قُلۡ يُحۡيِيهَا ٱلَّذِيٓ أَنشَأَهَآ أَوَّلَ مَرَّةٖۖ وَهُوَ بِكُلِّ خَلۡقٍ عَلِيمٌ
Ka ce: “Wannan da Ya fare su tun farko Shi ne zai raya su; Shi kuwa Masanin kowacce irin halitta ne
ٱلَّذِي جَعَلَ لَكُم مِّنَ ٱلشَّجَرِ ٱلۡأَخۡضَرِ نَارٗا فَإِذَآ أَنتُم مِّنۡهُ تُوقِدُونَ
“Wanda kuma Ya samar muku wuta daga koriyar bishiya, sai ga shi kuna hura wuta daga gare ta.”
أَوَلَيۡسَ ٱلَّذِي خَلَقَ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضَ بِقَٰدِرٍ عَلَىٰٓ أَن يَخۡلُقَ مِثۡلَهُمۚ بَلَىٰ وَهُوَ ٱلۡخَلَّـٰقُ ٱلۡعَلِيمُ
Yanzu wanda Ya halacci sammai da qasa ba zai zama Mai ikon halitta irinsu ba? Ai tabbas zai iya, kuma Shi ne Mai yawan yin halitta, Masani
إِنَّمَآ أَمۡرُهُۥٓ إِذَآ أَرَادَ شَيۡـًٔا أَن يَقُولَ لَهُۥ كُن فَيَكُونُ
Umarninsa kawai idan Ya yi nufin wani abu sai Ya ce da shi: “Kasance”, sai ya kasance
وَٱللَّهُ خَلَقَكُمۡ وَمَا تَعۡمَلُونَ
“Alhali kuwa Allah ne Ya halicce ku, da ma abin da kuke aikatawa?”
خَلَقَ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضَ بِٱلۡحَقِّۖ يُكَوِّرُ ٱلَّيۡلَ عَلَى ٱلنَّهَارِ وَيُكَوِّرُ ٱلنَّهَارَ عَلَى ٱلَّيۡلِۖ وَسَخَّرَ ٱلشَّمۡسَ وَٱلۡقَمَرَۖ كُلّٞ يَجۡرِي لِأَجَلٖ مُّسَمًّىۗ أَلَا هُوَ ٱلۡعَزِيزُ ٱلۡغَفَّـٰرُ
Ya halicci sammai da qasa da gaskiya; Yana naxa dare a kan yini, Ya kuma naxa yini a kan dare; kuma Ya hore rana da wata; kowane yana tafiya zuwa wani lokaci qayyadajje. Ku saurara! Shi ne Mabuwayi, Mai yawan gafara
خَلَقَكُم مِّن نَّفۡسٖ وَٰحِدَةٖ ثُمَّ جَعَلَ مِنۡهَا زَوۡجَهَا وَأَنزَلَ لَكُم مِّنَ ٱلۡأَنۡعَٰمِ ثَمَٰنِيَةَ أَزۡوَٰجٖۚ يَخۡلُقُكُمۡ فِي بُطُونِ أُمَّهَٰتِكُمۡ خَلۡقٗا مِّنۢ بَعۡدِ خَلۡقٖ فِي ظُلُمَٰتٖ ثَلَٰثٖۚ ذَٰلِكُمُ ٱللَّهُ رَبُّكُمۡ لَهُ ٱلۡمُلۡكُۖ لَآ إِلَٰهَ إِلَّا هُوَۖ فَأَنَّىٰ تُصۡرَفُونَ
Ya halicce ku daga rai guda (shi ne Adamu), sannan Ya halicci matarsa daga gare shi, Ya kuma halitta muku dangogi guda takwas na dabbobin ni’ima. Yana (shirya) halittarku a cikin cikkunan iyayenku mata, matakin halitta bayan wani matakin, cikin duffai guda uku[1]. Wannan kuwa Shi ne Allah Ubangijinku; Wanda mulki nasa ne; babu wani abin bauta da gaskiya sai Shi. To ta ina ne ake juyar da ku?
1- Watau duhun ciki da duhun mahaifa da kuma duhun mabiyiya.
ٱللَّهُ خَٰلِقُ كُلِّ شَيۡءٖۖ وَهُوَ عَلَىٰ كُلِّ شَيۡءٖ وَكِيلٞ
Allah ne Mahaliccin komai; kuma Shi ne Wakili a kan komai
لَخَلۡقُ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِ أَكۡبَرُ مِنۡ خَلۡقِ ٱلنَّاسِ وَلَٰكِنَّ أَكۡثَرَ ٱلنَّاسِ لَا يَعۡلَمُونَ
Tabbas halittar sammai da qasa ta fi girma a kan halittar mutane, sai dai kuma yawancin mutane ba sa sanin (haka)
ذَٰلِكُمُ ٱللَّهُ رَبُّكُمۡ خَٰلِقُ كُلِّ شَيۡءٖ لَّآ إِلَٰهَ إِلَّا هُوَۖ فَأَنَّىٰ تُؤۡفَكُونَ
Wannan Shi ne Allah Ubangijinku, Mahaliccin komai, babu wani abin bauta da gaskiya sai Shi; to ina ne ake kautar da ku?
ٱللَّهُ ٱلَّذِي جَعَلَ لَكُمُ ٱلۡأَرۡضَ قَرَارٗا وَٱلسَّمَآءَ بِنَآءٗ وَصَوَّرَكُمۡ فَأَحۡسَنَ صُوَرَكُمۡ وَرَزَقَكُم مِّنَ ٱلطَّيِّبَٰتِۚ ذَٰلِكُمُ ٱللَّهُ رَبُّكُمۡۖ فَتَبَارَكَ ٱللَّهُ رَبُّ ٱلۡعَٰلَمِينَ
Allah ne wanda Ya sanya muku qasa ta zama wurin zama, sama kuma ta zama rufi, Ya kuma suranta ku, sai Ya kyautata surorinku, Ya kuma arzuta ku da daxaxan abubuwa. Wannan fa Shi ne Allah Ubangijinku. To Allah Ubangijin talikai albarkatunsa sun yawaita
هُوَ ٱلَّذِي خَلَقَكُم مِّن تُرَابٖ ثُمَّ مِن نُّطۡفَةٖ ثُمَّ مِنۡ عَلَقَةٖ ثُمَّ يُخۡرِجُكُمۡ طِفۡلٗا ثُمَّ لِتَبۡلُغُوٓاْ أَشُدَّكُمۡ ثُمَّ لِتَكُونُواْ شُيُوخٗاۚ وَمِنكُم مَّن يُتَوَفَّىٰ مِن قَبۡلُۖ وَلِتَبۡلُغُوٓاْ أَجَلٗا مُّسَمّٗى وَلَعَلَّكُمۡ تَعۡقِلُونَ
“Shi ne wanda Ya halicce ku daga qasa, sannan daga xigon maniyyi, sannan daga gudan jini, daga nan Ya fito da ku kuna jarirai, sannan don ku kai qarfinku, sannan kuma ku zama tsofaffi. Daga cikinku kuma akwai wanda ake karvar ransa kafin wannan; don kuma ku isa zuwa wani lokaci qayyadajje[1], don kuma ku hankalta
1- Wanda ba za su rage ba ba kuma za su qara ba, watau lokacin mutuwarsu.
هُوَ ٱلَّذِي يُحۡيِۦ وَيُمِيتُۖ فَإِذَا قَضَىٰٓ أَمۡرٗا فَإِنَّمَا يَقُولُ لَهُۥ كُن فَيَكُونُ
“Shi ne wanda Yake rayawa Yake kuma kashewa; to idan zai hukunta wani al’amari sai kawai Ya ce da shi: ‘Kasance’, sai ya kasance.”
وَمِنۡ ءَايَٰتِهِۦٓ أَنَّكَ تَرَى ٱلۡأَرۡضَ خَٰشِعَةٗ فَإِذَآ أَنزَلۡنَا عَلَيۡهَا ٱلۡمَآءَ ٱهۡتَزَّتۡ وَرَبَتۡۚ إِنَّ ٱلَّذِيٓ أَحۡيَاهَا لَمُحۡيِ ٱلۡمَوۡتَىٰٓۚ إِنَّهُۥ عَلَىٰ كُلِّ شَيۡءٖ قَدِيرٌ
Yana kuma daga ayoyinsa cewa lalle za ka ga qasa a qeqashe, to idan Mun saukar mata da ruwa sai ta girgiza ta kumbura (ta fitar da tsirrai). Lalle wanda Ya raya ta Shi ne Mai raya matattu. Lalle Shi Mai iko ne a kan komai
أَمِ ٱتَّخَذُواْ مِن دُونِهِۦٓ أَوۡلِيَآءَۖ فَٱللَّهُ هُوَ ٱلۡوَلِيُّ وَهُوَ يُحۡيِ ٱلۡمَوۡتَىٰ وَهُوَ عَلَىٰ كُلِّ شَيۡءٖ قَدِيرٞ
Ko dai sun riqi wasu majivinta ne ba Shi ba. To Allah Shi ne Majivinci, Shi ne kuma Yake raya matattu, Shi kuma Mai iko ne a kan komai
مَا خَلَقۡنَا ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضَ وَمَا بَيۡنَهُمَآ إِلَّا بِٱلۡحَقِّ وَأَجَلٖ مُّسَمّٗىۚ وَٱلَّذِينَ كَفَرُواْ عَمَّآ أُنذِرُواْ مُعۡرِضُونَ
Ba Mu halicci sammai da qasa da abin da yake tsakaninsu ba sai don gaskiya da kuma (zuwa) wani lokaci qayyadajje. Waxanda kuwa suka kafirta masu bijire wa abin da aka yi musu gargaxi da shi ne
أَوَلَمۡ يَرَوۡاْ أَنَّ ٱللَّهَ ٱلَّذِي خَلَقَ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضَ وَلَمۡ يَعۡيَ بِخَلۡقِهِنَّ بِقَٰدِرٍ عَلَىٰٓ أَن يُحۡـِۧيَ ٱلۡمَوۡتَىٰۚ بَلَىٰٓۚ إِنَّهُۥ عَلَىٰ كُلِّ شَيۡءٖ قَدِيرٞ
Ba sa ganin cewa Allah wanda Ya halicci sammai da qasa, Bai kuma gajiya ba wajen halittar su, Mai iko ne kan Ya raya matattu? Haka ne, lalle Shi Mai iko ne a kan komai
رِّزۡقٗا لِّلۡعِبَادِۖ وَأَحۡيَيۡنَا بِهِۦ بَلۡدَةٗ مَّيۡتٗاۚ كَذَٰلِكَ ٱلۡخُرُوجُ
Don arzuta bayi, Muka kuma raya busasshen gari da shi. Kamar haka ne fitowa (daga qabari) take
إِنَّا نَحۡنُ نُحۡيِۦ وَنُمِيتُ وَإِلَيۡنَا ٱلۡمَصِيرُ
Lalle Mu ne Muke rayawa, Muke kuma kashewa, kuma makoma zuwa gare Mu ne
وَمِن كُلِّ شَيۡءٍ خَلَقۡنَا زَوۡجَيۡنِ لَعَلَّكُمۡ تَذَكَّرُونَ
Daga kowane abu kuma Mun halicci nau’i biyu, don ku wa’azantu
خَلَقَ ٱلۡإِنسَٰنَ مِن صَلۡصَٰلٖ كَٱلۡفَخَّارِ
Ya halicci mutum daga busasshen tavo kamar kasko
وَخَلَقَ ٱلۡجَآنَّ مِن مَّارِجٖ مِّن نَّارٖ
Ya kuma halicci aljani daga harshen wuta
نَحۡنُ خَلَقۡنَٰكُمۡ فَلَوۡلَا تُصَدِّقُونَ
Mu ne Muka halicce ku, me ya sa ba kwa gaskatawa?
أَفَرَءَيۡتُم مَّا تُمۡنُونَ
Ba kwa ganin maniyyi da kuke zubawa
ءَأَنتُمۡ تَخۡلُقُونَهُۥٓ أَمۡ نَحۡنُ ٱلۡخَٰلِقُونَ
Shin ku ne kuke halittar sa, ko kuwa Mu ne Masu halittar?
نَحۡنُ قَدَّرۡنَا بَيۡنَكُمُ ٱلۡمَوۡتَ وَمَا نَحۡنُ بِمَسۡبُوقِينَ
Mu ne Muke qaddara mutuwa a tsakaninku, kuma Mu ba Masu gajiyawa ba ne
عَلَىٰٓ أَن نُّبَدِّلَ أَمۡثَٰلَكُمۡ وَنُنشِئَكُمۡ فِي مَا لَا تَعۡلَمُونَ
A kan Mu musanya irinku Mu kuma halitta ku cikin abin da ba ku sani ba
وَلَقَدۡ عَلِمۡتُمُ ٱلنَّشۡأَةَ ٱلۡأُولَىٰ فَلَوۡلَا تَذَكَّرُونَ
Haqiqa kuma ku kun san halitta ta farko, don me ba kwa wa’azantuwa?
لَهُۥ مُلۡكُ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِۖ يُحۡيِۦ وَيُمِيتُۖ وَهُوَ عَلَىٰ كُلِّ شَيۡءٖ قَدِيرٌ
Mulkin sammai da qasa nasa ne; Yana rayawa, Yana kuma kashewa; kuma Shi Mai iko ne a kan komai
هُوَ ٱلَّذِي خَلَقَ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضَ فِي سِتَّةِ أَيَّامٖ ثُمَّ ٱسۡتَوَىٰ عَلَى ٱلۡعَرۡشِۖ يَعۡلَمُ مَا يَلِجُ فِي ٱلۡأَرۡضِ وَمَا يَخۡرُجُ مِنۡهَا وَمَا يَنزِلُ مِنَ ٱلسَّمَآءِ وَمَا يَعۡرُجُ فِيهَاۖ وَهُوَ مَعَكُمۡ أَيۡنَ مَا كُنتُمۡۚ وَٱللَّهُ بِمَا تَعۡمَلُونَ بَصِيرٞ
Shi ne wanda Ya halicci sammai da qasa cikin kwana shida, sannan Ya daidaitu a kan Al’arshi. Yana sane da abin da yake shiga cikin qasa da abin da yake fitowa daga cikinta, da kuma abin da yake saukowa daga sama da abin da yake hawa cikinta; kuma Shi Yana tare da ku a duk inda kuka kasance[1]. Allah kuwa Mai ganin duk abin da kuke aikatawa ne
1- Watau da iliminsa. Babu wani abu da yake vuya a gare shi, yana kuma ganin duk abin da suke aikatawa.