وَأَنَّا ظَنَنَّآ أَن لَّن تَقُولَ ٱلۡإِنسُ وَٱلۡجِنُّ عَلَى ٱللَّهِ كَذِبٗا
“Lalle kuma mun yi tsammanin mutum da aljan ba za su tava faxar qarya game da Allah ba
وَأَنَّهُۥ كَانَ رِجَالٞ مِّنَ ٱلۡإِنسِ يَعُوذُونَ بِرِجَالٖ مِّنَ ٱلۡجِنِّ فَزَادُوهُمۡ رَهَقٗا
“Kuma lalle yadda lamarin yake, wasu mazaje daga mutane sun kasance suna neman tsari daga wasu mazaje na aljannu, saboda haka suka qara musu girman kai
وَأَنَّهُمۡ ظَنُّواْ كَمَا ظَنَنتُمۡ أَن لَّن يَبۡعَثَ ٱللَّهُ أَحَدٗا
“Kuma lalle su sun yi tsammanin-kamar yadda kuka yi tsammani-cewar Allah ba zai tashi kowa ba har abada
وَأَنَّا لَمَسۡنَا ٱلسَّمَآءَ فَوَجَدۡنَٰهَا مُلِئَتۡ حَرَسٗا شَدِيدٗا وَشُهُبٗا
“Kuma lalle mu mun nemi hawa sama, sai muka same ta an cika ta da matsanancin tsaro da taurari (masu jifa da garwashi)
وَأَنَّا كُنَّا نَقۡعُدُ مِنۡهَا مَقَٰعِدَ لِلسَّمۡعِۖ فَمَن يَسۡتَمِعِ ٱلۡأٓنَ يَجِدۡ لَهُۥ شِهَابٗا رَّصَدٗا
“Lalle kuma mun zamanto a da muna hawa wasu wurare nata don yin sauraro[1]; to duk wanda ya nemi yin sauraro a yanzu zai sama wa kansa wani tauraro wanda aka tanada (don jifan sa)
1- Watau a da can lokacin jahiliyya aljannu sun saba hawa sama domin sato bayanan sirri daga tattaunawar mala’iku, suna isar da su ga bokaye a qasa.
وَأَنَّا لَا نَدۡرِيٓ أَشَرٌّ أُرِيدَ بِمَن فِي ٱلۡأَرۡضِ أَمۡ أَرَادَ بِهِمۡ رَبُّهُمۡ رَشَدٗا
“Kuma lalle mu ba mu sani ba, shin wani sharri ake nufi da waxanda ke qasa, ko kuwa Ubangijinsu Yana nufin su da shiriya ne?
وَأَنَّا مِنَّا ٱلصَّـٰلِحُونَ وَمِنَّا دُونَ ذَٰلِكَۖ كُنَّا طَرَآئِقَ قِدَدٗا
“Lalle daga cikinmu akwai salihai, daga cikinmu kuma akwai waxanda ba haka suke ba; mun zamanto hanyoyi daban-daban
وَأَنَّا ظَنَنَّآ أَن لَّن نُّعۡجِزَ ٱللَّهَ فِي ٱلۡأَرۡضِ وَلَن نُّعۡجِزَهُۥ هَرَبٗا
“Kuma lalle mu mun tabbatar cewa ba za mu gagari Allah ba a bayan qasa, ba kuma za mu gagare Shi ba a guje
وَأَنَّا لَمَّا سَمِعۡنَا ٱلۡهُدَىٰٓ ءَامَنَّا بِهِۦۖ فَمَن يُؤۡمِنۢ بِرَبِّهِۦ فَلَا يَخَافُ بَخۡسٗا وَلَا رَهَقٗا
“Lalle kuma mu lokacin da muka ji Alqur’ani, sai muka yi imani da shi, to duk wanda zai yi imani da Ubangijinsa, to ba zai ji tsoron qwara ko zalunci ba[1]
1- Watau ba za a tauye masa ladansa ba, kuma ba za a qara masa wani laifin da bai aikata ba.
وَأَنَّا مِنَّا ٱلۡمُسۡلِمُونَ وَمِنَّا ٱلۡقَٰسِطُونَۖ فَمَنۡ أَسۡلَمَ فَأُوْلَـٰٓئِكَ تَحَرَّوۡاْ رَشَدٗا
“Kuma lalle mu a cikinmu akwai Musulmi, a cikinmu kuma akwai karkatattu; saboda haka duk wanda ya musulunta, to waxannan sun nufi hanyar shiriya
وَأَمَّا ٱلۡقَٰسِطُونَ فَكَانُواْ لِجَهَنَّمَ حَطَبٗا
“Amma kuma karkatattu, to sun kasance makamashi ne ga (wutar) Jahannama.”
وَأَلَّوِ ٱسۡتَقَٰمُواْ عَلَى ٱلطَّرِيقَةِ لَأَسۡقَيۡنَٰهُم مَّآءً غَدَقٗا
Da kuwa (mutan Makka) sun daidaita a kan (Musulunci), to lalle da Mun shayar da su ruwa mai yawa
لِّنَفۡتِنَهُمۡ فِيهِۚ وَمَن يُعۡرِضۡ عَن ذِكۡرِ رَبِّهِۦ يَسۡلُكۡهُ عَذَابٗا صَعَدٗا
Don Mu jarrabe su game da shi. Duk kuwa wanda ya kau da kai daga ambaton Ubangijinsa[1] to zai saka shi cikin azaba mai wahala
1- Watau ya bijire wa Alqur’ani da wa’azuzzukan da ke cikinsa.
وَأَنَّ ٱلۡمَسَٰجِدَ لِلَّهِ فَلَا تَدۡعُواْ مَعَ ٱللَّهِ أَحَدٗا
Kuma lalle masallatai na Allah ne, saboda haka kada ku bauta wa wani tare da Allah
وَأَنَّهُۥ لَمَّا قَامَ عَبۡدُ ٱللَّهِ يَدۡعُوهُ كَادُواْ يَكُونُونَ عَلَيۡهِ لِبَدٗا
Kuma lalle yadda lamarin yake, yayin da Bawan Allah (Annabi Muhammadu) ya tashi yana bauta masa, sai (aljannu) suka kusa su zamo wasu kan wasu don cincirindo a kansa[1]
1- Watau a Baxnu Nakhla lokacin da yake tsaye yana karatun Alqur’ani.
قُلۡ إِنَّمَآ أَدۡعُواْ رَبِّي وَلَآ أُشۡرِكُ بِهِۦٓ أَحَدٗا
Ka ce: “Lalle ina bauta wa Ubangijina ne kawai, ba kuwa na tara wani da Shi.”
قُلۡ إِنِّي لَآ أَمۡلِكُ لَكُمۡ ضَرّٗا وَلَا رَشَدٗا
Kuma ka ce: “Lalle ni ban mallaki kare muku wata cuta ko janyo muku wani alhairi ba.”
قُلۡ إِنِّي لَن يُجِيرَنِي مِنَ ٱللَّهِ أَحَدٞ وَلَنۡ أَجِدَ مِن دُونِهِۦ مُلۡتَحَدًا
Ka ce: “Lalle ni ba wani mai kare ni daga (azabar) Allah, kuma ba zan tava samun wata mafaka in ba tasa ba
إِلَّا بَلَٰغٗا مِّنَ ٱللَّهِ وَرِسَٰلَٰتِهِۦۚ وَمَن يَعۡصِ ٱللَّهَ وَرَسُولَهُۥ فَإِنَّ لَهُۥ نَارَ جَهَنَّمَ خَٰلِدِينَ فِيهَآ أَبَدًا
“Sai dai isar da aike daga Allah da kuma saqwanninsa. Duk kuwa waxanda suka sava wa Allah da Manzonsa, to lalle suna da wutar Jahannama, suna madawwama a cikinta har abada.”
حَتَّىٰٓ إِذَا رَأَوۡاْ مَا يُوعَدُونَ فَسَيَعۡلَمُونَ مَنۡ أَضۡعَفُ نَاصِرٗا وَأَقَلُّ عَدَدٗا
Har yayin da (kafirai) suka ga abin da ake yi musu alqawari da shi, to ba da daxewa ba za su san wa ya fi raunanan mataimaka da kuma qanqantar jama’a
قُلۡ إِنۡ أَدۡرِيٓ أَقَرِيبٞ مَّا تُوعَدُونَ أَمۡ يَجۡعَلُ لَهُۥ رَبِّيٓ أَمَدًا
Ka ce: “Ni ban sani ba, shin kusa yake abin da ake yi muku alqawarinsa ko kuwa Ubangijina zai sanya masa zamani mai tsawo?”
عَٰلِمُ ٱلۡغَيۡبِ فَلَا يُظۡهِرُ عَلَىٰ غَيۡبِهِۦٓ أَحَدًا
“(Shi ne) Masanin gaibu, sannan ba Ya bayyana gaibunsa ga wani
إِلَّا مَنِ ٱرۡتَضَىٰ مِن رَّسُولٖ فَإِنَّهُۥ يَسۡلُكُ مِنۢ بَيۡنِ يَدَيۡهِ وَمِنۡ خَلۡفِهِۦ رَصَدٗا
“Sai manzo da ya yarda da shi, shi kuma lalle Yakan sanya masa tsaro ta gabansa da ta bayansa[1]
1- Watau ta hanyar sa masa mala’iku masu tsaron sa domin kada shaixanu su samu kusantar sa.
لِّيَعۡلَمَ أَن قَدۡ أَبۡلَغُواْ رِسَٰلَٰتِ رَبِّهِمۡ وَأَحَاطَ بِمَا لَدَيۡهِمۡ وَأَحۡصَىٰ كُلَّ شَيۡءٍ عَدَدَۢا
“Don Ya bayyanar da cewa, haqiqa sun isar da saqwannin Ubangijinsu, Ya kuma kewaye da (sanin) abin da yake tare da su, Ya kuma qididdige adadin kowane abu.”
يَـٰٓأَيُّهَا ٱلۡمُزَّمِّلُ
Ya kai wannan mai lulluva[1]!
1- Shi ne Manzon Allah () bayan an saukar masa da wahayin farko a kogon Hira, ya dawo gida a tsorace ya lulluva da tufafinsa.
قُمِ ٱلَّيۡلَ إِلَّا قَلِيلٗا
Ka yi tsaiwar dare sai xan kaxan (daga cikinsa)
نِّصۡفَهُۥٓ أَوِ ٱنقُصۡ مِنۡهُ قَلِيلًا
Rabinsa ko kuma ka rage kaxan daga gare shi
أَوۡ زِدۡ عَلَيۡهِ وَرَتِّلِ ٱلۡقُرۡءَانَ تَرۡتِيلًا
Ko ka qara a kansa, ka kuma karanta Alqur’ani daki-daki
إِنَّا سَنُلۡقِي عَلَيۡكَ قَوۡلٗا ثَقِيلًا
Lalle Mu da sannu za Mu saukar maka da zance mai nauyi[1]
1- Watau Alqur’ani da zai yiwo masa wahayinsa.
إِنَّ نَاشِئَةَ ٱلَّيۡلِ هِيَ أَشَدُّ وَطۡـٔٗا وَأَقۡوَمُ قِيلًا
Lalle tsayuwar dare ita ta fi tsananin dacewa (game da nutsuwa), ta kuma fi daidaitar magana[1]
1- Watau sallar dare ta fi dacewa da nutsuwar zuciya da taimakawa wajen fahimtar zance daidai.