لَّا تَرَىٰ فِيهَا عِوَجٗا وَلَآ أَمۡتٗا
“Ba za ka ga wani kwari ko tudu a kanta ba.”
يَوۡمَئِذٖ يَتَّبِعُونَ ٱلدَّاعِيَ لَا عِوَجَ لَهُۥۖ وَخَشَعَتِ ٱلۡأَصۡوَاتُ لِلرَّحۡمَٰنِ فَلَا تَسۡمَعُ إِلَّا هَمۡسٗا
A wannan rana ne za su bi mai kira (zuwa matattara), ba mai bauxe masa; kuma (duk) muryoyi su yi qasa-qasa saboda (girman Allah) Mai rahama, sannan ba za ka ji (komai) ba sai raxa
يَوۡمَئِذٖ لَّا تَنفَعُ ٱلشَّفَٰعَةُ إِلَّا مَنۡ أَذِنَ لَهُ ٱلرَّحۡمَٰنُ وَرَضِيَ لَهُۥ قَوۡلٗا
A wannan ranar ceto ba ya amfani sai ga wanda (Allah) Mai rahama Ya yi wa izini, kuma Ya yarda da maganarsa
يَعۡلَمُ مَا بَيۡنَ أَيۡدِيهِمۡ وَمَا خَلۡفَهُمۡ وَلَا يُحِيطُونَ بِهِۦ عِلۡمٗا
(Allah) Yana sane da abin da yake gaba gare su (na ranar alqiyama) da kuma abin da yake bayansu (na ayyukan da suka yi a duniya), su kuwa ba za su kewaye da saninsa ba
۞وَعَنَتِ ٱلۡوُجُوهُ لِلۡحَيِّ ٱلۡقَيُّومِۖ وَقَدۡ خَابَ مَنۡ حَمَلَ ظُلۡمٗا
Kuma dukkanin fuskoki suka qasqanta ga (Allah) Rayayye, Tsayayye (da Zatinsa). Haqiqa kuma duk wanda ya yo dakon zalunci ya tave
وَمَن يَعۡمَلۡ مِنَ ٱلصَّـٰلِحَٰتِ وَهُوَ مُؤۡمِنٞ فَلَا يَخَافُ ظُلۡمٗا وَلَا هَضۡمٗا
Duk kuma wanda yake yin aiki na gari alhali kuwa shi mumini ne, to ba zai ji tsoron zalunci ba ko kuma qwauro
وَكَذَٰلِكَ أَنزَلۡنَٰهُ قُرۡءَانًا عَرَبِيّٗا وَصَرَّفۡنَا فِيهِ مِنَ ٱلۡوَعِيدِ لَعَلَّهُمۡ يَتَّقُونَ أَوۡ يُحۡدِثُ لَهُمۡ ذِكۡرٗا
Kuma kamar haka Muka saukar da shi (Alqur’ani) Balarabe (watau da harshen Larabci), Muka kuma sarrafa ayoyin gargaxi a cikinsa don su kiyaye dokokin (Allah) ko kuma ya sa su su wa’azantu
فَتَعَٰلَى ٱللَّهُ ٱلۡمَلِكُ ٱلۡحَقُّۗ وَلَا تَعۡجَلۡ بِٱلۡقُرۡءَانِ مِن قَبۡلِ أَن يُقۡضَىٰٓ إِلَيۡكَ وَحۡيُهُۥۖ وَقُل رَّبِّ زِدۡنِي عِلۡمٗا
Kuma fa Allah Sarki na gaskiya Ya xaukaka (daga maganganun kafirai). Kada kuma ka yi garaje da (karatun) Alqur’ani tun kafin a gama yi maka wahayinsa, kuma ka ce: “Ubangiji Ka qara min ilimi.”
وَلَقَدۡ عَهِدۡنَآ إِلَىٰٓ ءَادَمَ مِن قَبۡلُ فَنَسِيَ وَلَمۡ نَجِدۡ لَهُۥ عَزۡمٗا
Kuma haqiqa Mun yi alqawari da Adamu tun da farko (cewa kada ya ci itaciyar da aka hana shi), sai ya manta, sai ba Mu same shi da qarfin quduri ba
وَإِذۡ قُلۡنَا لِلۡمَلَـٰٓئِكَةِ ٱسۡجُدُواْ لِأٓدَمَ فَسَجَدُوٓاْ إِلَّآ إِبۡلِيسَ أَبَىٰ
Kuma (ka tuna) lokacin da Muka ce da mala’iku: “Ku yi sujjada ga Adamu” sai suka yi sujjadar sai Iblis ne kawai ya qi
فَقُلۡنَا يَـٰٓـَٔادَمُ إِنَّ هَٰذَا عَدُوّٞ لَّكَ وَلِزَوۡجِكَ فَلَا يُخۡرِجَنَّكُمَا مِنَ ٱلۡجَنَّةِ فَتَشۡقَىٰٓ
Sannan Muka ce: “Ya Adamu, lalle wannan maqiyinka ne kai da matarka, to kada (ku yarda) ya fitar da ku daga Aljanna, sai ka wahala
إِنَّ لَكَ أَلَّا تَجُوعَ فِيهَا وَلَا تَعۡرَىٰ
“Lalle (Allah) Ya yi maka alqawarin ba za ka ji yunwa ba a cikinta, kuma ba za ka yi tsiraici ba
وَأَنَّكَ لَا تَظۡمَؤُاْ فِيهَا وَلَا تَضۡحَىٰ
“Kuma lalle kai ba za ka ji qishi ba a cikinta, kuma ba za ka ji zafin rana ba.”
فَوَسۡوَسَ إِلَيۡهِ ٱلشَّيۡطَٰنُ قَالَ يَـٰٓـَٔادَمُ هَلۡ أَدُلُّكَ عَلَىٰ شَجَرَةِ ٱلۡخُلۡدِ وَمُلۡكٖ لَّا يَبۡلَىٰ
Sai Shaixan ya yi masa waswasi ya ce: “Ya Adamu, yanzu ba na nuna maka wata bishiya ta dawwama da kuma mulki wanda ba zai qare ba?”
فَأَكَلَا مِنۡهَا فَبَدَتۡ لَهُمَا سَوۡءَٰتُهُمَا وَطَفِقَا يَخۡصِفَانِ عَلَيۡهِمَا مِن وَرَقِ ٱلۡجَنَّةِۚ وَعَصَىٰٓ ءَادَمُ رَبَّهُۥ فَغَوَىٰ
Sai suka ci wani abu daga gare ta, sai ga tsiraicinsu ya bayyana gare su, sai suka riqa lulluve (jikinsu) da ganyen Aljanna. Kuma Adamu ya sava wa Ubangijinsa ya bar shiriya
ثُمَّ ٱجۡتَبَٰهُ رَبُّهُۥ فَتَابَ عَلَيۡهِ وَهَدَىٰ
Sannan Ubangijinsa Ya zave shi, sai Ya yafe masa Ya kuma shirye (shi)
قَالَ ٱهۡبِطَا مِنۡهَا جَمِيعَۢاۖ بَعۡضُكُمۡ لِبَعۡضٍ عَدُوّٞۖ فَإِمَّا يَأۡتِيَنَّكُم مِّنِّي هُدٗى فَمَنِ ٱتَّبَعَ هُدَايَ فَلَا يَضِلُّ وَلَا يَشۡقَىٰ
(Allah) Ya ce (da Adamu da Hauwa’u): “Ku sauka daga gare ta (Aljannar) gaba xayanku, sashinku ya dinga gaba da sashi; sannan idan shiriya ta zo muku daga gare Ni, to duk wanda ya bi shiriyata ba zai tave ba, kuma ba zai wahala ba
وَمَنۡ أَعۡرَضَ عَن ذِكۡرِي فَإِنَّ لَهُۥ مَعِيشَةٗ ضَنكٗا وَنَحۡشُرُهُۥ يَوۡمَ ٱلۡقِيَٰمَةِ أَعۡمَىٰ
“Wanda kuma ya bijire wa Alqur’ani to lalle zai yi rayuwa mai qunci, kuma Mu tashe shi makaho ranar alqiyama.”
قَالَ رَبِّ لِمَ حَشَرۡتَنِيٓ أَعۡمَىٰ وَقَدۡ كُنتُ بَصِيرٗا
Zai ce: “Ubangijina me ya sa Ka tashe ni makaho, alhali kuwa na kasance mai gani?”
قَالَ كَذَٰلِكَ أَتَتۡكَ ءَايَٰتُنَا فَنَسِيتَهَاۖ وَكَذَٰلِكَ ٱلۡيَوۡمَ تُنسَىٰ
(Allah) Ya ce: “Kamar haka ne ayoyinmu suka zo maka sai ka manta su, to kamar haka kuwa (kai ma) za a manta da kai a yau.”
وَكَذَٰلِكَ نَجۡزِي مَنۡ أَسۡرَفَ وَلَمۡ يُؤۡمِنۢ بِـَٔايَٰتِ رَبِّهِۦۚ وَلَعَذَابُ ٱلۡأٓخِرَةِ أَشَدُّ وَأَبۡقَىٰٓ
Kamar haka Muke saka wa (duk) wanda ya yi varna kuma bai yi imani da ayoyin Ubangijinsa ba. Kuma azabar lahira tabbas ta fi tsanani ta kuma fi dawwama
أَفَلَمۡ يَهۡدِ لَهُمۡ كَمۡ أَهۡلَكۡنَا قَبۡلَهُم مِّنَ ٱلۡقُرُونِ يَمۡشُونَ فِي مَسَٰكِنِهِمۡۚ إِنَّ فِي ذَٰلِكَ لَأٓيَٰتٖ لِّأُوْلِي ٱلنُّهَىٰ
Yanzu (mutanen Makka) ba su gane cewa al’ummu nawa muka hallaka a gabaninsu ba waxanda suna wucewa ta gidajensu? Lalle a game da wannan akwai ayoyi ga ma’abota hankali
وَلَوۡلَا كَلِمَةٞ سَبَقَتۡ مِن رَّبِّكَ لَكَانَ لِزَامٗا وَأَجَلٞ مُّسَمّٗى
Ba don kuwa wata kalma da ta rigaya daga Ubangijinka ba[1], da kuma wani wa’adi qayyadajje[2], to da (azaba) ta zama dole (a kansu tun a duniya)
1- Watau alqawari na cewa ba zai hallakar da kowa ba har sai ya tsayar masa da hujja.
2- Watau ajali na rayuwa da ya riga ya qayyade wa kowa a duniya.
فَٱصۡبِرۡ عَلَىٰ مَا يَقُولُونَ وَسَبِّحۡ بِحَمۡدِ رَبِّكَ قَبۡلَ طُلُوعِ ٱلشَّمۡسِ وَقَبۡلَ غُرُوبِهَاۖ وَمِنۡ ءَانَآيِٕ ٱلَّيۡلِ فَسَبِّحۡ وَأَطۡرَافَ ٱلنَّهَارِ لَعَلَّكَ تَرۡضَىٰ
Sai ka yi haquri a kan abin da suke faxa, kuma ka yi tasbihi da godiyar Ubangijinka kafin hudowar rana, da kuma gabanin faxuwarta; a (wasu) lokatai na dare kuma ka yi tasbihi, da kuma gefukan wuni don (a saka maka da abin da) za ka yarda
وَلَا تَمُدَّنَّ عَيۡنَيۡكَ إِلَىٰ مَا مَتَّعۡنَا بِهِۦٓ أَزۡوَٰجٗا مِّنۡهُمۡ زَهۡرَةَ ٱلۡحَيَوٰةِ ٱلدُّنۡيَا لِنَفۡتِنَهُمۡ فِيهِۚ وَرِزۡقُ رَبِّكَ خَيۡرٞ وَأَبۡقَىٰ
Kada kuma ka zura idanuwanka a kan dangogin daxin da Muka jiyar da wasu daga cikinsu, na adon rayuwar duniya ne don Mu jarrabe su da shi. Arzikin Ubangijinka kuwa (shi) ya fi alheri ya kuma fi dawwama
وَأۡمُرۡ أَهۡلَكَ بِٱلصَّلَوٰةِ وَٱصۡطَبِرۡ عَلَيۡهَاۖ لَا نَسۡـَٔلُكَ رِزۡقٗاۖ نَّحۡنُ نَرۡزُقُكَۗ وَٱلۡعَٰقِبَةُ لِلتَّقۡوَىٰ
Ka kuma umarci iyalinka da (tsai da) salla, kuma ka dawwama a kanta; ba Ma neman ka arzuta (kanka da iyalinka); Mu ne za Mu arzuta ka. Kyakkyawan qarshe kuwa yana ga masu taqawa
وَقَالُواْ لَوۡلَا يَأۡتِينَا بِـَٔايَةٖ مِّن رَّبِّهِۦٓۚ أَوَلَمۡ تَأۡتِهِم بَيِّنَةُ مَا فِي ٱلصُّحُفِ ٱلۡأُولَىٰ
Suka kuma ce: “Me ya sa bai zo mana da wata aya daga Ubangijinsa ba?” Yanzu hujjar abin da yake cikin littattafan farko ba ta zo musu ba (wato Alqur’ani)?
وَلَوۡ أَنَّآ أَهۡلَكۡنَٰهُم بِعَذَابٖ مِّن قَبۡلِهِۦ لَقَالُواْ رَبَّنَا لَوۡلَآ أَرۡسَلۡتَ إِلَيۡنَا رَسُولٗا فَنَتَّبِعَ ءَايَٰتِكَ مِن قَبۡلِ أَن نَّذِلَّ وَنَخۡزَىٰ
In da a ce Mun hallaka su ne da azaba tun gabaninsa (wato Annabi Muhammadu), to da sun ce: “Ubangijinmu, me ya sa ba Ka aiko mana da wani manzo ba sai mu bi ayoyinka tun kafin mu qasqanta mu kuma wulaqanta?”
قُلۡ كُلّٞ مُّتَرَبِّصٞ فَتَرَبَّصُواْۖ فَسَتَعۡلَمُونَ مَنۡ أَصۡحَٰبُ ٱلصِّرَٰطِ ٱلسَّوِيِّ وَمَنِ ٱهۡتَدَىٰ
Ka ce (da su): “Kowanne (ni da ku) mai sauraro ne, sai ku saurara; to ba da daxewa ba za ku san su wane ne ma’abota hanya madaidaiciya, kuma su wane ne suke kan shiriya.”