Sourate: Suratun Namli

Verset : 17

وَحُشِرَ لِسُلَيۡمَٰنَ جُنُودُهُۥ مِنَ ٱلۡجِنِّ وَٱلۡإِنسِ وَٱلطَّيۡرِ فَهُمۡ يُوزَعُونَ

Aka kuma tattara wa Sulaimanu rundunoninsa na aljannu da mutane da kuma tsuntsaye, sai aka riqa turo su sahu-sahu



Sourate: Suratun Namli

Verset : 18

حَتَّىٰٓ إِذَآ أَتَوۡاْ عَلَىٰ وَادِ ٱلنَّمۡلِ قَالَتۡ نَمۡلَةٞ يَـٰٓأَيُّهَا ٱلنَّمۡلُ ٱدۡخُلُواْ مَسَٰكِنَكُمۡ لَا يَحۡطِمَنَّكُمۡ سُلَيۡمَٰنُ وَجُنُودُهُۥ وَهُمۡ لَا يَشۡعُرُونَ

Har dai zuwa lokacin da suka iso kwarin tururuwa, sai wata tururuwa ta ce: “Ya ku waxannan taron tururuwa, ku shige gidajenku kada Sulaimanu da rundunoninsa su tattake ku alhali kuwa ba da saninsu ba.”



Sourate: Suratun Namli

Verset : 19

فَتَبَسَّمَ ضَاحِكٗا مِّن قَوۡلِهَا وَقَالَ رَبِّ أَوۡزِعۡنِيٓ أَنۡ أَشۡكُرَ نِعۡمَتَكَ ٱلَّتِيٓ أَنۡعَمۡتَ عَلَيَّ وَعَلَىٰ وَٰلِدَيَّ وَأَنۡ أَعۡمَلَ صَٰلِحٗا تَرۡضَىٰهُ وَأَدۡخِلۡنِي بِرَحۡمَتِكَ فِي عِبَادِكَ ٱلصَّـٰلِحِينَ

Sai ya yi murmushi yana mai dariya saboda maganarta, ya kuma ce: “Ubangijina Ka kimsa min yadda zan gode wa ni’imar da Ka yi min ni da mahaifana, da kuma yadda zan yi aiki na gari wanda za Ka yarda da shi, kuma Ka shigar da ni don rahamarka cikin bayinka na gari.”



Sourate: Suratun Namli

Verset : 20

وَتَفَقَّدَ ٱلطَّيۡرَ فَقَالَ مَالِيَ لَآ أَرَى ٱلۡهُدۡهُدَ أَمۡ كَانَ مِنَ ٱلۡغَآئِبِينَ

Kuma ya bincika tsuntsaye, sai ya ce: “Me ya sa ba na ganin Alhudahuda, ko kuwa yana cikin waxanda ba sa nan ne?



Sourate: Suratun Namli

Verset : 21

لَأُعَذِّبَنَّهُۥ عَذَابٗا شَدِيدًا أَوۡ لَأَاْذۡبَحَنَّهُۥٓ أَوۡ لَيَأۡتِيَنِّي بِسُلۡطَٰنٖ مُّبِينٖ

“Na rantse zan yi masa azaba mai tsanani, ko kuma tabbas zan yanka shi, ko kuma lalle ya zo min da hujja bayyananna.”



Sourate: Suratun Namli

Verset : 22

فَمَكَثَ غَيۡرَ بَعِيدٖ فَقَالَ أَحَطتُ بِمَا لَمۡ تُحِطۡ بِهِۦ وَجِئۡتُكَ مِن سَبَإِۭ بِنَبَإٖ يَقِينٍ

Sai ko ba da daxewa ba ya dawo, sannan (bayan an tambaye shi) ya ce: “Ni fa na gano abin da ba ka sani ba, na kuma zo maka da tabbataccen labari daga birnin Saba’u



Sourate: Suratun Namli

Verset : 23

إِنِّي وَجَدتُّ ٱمۡرَأَةٗ تَمۡلِكُهُمۡ وَأُوتِيَتۡ مِن كُلِّ شَيۡءٖ وَلَهَا عَرۡشٌ عَظِيمٞ

“(Shi ne) lalle na sami wata mace tana mulkar su, an kuma ba ta daga kowane abu (na mulki), tana kuma da gadon sarauta mai girma



Sourate: Suratun Namli

Verset : 24

وَجَدتُّهَا وَقَوۡمَهَا يَسۡجُدُونَ لِلشَّمۡسِ مِن دُونِ ٱللَّهِ وَزَيَّنَ لَهُمُ ٱلشَّيۡطَٰنُ أَعۡمَٰلَهُمۡ فَصَدَّهُمۡ عَنِ ٱلسَّبِيلِ فَهُمۡ لَا يَهۡتَدُونَ

“Na same ta ita da mutanenta suna sujjada ga rana ba Allah ba. Shaixan kuma ya qawata musu ayyukansu, sai ya kange su daga bin hanya ta gaskiya, don haka su ba sa kan shiriya



Sourate: Suratun Namli

Verset : 25

أَلَّاۤ يَسۡجُدُواْۤ لِلَّهِ ٱلَّذِي يُخۡرِجُ ٱلۡخَبۡءَ فِي ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِ وَيَعۡلَمُ مَا تُخۡفُونَ وَمَا تُعۡلِنُونَ

“Don kada su yi sujjada ga Allah wanda Yake fito da abin da yake voye a cikin sammai da qasa, kuma Yake sane da abin da kuke voyewa da abin da kuke bayyanawa



Sourate: Suratun Namli

Verset : 26

ٱللَّهُ لَآ إِلَٰهَ إِلَّا هُوَ رَبُّ ٱلۡعَرۡشِ ٱلۡعَظِيمِ۩

“(Shi ne) Allah Wanda babu wani abin bauta da gaskiya sai Shi, Ubangijin Al’arshi mai girma.”



Sourate: Suratun Namli

Verset : 27

۞قَالَ سَنَنظُرُ أَصَدَقۡتَ أَمۡ كُنتَ مِنَ ٱلۡكَٰذِبِينَ

Sai (Sulaimana) ya ce: “To za mu duba ko ka yi gaskiya ko kuwa ka zama cikin maqaryata



Sourate: Suratun Namli

Verset : 28

ٱذۡهَب بِّكِتَٰبِي هَٰذَا فَأَلۡقِهۡ إِلَيۡهِمۡ ثُمَّ تَوَلَّ عَنۡهُمۡ فَٱنظُرۡ مَاذَا يَرۡجِعُونَ

“Ka tafi da wannan wasiqar tawa sai ka jefa musu ita sannan ka ja da baya kaxan, sai ka ga da me za su mayar da martani?”



Sourate: Suratun Namli

Verset : 29

قَالَتۡ يَـٰٓأَيُّهَا ٱلۡمَلَؤُاْ إِنِّيٓ أُلۡقِيَ إِلَيَّ كِتَٰبٞ كَرِيمٌ

Sai ta ce: “Ya ku manyan fada, lalle an jefo min wata wasiqa mai daraja



Sourate: Suratun Namli

Verset : 30

إِنَّهُۥ مِن سُلَيۡمَٰنَ وَإِنَّهُۥ بِسۡمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحۡمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ

“(Mai cewa): Lalle wannan (wasiqar) daga Sulaimana ne kuma lalle ina farawa da Bismillahi Arrahamani Arrahim



Sourate: Suratun Namli

Verset : 31

أَلَّا تَعۡلُواْ عَلَيَّ وَأۡتُونِي مُسۡلِمِينَ

“Kada ku yi min girman kai, ku zo min kuna masu miqa wuya!”



Sourate: Suratun Namli

Verset : 32

قَالَتۡ يَـٰٓأَيُّهَا ٱلۡمَلَؤُاْ أَفۡتُونِي فِيٓ أَمۡرِي مَا كُنتُ قَاطِعَةً أَمۡرًا حَتَّىٰ تَشۡهَدُونِ

(Sai Sarauniyar) ta ce: “Ya ku manyan fada, ku ba ni shawara game da al’amarina, (domin) ni ba zan yanke (shawarar) wani al’amari ba sai kuna nan.”



Sourate: Suratun Namli

Verset : 33

قَالُواْ نَحۡنُ أُوْلُواْ قُوَّةٖ وَأُوْلُواْ بَأۡسٖ شَدِيدٖ وَٱلۡأَمۡرُ إِلَيۡكِ فَٱنظُرِي مَاذَا تَأۡمُرِينَ

Sai suka ce: “Mu dai qarfafa ne kuma mayaqa sosai, al’amarin kuwa yana hannunki, sai ki duba abin da za ki yi umarni.”



Sourate: Suratun Namli

Verset : 34

قَالَتۡ إِنَّ ٱلۡمُلُوكَ إِذَا دَخَلُواْ قَرۡيَةً أَفۡسَدُوهَا وَجَعَلُوٓاْ أَعِزَّةَ أَهۡلِهَآ أَذِلَّةٗۚ وَكَذَٰلِكَ يَفۡعَلُونَ

Sai ta ce: “Lalle sarakuna idan suka shigo wata alqarya sai su yi kaca-kaca da ita, kuma su mayar da manyanta qasqantattu; kuma haka suke aikatawa



Sourate: Suratun Namli

Verset : 35

وَإِنِّي مُرۡسِلَةٌ إِلَيۡهِم بِهَدِيَّةٖ فَنَاظِرَةُۢ بِمَ يَرۡجِعُ ٱلۡمُرۡسَلُونَ

“Ni kam lalle zan aika musu ne da wata kyauta sannan in saurari abin da manzanni za su dawo da shi.”



Sourate: Suratun Namli

Verset : 36

فَلَمَّا جَآءَ سُلَيۡمَٰنَ قَالَ أَتُمِدُّونَنِ بِمَالٖ فَمَآ ءَاتَىٰنِۦَ ٱللَّهُ خَيۡرٞ مِّمَّآ ءَاتَىٰكُمۚ بَلۡ أَنتُم بِهَدِيَّتِكُمۡ تَفۡرَحُونَ

To lokacin da (manzo) ya zo wa Sulaimanu sai ya ce: “Yanzu kwa qare ni da wata dukiya, alhali abin da Allah Ya ba ni ya fi wanda Ya ba ku? A’a, ku ne kuke farin ciki da kyautarku



Sourate: Suratun Namli

Verset : 37

ٱرۡجِعۡ إِلَيۡهِمۡ فَلَنَأۡتِيَنَّهُم بِجُنُودٖ لَّا قِبَلَ لَهُم بِهَا وَلَنُخۡرِجَنَّهُم مِّنۡهَآ أَذِلَّةٗ وَهُمۡ صَٰغِرُونَ

“Koma musu (da kyautarsu) sannan (ka gaya musu) lalle za mu zo musu da runduna wadda ba za su iya tunkarar ta ba, kuma lalle za mu fitar da su daga cikinta (alqaryar) a wulaqance suna qasqantattu!”



Sourate: Suratun Namli

Verset : 38

قَالَ يَـٰٓأَيُّهَا ٱلۡمَلَؤُاْ أَيُّكُمۡ يَأۡتِينِي بِعَرۡشِهَا قَبۡلَ أَن يَأۡتُونِي مُسۡلِمِينَ

Sai (Sulaimanu) ya ce: “Ya ku manyan fada, wane ne daga cikinku zai zo min da gadon mulkinta tun kafin su zo min suna masu miqa wuya?”



Sourate: Suratun Namli

Verset : 39

قَالَ عِفۡرِيتٞ مِّنَ ٱلۡجِنِّ أَنَا۠ ءَاتِيكَ بِهِۦ قَبۡلَ أَن تَقُومَ مِن مَّقَامِكَۖ وَإِنِّي عَلَيۡهِ لَقَوِيٌّ أَمِينٞ

Sai wani ifritu[1] daga cikin aljannu ya ce: “Ni zan zo maka da shi kafin ka tashi daga majalisarka; lalle ni kuma mai qarfi ne amintacce game da (kawo) shi.”


1- Watau wani qaqqarfan aljani.


Sourate: Suratun Namli

Verset : 40

قَالَ ٱلَّذِي عِندَهُۥ عِلۡمٞ مِّنَ ٱلۡكِتَٰبِ أَنَا۠ ءَاتِيكَ بِهِۦ قَبۡلَ أَن يَرۡتَدَّ إِلَيۡكَ طَرۡفُكَۚ فَلَمَّا رَءَاهُ مُسۡتَقِرًّا عِندَهُۥ قَالَ هَٰذَا مِن فَضۡلِ رَبِّي لِيَبۡلُوَنِيٓ ءَأَشۡكُرُ أَمۡ أَكۡفُرُۖ وَمَن شَكَرَ فَإِنَّمَا يَشۡكُرُ لِنَفۡسِهِۦۖ وَمَن كَفَرَ فَإِنَّ رَبِّي غَنِيّٞ كَرِيمٞ

Sai wani (mutum) wanda yake da ilimin Littafi (na Attaura) ya ce: “Ni zan kawo maka shi kafin ka qifta idonka!” To lokacin da (Sulaimanu) ya gan shi ga shi nan a gabansa sai ya ce: “Wannan yana daga falalar Ubangijina don Ya jarraba ni (Ya gani) shin zan gode ne ko zan butulce; to duk wanda ya gode kansa ya yi wa; wanda kuwa ya butulce, to lalle Ubangijina Mawadaci ne, Mai karamci.”



Sourate: Suratun Namli

Verset : 41

قَالَ نَكِّرُواْ لَهَا عَرۡشَهَا نَنظُرۡ أَتَهۡتَدِيٓ أَمۡ تَكُونُ مِنَ ٱلَّذِينَ لَا يَهۡتَدُونَ

(Sai Sulaimanu) ya ce: “Ku sauya kamannin gadon nata mu gani za ta gane (shi) ko kuwa za ta zamanto cikin waxanda ba sa ganewa?”



Sourate: Suratun Namli

Verset : 42

فَلَمَّا جَآءَتۡ قِيلَ أَهَٰكَذَا عَرۡشُكِۖ قَالَتۡ كَأَنَّهُۥ هُوَۚ وَأُوتِينَا ٱلۡعِلۡمَ مِن قَبۡلِهَا وَكُنَّا مُسۡلِمِينَ

To lokacin da ta zo, sai aka ce (da ita): “Shin haka kuwa gadonki yake?” Sai ta ce: “Sai ka ce shi.” (Sulaimanu ya ce): “An kuwa ba mu ilimi tun gabaninta, kuma mun kasance Musulmi



Sourate: Suratun Namli

Verset : 43

وَصَدَّهَا مَا كَانَت تَّعۡبُدُ مِن دُونِ ٱللَّهِۖ إِنَّهَا كَانَتۡ مِن قَوۡمٖ كَٰفِرِينَ

“Kuma abin da ta kasance tana bauta wa ba Allah ba, shi ya hana ta (yin imani); lalle ita ta kasance cikin mutane kafurai.”



Sourate: Suratun Namli

Verset : 44

قِيلَ لَهَا ٱدۡخُلِي ٱلصَّرۡحَۖ فَلَمَّا رَأَتۡهُ حَسِبَتۡهُ لُجَّةٗ وَكَشَفَتۡ عَن سَاقَيۡهَاۚ قَالَ إِنَّهُۥ صَرۡحٞ مُّمَرَّدٞ مِّن قَوَارِيرَۗ قَالَتۡ رَبِّ إِنِّي ظَلَمۡتُ نَفۡسِي وَأَسۡلَمۡتُ مَعَ سُلَيۡمَٰنَ لِلَّهِ رَبِّ ٱلۡعَٰلَمِينَ

Aka ce da ita: “Ki shiga fadar;” to lokacin da ta gan ta sai ta zace ta ruwa ne mai zurfi, sai kuwa ta yaye qwaurinta. Sai (Sulaimanu) ya ce: “Ai ita fada ce da aka gina da gogaggun kasaken qarau (ruwa yake gudana ta qarqashinsu).” Ta ce: “Ya Ubangijina, haqiqa na zalunci kaina, na kuma miqa wuya ga Allah Ubangijin talikai tare da Sulaimanu.”



Sourate: Suratun Namli

Verset : 45

وَلَقَدۡ أَرۡسَلۡنَآ إِلَىٰ ثَمُودَ أَخَاهُمۡ صَٰلِحًا أَنِ ٱعۡبُدُواْ ٱللَّهَ فَإِذَا هُمۡ فَرِيقَانِ يَخۡتَصِمُونَ

Haqiqa kuma Mun aiko wa Samudawa xan’uwansu Salihu da cewa: “Ku bauta wa Allah,” sai ga su sun rabu qungiyoyi biyu[1] suna jayayya


1- Watau qungiya ta farko su ne waxanda suka yi imani da Annabi Salihu, qungiya ta biyu su ne waxanda suka kafirce masa.


Sourate: Suratun Namli

Verset : 46

قَالَ يَٰقَوۡمِ لِمَ تَسۡتَعۡجِلُونَ بِٱلسَّيِّئَةِ قَبۡلَ ٱلۡحَسَنَةِۖ لَوۡلَا تَسۡتَغۡفِرُونَ ٱللَّهَ لَعَلَّكُمۡ تُرۡحَمُونَ

Ya ce: “Ya ku mutanena, don me kuke neman gaggautowar mummunan sakamako tun gabanin kyakkyawa[1]? Don me ba za ku nemi gafarar Allah ba don a ji qan ku.”


1- Watau suna neman a kawo musu azaba, maimakon su roqi rahamar Allah.