كَيۡفَ تَكۡفُرُونَ بِٱللَّهِ وَكُنتُمۡ أَمۡوَٰتٗا فَأَحۡيَٰكُمۡۖ ثُمَّ يُمِيتُكُمۡ ثُمَّ يُحۡيِيكُمۡ ثُمَّ إِلَيۡهِ تُرۡجَعُونَ
Ta yaya kuke kafirce wa Allah alhalin a da kun kasance matattu, sannan Ya raya ku, sannan zai kuma mayar da ku matattu sannan Ya raya ku (a karo na biyu) sannan zuwa gare Shi ake mayar da ku?
وَلَا تَقُولُواْ لِمَن يُقۡتَلُ فِي سَبِيلِ ٱللَّهِ أَمۡوَٰتُۢۚ بَلۡ أَحۡيَآءٞ وَلَٰكِن لَّا تَشۡعُرُونَ
Kada kuma ku ce wa waxanda ake kashewa a kan hanyar Allah su matattu ne. A’a, rayayyu ne, sai dai ku ne ba ku sani ba
وَلَكُمۡ فِي ٱلۡقِصَاصِ حَيَوٰةٞ يَـٰٓأُوْلِي ٱلۡأَلۡبَٰبِ لَعَلَّكُمۡ تَتَّقُونَ
Kuma a cikin (hukuncin) qisasi akwai (tsare) rayuwa a gare ku, ya ku ma’abota hankula, don ku samu taqawa
تُولِجُ ٱلَّيۡلَ فِي ٱلنَّهَارِ وَتُولِجُ ٱلنَّهَارَ فِي ٱلَّيۡلِۖ وَتُخۡرِجُ ٱلۡحَيَّ مِنَ ٱلۡمَيِّتِ وَتُخۡرِجُ ٱلۡمَيِّتَ مِنَ ٱلۡحَيِّۖ وَتَرۡزُقُ مَن تَشَآءُ بِغَيۡرِ حِسَابٖ
“Kana shigar da dare a cikin yini, kuma Kana shigar da yini a cikin dare, kuma Kana fitar da mai rai daga cikin matacce, kuma Kana fitar da matacce daga cikin mai rai; kuma Kana arzurta wanda Ka ga dama ba tare da lissafi ba.”
يَـٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ لَا تَكُونُواْ كَٱلَّذِينَ كَفَرُواْ وَقَالُواْ لِإِخۡوَٰنِهِمۡ إِذَا ضَرَبُواْ فِي ٱلۡأَرۡضِ أَوۡ كَانُواْ غُزّٗى لَّوۡ كَانُواْ عِندَنَا مَا مَاتُواْ وَمَا قُتِلُواْ لِيَجۡعَلَ ٱللَّهُ ذَٰلِكَ حَسۡرَةٗ فِي قُلُوبِهِمۡۗ وَٱللَّهُ يُحۡيِۦ وَيُمِيتُۗ وَٱللَّهُ بِمَا تَعۡمَلُونَ بَصِيرٞ
Ya ku waxanda suka yi imani, kada ku kasance kamar waxanda suka kafirta, kuma suka riqa faxa wa ‘yan’uwansu yayin da suka yi tafiya a bayan qasa, ko kuma suka kasance mayaqa: “In da sun kasance tare da mu, ai da ba su mutu ba, kuma da ba a kashe su ba,” don Allah Ya sanya waccan (maganar) ta zamo nadama a cikin zukatansu. Kuma Allah Shi ne Mai rayawa, kuma Shi ne Mai kashewa. Kuma Allah Mai ganin abin da kuke aikatawa ne
وَلَا تَحۡسَبَنَّ ٱلَّذِينَ قُتِلُواْ فِي سَبِيلِ ٱللَّهِ أَمۡوَٰتَۢاۚ بَلۡ أَحۡيَآءٌ عِندَ رَبِّهِمۡ يُرۡزَقُونَ
Kuma kada ka yi tsammanin waxanda aka kashe su a wajen yaxa kalmar Allah matattu ne. A’a, rayayyu ne a wajen Ubangijinsu, ana arzurta su
يَـٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ لَا تَأۡكُلُوٓاْ أَمۡوَٰلَكُم بَيۡنَكُم بِٱلۡبَٰطِلِ إِلَّآ أَن تَكُونَ تِجَٰرَةً عَن تَرَاضٖ مِّنكُمۡۚ وَلَا تَقۡتُلُوٓاْ أَنفُسَكُمۡۚ إِنَّ ٱللَّهَ كَانَ بِكُمۡ رَحِيمٗا
Ya ku waxanda suka yi imani, kada ku ci dukiyoyinku a tsakaninku ta hanyar rashin gaskiya, sai dai in ya kasance kasuwanci ne bisa yarjejeniya a tsakaninku. Kuma kada ku kashe kawunanku. Lalle Allah Ya kasance Mai tausaya muku ne
مِنۡ أَجۡلِ ذَٰلِكَ كَتَبۡنَا عَلَىٰ بَنِيٓ إِسۡرَـٰٓءِيلَ أَنَّهُۥ مَن قَتَلَ نَفۡسَۢا بِغَيۡرِ نَفۡسٍ أَوۡ فَسَادٖ فِي ٱلۡأَرۡضِ فَكَأَنَّمَا قَتَلَ ٱلنَّاسَ جَمِيعٗا وَمَنۡ أَحۡيَاهَا فَكَأَنَّمَآ أَحۡيَا ٱلنَّاسَ جَمِيعٗاۚ وَلَقَدۡ جَآءَتۡهُمۡ رُسُلُنَا بِٱلۡبَيِّنَٰتِ ثُمَّ إِنَّ كَثِيرٗا مِّنۡهُم بَعۡدَ ذَٰلِكَ فِي ٱلۡأَرۡضِ لَمُسۡرِفُونَ
Saboda wannan ne muka wajabta wa Banu-Isra’ila cewa, duk wanda ya kashe wani rai ba tare da (laifin kisan) kai ba, ko kuma wata varna a bayan qasa, to kamar ya kashe mutane ne gaba xaya, wanda kuwa ya raya shi, to kamar ya raya mutane ne gaba xaya. Kuma lalle haqiqa manzanninmu sun zo musu da (hujjoji) mabayyana, amma sai ga shi da yawa daga cikinsu bayan hakan, lalle masu varna ne a bayan qasa
وَلَا تَأۡكُلُواْ مِمَّا لَمۡ يُذۡكَرِ ٱسۡمُ ٱللَّهِ عَلَيۡهِ وَإِنَّهُۥ لَفِسۡقٞۗ وَإِنَّ ٱلشَّيَٰطِينَ لَيُوحُونَ إِلَىٰٓ أَوۡلِيَآئِهِمۡ لِيُجَٰدِلُوكُمۡۖ وَإِنۡ أَطَعۡتُمُوهُمۡ إِنَّكُمۡ لَمُشۡرِكُونَ
Kuma kada ku ci daga abin da ba a ambaci sunan Allah a kansa ba, kuma lalle shi tabbas fasiqanci ne. Haqiqa shaixanu tabbas suna kimsa wa masoyansu, don su yi jayayya da ku; idan kuwa kuka bi su to lalle tabbas ku mushirikai ne
۞قُلۡ تَعَالَوۡاْ أَتۡلُ مَا حَرَّمَ رَبُّكُمۡ عَلَيۡكُمۡۖ أَلَّا تُشۡرِكُواْ بِهِۦ شَيۡـٔٗاۖ وَبِٱلۡوَٰلِدَيۡنِ إِحۡسَٰنٗاۖ وَلَا تَقۡتُلُوٓاْ أَوۡلَٰدَكُم مِّنۡ إِمۡلَٰقٖ نَّحۡنُ نَرۡزُقُكُمۡ وَإِيَّاهُمۡۖ وَلَا تَقۡرَبُواْ ٱلۡفَوَٰحِشَ مَا ظَهَرَ مِنۡهَا وَمَا بَطَنَۖ وَلَا تَقۡتُلُواْ ٱلنَّفۡسَ ٱلَّتِي حَرَّمَ ٱللَّهُ إِلَّا بِٱلۡحَقِّۚ ذَٰلِكُمۡ وَصَّىٰكُم بِهِۦ لَعَلَّكُمۡ تَعۡقِلُونَ
Ka ce: “Ku taho in karanta muku abin da Ubangijinku Ya haramta muku; kada ku haxa Shi da wani; kuma ku kyautata wa mahaifa; kuma kar ku kashe ‘ya’yanku saboda talauci; Mu ne za Mu arzuta ku har da su; kuma kada ku kusanci munanan (ayyuka) na sarari da na voye; kuma kada ku kashe ran da Allah Ya haramta (a kashe shi), sai idan da wani hakki. Wannan shi ne abin da (Allah) Ya yi muku wasiyya da shi, don ku zamo masu hankali
هُوَ يُحۡيِۦ وَيُمِيتُ وَإِلَيۡهِ تُرۡجَعُونَ
Shi ne Yake rayawa Yake kuma kashewa, kuma wurinsa za a mai da ku
وَإِنَّا لَنَحۡنُ نُحۡيِۦ وَنُمِيتُ وَنَحۡنُ ٱلۡوَٰرِثُونَ
Lalle kuma tabbas Mu Muke rayawa kuma Muke kashewa, Mu ne kuma Masu gaje (komai)
وَلَا تَقۡتُلُوٓاْ أَوۡلَٰدَكُمۡ خَشۡيَةَ إِمۡلَٰقٖۖ نَّحۡنُ نَرۡزُقُهُمۡ وَإِيَّاكُمۡۚ إِنَّ قَتۡلَهُمۡ كَانَ خِطۡـٔٗا كَبِيرٗا
Kada kuma ku kashe ‘ya’yayenku don tsoron talauci: Mu ne Muke arzuta su har ma da ku. Lalle kashe su kuskure ne babba
وَلَا تَقۡتُلُواْ ٱلنَّفۡسَ ٱلَّتِي حَرَّمَ ٱللَّهُ إِلَّا بِٱلۡحَقِّۗ وَمَن قُتِلَ مَظۡلُومٗا فَقَدۡ جَعَلۡنَا لِوَلِيِّهِۦ سُلۡطَٰنٗا فَلَا يُسۡرِف فِّي ٱلۡقَتۡلِۖ إِنَّهُۥ كَانَ مَنصُورٗا
Kuma kada ku kashe ran da Allah Ya haramta (kashewa) sai da haqqi. Wanda aka kashe ta hanyar zalunci, to lalle Mun bai wa magajinsa dama (ta ramuwa)[1], to (amma) kada ya wuce gona da iri wajen kisa; lalle shi ya zamanto abin dafa wa baya ne
1- Watau ta hanyar shari’a.
أَوَلَمۡ يَرَ ٱلَّذِينَ كَفَرُوٓاْ أَنَّ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضَ كَانَتَا رَتۡقٗا فَفَتَقۡنَٰهُمَاۖ وَجَعَلۡنَا مِنَ ٱلۡمَآءِ كُلَّ شَيۡءٍ حَيٍّۚ أَفَلَا يُؤۡمِنُونَ
Yanzu waxanda suka kafirta ba sa ganin cewa a da can sammai da qasa a haxe suke, sannan Muka raba su[1]; Muka kuma halicci duk wani abu mai rai daga ruwa? To me ya sa ba za su yi imani ba?
1- Watau Allah () ya fara halittar sammai da qasa a manne da juna daga bisani ya raba tsakaninsu.
وَهُوَ ٱلَّذِيٓ أَحۡيَاكُمۡ ثُمَّ يُمِيتُكُمۡ ثُمَّ يُحۡيِيكُمۡۗ إِنَّ ٱلۡإِنسَٰنَ لَكَفُورٞ
Shi ne kuma Wanda Ya raya ku sannan zai kashe ku sannan Ya (sake) raya ku. Lalle mutum tabbas mai yawan butulci ne
وَهُوَ ٱلَّذِي يُحۡيِۦ وَيُمِيتُ وَلَهُ ٱخۡتِلَٰفُ ٱلَّيۡلِ وَٱلنَّهَارِۚ أَفَلَا تَعۡقِلُونَ
Kuma Shi ne Yake rayawa Yake kuma kashewa, kuma sassavawar dare da rana nasa ne. Me ya sa ba kwa hankalta ne?
يُخۡرِجُ ٱلۡحَيَّ مِنَ ٱلۡمَيِّتِ وَيُخۡرِجُ ٱلۡمَيِّتَ مِنَ ٱلۡحَيِّ وَيُحۡيِ ٱلۡأَرۡضَ بَعۡدَ مَوۡتِهَاۚ وَكَذَٰلِكَ تُخۡرَجُونَ
Yana fitar da rayayye daga matacce, Yana kuma fitar da matacce daga rayayye, kuma Yana raya qasa bayan mutuwarta. Kamar haka ne kuma za a fito da ku (daga qaburburanku)
إِنَّا نَحۡنُ نُحۡيِۦ وَنُمِيتُ وَإِلَيۡنَا ٱلۡمَصِيرُ
Lalle Mu ne Muke rayawa, Muke kuma kashewa, kuma makoma zuwa gare Mu ne
لَهُۥ مُلۡكُ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِۖ يُحۡيِۦ وَيُمِيتُۖ وَهُوَ عَلَىٰ كُلِّ شَيۡءٖ قَدِيرٌ
Mulkin sammai da qasa nasa ne; Yana rayawa, Yana kuma kashewa; kuma Shi Mai iko ne a kan komai
ٱلَّذِي خَلَقَ ٱلۡمَوۡتَ وَٱلۡحَيَوٰةَ لِيَبۡلُوَكُمۡ أَيُّكُمۡ أَحۡسَنُ عَمَلٗاۚ وَهُوَ ٱلۡعَزِيزُ ٱلۡغَفُورُ
Wanda Ya halicci mutuwa da rayuwa don Ya jarraba ku (Ya bayyana) wane ne a cikinku ya fi kyakkyawan aiki? Shi kuma Mabuwayi ne, Mai gafara