Sourate: Suratul Hajji

Verset : 39

أُذِنَ لِلَّذِينَ يُقَٰتَلُونَ بِأَنَّهُمۡ ظُلِمُواْۚ وَإِنَّ ٱللَّهَ عَلَىٰ نَصۡرِهِمۡ لَقَدِيرٌ

An yi izini (na yin yaqi) ga waxanda ake yaqa[1] don ko lalle an zalunce su. Lalle kuma Allah Mai iko ne bisa taimakon su


1- Watau sahabban Annabi () waxanda kafirai a lokacin suke yaqar su.


Sourate: Suratul Hajji

Verset : 40

ٱلَّذِينَ أُخۡرِجُواْ مِن دِيَٰرِهِم بِغَيۡرِ حَقٍّ إِلَّآ أَن يَقُولُواْ رَبُّنَا ٱللَّهُۗ وَلَوۡلَا دَفۡعُ ٱللَّهِ ٱلنَّاسَ بَعۡضَهُم بِبَعۡضٖ لَّهُدِّمَتۡ صَوَٰمِعُ وَبِيَعٞ وَصَلَوَٰتٞ وَمَسَٰجِدُ يُذۡكَرُ فِيهَا ٱسۡمُ ٱللَّهِ كَثِيرٗاۗ وَلَيَنصُرَنَّ ٱللَّهُ مَن يَنصُرُهُۥٓۚ إِنَّ ٱللَّهَ لَقَوِيٌّ عَزِيزٌ

(Su ne) waxanda aka fitar da su daga gidajensu ba da wani laifi ba, sai don kawai sun ce: “Allah ne Ubangijinmu”. Kuma ba don kariyar Allah ga wasu mutane ta hanyar wasu ba, to da lalle an rusa wuraren bauta (na Nasara da suka qaurace wa ‘yan’uwansu), da coci-coci da wuraren bautar Yahudawa da masallatai (na Musulmi) waxanda ake ambaton sunan Allah da yawa a cikinsu. Kuma tabbas Allah zai taimaki mai taimakon Sa. Lalle Allah Mai qarfi ne, Mabuwayi



Sourate: Suratul Hajji

Verset : 41

ٱلَّذِينَ إِن مَّكَّنَّـٰهُمۡ فِي ٱلۡأَرۡضِ أَقَامُواْ ٱلصَّلَوٰةَ وَءَاتَوُاْ ٱلزَّكَوٰةَ وَأَمَرُواْ بِٱلۡمَعۡرُوفِ وَنَهَوۡاْ عَنِ ٱلۡمُنكَرِۗ وَلِلَّهِ عَٰقِبَةُ ٱلۡأُمُورِ

(Su ne) waxanda, idan Muka kafa su a bayan qasa sai su tsai da salla su kuma ba da zakka kuma su yi umarni da aikin alheri su kuma yi hani daga mummunan aiki. Qarshen al’amura kuwa na Allah ne



Sourate: Suratul Hajji

Verset : 42

وَإِن يُكَذِّبُوكَ فَقَدۡ كَذَّبَتۡ قَبۡلَهُمۡ قَوۡمُ نُوحٖ وَعَادٞ وَثَمُودُ

Idan kuwa suka qaryata ka, to haqiqa mutanen Nuhu da Adawa da Samudawa sun qaryata (manzanni) kafin su



Sourate: Suratul Hajji

Verset : 43

وَقَوۡمُ إِبۡرَٰهِيمَ وَقَوۡمُ لُوطٖ

Da mutanen Ibrahimu da mutanen Luxu (su ma sun qaryata)



Sourate: Suratul Hajji

Verset : 44

وَأَصۡحَٰبُ مَدۡيَنَۖ وَكُذِّبَ مُوسَىٰۖ فَأَمۡلَيۡتُ لِلۡكَٰفِرِينَ ثُمَّ أَخَذۡتُهُمۡۖ فَكَيۡفَ كَانَ نَكِيرِ

Da ma mutanen Madyana (su ma sun qaryata); an kuma qaryata Musa, sai Na jinkirta wa kafurai, sannan Na kama su (da azabata); to qaqa (qarshen) kashedina (a gare su) ya kasance?



Sourate: Suratul Hajji

Verset : 45

فَكَأَيِّن مِّن قَرۡيَةٍ أَهۡلَكۡنَٰهَا وَهِيَ ظَالِمَةٞ فَهِيَ خَاوِيَةٌ عَلَىٰ عُرُوشِهَا وَبِئۡرٖ مُّعَطَّلَةٖ وَقَصۡرٖ مَّشِيدٍ

Sannan alqarya nawa muka hallaka su alhalin suna azzalumai, sai ga su suna rugurguje a kan rufinsu sun zama kufai, da kuma rijiyoyin da aka watsar da amfani da su, da manya-manyan gine-gine da aka xaukaka su?



Sourate: Suratul Hajji

Verset : 46

أَفَلَمۡ يَسِيرُواْ فِي ٱلۡأَرۡضِ فَتَكُونَ لَهُمۡ قُلُوبٞ يَعۡقِلُونَ بِهَآ أَوۡ ءَاذَانٞ يَسۡمَعُونَ بِهَاۖ فَإِنَّهَا لَا تَعۡمَى ٱلۡأَبۡصَٰرُ وَلَٰكِن تَعۡمَى ٱلۡقُلُوبُ ٱلَّتِي فِي ٱلصُّدُورِ

Yanzu ba za su yi tafiya a bayan qasa ba don su samu zukata da za su riqa tunani da su, ko kuwa kunnuwa da za su riqa ji da su? To lalle yadda lamarin yake ba idanduna ba ne suke makancewa sai dai zukatan da suke cikin qiraza su ne suke makancewa



Sourate: Suratul Hajji

Verset : 47

وَيَسۡتَعۡجِلُونَكَ بِٱلۡعَذَابِ وَلَن يُخۡلِفَ ٱللَّهُ وَعۡدَهُۥۚ وَإِنَّ يَوۡمًا عِندَ رَبِّكَ كَأَلۡفِ سَنَةٖ مِّمَّا تَعُدُّونَ

Kuma suna neman ka da gaggauto musu da azaba, Allah kuwa ba Ya sava alqawarinsa. Lalle kuma yini xaya a wurin Ubangijinka kamar shekara dubu ne daga irin waxanda kuke qirgawa



Sourate: Suratul Hajji

Verset : 48

وَكَأَيِّن مِّن قَرۡيَةٍ أَمۡلَيۡتُ لَهَا وَهِيَ ظَالِمَةٞ ثُمَّ أَخَذۡتُهَا وَإِلَيَّ ٱلۡمَصِيرُ

Kuma alqaryu nawa ne Na saurara musu, alhali kuwa suna kafirai, sannan (daga baya) Na kama su? Makoma kuma zuwa gare Ni ne



Sourate: Suratul Hajji

Verset : 49

قُلۡ يَـٰٓأَيُّهَا ٱلنَّاسُ إِنَّمَآ أَنَا۠ لَكُمۡ نَذِيرٞ مُّبِينٞ

Ka ce: “Ya ku mutane, ni dai kawai mai gargarxi ne a gare ku mai bayyana (gargaxi).”



Sourate: Suratul Hajji

Verset : 50

فَٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ وَعَمِلُواْ ٱلصَّـٰلِحَٰتِ لَهُم مَّغۡفِرَةٞ وَرِزۡقٞ كَرِيمٞ

To waxanda suka yi imani suka kuma yi aiki na gari, suna da gafara da kuma arziki mai girma



Sourate: Suratul Hajji

Verset : 51

وَٱلَّذِينَ سَعَوۡاْ فِيٓ ءَايَٰتِنَا مُعَٰجِزِينَ أُوْلَـٰٓئِكَ أَصۡحَٰبُ ٱلۡجَحِيمِ

Waxanda kuwa suka yi iya qoqarinsu game da vata ayoyinmu suna ganin za su gagare Mu, to waxannan su ne ma’abota (wutar) Jahima



Sourate: Suratul Hajji

Verset : 52

وَمَآ أَرۡسَلۡنَا مِن قَبۡلِكَ مِن رَّسُولٖ وَلَا نَبِيٍّ إِلَّآ إِذَا تَمَنَّىٰٓ أَلۡقَى ٱلشَّيۡطَٰنُ فِيٓ أُمۡنِيَّتِهِۦ فَيَنسَخُ ٱللَّهُ مَا يُلۡقِي ٱلشَّيۡطَٰنُ ثُمَّ يُحۡكِمُ ٱللَّهُ ءَايَٰتِهِۦۗ وَٱللَّهُ عَلِيمٌ حَكِيمٞ

Kuma babu wani manzo ko wani annabi[1] da Muka aiko a gabaninka face idan ya yi karatu sai Shaixan ya jefa (ruxu da wasiwasi) cikin karatunsa; sannan Allah Yakan vata abin da shi Shaixan yake jefawa, sannan Allah Ya tabbatar da ayoyinsa. Allah kuwa Masani ne Mai hikima


1- Manzo, shi ne wanda Allah () ya aika shi zuwa ga kafirai ‘yan jahiliyya. Annabi kuwa shi ne wanda ya aika shi zuwa ga mutanen da ba ‘yan jahiliyya ba, amma suna da buqatar a jaddada musu addininsu.


Sourate: Suratul Hajji

Verset : 53

لِّيَجۡعَلَ مَا يُلۡقِي ٱلشَّيۡطَٰنُ فِتۡنَةٗ لِّلَّذِينَ فِي قُلُوبِهِم مَّرَضٞ وَٱلۡقَاسِيَةِ قُلُوبُهُمۡۗ وَإِنَّ ٱلظَّـٰلِمِينَ لَفِي شِقَاقِۭ بَعِيدٖ

(Yakan yi haka ne) don Ya sanya abin da Shaixan yake jefawa ya zama fitina ga waxanda suke da cuta a cikin zukatansu, da kuma masu qeqasassun zukata. Lalle kuma azzalumai tabbas suna cikin savani mai nisa



Sourate: Suratul Hajji

Verset : 54

وَلِيَعۡلَمَ ٱلَّذِينَ أُوتُواْ ٱلۡعِلۡمَ أَنَّهُ ٱلۡحَقُّ مِن رَّبِّكَ فَيُؤۡمِنُواْ بِهِۦ فَتُخۡبِتَ لَهُۥ قُلُوبُهُمۡۗ وَإِنَّ ٱللَّهَ لَهَادِ ٱلَّذِينَ ءَامَنُوٓاْ إِلَىٰ صِرَٰطٖ مُّسۡتَقِيمٖ

Don kuma waxanda aka bai wa ilimi su san cewa shi (Alqur’ani) gaskiya ne daga Ubangijinka yake, sai su yi imani da shi sai zukatansu su nutsu da shi. Kuma lalle Allah tabbas Mai shiryar da waxanda suka yi imani ne zuwa ga tafarki madaidaici



Sourate: Suratul Hajji

Verset : 55

وَلَا يَزَالُ ٱلَّذِينَ كَفَرُواْ فِي مِرۡيَةٖ مِّنۡهُ حَتَّىٰ تَأۡتِيَهُمُ ٱلسَّاعَةُ بَغۡتَةً أَوۡ يَأۡتِيَهُمۡ عَذَابُ يَوۡمٍ عَقِيمٍ

Waxanda kuwa suka kafirce ba za su daina kokwanton sa ba (watau Alqur’ani) har sai alqiyama ta zo musu ba zato ba tsammani, ko kuma azabar rana bakarara[1] ta zo musu


1- Watau ranar da kafirai ba za su samu wata rahama ko wani alheri ba.


Sourate: Suratul Hajji

Verset : 56

ٱلۡمُلۡكُ يَوۡمَئِذٖ لِّلَّهِ يَحۡكُمُ بَيۡنَهُمۡۚ فَٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ وَعَمِلُواْ ٱلصَّـٰلِحَٰتِ فِي جَنَّـٰتِ ٱلنَّعِيمِ

Mulki a wannan ranar na Allah ne, zai yi hukunci a tsakaninsu. To waxanda suka yi imani suka kuma yi kyawawan ayyuka, suna cikin gidajen Aljanna na ni’ima



Sourate: Suratul Hajji

Verset : 57

وَٱلَّذِينَ كَفَرُواْ وَكَذَّبُواْ بِـَٔايَٰتِنَا فَأُوْلَـٰٓئِكَ لَهُمۡ عَذَابٞ مُّهِينٞ

Waxanda kuwa suka kafirta suka kuma qaryata ayoyinmu, to waxannan suna da azaba mai wulaqantawa



Sourate: Suratul Hajji

Verset : 58

وَٱلَّذِينَ هَاجَرُواْ فِي سَبِيلِ ٱللَّهِ ثُمَّ قُتِلُوٓاْ أَوۡ مَاتُواْ لَيَرۡزُقَنَّهُمُ ٱللَّهُ رِزۡقًا حَسَنٗاۚ وَإِنَّ ٱللَّهَ لَهُوَ خَيۡرُ ٱلرَّـٰزِقِينَ

Waxanda kuwa suka yi hijira saboda Allah sannan aka kashe su ko kuma suka mutu, to lalle Allah tabbas zai arzuta su da kyakkyawan arziki. Kuma lalle Allah tabbas Shi ne Fiyayyen masu arzutawa



Sourate: Suratul Hajji

Verset : 59

لَيُدۡخِلَنَّهُم مُّدۡخَلٗا يَرۡضَوۡنَهُۥۚ وَإِنَّ ٱللَّهَ لَعَلِيمٌ حَلِيمٞ

Lalle tabbas Zai shigar da su wata mashiga da za su yarda da ita. Kuma lalle Allah tabbas Masani ne, Mai hakuri



Sourate: Suratul Hajji

Verset : 60

۞ذَٰلِكَۖ وَمَنۡ عَاقَبَ بِمِثۡلِ مَا عُوقِبَ بِهِۦ ثُمَّ بُغِيَ عَلَيۡهِ لَيَنصُرَنَّهُ ٱللَّهُۚ إِنَّ ٱللَّهَ لَعَفُوٌّ غَفُورٞ

Wannan (abu da aka ambata haka yake), duk wanda ya yi uquba da irin abin da aka yi masa uquba da shi, sannan aka daxa yi masa ta’addanci, to lalle Allah tabbas zai taimake shi. Lalle Allah tabbas Mai afuwa ne, Mai gafara



Sourate: Suratul Hajji

Verset : 61

ذَٰلِكَ بِأَنَّ ٱللَّهَ يُولِجُ ٱلَّيۡلَ فِي ٱلنَّهَارِ وَيُولِجُ ٱلنَّهَارَ فِي ٱلَّيۡلِ وَأَنَّ ٱللَّهَ سَمِيعُۢ بَصِيرٞ

Wannan (taimakon kuwa zai kasance ne) saboda lalle Allah Shi Yake shigar da dare cikin rana, Yake kuma shigar da rana cikin dare, kuma lalle Allah Mai ji ne, Mai gani



Sourate: Suratul Hajji

Verset : 62

ذَٰلِكَ بِأَنَّ ٱللَّهَ هُوَ ٱلۡحَقُّ وَأَنَّ مَا يَدۡعُونَ مِن دُونِهِۦ هُوَ ٱلۡبَٰطِلُ وَأَنَّ ٱللَّهَ هُوَ ٱلۡعَلِيُّ ٱلۡكَبِيرُ

Wannan kuwa saboda lalle Allah Shi ne (abin bauta) na gaskiya, kuma lalle abin da suke bauta wa wanda ba Shi ba shi na qarya ne, kuma lalle Allah Shi ne Maxaukaki, Mai girma



Sourate: Suratul Hajji

Verset : 63

أَلَمۡ تَرَ أَنَّ ٱللَّهَ أَنزَلَ مِنَ ٱلسَّمَآءِ مَآءٗ فَتُصۡبِحُ ٱلۡأَرۡضُ مُخۡضَرَّةًۚ إِنَّ ٱللَّهَ لَطِيفٌ خَبِيرٞ

Shin ba ka ga cewa Allah ne Ya saukar da ruwa daga sama ba, sai qasa ta zama koriya shar? Lalle Allah Mai tausasawa ne, Masani



Sourate: Suratul Hajji

Verset : 64

لَّهُۥ مَا فِي ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَمَا فِي ٱلۡأَرۡضِۚ وَإِنَّ ٱللَّهَ لَهُوَ ٱلۡغَنِيُّ ٱلۡحَمِيدُ

Abin da yake cikin sammai da abin da yake cikin qasa nasa ne. Kuma lalle Allah tabbas Shi ne Mawadaci, Sha-Yabo



Sourate: Suratul Hajji

Verset : 65

أَلَمۡ تَرَ أَنَّ ٱللَّهَ سَخَّرَ لَكُم مَّا فِي ٱلۡأَرۡضِ وَٱلۡفُلۡكَ تَجۡرِي فِي ٱلۡبَحۡرِ بِأَمۡرِهِۦ وَيُمۡسِكُ ٱلسَّمَآءَ أَن تَقَعَ عَلَى ٱلۡأَرۡضِ إِلَّا بِإِذۡنِهِۦٓۚ إِنَّ ٱللَّهَ بِٱلنَّاسِ لَرَءُوفٞ رَّحِيمٞ

Shin ba ka ga cewa Allah Ya hore muku abin da yake cikin qasa, da kuma jiragen ruwa da suke gudu a cikin kogi da umarninsa, kuma Yake riqe sama don kada ta faxo a kan qasa, sai da izininsa? Lalle Allah Mai tausayi ne, Mai rahama ga mutane



Sourate: Suratul Hajji

Verset : 66

وَهُوَ ٱلَّذِيٓ أَحۡيَاكُمۡ ثُمَّ يُمِيتُكُمۡ ثُمَّ يُحۡيِيكُمۡۗ إِنَّ ٱلۡإِنسَٰنَ لَكَفُورٞ

Shi ne kuma Wanda Ya raya ku sannan zai kashe ku sannan Ya (sake) raya ku. Lalle mutum tabbas mai yawan butulci ne



Sourate: Suratul Hajji

Verset : 67

لِّكُلِّ أُمَّةٖ جَعَلۡنَا مَنسَكًا هُمۡ نَاسِكُوهُۖ فَلَا يُنَٰزِعُنَّكَ فِي ٱلۡأَمۡرِۚ وَٱدۡعُ إِلَىٰ رَبِّكَۖ إِنَّكَ لَعَلَىٰ هُدٗى مُّسۡتَقِيمٖ

Kowacce al’umma Mun sanya mata hanyar (shari’a) da za su yi aiki da ita; to lalle kada su yi jayayya da kai game da lamarin (addini). Kuma ka yi kira zuwa ga (addinin) Ubangijinka; lalle kai tabbas kana bisa shiriya madaidaiciya



Sourate: Suratul Hajji

Verset : 68

وَإِن جَٰدَلُوكَ فَقُلِ ٱللَّهُ أَعۡلَمُ بِمَا تَعۡمَلُونَ

Idan kuwa suka yi maka jayayya, sai ka ce: “Allah ne Ya fi sanin abin da kuke aikatawa.”