وَخَلَقَ ٱلۡجَآنَّ مِن مَّارِجٖ مِّن نَّارٖ
Ya kuma halicci aljani daga harshen wuta
Partager :
فَبِأَيِّ ءَالَآءِ رَبِّكُمَا تُكَذِّبَانِ
Da waxanne ni’imomin Ubangijinku ne (ku mutane da aljannu) kuke qaryatawa?
رَبُّ ٱلۡمَشۡرِقَيۡنِ وَرَبُّ ٱلۡمَغۡرِبَيۡنِ
Ubangijin mahudar rana biyu da mafaxarta biyu[1]
1- Watau a lokacin sanyi da kuma lokacin zafi.
مَرَجَ ٱلۡبَحۡرَيۡنِ يَلۡتَقِيَانِ
Ya gudanar da koguna guda biyu suna haxuwa (da juna)
بَيۡنَهُمَا بَرۡزَخٞ لَّا يَبۡغِيَانِ
A tsakaninsu (kuma) akwai wani shamaki da ya hana su shiga juna
يَخۡرُجُ مِنۡهُمَا ٱللُّؤۡلُؤُ وَٱلۡمَرۡجَانُ
Lu’ulu’u da murjani suna fita daga cikinsu
وَلَهُ ٱلۡجَوَارِ ٱلۡمُنشَـَٔاتُ فِي ٱلۡبَحۡرِ كَٱلۡأَعۡلَٰمِ
Jiragen ruwa kuma da aka yi su suna gudu a cikin kogi kamar manya-manyan duwatsu nasa ne
كُلُّ مَنۡ عَلَيۡهَا فَانٖ
Dukkan wanda yake kanta (qasar) qararre ne
وَيَبۡقَىٰ وَجۡهُ رَبِّكَ ذُو ٱلۡجَلَٰلِ وَٱلۡإِكۡرَامِ
Fuskar Ubangijinka kuwa Ma’abocin girma da karamci ne kawai take wanzuwa
يَسۡـَٔلُهُۥ مَن فِي ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِۚ كُلَّ يَوۡمٍ هُوَ فِي شَأۡنٖ
Duk wanda yake cikin sammai da qasa yana roqon Sa. Kowane lokacin Shi a cikin wani sha’ani yake
سَنَفۡرُغُ لَكُمۡ أَيُّهَ ٱلثَّقَلَانِ
Ba da daxewa ba za Mu dawo kanku ya ku mutane da aljannu
يَٰمَعۡشَرَ ٱلۡجِنِّ وَٱلۡإِنسِ إِنِ ٱسۡتَطَعۡتُمۡ أَن تَنفُذُواْ مِنۡ أَقۡطَارِ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِ فَٱنفُذُواْۚ لَا تَنفُذُونَ إِلَّا بِسُلۡطَٰنٖ
Ya ku jama’ar aljannu da mutane, idan kun sami ikon ficewa daga cikin sassan sammai da qasa to ku fice. Ba za ku fice ba sai da samun wani qarfi[1]
1- Watau ba za su kuvuce wa Allah ba sai idan suna da wata hujja ko wani qarfi, wanda kuma su ma sun tabbata ba su da shi.
يُرۡسَلُ عَلَيۡكُمَا شُوَاظٞ مِّن نَّارٖ وَنُحَاسٞ فَلَا تَنتَصِرَانِ
Za a aiko muku (ku mutane da aljannu) da balbalin wuta da kuma hayaqi, saboda haka ba za ku iya kare kanku (daga gare shi) ba
فَإِذَا ٱنشَقَّتِ ٱلسَّمَآءُ فَكَانَتۡ وَرۡدَةٗ كَٱلدِّهَانِ
Sannan idan sama ta kekkece ta zama jajir kamar jar fata[1]
1- Watau saboda an gusar da hasken taurarin cikinta gaba xaya.
فَيَوۡمَئِذٖ لَّا يُسۡـَٔلُ عَن ذَنۢبِهِۦٓ إِنسٞ وَلَا جَآنّٞ
Sannan a wannan rana ba a tambayar mutum ko aljan laifinsa
يُعۡرَفُ ٱلۡمُجۡرِمُونَ بِسِيمَٰهُمۡ فَيُؤۡخَذُ بِٱلنَّوَٰصِي وَٱلۡأَقۡدَامِ
Ana gane manyan masu laifi da alamominsu[1], sai a kama su ta makwarkwaxa da dugadugai
1- Saboda fuskokinsu za su yi baqi qirin, idanuwansu kuma za su yi jawur.
هَٰذِهِۦ جَهَنَّمُ ٱلَّتِي يُكَذِّبُ بِهَا ٱلۡمُجۡرِمُونَ
(Za a ce da su): Wannan ita ce Jahannamar da manyan masu laifi suke qaryatawa
يَطُوفُونَ بَيۡنَهَا وَبَيۡنَ حَمِيمٍ ءَانٖ
Za su riqa kai-kawo tsakaninta da tafasasshen ruwa mai tsananin zafi