يَوۡمَ يَبۡعَثُهُمُ ٱللَّهُ جَمِيعٗا فَيُنَبِّئُهُم بِمَا عَمِلُوٓاْۚ أَحۡصَىٰهُ ٱللَّهُ وَنَسُوهُۚ وَٱللَّهُ عَلَىٰ كُلِّ شَيۡءٖ شَهِيدٌ
A ranar da Allah zai tashe su gaba xaya, sannan Ya ba su labarin abin da suka aikata. Allah Ya qididdige shi, su kuwa sun manta shi. Allah kuwa Mai ganin kowane abu ne
يَوۡمَ يَبۡعَثُهُمُ ٱللَّهُ جَمِيعٗا فَيَحۡلِفُونَ لَهُۥ كَمَا يَحۡلِفُونَ لَكُمۡ وَيَحۡسَبُونَ أَنَّهُمۡ عَلَىٰ شَيۡءٍۚ أَلَآ إِنَّهُمۡ هُمُ ٱلۡكَٰذِبُونَ
A ranar da Allah zai tashe su baki xaya sai su rantse Masa kamar yadda suke rantse muku, su kuma riqa tsammanin su sun yi wani abu (mai amfani). Ku saurara, lalle kam su ne maqaryata
هُوَ ٱللَّهُ ٱلۡخَٰلِقُ ٱلۡبَارِئُ ٱلۡمُصَوِّرُۖ لَهُ ٱلۡأَسۡمَآءُ ٱلۡحُسۡنَىٰۚ يُسَبِّحُ لَهُۥ مَا فِي ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِۖ وَهُوَ ٱلۡعَزِيزُ ٱلۡحَكِيمُ
Shi ne Allah Mahalicci, Mai qagawa Mai surantawa[1]; Yana da sunaye mafiya kyau. Duk abin da yake cikin sammai da qasa yana tsarkake Shi; kuma Shi Mabuwayi ne, Mai hikima
1- Watau mai suranta kamannin abin da ya halitta yadda ya ga dama.
هُوَ ٱلَّذِي خَلَقَكُمۡ فَمِنكُمۡ كَافِرٞ وَمِنكُم مُّؤۡمِنٞۚ وَٱللَّهُ بِمَا تَعۡمَلُونَ بَصِيرٌ
Shi ne Wanda Ya halicce ku, don haka daga cikinku akwai kafiri, daga cikinku kuma akwai mumini. Allah kuwa Mai ganin abin da kuke aikatawa ne
خَلَقَ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضَ بِٱلۡحَقِّ وَصَوَّرَكُمۡ فَأَحۡسَنَ صُوَرَكُمۡۖ وَإِلَيۡهِ ٱلۡمَصِيرُ
Ya halicci sammai da qasa da gaskiya, kuma Ya suranta ku, sannan Ya kyautata surorinku; zuwa gare Shi ne kuma makomarku take
زَعَمَ ٱلَّذِينَ كَفَرُوٓاْ أَن لَّن يُبۡعَثُواْۚ قُلۡ بَلَىٰ وَرَبِّي لَتُبۡعَثُنَّ ثُمَّ لَتُنَبَّؤُنَّ بِمَا عَمِلۡتُمۡۚ وَذَٰلِكَ عَلَى ٱللَّهِ يَسِيرٞ
Waxanda suka kafirta sun riya cewa ba za a tashe su ba har abada. Ka ce: “A’a, na rantse da Ubangijina tabbas za a tashe ku, sannan kuma tabbas za a ba ku labarin abin da kuka aikata. Wannan kuwa mai sauqi ne a wurin Allah
ٱللَّهُ ٱلَّذِي خَلَقَ سَبۡعَ سَمَٰوَٰتٖ وَمِنَ ٱلۡأَرۡضِ مِثۡلَهُنَّۖ يَتَنَزَّلُ ٱلۡأَمۡرُ بَيۡنَهُنَّ لِتَعۡلَمُوٓاْ أَنَّ ٱللَّهَ عَلَىٰ كُلِّ شَيۡءٖ قَدِيرٞ وَأَنَّ ٱللَّهَ قَدۡ أَحَاطَ بِكُلِّ شَيۡءٍ عِلۡمَۢا
Allah ne Wanda Ya halicci sammai bakwai, qasa ma Ya halicci kwatankwacinsu (watau sammai), umarni yana sauka a tsakaninsu, don ku san cewa, Allah Mai iko ne a kan komai, kuma haqiqa Allah iliminsa ya kewaye kowane abu
ٱلَّذِي خَلَقَ ٱلۡمَوۡتَ وَٱلۡحَيَوٰةَ لِيَبۡلُوَكُمۡ أَيُّكُمۡ أَحۡسَنُ عَمَلٗاۚ وَهُوَ ٱلۡعَزِيزُ ٱلۡغَفُورُ
Wanda Ya halicci mutuwa da rayuwa don Ya jarraba ku (Ya bayyana) wane ne a cikinku ya fi kyakkyawan aiki? Shi kuma Mabuwayi ne, Mai gafara
ٱلَّذِي خَلَقَ سَبۡعَ سَمَٰوَٰتٖ طِبَاقٗاۖ مَّا تَرَىٰ فِي خَلۡقِ ٱلرَّحۡمَٰنِ مِن تَفَٰوُتٖۖ فَٱرۡجِعِ ٱلۡبَصَرَ هَلۡ تَرَىٰ مِن فُطُورٖ
Wanda Ya halicci sammai bakwai hawa-hawa; ba za ka ga wata tangarxa cikin halittar (Allah) Mai rahama ba. Ka maimaita dubanka, shin za ka ga wata tsaga?
أَيَحۡسَبُ ٱلۡإِنسَٰنُ أَلَّن نَّجۡمَعَ عِظَامَهُۥ
Yanzu mutum yana tsammanin ba za Mu tattara qasusuwansa ba?
بَلَىٰ قَٰدِرِينَ عَلَىٰٓ أَن نُّسَوِّيَ بَنَانَهُۥ
E, (Mu) Masu iko ne a kan Mu daidaita gavovin yatsunsa
أَلَمۡ يَكُ نُطۡفَةٗ مِّن مَّنِيّٖ يُمۡنَىٰ
Shin bai kasance wani xigo na maniyyi da ake zuba shi (a mahaifa) ba?
ثُمَّ كَانَ عَلَقَةٗ فَخَلَقَ فَسَوَّىٰ
Sannan ya zama gudan jini sannan (Allah) Ya halicce (shi) sai Ya daidaita (shi)?
فَجَعَلَ مِنۡهُ ٱلزَّوۡجَيۡنِ ٱلذَّكَرَ وَٱلۡأُنثَىٰٓ
Sannan Ya halicci dangi biyu daga gare shi, namiji da mace?
أَلَيۡسَ ذَٰلِكَ بِقَٰدِرٍ عَلَىٰٓ أَن يُحۡـِۧيَ ٱلۡمَوۡتَىٰ
Yanzu wannan bai zama Mai iko a kan ya raya matattu ba?
ءَأَنتُمۡ أَشَدُّ خَلۡقًا أَمِ ٱلسَّمَآءُۚ بَنَىٰهَا
Yanzu ku ne halittarku ta fi tsanani ko kuwa sama wadda Shi ne Ya gina ta?
رَفَعَ سَمۡكَهَا فَسَوَّىٰهَا
Ya xaukaka rufinta Ya kuma daidaita ta[1]
1- Watau ya zama babu wata varaka ko tsagewa ko wani aibi tare da ita.
وَأَغۡطَشَ لَيۡلَهَا وَأَخۡرَجَ ضُحَىٰهَا
Ya lulluve darenta da duhu Ya kuma fitar da hasken hantsinta
وَٱلۡأَرۡضَ بَعۡدَ ذَٰلِكَ دَحَىٰهَآ
Qasa kuma bayan haka Ya shimfixa ta
أَخۡرَجَ مِنۡهَا مَآءَهَا وَمَرۡعَىٰهَا
Ya fitar da ruwanta da makiyayarta daga gare ta
وَٱلۡجِبَالَ أَرۡسَىٰهَا
Duwatsu kuma Ya kafa su
مَتَٰعٗا لَّكُمۡ وَلِأَنۡعَٰمِكُمۡ
Don jin daxinku da na dabbobinku
ٱلَّذِي خَلَقَكَ فَسَوَّىٰكَ فَعَدَلَكَ
Wanda Ya halicce ka Ya kuma daidaita ka Ya miqar da kai[1]?
1- Watau ya lura da girman ni’imar da ya yi masa yayin da bai yi masa irin halittar jaki ba ko ta biri ko ta kare.
فِيٓ أَيِّ صُورَةٖ مَّا شَآءَ رَكَّبَكَ
Ya harhaxa ka cikin irin surar da Ya ga dama?
إِنَّهُۥ هُوَ يُبۡدِئُ وَيُعِيدُ
Lalle Shi ne Yake farar (da komai) Yake kuma dawo (da shi)
إِنَّهُۥ عَلَىٰ رَجۡعِهِۦ لَقَادِرٞ
Lalle Shi (Allah) Mai iko ne a kan dawo da shi