Sourate: Suratul A’araf

Verset : 6

فَلَنَسۡـَٔلَنَّ ٱلَّذِينَ أُرۡسِلَ إِلَيۡهِمۡ وَلَنَسۡـَٔلَنَّ ٱلۡمُرۡسَلِينَ

To lalle tabbas sai Mun tambayi waxanda aka aiko musu manzanni, kuma lalle tabbas, sai mun tambayi manzannin (su kansu)



Sourate: Suratul A’araf

Verset : 7

فَلَنَقُصَّنَّ عَلَيۡهِم بِعِلۡمٖۖ وَمَا كُنَّا غَآئِبِينَ

Kuma lalle za Mu ba su labarin (komai) da ilimi; kuma ba Mu zamanto ba ma nan ba



Sourate: Suratul A’araf

Verset : 8

وَٱلۡوَزۡنُ يَوۡمَئِذٍ ٱلۡحَقُّۚ فَمَن ثَقُلَتۡ مَوَٰزِينُهُۥ فَأُوْلَـٰٓئِكَ هُمُ ٱلۡمُفۡلِحُونَ

Awo kuma a wannan ranar gaskiya ne. Don haka duk wanda ma’aunansa suka yi nauyi, to waxannan su ne masu rabauta



Sourate: Suratul A’araf

Verset : 9

وَمَنۡ خَفَّتۡ مَوَٰزِينُهُۥ فَأُوْلَـٰٓئِكَ ٱلَّذِينَ خَسِرُوٓاْ أَنفُسَهُم بِمَا كَانُواْ بِـَٔايَٰتِنَا يَظۡلِمُونَ

Wanda kuwa ma’aunansa suka yi sakayau, to waxannan su ne waxanda suka yi hasarar kawunansu, saboda abin da suka kasance suna yi na zalunci da ayoyinmu



Sourate: Suratul A’araf

Verset : 10

وَلَقَدۡ مَكَّنَّـٰكُمۡ فِي ٱلۡأَرۡضِ وَجَعَلۡنَا لَكُمۡ فِيهَا مَعَٰيِشَۗ قَلِيلٗا مَّا تَشۡكُرُونَ

Kuma lalle haqiqa Mun kafa ku a bayan qasa, kuma Muka sanya muku wuraren rayuwa a cikinta. Kaxan ne qwarai kuke godiya



Sourate: Suratul A’araf

Verset : 11

وَلَقَدۡ خَلَقۡنَٰكُمۡ ثُمَّ صَوَّرۡنَٰكُمۡ ثُمَّ قُلۡنَا لِلۡمَلَـٰٓئِكَةِ ٱسۡجُدُواْ لِأٓدَمَ فَسَجَدُوٓاْ إِلَّآ إِبۡلِيسَ لَمۡ يَكُن مِّنَ ٱلسَّـٰجِدِينَ

Kuma lalle haqiqa Mun halicce ku, sannan kuma Muka suranta ku; sannan Muka ce wa mala’iku: “Ku yi sujjada ga Adamu,” sai suka yi sujjada, sai Iblis ne kaxai bai kasance cikin masu sujjada ba



Sourate: Suratul A’araf

Verset : 12

قَالَ مَا مَنَعَكَ أَلَّا تَسۡجُدَ إِذۡ أَمَرۡتُكَۖ قَالَ أَنَا۠ خَيۡرٞ مِّنۡهُ خَلَقۡتَنِي مِن نَّارٖ وَخَلَقۡتَهُۥ مِن طِينٖ

(Allah) Ya ce: “Me ya hana ka yin sujada lokacin da Na umarce ka?” Sai ya ce: “Ai ni na fi shi alheri; Ka halicce ni da wuta, shi kuwa Ka halicce shi da tavo.”



Sourate: Suratul A’araf

Verset : 13

قَالَ فَٱهۡبِطۡ مِنۡهَا فَمَا يَكُونُ لَكَ أَن تَتَكَبَّرَ فِيهَا فَٱخۡرُجۡ إِنَّكَ مِنَ ٱلصَّـٰغِرِينَ

Sai Ya ce: “To ka sauka daga cikinta, bai dace gare ka ka yi girman kai a cikinta ba, don haka sai ka fita, lalle kai kana cikin qasqantattu.”



Sourate: Suratul A’araf

Verset : 14

قَالَ أَنظِرۡنِيٓ إِلَىٰ يَوۡمِ يُبۡعَثُونَ

Sai ya ce: “Ka yi min jinkiri zuwa ranar da za a tashe su (mutane).”



Sourate: Suratul A’araf

Verset : 15

قَالَ إِنَّكَ مِنَ ٱلۡمُنظَرِينَ

Sai Ya ce: “Lalle kai kana cikin waxanda za a yi wa jinkiri.”



Sourate: Suratul A’araf

Verset : 16

قَالَ فَبِمَآ أَغۡوَيۡتَنِي لَأَقۡعُدَنَّ لَهُمۡ صِرَٰطَكَ ٱلۡمُسۡتَقِيمَ

Ya ce: “Saboda vatar da ni da Ka yi, lalle sai na zaune musu tafarkinka madaidaici



Sourate: Suratul A’araf

Verset : 17

ثُمَّ لَأٓتِيَنَّهُم مِّنۢ بَيۡنِ أَيۡدِيهِمۡ وَمِنۡ خَلۡفِهِمۡ وَعَنۡ أَيۡمَٰنِهِمۡ وَعَن شَمَآئِلِهِمۡۖ وَلَا تَجِدُ أَكۡثَرَهُمۡ شَٰكِرِينَ

“Sannan lalle zan zo musu ta gabansu da kuma ta bayansu da kuma ta damansu, da kuma ta hagunsu; kuma ba za Ka samu yawancinsu masu godiya ba.”



Sourate: Suratul A’araf

Verset : 18

قَالَ ٱخۡرُجۡ مِنۡهَا مَذۡءُومٗا مَّدۡحُورٗاۖ لَّمَن تَبِعَكَ مِنۡهُمۡ لَأَمۡلَأَنَّ جَهَنَّمَ مِنكُمۡ أَجۡمَعِينَ

Ya ce: “Ka fita daga cikinta kana abin aibatawa, korarre (daga rahama); Na rantse duk wanda ya bi ka daga cikinsu, lalle zan cika Jahannama da ku gaba xaya.”



Sourate: Suratul A’araf

Verset : 19

وَيَـٰٓـَٔادَمُ ٱسۡكُنۡ أَنتَ وَزَوۡجُكَ ٱلۡجَنَّةَ فَكُلَا مِنۡ حَيۡثُ شِئۡتُمَا وَلَا تَقۡرَبَا هَٰذِهِ ٱلشَّجَرَةَ فَتَكُونَا مِنَ ٱلظَّـٰلِمِينَ

“Kuma ya kai Adam, ka zauna cikin Aljanna, da kai da matarka, kuma ku ci duk abin da kuka ga dama, amma kada ku kusanci wannan bishiyar, sai ku kasance cikin azzalumai.”



Sourate: Suratul A’araf

Verset : 20

فَوَسۡوَسَ لَهُمَا ٱلشَّيۡطَٰنُ لِيُبۡدِيَ لَهُمَا مَا وُۥرِيَ عَنۡهُمَا مِن سَوۡءَٰتِهِمَا وَقَالَ مَا نَهَىٰكُمَا رَبُّكُمَا عَنۡ هَٰذِهِ ٱلشَّجَرَةِ إِلَّآ أَن تَكُونَا مَلَكَيۡنِ أَوۡ تَكُونَا مِنَ ٱلۡخَٰلِدِينَ

Sai Shaixan ya yi musu waswasi, domin ya bayyana musu abin da aka voye musu na tsiraicinsu, kuma ya ce: “Ba abin da ya sa Ubangijinku Ya hane ku daga wannan bishiyar, sai don kawai kada ku zama mala’iku ko kuma ku zama daga cikin dawwamammu.”



Sourate: Suratul A’araf

Verset : 21

وَقَاسَمَهُمَآ إِنِّي لَكُمَا لَمِنَ ٱلنَّـٰصِحِينَ

Kuma ya yi musu rantsuwa cewa: “Lalle ni mai yi muku nasiha ne.”



Sourate: Suratul A’araf

Verset : 22

فَدَلَّىٰهُمَا بِغُرُورٖۚ فَلَمَّا ذَاقَا ٱلشَّجَرَةَ بَدَتۡ لَهُمَا سَوۡءَٰتُهُمَا وَطَفِقَا يَخۡصِفَانِ عَلَيۡهِمَا مِن وَرَقِ ٱلۡجَنَّةِۖ وَنَادَىٰهُمَا رَبُّهُمَآ أَلَمۡ أَنۡهَكُمَا عَن تِلۡكُمَا ٱلشَّجَرَةِ وَأَقُل لَّكُمَآ إِنَّ ٱلشَّيۡطَٰنَ لَكُمَا عَدُوّٞ مُّبِينٞ

Sai ya yaudare su da ruxi. Don haka yayin da suka xanxani wannan bishiyar, sai tsiraicinsu ya bayyana a gare su, sai suka fara lulluva da ganyayen Aljanna; sai Ubangijinsu Ya kira su: “Yanzu ban hana ku cin wannan bishiyar ba, ban kuma ce da ku ba lalle Shaixan maqiyi ne a gare ku mabayyani?”



Sourate: Suratul A’araf

Verset : 23

قَالَا رَبَّنَا ظَلَمۡنَآ أَنفُسَنَا وَإِن لَّمۡ تَغۡفِرۡ لَنَا وَتَرۡحَمۡنَا لَنَكُونَنَّ مِنَ ٱلۡخَٰسِرِينَ

Sai suka ce: “Ya Ubangijinmu, lalle kam mun zalunci kawunanmu, kuma idan har ba Ka yi mana gafara ba, kuma ba Ka ji qan mu ba, to lalle fa za mu kasance cikin hasararru.”



Sourate: Suratul A’araf

Verset : 24

قَالَ ٱهۡبِطُواْ بَعۡضُكُمۡ لِبَعۡضٍ عَدُوّٞۖ وَلَكُمۡ فِي ٱلۡأَرۡضِ مُسۡتَقَرّٞ وَمَتَٰعٌ إِلَىٰ حِينٖ

Sai Ya ce: “Ku sauka, sashinku zai zama abokin adawa ga sashi; kuma kuna da wurin zama a qasa da abin jin daxi zuwa xan wani lokaci.”



Sourate: Suratul A’araf

Verset : 25

قَالَ فِيهَا تَحۡيَوۡنَ وَفِيهَا تَمُوتُونَ وَمِنۡهَا تُخۡرَجُونَ

Ya ce: “A cikinta za ku rayu, kuma a cikinta za ku mutu, kuma daga cikinta za a fito da ku.”



Sourate: Suratul A’araf

Verset : 26

يَٰبَنِيٓ ءَادَمَ قَدۡ أَنزَلۡنَا عَلَيۡكُمۡ لِبَاسٗا يُوَٰرِي سَوۡءَٰتِكُمۡ وَرِيشٗاۖ وَلِبَاسُ ٱلتَّقۡوَىٰ ذَٰلِكَ خَيۡرٞۚ ذَٰلِكَ مِنۡ ءَايَٰتِ ٱللَّهِ لَعَلَّهُمۡ يَذَّكَّرُونَ

Ya ku ‘yan’adam, haqiqa Mun saukar muku da tufafi wanda zai suturce muku tsiraicinku, da kayan ado; tufafi na taqawa kuwa wannan shi ya fi alheri. Wannan yana daga cikin ayoyin Allah, ko sa yi tuntuntuni



Sourate: Suratul A’araf

Verset : 27

يَٰبَنِيٓ ءَادَمَ لَا يَفۡتِنَنَّكُمُ ٱلشَّيۡطَٰنُ كَمَآ أَخۡرَجَ أَبَوَيۡكُم مِّنَ ٱلۡجَنَّةِ يَنزِعُ عَنۡهُمَا لِبَاسَهُمَا لِيُرِيَهُمَا سَوۡءَٰتِهِمَآۚ إِنَّهُۥ يَرَىٰكُمۡ هُوَ وَقَبِيلُهُۥ مِنۡ حَيۡثُ لَا تَرَوۡنَهُمۡۗ إِنَّا جَعَلۡنَا ٱلشَّيَٰطِينَ أَوۡلِيَآءَ لِلَّذِينَ لَا يُؤۡمِنُونَ

Ya ku ‘yan’adam, kada Shaixan ya fitine ku kamar yadda ya fitar da iyayenku daga cikin Aljanna, yana mai cire musu tufafinsu don ya nuna musu tsiraicin junansu. Lalle shi yana ganin ku, shi da jama’arsa ta inda ku ba kwa ganin su. Lalle Mu Mun sanya shaixanu su zamo masoya ga waxanda ba sa yin imani



Sourate: Suratul A’araf

Verset : 28

وَإِذَا فَعَلُواْ فَٰحِشَةٗ قَالُواْ وَجَدۡنَا عَلَيۡهَآ ءَابَآءَنَا وَٱللَّهُ أَمَرَنَا بِهَاۗ قُلۡ إِنَّ ٱللَّهَ لَا يَأۡمُرُ بِٱلۡفَحۡشَآءِۖ أَتَقُولُونَ عَلَى ٱللَّهِ مَا لَا تَعۡلَمُونَ

Idan kuma sun aikata wani mummunan aiki sai su ce: “Mun sami iyayenmu ne a kansa, kuma Allah ne Ya umarce mu da shi.” Ka ce: “Lalle Allah ba Ya umarni da mummunan aiki; yanzu kwa riqa faxin abin da ba ku sani ba kuna jingina wa Allah?”



Sourate: Suratul A’araf

Verset : 29

قُلۡ أَمَرَ رَبِّي بِٱلۡقِسۡطِۖ وَأَقِيمُواْ وُجُوهَكُمۡ عِندَ كُلِّ مَسۡجِدٖ وَٱدۡعُوهُ مُخۡلِصِينَ لَهُ ٱلدِّينَۚ كَمَا بَدَأَكُمۡ تَعُودُونَ

Ka ce: “Ubangijina Ya yi umarni da adalci; kuma ku tsai da fuskokinku (don Allah) a kowace salla, ku kuma roqe Shi kuna masu tsantsanta addini gare Shi. Kamar yadda Ya fari halittarku, haka za ku koma (wurinsa)



Sourate: Suratul A’araf

Verset : 30

فَرِيقًا هَدَىٰ وَفَرِيقًا حَقَّ عَلَيۡهِمُ ٱلضَّلَٰلَةُۚ إِنَّهُمُ ٱتَّخَذُواْ ٱلشَّيَٰطِينَ أَوۡلِيَآءَ مِن دُونِ ٱللَّهِ وَيَحۡسَبُونَ أَنَّهُم مُّهۡتَدُونَ

Wani sashi Ya shirye su, wani sashin kuma vata ya tabbata a kansu. Lalle su sun mayar da shaixanu masoya ba Allah ba, suna kuma tsammanin cewa lalle su shiryayyu ne



Sourate: Suratul A’araf

Verset : 31

۞يَٰبَنِيٓ ءَادَمَ خُذُواْ زِينَتَكُمۡ عِندَ كُلِّ مَسۡجِدٖ وَكُلُواْ وَٱشۡرَبُواْ وَلَا تُسۡرِفُوٓاْۚ إِنَّهُۥ لَا يُحِبُّ ٱلۡمُسۡرِفِينَ

Ya ku ‘yan’adam, ku yi adonku a wurin kowane masallaci[1], ku ci, kuma ku sha, amma kada ku yi almubazzaranci. Lalle Shi (Allah) ba ya son masu almubazzaranci


1- Wannan ayar ta sauka ne game da mushirikai masu yin xawafi tsirara, suna cewa, wai bai dace su bauta wa Allah da tufafin da suka yi savo da su ba.


Sourate: Suratul A’araf

Verset : 32

قُلۡ مَنۡ حَرَّمَ زِينَةَ ٱللَّهِ ٱلَّتِيٓ أَخۡرَجَ لِعِبَادِهِۦ وَٱلطَّيِّبَٰتِ مِنَ ٱلرِّزۡقِۚ قُلۡ هِيَ لِلَّذِينَ ءَامَنُواْ فِي ٱلۡحَيَوٰةِ ٱلدُّنۡيَا خَالِصَةٗ يَوۡمَ ٱلۡقِيَٰمَةِۗ كَذَٰلِكَ نُفَصِّلُ ٱلۡأٓيَٰتِ لِقَوۡمٖ يَعۡلَمُونَ

Ka ce: “Wane ne ya haramta kayan ado na Allah waxanda (Allah) Ya fitar domin bayinsa da kuma daxaxan abubuwa na arziki?” Ka ce: “Waxannan abubuwa na waxanda suka yi imani ne a nan duniya, kuma nasu ne a kevance a ranar lahira.” Kamar haka ne Muke rarrabe ayoyi ga mutanen da suke da sani



Sourate: Suratul A’araf

Verset : 33

قُلۡ إِنَّمَا حَرَّمَ رَبِّيَ ٱلۡفَوَٰحِشَ مَا ظَهَرَ مِنۡهَا وَمَا بَطَنَ وَٱلۡإِثۡمَ وَٱلۡبَغۡيَ بِغَيۡرِ ٱلۡحَقِّ وَأَن تُشۡرِكُواْ بِٱللَّهِ مَا لَمۡ يُنَزِّلۡ بِهِۦ سُلۡطَٰنٗا وَأَن تَقُولُواْ عَلَى ٱللَّهِ مَا لَا تَعۡلَمُونَ

Ka ce, “Ubangijina kawai Ya haramta munanan ayyuka na sarari da na voye da savo da cutar wani ba da haqqi ba, kuma (Ya haramta) ku haxa Allah da wani, irin abin da bai saukar da wani dalili a kai ba, kuma (Ya haramta) ku faxi wani abu game da Allah wanda ba ku sani ba.”



Sourate: Suratul A’araf

Verset : 34

وَلِكُلِّ أُمَّةٍ أَجَلٞۖ فَإِذَا جَآءَ أَجَلُهُمۡ لَا يَسۡتَأۡخِرُونَ سَاعَةٗ وَلَا يَسۡتَقۡدِمُونَ

Kuma kowace al’umma tana da lokaci qayyadajje; don haka idan ajalinsu ya zo, ba za a yi musu jinkirin sa’a xaya ba; ba kuma za a gaggauta musu ba



Sourate: Suratul A’araf

Verset : 35

يَٰبَنِيٓ ءَادَمَ إِمَّا يَأۡتِيَنَّكُمۡ رُسُلٞ مِّنكُمۡ يَقُصُّونَ عَلَيۡكُمۡ ءَايَٰتِي فَمَنِ ٱتَّقَىٰ وَأَصۡلَحَ فَلَا خَوۡفٌ عَلَيۡهِمۡ وَلَا هُمۡ يَحۡزَنُونَ

Ya ku ‘yan’adam, idan har manzanni suka zo muku daga cikinku, suna karanta muku ayoyina, to duk wanda ya yi taqawa, kuma ya kyautata aiki, to babu jin tsoro tare da su, kuma ba za su yi baqin ciki ba