رَبَّنَآ إِنَّكَ تَعۡلَمُ مَا نُخۡفِي وَمَا نُعۡلِنُۗ وَمَا يَخۡفَىٰ عَلَى ٱللَّهِ مِن شَيۡءٖ فِي ٱلۡأَرۡضِ وَلَا فِي ٱلسَّمَآءِ
“Ya Ubangijinmu, lalle Kai Ka san abin da muke voyewa da abin da muke bayyanawa. Babu wani abu a cikin qasa ko a cikin sama da zai vuya ga Allah
وَلَقَدۡ عَلِمۡنَا ٱلۡمُسۡتَقۡدِمِينَ مِنكُمۡ وَلَقَدۡ عَلِمۡنَا ٱلۡمُسۡتَـٔۡخِرِينَ
Haqiqa kuma Mun san marigaya daga cikinku kuma haqiqa Mun san masu biyowa baya[1]
1- Watau Allah () ya san waxanda za a riga haihuwarsu su riga mutuwa, ya san kuma waxanda za a haife su, daga baya su mutu.
وَٱللَّهُ يَعۡلَمُ مَا تُسِرُّونَ وَمَا تُعۡلِنُونَ
Allah kuma Ya san abin da kuke voyewa da abin da kuke bayyanawa
لَا جَرَمَ أَنَّ ٱللَّهَ يَعۡلَمُ مَا يُسِرُّونَ وَمَا يُعۡلِنُونَۚ إِنَّهُۥ لَا يُحِبُّ ٱلۡمُسۡتَكۡبِرِينَ
Ba shakka, lalle Allah Yana sane da abin da suke voyewa da abin da suke bayyanawa. Lalle Shi ba Ya son masu girman kai
ٱلَّذِينَ تَتَوَفَّىٰهُمُ ٱلۡمَلَـٰٓئِكَةُ ظَالِمِيٓ أَنفُسِهِمۡۖ فَأَلۡقَوُاْ ٱلسَّلَمَ مَا كُنَّا نَعۡمَلُ مِن سُوٓءِۭۚ بَلَىٰٓۚ إِنَّ ٱللَّهَ عَلِيمُۢ بِمَا كُنتُمۡ تَعۡمَلُونَ
Waxanda mala’iku suke karvar ransu suna masu zaluntar kawunansu; sai suka ba da kai (suna cewa,): “Ba mu kasance muna yin wani mummunan aiki ba.” A’a, ba haka ba ne, lalle Allah Masanin abin da kuka zamanto kuna aikatawa ne
فَلَا تَضۡرِبُواْ لِلَّهِ ٱلۡأَمۡثَالَۚ إِنَّ ٱللَّهَ يَعۡلَمُ وَأَنتُمۡ لَا تَعۡلَمُونَ
Kada kuma ku sanya wa Allah abokan tarayya. Lalle Allah Yana sane, ku ne ba ku sani ba
وَأَوۡفُواْ بِعَهۡدِ ٱللَّهِ إِذَا عَٰهَدتُّمۡ وَلَا تَنقُضُواْ ٱلۡأَيۡمَٰنَ بَعۡدَ تَوۡكِيدِهَا وَقَدۡ جَعَلۡتُمُ ٱللَّهَ عَلَيۡكُمۡ كَفِيلًاۚ إِنَّ ٱللَّهَ يَعۡلَمُ مَا تَفۡعَلُونَ
Ku kuma cika alqawarin Allah idan kuka xauki alqawari, kada kuma ku warware rantsuwa bayan kun qarfafa ta, alhali kuwa kun sanya Allah shaida a kanku. Lalle Allah Yana sane da abin da kuke aikatawa
ٱدۡعُ إِلَىٰ سَبِيلِ رَبِّكَ بِٱلۡحِكۡمَةِ وَٱلۡمَوۡعِظَةِ ٱلۡحَسَنَةِۖ وَجَٰدِلۡهُم بِٱلَّتِي هِيَ أَحۡسَنُۚ إِنَّ رَبَّكَ هُوَ أَعۡلَمُ بِمَن ضَلَّ عَن سَبِيلِهِۦ وَهُوَ أَعۡلَمُ بِٱلۡمُهۡتَدِينَ
Ka yi kira zuwa ga tafarkin Ubangiijnka cikin hikima da kyakkyawan wa’azi, ka kuma yi jayayya da su ta hanyar da ta fi kyau. Lalle Ubangijinka Shi ne Mafi sanin wanda ya vace daga hanyarsa, kuma Shi ne Mafi sanin shiryayyu
رَّبُّكُمۡ أَعۡلَمُ بِمَا فِي نُفُوسِكُمۡۚ إِن تَكُونُواْ صَٰلِحِينَ فَإِنَّهُۥ كَانَ لِلۡأَوَّـٰبِينَ غَفُورٗا
Ubangijinku ne Mafi sanin abin da yake zukatanku. Idan kuka zamanto nagari, to lalle Shi Ya tabbata Mai gafara ne ga masu komawa gare Shi da tuba
رَّبُّكُمۡ أَعۡلَمُ بِكُمۡۖ إِن يَشَأۡ يَرۡحَمۡكُمۡ أَوۡ إِن يَشَأۡ يُعَذِّبۡكُمۡۚ وَمَآ أَرۡسَلۡنَٰكَ عَلَيۡهِمۡ وَكِيلٗا
Ubangijinku (Shi) Ya fi sanin ku; in Ya ga dama sai Ya ji qan ku ko kuma in Ya ga dama sai Ya azabtar da ku. Ba Mu kuwa aiko ka ba don ka zama wakili a kansu
وَرَبُّكَ أَعۡلَمُ بِمَن فِي ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِۗ وَلَقَدۡ فَضَّلۡنَا بَعۡضَ ٱلنَّبِيِّـۧنَ عَلَىٰ بَعۡضٖۖ وَءَاتَيۡنَا دَاوُۥدَ زَبُورٗا
Ubangijinka kuma (Shi ne) Mafi sanin abin da yake cikin sammai da qasa. Haqiqa kuma Mun fifita wasu annabawa a kan wasu; Muka kuma bai wa Dawuda (littafin) Zabura
قُلۡ كُلّٞ يَعۡمَلُ عَلَىٰ شَاكِلَتِهِۦ فَرَبُّكُمۡ أَعۡلَمُ بِمَنۡ هُوَ أَهۡدَىٰ سَبِيلٗا
Ka ce: “Kowa ya yi aiki bisa hanyarsa sai dai Ubangijinku (Shi ne) Mafi sanin wanda ya fi shiriya a kan madaidaiciyar hanya.”
وَيَسۡـَٔلُونَكَ عَنِ ٱلرُّوحِۖ قُلِ ٱلرُّوحُ مِنۡ أَمۡرِ رَبِّي وَمَآ أُوتِيتُم مِّنَ ٱلۡعِلۡمِ إِلَّا قَلِيلٗا
Suna kuma tambayar ka game da ruhi. Ka ce da su: “Shi ruhi yana daga al’amarin Ubangijina, ba abin da aka ba ku na ilimi sai xan kaxan.”
ثُمَّ لَنَحۡنُ أَعۡلَمُ بِٱلَّذِينَ هُمۡ أَوۡلَىٰ بِهَا صِلِيّٗا
Sannan babu shakka Mu Muka fi sanin waxanda suka fi cancanta da qonuwa da ita (watau wuta)
وَإِن تَجۡهَرۡ بِٱلۡقَوۡلِ فَإِنَّهُۥ يَعۡلَمُ ٱلسِّرَّ وَأَخۡفَى
Idan kuma ka xaga murya da furuci to lalle Shi Yana sane da sirri da abin da ya fi (sirri) vuya
قَالَ عِلۡمُهَا عِندَ رَبِّي فِي كِتَٰبٖۖ لَّا يَضِلُّ رَبِّي وَلَا يَنسَى
(Musa) ya ce: “Saninsu yana wurin Ubangijina a cikin Lauhul-Mahafuzu; Ubangijina kuma ba Ya kuskure (cikin iliminsa) kuma ba Ya mantuwa
إِنَّمَآ إِلَٰهُكُمُ ٱللَّهُ ٱلَّذِي لَآ إِلَٰهَ إِلَّا هُوَۚ وَسِعَ كُلَّ شَيۡءٍ عِلۡمٗا
Abin bautarku kawai shi ne Allah wanda babu wani abin bauta da gaskiya sai Shi. Ya yalwaci komai da iliminsa
نَّحۡنُ أَعۡلَمُ بِمَا يَقُولُونَ إِذۡ يَقُولُ أَمۡثَلُهُمۡ طَرِيقَةً إِن لَّبِثۡتُمۡ إِلَّا يَوۡمٗا
Mu Muka fi sanin abin da suke faxi lokacin da wanda ya fi tunani daga cikinsu yake cewa: “Ba ku zauna ba face rana guda.”
يَعۡلَمُ مَا بَيۡنَ أَيۡدِيهِمۡ وَمَا خَلۡفَهُمۡ وَلَا يُحِيطُونَ بِهِۦ عِلۡمٗا
(Allah) Yana sane da abin da yake gaba gare su (na ranar alqiyama) da kuma abin da yake bayansu (na ayyukan da suka yi a duniya), su kuwa ba za su kewaye da saninsa ba
قَالَ رَبِّي يَعۡلَمُ ٱلۡقَوۡلَ فِي ٱلسَّمَآءِ وَٱلۡأَرۡضِۖ وَهُوَ ٱلسَّمِيعُ ٱلۡعَلِيمُ
Ya ce: “Ubangijina Yana sane da (kowace) magana a cikin sammai da qasa; Shi kuwa Mai ji ne, Masani
يَعۡلَمُ مَا بَيۡنَ أَيۡدِيهِمۡ وَمَا خَلۡفَهُمۡ وَلَا يَشۡفَعُونَ إِلَّا لِمَنِ ٱرۡتَضَىٰ وَهُم مِّنۡ خَشۡيَتِهِۦ مُشۡفِقُونَ
Yana sane da ayyukansu da suka gabatar da na nan gaba, ba kuma za su yi ceto ba sai ga wanda Ya yarda (daga bayinsa), suna kuwa masu kaffa-kaffa don tsoron Sa
۞وَلَقَدۡ ءَاتَيۡنَآ إِبۡرَٰهِيمَ رُشۡدَهُۥ مِن قَبۡلُ وَكُنَّا بِهِۦ عَٰلِمِينَ
Haqiqa kuma Mun bai wa Ibrahimu shiriyarsa tun da farko, Mun kuma zamanto Muna sane da shi
وَلِسُلَيۡمَٰنَ ٱلرِّيحَ عَاصِفَةٗ تَجۡرِي بِأَمۡرِهِۦٓ إِلَى ٱلۡأَرۡضِ ٱلَّتِي بَٰرَكۡنَا فِيهَاۚ وَكُنَّا بِكُلِّ شَيۡءٍ عَٰلِمِينَ
Sulaimanu kuwa (Muka hore masa) iska mai qarfi tana gudu da umarninsa zuwa qasar da Muka yi albarka a cikinta, (watau Sham). Mun kuwa kasance Masana ga kowanne abu
إِنَّهُۥ يَعۡلَمُ ٱلۡجَهۡرَ مِنَ ٱلۡقَوۡلِ وَيَعۡلَمُ مَا تَكۡتُمُونَ
“Lalle Shi (Allah) Yana sane da (abin da kuke) bayyanawa na magana Yana kuma sane da abin da kuke voyewa
أَلَمۡ تَعۡلَمۡ أَنَّ ٱللَّهَ يَعۡلَمُ مَا فِي ٱلسَّمَآءِ وَٱلۡأَرۡضِۚ إِنَّ ذَٰلِكَ فِي كِتَٰبٍۚ إِنَّ ذَٰلِكَ عَلَى ٱللَّهِ يَسِيرٞ
Shin ba ka sani ba cewa lalle Allah Yana sane da abin da yake cikin sama da wanda yake qasa? Lalle wannan yana cikin littafi (wato Lauhul-Mahafuzu). Lalle wannan mai sauqi ne a wurin Allah
يَعۡلَمُ مَا بَيۡنَ أَيۡدِيهِمۡ وَمَا خَلۡفَهُمۡۚ وَإِلَى ٱللَّهِ تُرۡجَعُ ٱلۡأُمُورُ
Yana sane da abin da yake gabansu da abin da yake bayansu. Zuwa ga Allah ne kawai ake komar da al’amura
ٱدۡفَعۡ بِٱلَّتِي هِيَ أَحۡسَنُ ٱلسَّيِّئَةَۚ نَحۡنُ أَعۡلَمُ بِمَا يَصِفُونَ
Ka ingije mummunan abu da wanda ya fi kyau. Mu ne Muka fi sanin abin da suke siffata (ka da shi)
إِنَّ ٱلَّذِينَ يُحِبُّونَ أَن تَشِيعَ ٱلۡفَٰحِشَةُ فِي ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ لَهُمۡ عَذَابٌ أَلِيمٞ فِي ٱلدُّنۡيَا وَٱلۡأٓخِرَةِۚ وَٱللَّهُ يَعۡلَمُ وَأَنتُمۡ لَا تَعۡلَمُونَ
Lalle waxanda suke son yaxuwar mummunan abu a cikin waxanda suka yi imani suna da (sakamakon) azaba mai raxaxi a duniya da lahira, kuma Allah (Shi) ne Yake sane, ku ba ba ku san komai ba
فَإِن لَّمۡ تَجِدُواْ فِيهَآ أَحَدٗا فَلَا تَدۡخُلُوهَا حَتَّىٰ يُؤۡذَنَ لَكُمۡۖ وَإِن قِيلَ لَكُمُ ٱرۡجِعُواْ فَٱرۡجِعُواْۖ هُوَ أَزۡكَىٰ لَكُمۡۚ وَٱللَّهُ بِمَا تَعۡمَلُونَ عَلِيمٞ
To idan ba ku sami kowa a cikinsu ba to kada ku shige su har sai an yi muku izini; idan kuwa aka ce da ku ku koma sai ku koma; wannan shi ya fi tsarki a gare ku. Allah kuwa Masanin abin da kuke aikatawa ne
لَّيۡسَ عَلَيۡكُمۡ جُنَاحٌ أَن تَدۡخُلُواْ بُيُوتًا غَيۡرَ مَسۡكُونَةٖ فِيهَا مَتَٰعٞ لَّكُمۡۚ وَٱللَّهُ يَعۡلَمُ مَا تُبۡدُونَ وَمَا تَكۡتُمُونَ
Babu wani laifi a kanku ku shiga gidaje waxanda ba wani zaune a cikinsu, kuma akwai kayanku a cikinsu[1], kuma Allah Yana sane da abin da kuke bayyanawa da abin da kuke voyewa
1- Watau wuraren da aka tanada domin amfanin kowa da kowa, kamar xakunan karatu ko shaguna a kasuwanni.