulo: Suratul Kahf 

Verso : 45

وَٱضۡرِبۡ لَهُم مَّثَلَ ٱلۡحَيَوٰةِ ٱلدُّنۡيَا كَمَآءٍ أَنزَلۡنَٰهُ مِنَ ٱلسَّمَآءِ فَٱخۡتَلَطَ بِهِۦ نَبَاتُ ٱلۡأَرۡضِ فَأَصۡبَحَ هَشِيمٗا تَذۡرُوهُ ٱلرِّيَٰحُۗ وَكَانَ ٱللَّهُ عَلَىٰ كُلِّ شَيۡءٖ مُّقۡتَدِرًا

Kuma ka ba su misalin rayuwar duniya (wadda take) kamar ruwa ne da Muka saukar da shi daga sama, sai tsirran qasa suka cakuxa da shi, sannan ya zama busasshe, iska tana xaixaita shi. Allah kuwa Ya kasance Mai iko ne a kan komai



Capítulo: Suratul Kahf 

Verso : 51

۞مَّآ أَشۡهَدتُّهُمۡ خَلۡقَ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِ وَلَا خَلۡقَ أَنفُسِهِمۡ وَمَا كُنتُ مُتَّخِذَ ٱلۡمُضِلِّينَ عَضُدٗا

Ban halarto da su ba lokacin halittar sammai da qasa, ko ma halittar kawunansu, ban kuma kasance Mai riqon masu vatarwa mataimaka ba



Capítulo: Suratul Kahf 

Verso : 58

وَرَبُّكَ ٱلۡغَفُورُ ذُو ٱلرَّحۡمَةِۖ لَوۡ يُؤَاخِذُهُم بِمَا كَسَبُواْ لَعَجَّلَ لَهُمُ ٱلۡعَذَابَۚ بَل لَّهُم مَّوۡعِدٞ لَّن يَجِدُواْ مِن دُونِهِۦ مَوۡئِلٗا

Ubangijinka kuwa Mai yawan gafara ne Ma’abocin rahama; da Yana kama su da abin da suka aikata, to da Ya gaggauta musu azaba. A’a, (ba Ya yin haka), sai dai suna da qayyadajjen lokaci wanda ba za su sami wata makauta ba daga gare shi



Capítulo: Suratul Kahf 

Verso : 101

ٱلَّذِينَ كَانَتۡ أَعۡيُنُهُمۡ فِي غِطَآءٍ عَن ذِكۡرِي وَكَانُواْ لَا يَسۡتَطِيعُونَ سَمۡعًا

(Su ne) waxanda idanuwansu suka makance daga ambatona, suka kuma kasance ba sa iya jin (gaskiya)



Capítulo: Suratul Kahf 

Verso : 110

قُلۡ إِنَّمَآ أَنَا۠ بَشَرٞ مِّثۡلُكُمۡ يُوحَىٰٓ إِلَيَّ أَنَّمَآ إِلَٰهُكُمۡ إِلَٰهٞ وَٰحِدٞۖ فَمَن كَانَ يَرۡجُواْ لِقَآءَ رَبِّهِۦ فَلۡيَعۡمَلۡ عَمَلٗا صَٰلِحٗا وَلَا يُشۡرِكۡ بِعِبَادَةِ رَبِّهِۦٓ أَحَدَۢا

Ka ce: “Ni dai mutum ne kawai kamarku da ake yi mini wahayi cewa abin bautarku abin bauta ne Xaya; don haka wanda ya kasance yana tsoron gamuwa da Ubangijinsa, to sai ya yi aiki nagari, kada kuma ya tara wani cikin bautar Ubangijinsa.”



Capítulo: Suratu Maryam

Verso : 35

مَا كَانَ لِلَّهِ أَن يَتَّخِذَ مِن وَلَدٖۖ سُبۡحَٰنَهُۥٓۚ إِذَا قَضَىٰٓ أَمۡرٗا فَإِنَّمَا يَقُولُ لَهُۥ كُن فَيَكُونُ

Ba zai yiwu a ce Allah yana da xa ba; tsarki ya tabbata a gare Shi. Idan Ya nufi zartar da wani lamari sai kawai Ya ce masa: “Kasance”, sai ko ya kasance



Capítulo: Suratu Maryam

Verso : 40

إِنَّا نَحۡنُ نَرِثُ ٱلۡأَرۡضَ وَمَنۡ عَلَيۡهَا وَإِلَيۡنَا يُرۡجَعُونَ

Lalle Mu ne za Mu gaje qasa da wanda yake bayanta kuma gare Mu ne za a komar da su



Capítulo: Suratu Maryam

Verso : 50

وَوَهَبۡنَا لَهُم مِّن رَّحۡمَتِنَا وَجَعَلۡنَا لَهُمۡ لِسَانَ صِدۡقٍ عَلِيّٗا

Muka kuma yi musu baiwa da rahamarmu, kuma Muka sanya musu kyakkyawan ambato maxaukaki[1]


1- Watau ya sa suka zamanto ababen yabo mai xorewa a gun kowa.


Capítulo: Suratu Maryam

Verso : 53

وَوَهَبۡنَا لَهُۥ مِن رَّحۡمَتِنَآ أَخَاهُ هَٰرُونَ نَبِيّٗا

Kuma cikin rahamarmu Muka yi masa baiwa da xan’uwansa Haruna (shi ma) Annabi



Capítulo: Suratu Maryam

Verso : 67

أَوَلَا يَذۡكُرُ ٱلۡإِنسَٰنُ أَنَّا خَلَقۡنَٰهُ مِن قَبۡلُ وَلَمۡ يَكُ شَيۡـٔٗا

Yanzu shi kafiri ba zai tuna ba cewa Mu Muka halicce shi tun farko kafin ya zama komai?



Capítulo: Suratu Maryam

Verso : 70

ثُمَّ لَنَحۡنُ أَعۡلَمُ بِٱلَّذِينَ هُمۡ أَوۡلَىٰ بِهَا صِلِيّٗا

Sannan babu shakka Mu Muka fi sanin waxanda suka fi cancanta da qonuwa da ita (watau wuta)



Capítulo: Suratu Maryam

Verso : 80

وَنَرِثُهُۥ مَا يَقُولُ وَيَأۡتِينَا فَرۡدٗا

Kuma Mu gaje abin da yake faxa xin (na dukiyarsa da ‘ya’yansa), ya kuma zo mana shi kaxai[1]


1- Watau Allah zai xauke shi kacokam lokacin mutuwarsa, ya raba shi da dukiyarsa da ‘ya’yansa da yake taqama da su.


Capítulo: Suratu Xa Ha

Verso : 7

وَإِن تَجۡهَرۡ بِٱلۡقَوۡلِ فَإِنَّهُۥ يَعۡلَمُ ٱلسِّرَّ وَأَخۡفَى

Idan kuma ka xaga murya da furuci to lalle Shi Yana sane da sirri da abin da ya fi (sirri) vuya



Capítulo: Suratu Xa Ha

Verso : 8

ٱللَّهُ لَآ إِلَٰهَ إِلَّا هُوَۖ لَهُ ٱلۡأَسۡمَآءُ ٱلۡحُسۡنَىٰ

Allah (Shi ne wanda) babu wani abin bauta da gaskiya sai Shi; Yana da sunaye mafiya kyau



Capítulo: Suratu Xa Ha

Verso : 14

إِنَّنِيٓ أَنَا ٱللَّهُ لَآ إِلَٰهَ إِلَّآ أَنَا۠ فَٱعۡبُدۡنِي وَأَقِمِ ٱلصَّلَوٰةَ لِذِكۡرِيٓ

“Lalle Ni, Ni ne Allah, babu wani abin bauta sai Ni, to ka bauta mini, kuma ka tsai da salla don tuna Ni



Capítulo: Suratu Xa Ha

Verso : 46

قَالَ لَا تَخَافَآۖ إِنَّنِي مَعَكُمَآ أَسۡمَعُ وَأَرَىٰ

Ya ce: “Kada ku ji tsoro; haqiqa Ni ina tare da ku, ina ji kuma ina ganin (komai)



Capítulo: Suratu Xa Ha

Verso : 52

قَالَ عِلۡمُهَا عِندَ رَبِّي فِي كِتَٰبٖۖ لَّا يَضِلُّ رَبِّي وَلَا يَنسَى

(Musa) ya ce: “Saninsu yana wurin Ubangijina a cikin Lauhul-Mahafuzu; Ubangijina kuma ba Ya kuskure (cikin iliminsa) kuma ba Ya mantuwa



Capítulo: Suratu Xa Ha

Verso : 55

۞مِنۡهَا خَلَقۡنَٰكُمۡ وَفِيهَا نُعِيدُكُمۡ وَمِنۡهَا نُخۡرِجُكُمۡ تَارَةً أُخۡرَىٰ

Daga ita (qasar) Muka halicce ku, kuma a cikinta za Mu mayar da ku, daga ita kuma za Mu fito da ku a wani karon



Capítulo: Suratu Xa Ha

Verso : 81

كُلُواْ مِن طَيِّبَٰتِ مَا رَزَقۡنَٰكُمۡ وَلَا تَطۡغَوۡاْ فِيهِ فَيَحِلَّ عَلَيۡكُمۡ غَضَبِيۖ وَمَن يَحۡلِلۡ عَلَيۡهِ غَضَبِي فَقَدۡ هَوَىٰ

Ku ci daga daxaxan abin da Muka arzuta ku da shi (na halal), kada kuwa ku qetare shi (zuwa haramun), sai fushina ya faxa muku; wanda kuwa fushina ya faxa masa, to haqiqa ya hallaka



Capítulo: Suratu Xa Ha

Verso : 82

وَإِنِّي لَغَفَّارٞ لِّمَن تَابَ وَءَامَنَ وَعَمِلَ صَٰلِحٗا ثُمَّ ٱهۡتَدَىٰ

Lalle Ni kuma Mai yawan gafara ne ga wanda ya tuba kuma ya yi aiki na gari sannan ya (tabbata bisa) shiriya