فَتَوَكَّلۡ عَلَى ٱللَّهِۖ إِنَّكَ عَلَى ٱلۡحَقِّ ٱلۡمُبِينِ
To ka dogara ga Allah; lalle kai kana kan gaskiya mabayyaniya
ٱلَّذِينَ صَبَرُواْ وَعَلَىٰ رَبِّهِمۡ يَتَوَكَّلُونَ
(Su ne) waxanda suka yi haquri, kuma ga Ubangijinsu kawai suke dogara
وَتَوَكَّلۡ عَلَى ٱللَّهِۚ وَكَفَىٰ بِٱللَّهِ وَكِيلٗا
Ka kuma dogara ga Allah. Allah kuwa Ya isa wakili
وَلَا تُطِعِ ٱلۡكَٰفِرِينَ وَٱلۡمُنَٰفِقِينَ وَدَعۡ أَذَىٰهُمۡ وَتَوَكَّلۡ عَلَى ٱللَّهِۚ وَكَفَىٰ بِٱللَّهِ وَكِيلٗا
Kada kuma ka yi wa kafirai da munafukai xa’a, ka kuma bar cutarsu (da suke yi maka), ka kuma dogara ga Allah. Allah kuwa Ya isa Ya zama abin dogara
وَلَئِن سَأَلۡتَهُم مَّنۡ خَلَقَ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضَ لَيَقُولُنَّ ٱللَّهُۚ قُلۡ أَفَرَءَيۡتُم مَّا تَدۡعُونَ مِن دُونِ ٱللَّهِ إِنۡ أَرَادَنِيَ ٱللَّهُ بِضُرٍّ هَلۡ هُنَّ كَٰشِفَٰتُ ضُرِّهِۦٓ أَوۡ أَرَادَنِي بِرَحۡمَةٍ هَلۡ هُنَّ مُمۡسِكَٰتُ رَحۡمَتِهِۦۚ قُلۡ حَسۡبِيَ ٱللَّهُۖ عَلَيۡهِ يَتَوَكَّلُ ٱلۡمُتَوَكِّلُونَ
Tabbas da za ka tambaye su wanda ya halicci sammai da qasa, lalle za su ce: “Allah ne.” Ka ce (da su): “Ku ba ni labarin waxanda kuke bauta wa ba Allah ba, idan Allah Ya nufe ni da wata cuta, yanzu za su iya yaye cutar tasa, ko kuwa idan Ya nufe ni da rahama yanzu za su iya riqe rahamarsa?” Ka ce: “Allah Ya ishe ni; a gare Shi ne kawai masu dogaro suke dogaro.”
فَسَتَذۡكُرُونَ مَآ أَقُولُ لَكُمۡۚ وَأُفَوِّضُ أَمۡرِيٓ إِلَى ٱللَّهِۚ إِنَّ ٱللَّهَ بَصِيرُۢ بِٱلۡعِبَادِ
“To ba da daxewa ba za ku tuna abin da nake gaya muku. Ina kuma miqa al’amarina zuwa ga Allah. Lalle Allah Mai ganin bayi ne.”
وَمَا ٱخۡتَلَفۡتُمۡ فِيهِ مِن شَيۡءٖ فَحُكۡمُهُۥٓ إِلَى ٱللَّهِۚ ذَٰلِكُمُ ٱللَّهُ رَبِّي عَلَيۡهِ تَوَكَّلۡتُ وَإِلَيۡهِ أُنِيبُ
Kuma duk wani abu da kuka yi savani a kansa, to sai ku mai da hukuncinsa ga Allah. Wannan Shi ne Allah Ubangijina, gare Shi kawai na dogara, kuma wurinsa kawai nake mayar da al’amarina
فَمَآ أُوتِيتُم مِّن شَيۡءٖ فَمَتَٰعُ ٱلۡحَيَوٰةِ ٱلدُّنۡيَاۚ وَمَا عِندَ ٱللَّهِ خَيۡرٞ وَأَبۡقَىٰ لِلَّذِينَ ءَامَنُواْ وَعَلَىٰ رَبِّهِمۡ يَتَوَكَّلُونَ
Sannan duk wani abu da aka ba ku to jin daxin rayuwar duniya ne; kuma abin da yake wurin Allah shi ya fi alheri ya kuma fi wanzuwa ga waxanda suka yi imani suke kuma dogara ga Ubangijinsu
إِنَّمَا ٱلنَّجۡوَىٰ مِنَ ٱلشَّيۡطَٰنِ لِيَحۡزُنَ ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ وَلَيۡسَ بِضَآرِّهِمۡ شَيۡـًٔا إِلَّا بِإِذۡنِ ٱللَّهِۚ وَعَلَى ٱللَّهِ فَلۡيَتَوَكَّلِ ٱلۡمُؤۡمِنُونَ
Ganawar (tasu) kawai daga Shaixan take, don ya baqanta ran waxanda suka yi imani, ba kuwa zai cuce su da komai ba sai da izinin Allah. Ga Allah ne kuma muminai za su dogara
قَدۡ كَانَتۡ لَكُمۡ أُسۡوَةٌ حَسَنَةٞ فِيٓ إِبۡرَٰهِيمَ وَٱلَّذِينَ مَعَهُۥٓ إِذۡ قَالُواْ لِقَوۡمِهِمۡ إِنَّا بُرَءَـٰٓؤُاْ مِنكُمۡ وَمِمَّا تَعۡبُدُونَ مِن دُونِ ٱللَّهِ كَفَرۡنَا بِكُمۡ وَبَدَا بَيۡنَنَا وَبَيۡنَكُمُ ٱلۡعَدَٰوَةُ وَٱلۡبَغۡضَآءُ أَبَدًا حَتَّىٰ تُؤۡمِنُواْ بِٱللَّهِ وَحۡدَهُۥٓ إِلَّا قَوۡلَ إِبۡرَٰهِيمَ لِأَبِيهِ لَأَسۡتَغۡفِرَنَّ لَكَ وَمَآ أَمۡلِكُ لَكَ مِنَ ٱللَّهِ مِن شَيۡءٖۖ رَّبَّنَا عَلَيۡكَ تَوَكَّلۡنَا وَإِلَيۡكَ أَنَبۡنَا وَإِلَيۡكَ ٱلۡمَصِيرُ
Haqiqa kyakkyawan abin koyi ya kasance a gare ku game da Ibrahimu da waxanda suke tare da shi, lokacin da suka ce da mutanensu: “Lalle mu ba ruwanmu da ku, har ma da abin da kuke bauta wa ba Allah ba, mun kafirce muku, kuma gaba da qiyayya sun bayyana a tsakaninmu da ku har abada, har sai kun yi imani da Allah Shi kaxai, in ban da faxar Ibrahimu ga babansa cewa: ‘Lalle zan nema maka gafara, ba na kuma amfana maka komai game da (sakamakon) Allah’; ya Ubangijinmu gare Ka muka dogara, kuma zuwa wurinka muka mayar da lamuranmu, kuma makoma zuwa gare Ka ne
ٱللَّهُ لَآ إِلَٰهَ إِلَّا هُوَۚ وَعَلَى ٱللَّهِ فَلۡيَتَوَكَّلِ ٱلۡمُؤۡمِنُونَ
Allah, babu wani abin bauta da gaskiya sai Shi, to sai muminai su dogara ga Allah kawai
وَيَرۡزُقۡهُ مِنۡ حَيۡثُ لَا يَحۡتَسِبُۚ وَمَن يَتَوَكَّلۡ عَلَى ٱللَّهِ فَهُوَ حَسۡبُهُۥٓۚ إِنَّ ٱللَّهَ بَٰلِغُ أَمۡرِهِۦۚ قَدۡ جَعَلَ ٱللَّهُ لِكُلِّ شَيۡءٖ قَدۡرٗا
Ya kuma arzuta shi ta inda ba ya tsammani. Duk wanda kuma ya dogara ga Allah to Shi Ya ishe shi. Lalle Allah Mai zartar da al’amarinsa ne. Haqiqa kuma Allah Ya sanya iyaka ga kowane abu
قُلۡ هُوَ ٱلرَّحۡمَٰنُ ءَامَنَّا بِهِۦ وَعَلَيۡهِ تَوَكَّلۡنَاۖ فَسَتَعۡلَمُونَ مَنۡ هُوَ فِي ضَلَٰلٖ مُّبِينٖ
Ka ce: “Shi ne (Allah) Mai rahama, mun yi imani da Shi, kuma a gare Shi muka dogara, to da sannu za ku san shin wane ne yake cikin vata mabayyani?”
رَّبُّ ٱلۡمَشۡرِقِ وَٱلۡمَغۡرِبِ لَآ إِلَٰهَ إِلَّا هُوَ فَٱتَّخِذۡهُ وَكِيلٗا
(Shi ne) Ubangijin mahudar rana da mafaxar rana, babu wani abin bauta wa da gaskiya sai Shi, saboda haka ka riqe Shi Abin dogara