قَدۡ كَانَ لَكُمۡ ءَايَةٞ فِي فِئَتَيۡنِ ٱلۡتَقَتَاۖ فِئَةٞ تُقَٰتِلُ فِي سَبِيلِ ٱللَّهِ وَأُخۡرَىٰ كَافِرَةٞ يَرَوۡنَهُم مِّثۡلَيۡهِمۡ رَأۡيَ ٱلۡعَيۡنِۚ وَٱللَّهُ يُؤَيِّدُ بِنَصۡرِهِۦ مَن يَشَآءُۚ إِنَّ فِي ذَٰلِكَ لَعِبۡرَةٗ لِّأُوْلِي ٱلۡأَبۡصَٰرِ
Haqiqa wata izina ta bayyana a gare ku game da wasu rundunoni biyu da suka gwabza, xaya rundunar tana yaqi saboda Allah, xayar kuma kafira ce, suna kallon su (kafiran) kamar ninki biyu a ganin ido[1]; kuma Allah Yana qarfafar wanda Ya ga dama da nasararsa. Lalle a cikin hakan akwai izina ga ma’abota basira
1- Qungiyar farko su ne Annabi () da sahabbai a lokacin yaqin Badar, suna ganin qungiya ta biyu wato kafirai, sun ninka su gida biyu. Wannan kuwa ya qara musu dogaro ga Allah.
كَمَآ أَخۡرَجَكَ رَبُّكَ مِنۢ بَيۡتِكَ بِٱلۡحَقِّ وَإِنَّ فَرِيقٗا مِّنَ ٱلۡمُؤۡمِنِينَ لَكَٰرِهُونَ
Kamar yadda Ubangijinka Ya fitar da kai daga gidanka (na Madina) da gaskiya, alhali lalle wata jama’a daga muminai tabbas suna qin (haka)
يُجَٰدِلُونَكَ فِي ٱلۡحَقِّ بَعۡدَ مَا تَبَيَّنَ كَأَنَّمَا يُسَاقُونَ إِلَى ٱلۡمَوۡتِ وَهُمۡ يَنظُرُونَ
Suna jayayya da kai game da abin da yake tabbas, kai ka ce ana kora su ne wajen mutuwa, alhali kuwa suna kallo
وَإِذۡ يَعِدُكُمُ ٱللَّهُ إِحۡدَى ٱلطَّآئِفَتَيۡنِ أَنَّهَا لَكُمۡ وَتَوَدُّونَ أَنَّ غَيۡرَ ذَاتِ ٱلشَّوۡكَةِ تَكُونُ لَكُمۡ وَيُرِيدُ ٱللَّهُ أَن يُحِقَّ ٱلۡحَقَّ بِكَلِمَٰتِهِۦ وَيَقۡطَعَ دَابِرَ ٱلۡكَٰفِرِينَ
(Ka tuna) kuma lokacin da Allah Ya yi muku alqawarin xayar jama’an nan guda biyu (na abokan gaba)[1] cewa, lalle taku ce, sai kuka riqa fatan marar wahalar ce za ta zama taku, alhali kuwa Allah Yana nufin Ya tabbatar da gaskiya da kalmominsa, Ya kuma tumvuke tushen kafirai
1- Watau ko dai su yi nasarar rutsawa da kayan ayarin fataken Quraishawa, ko kuma su haxu da rundunar mayaqan Makka.
لِيُحِقَّ ٱلۡحَقَّ وَيُبۡطِلَ ٱلۡبَٰطِلَ وَلَوۡ كَرِهَ ٱلۡمُجۡرِمُونَ
Don (kuma) Ya tabbatar da gaskiya, Ya kuma lalata varna ko da kuwa kafirai sun qi (hakan)
إِذۡ تَسۡتَغِيثُونَ رَبَّكُمۡ فَٱسۡتَجَابَ لَكُمۡ أَنِّي مُمِدُّكُم بِأَلۡفٖ مِّنَ ٱلۡمَلَـٰٓئِكَةِ مُرۡدِفِينَ
Ku tuna lokacin da kuke neman taimakon Ubangijinku, sai Ya amsa muku cewa: “Ni zan kawo muku xauki na mala’iku dubu masu bibiyar juna.”
وَمَا جَعَلَهُ ٱللَّهُ إِلَّا بُشۡرَىٰ وَلِتَطۡمَئِنَّ بِهِۦ قُلُوبُكُمۡۚ وَمَا ٱلنَّصۡرُ إِلَّا مِنۡ عِندِ ٱللَّهِۚ إِنَّ ٱللَّهَ عَزِيزٌ حَكِيمٌ
Kuma (wannan taimakon) Allah bai sanya shi ba, sai don albishir a gare ku, don kuma zukatanku su nutsu da shi. Babu kuma wata nasara sai daga wurin Allah. Lalle Allah Mabuwayi ne Mai hikima
إِذۡ يُغَشِّيكُمُ ٱلنُّعَاسَ أَمَنَةٗ مِّنۡهُ وَيُنَزِّلُ عَلَيۡكُم مِّنَ ٱلسَّمَآءِ مَآءٗ لِّيُطَهِّرَكُم بِهِۦ وَيُذۡهِبَ عَنكُمۡ رِجۡزَ ٱلشَّيۡطَٰنِ وَلِيَرۡبِطَ عَلَىٰ قُلُوبِكُمۡ وَيُثَبِّتَ بِهِ ٱلۡأَقۡدَامَ
(Ku kuma tuna) lokacin da gyangyaxi yake kwashe ku (Allah) Yana Mai amintar da ku (daga tunanin abokan gaba), Ya kuma riqa saukar da ruwa daga sama don Ya tsarkake ku da shi, Ya kuma tafiyar muku da waswasin shaixan, don kuma Ya qarfafa zukatanku Ya kuma tabbatar da dugaduganku da shi
إِذۡ يُوحِي رَبُّكَ إِلَى ٱلۡمَلَـٰٓئِكَةِ أَنِّي مَعَكُمۡ فَثَبِّتُواْ ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْۚ سَأُلۡقِي فِي قُلُوبِ ٱلَّذِينَ كَفَرُواْ ٱلرُّعۡبَ فَٱضۡرِبُواْ فَوۡقَ ٱلۡأَعۡنَاقِ وَٱضۡرِبُواْ مِنۡهُمۡ كُلَّ بَنَانٖ
(Ka kuma tuna) lokacin da Ubangijinka Yake wahayi zuwa ga mala’iku cewa: “Lalle Ni ina tare da ku, saboda haka ku qarfafa wa waxanda suka yi imani gwiwa. Da sannu zan jefa tsoro cikin zukatan waxanda suka kafirce, saboda haka ku doki wuyansu, kuma ku doki dukkanin gavovin hannaye da qafafu.”
ذَٰلِكَ بِأَنَّهُمۡ شَآقُّواْ ٱللَّهَ وَرَسُولَهُۥۚ وَمَن يُشَاقِقِ ٱللَّهَ وَرَسُولَهُۥ فَإِنَّ ٱللَّهَ شَدِيدُ ٱلۡعِقَابِ
Wannan kuwa saboda sun sava wa Allah da Manzonsa. Duk wanda kuwa ya sava wa Allah da Manzonsa to lalle Allah Mai tsananin uquba ne
ذَٰلِكُمۡ فَذُوقُوهُ وَأَنَّ لِلۡكَٰفِرِينَ عَذَابَ ٱلنَّارِ
Wannan (uqubar) sai ku xanxane ta (a duniya), kuma ba shakka kafirai suna da azabar wuta
يَـٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوٓاْ إِذَا لَقِيتُمُ ٱلَّذِينَ كَفَرُواْ زَحۡفٗا فَلَا تُوَلُّوهُمُ ٱلۡأَدۡبَارَ
Ya ku waxanda suka yi imani, idan kuka haxu da cincirindon waxanda suka kafirta, to kada ku ba su baya
وَمَن يُوَلِّهِمۡ يَوۡمَئِذٖ دُبُرَهُۥٓ إِلَّا مُتَحَرِّفٗا لِّقِتَالٍ أَوۡ مُتَحَيِّزًا إِلَىٰ فِئَةٖ فَقَدۡ بَآءَ بِغَضَبٖ مِّنَ ٱللَّهِ وَمَأۡوَىٰهُ جَهَنَّمُۖ وَبِئۡسَ ٱلۡمَصِيرُ
Duk kuwa wanda ya ba su baya a wannan ranar idan dai ba wanda ya gudu da niyyar juyowa ya kai xauki ko kuma mai niyyar haxuwa da wata jama’a (ta mayaqa) ba, to haqiqa ya komo da fushin Allah, kuma makomarsa Jahannama ce; wannan makoma kuwa ta munana
فَلَمۡ تَقۡتُلُوهُمۡ وَلَٰكِنَّ ٱللَّهَ قَتَلَهُمۡۚ وَمَا رَمَيۡتَ إِذۡ رَمَيۡتَ وَلَٰكِنَّ ٱللَّهَ رَمَىٰ وَلِيُبۡلِيَ ٱلۡمُؤۡمِنِينَ مِنۡهُ بَلَآءً حَسَنًاۚ إِنَّ ٱللَّهَ سَمِيعٌ عَلِيمٞ
Saboda haka ba ku kuka kashe su ba, Allah ne Ya kashe su[1]. Kuma ba ka jefa ba lokacin da ka jefa, sai dai Allah ne Ya jefa[2]. Don kuma Ya jarrabi muminai da kyakkyawar jarrabawa[3]. Lalle Allah Mai ji ne Masani
1- Domin komai ya faru ne da taimakonsa da agajinsa.
2- Watau shi ma Annabi () da ya xauki qasa da tafin hannunsa ya watsa ta a fuskokin kafirai ta kuma cika musu ido, to a haqiqa ba shi ne ya yi wannan jifan ba, Allah ne ya yi.
3- Domin su yi masa godiya a kan ni’imominsa.
ذَٰلِكُمۡ وَأَنَّ ٱللَّهَ مُوهِنُ كَيۡدِ ٱلۡكَٰفِرِينَ
Waccan (jarraba ku da aka yi gaskiya ne), kuma lalle Allah Mai raunana makircin kafirai ne
إِن تَسۡتَفۡتِحُواْ فَقَدۡ جَآءَكُمُ ٱلۡفَتۡحُۖ وَإِن تَنتَهُواْ فَهُوَ خَيۡرٞ لَّكُمۡۖ وَإِن تَعُودُواْ نَعُدۡ وَلَن تُغۡنِيَ عَنكُمۡ فِئَتُكُمۡ شَيۡـٔٗا وَلَوۡ كَثُرَتۡ وَأَنَّ ٱللَّهَ مَعَ ٱلۡمُؤۡمِنِينَ
Idan kuna neman zuwan hukunci ne (watau azaba), to haqiqa hukuncin ya zo muku. Idan kuka daina to shi ya fi muku alheri, idan kuma kuka koma, to za Mu koma, jama’arku kuma ba za ta amfana muku komai ba, komai yawanta kuwa, lalle kuma Allah Yana tare da muminai
إِذۡ أَنتُم بِٱلۡعُدۡوَةِ ٱلدُّنۡيَا وَهُم بِٱلۡعُدۡوَةِ ٱلۡقُصۡوَىٰ وَٱلرَّكۡبُ أَسۡفَلَ مِنكُمۡۚ وَلَوۡ تَوَاعَدتُّمۡ لَٱخۡتَلَفۡتُمۡ فِي ٱلۡمِيعَٰدِ وَلَٰكِن لِّيَقۡضِيَ ٱللَّهُ أَمۡرٗا كَانَ مَفۡعُولٗا لِّيَهۡلِكَ مَنۡ هَلَكَ عَنۢ بَيِّنَةٖ وَيَحۡيَىٰ مَنۡ حَيَّ عَنۢ بَيِّنَةٖۗ وَإِنَّ ٱللَّهَ لَسَمِيعٌ عَلِيمٌ
Ku tuna lokacin da kuke a gacin da ya fi kusa (da Madina) su kuma suna gacin da ya fi nisa, ayarin (Abu Sufyan) kuwa yana qasa da ku. Da kuwa kun yi alqawarin (haxuwa a Badar) to babu shakka da kun sava wajen cika alqawarin, sai dai kuma wannan ya faru ne saboda Allah Ya zartar da al’amarin da ya zamanto mai faruwa ne, don wanda ya hallaka ya hallaka da dalili, kuma wanda kuma ya rayu ya rayu da dalili. Lalle Allah Mai ji ne Masani
إِذۡ يُرِيكَهُمُ ٱللَّهُ فِي مَنَامِكَ قَلِيلٗاۖ وَلَوۡ أَرَىٰكَهُمۡ كَثِيرٗا لَّفَشِلۡتُمۡ وَلَتَنَٰزَعۡتُمۡ فِي ٱلۡأَمۡرِ وَلَٰكِنَّ ٱللَّهَ سَلَّمَۚ إِنَّهُۥ عَلِيمُۢ بِذَاتِ ٱلصُّدُورِ
Ka tuna lokacin da Allah Yake nuna maka su cikin baccinka suna ‘yan kaxan; da kuwa Ya nuna maka su da yawa fal, to ba shakka da kun tsorata kuma lalle da kun yi jayayya a cikin al’amarin, sai dai kuma Allah Ya kiyaye. Lalle Shi Masanin abin da ke zukata ne
وَإِذۡ يُرِيكُمُوهُمۡ إِذِ ٱلۡتَقَيۡتُمۡ فِيٓ أَعۡيُنِكُمۡ قَلِيلٗا وَيُقَلِّلُكُمۡ فِيٓ أَعۡيُنِهِمۡ لِيَقۡضِيَ ٱللَّهُ أَمۡرٗا كَانَ مَفۡعُولٗاۗ وَإِلَى ٱللَّهِ تُرۡجَعُ ٱلۡأُمُورُ
Ku kuma tuna lokacin da Yake nuna muku su a yayin da kuka gamu suna ‘yan kaxan a idanuwanku, Yake kuma qarantar da ku a idonsu, saboda Allah Ya hukunta al’amarin da yake mai afkuwa ne. Kuma wurin Allah ne ake mayar da duka al’amura
يَـٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوٓاْ إِذَا لَقِيتُمۡ فِئَةٗ فَٱثۡبُتُواْ وَٱذۡكُرُواْ ٱللَّهَ كَثِيرٗا لَّعَلَّكُمۡ تُفۡلِحُونَ
Ya ku waxanda suka yi imani, idan kuka haxu da wata qungiya (ta mayaqa), to sai ku dage, ku kuma ambaci Allah da yawa, don ku rabauta
وَأَطِيعُواْ ٱللَّهَ وَرَسُولَهُۥ وَلَا تَنَٰزَعُواْ فَتَفۡشَلُواْ وَتَذۡهَبَ رِيحُكُمۡۖ وَٱصۡبِرُوٓاْۚ إِنَّ ٱللَّهَ مَعَ ٱلصَّـٰبِرِينَ
Kuma ku bi Allah da Manzonsa, kada ku rarrabu sai ku zama matsorata kuma qarfinku ya tafi; ku kuma yi haquri. Lalle Allah Yana tare da masu haquri
وَلَا تَكُونُواْ كَٱلَّذِينَ خَرَجُواْ مِن دِيَٰرِهِم بَطَرٗا وَرِئَآءَ ٱلنَّاسِ وَيَصُدُّونَ عَن سَبِيلِ ٱللَّهِۚ وَٱللَّهُ بِمَا يَعۡمَلُونَ مُحِيطٞ
Kada kuma ku zama kamar waxanda suka fito daga gidajensu don fariya da kuma nuna wa mutane (watau riya), suna kuma hana (mutane) bin hanyar Allah. Allah kuwa Mai kewaye abin da suke aikatawa ne
وَإِذۡ زَيَّنَ لَهُمُ ٱلشَّيۡطَٰنُ أَعۡمَٰلَهُمۡ وَقَالَ لَا غَالِبَ لَكُمُ ٱلۡيَوۡمَ مِنَ ٱلنَّاسِ وَإِنِّي جَارٞ لَّكُمۡۖ فَلَمَّا تَرَآءَتِ ٱلۡفِئَتَانِ نَكَصَ عَلَىٰ عَقِبَيۡهِ وَقَالَ إِنِّي بَرِيٓءٞ مِّنكُمۡ إِنِّيٓ أَرَىٰ مَا لَا تَرَوۡنَ إِنِّيٓ أَخَافُ ٱللَّهَۚ وَٱللَّهُ شَدِيدُ ٱلۡعِقَابِ
Kuma ku tuna lokacin da Shaixan ya qawata musu ayyukansu, ya kuma ce: “Babu wasu mutane a yau da za su yi galaba a kanku, lalle kuma ni maqocinku ne.” Saboda haka lokacin da qungiyoyin biyu suka haxu sai ya tsere a guje, ya kuma ce: “Lalle ni ba ruwana da ku, lalle ni ina ganin abin da ku ba kwa gani, lalle ni ina tsoron Allah. Allah kuwa Mai tsananin azaba ne.”
سَيُهۡزَمُ ٱلۡجَمۡعُ وَيُوَلُّونَ ٱلدُّبُرَ
To ba da daxewa ba za a karya jama’ar tasu[1], su kuma su ba da baya
1- Haka kuwa ya faru a yaqin Badar lokacin da aka karya lagon kafiran Makka, aka kashe manyansu da dama.