سَبِّحِ ٱسۡمَ رَبِّكَ ٱلۡأَعۡلَى
Ka tsarkake sunan Ubangijinka Mafi xaukaka
Partager :
ٱلَّذِي خَلَقَ فَسَوَّىٰ
Wanda Ya yi halitta sai Ya daidaita (ta)
وَٱلَّذِي قَدَّرَ فَهَدَىٰ
Wanda kuma Ya qaddara (abubuwa) sannan Ya shiryar (da halittarsa)
وَٱلَّذِيٓ أَخۡرَجَ ٱلۡمَرۡعَىٰ
Wanda kuma Ya fitar da makiyaya
فَجَعَلَهُۥ غُثَآءً أَحۡوَىٰ
Sai Ya mayar da ita duddugaggiya mai baqi
سَنُقۡرِئُكَ فَلَا تَنسَىٰٓ
Za Mu karantar da kai (Alqur’ani) don haka ba za ka manta ba
إِلَّا مَا شَآءَ ٱللَّهُۚ إِنَّهُۥ يَعۡلَمُ ٱلۡجَهۡرَ وَمَا يَخۡفَىٰ
Sai abin da Allah Ya ga dama, Lalle Shi Yana sane da bayyanannen (abu) da kuma abin da yake vuya
وَنُيَسِّرُكَ لِلۡيُسۡرَىٰ
Kuma za Mu sauqaqe maka (al’umara) mafiya sauqi[1]
1- Watau al’ummuransa na addini da na rayuwa, domin ya sa damar da saqon Allah a cikin nutsuwa.
فَذَكِّرۡ إِن نَّفَعَتِ ٱلذِّكۡرَىٰ
To ka yi wa’azi idan wa’azin zai yi amfani
سَيَذَّكَّرُ مَن يَخۡشَىٰ
Wanda yake tsoron Allah zai wa’azantu
وَيَتَجَنَّبُهَا ٱلۡأَشۡقَى
Mafi shaqiyanci[1] kuma zai nesance shi
1- Watau kafiri tavavve.
ٱلَّذِي يَصۡلَى ٱلنَّارَ ٱلۡكُبۡرَىٰ
Wanda zai shiga wuta mafi girma
ثُمَّ لَا يَمُوتُ فِيهَا وَلَا يَحۡيَىٰ
Sannan ba zai mutu a cikinta ba kuma ba zai rayu (rayuwa mai daxi) ba
قَدۡ أَفۡلَحَ مَن تَزَكَّىٰ
Haqiqa wanda ya tsarkaka ya rabauta
وَذَكَرَ ٱسۡمَ رَبِّهِۦ فَصَلَّىٰ
Ya kuma ambaci sunan Ubangijinsa sannan ya yi salla
بَلۡ تُؤۡثِرُونَ ٱلۡحَيَوٰةَ ٱلدُّنۡيَا
Ba haka ba, ku dai kuna fifita rayuwar duniya ne
وَٱلۡأٓخِرَةُ خَيۡرٞ وَأَبۡقَىٰٓ
Lahira kuwa ita ta fi alheri ta kuma fi wanzuwa
إِنَّ هَٰذَا لَفِي ٱلصُّحُفِ ٱلۡأُولَىٰ
Lalle wannan (batu) tabbas yana cikin littattafan farko
صُحُفِ إِبۡرَٰهِيمَ وَمُوسَىٰ
Littattafan Ibrahimu da Musa
هَلۡ أَتَىٰكَ حَدِيثُ ٱلۡغَٰشِيَةِ
Shin labarin mai lulluvewa da (tsoro) ya zo maka?
وُجُوهٞ يَوۡمَئِذٍ خَٰشِعَةٌ
Wasu fuskoki a wannan ranar qasqantattu ne
عَامِلَةٞ نَّاصِبَةٞ
Masu aiki ne (tuquru)[1] masu shan wahala
1- Watau a wutar Jahannama.
تَصۡلَىٰ نَارًا حَامِيَةٗ
Za su shiga wuta mai tsananin quna
تُسۡقَىٰ مِنۡ عَيۡنٍ ءَانِيَةٖ
Za a shayar da su daga idon ruwa mai tsananin zafi
لَّيۡسَ لَهُمۡ طَعَامٌ إِلَّا مِن ضَرِيعٖ
Ba su da wani abinci sai na qayar tsidau
لَّا يُسۡمِنُ وَلَا يُغۡنِي مِن جُوعٖ
Ba ya sa qiba kuma ba ya maganin yunwa
وُجُوهٞ يَوۡمَئِذٖ نَّاعِمَةٞ
Waxansu fuskokin kuwa a wannan ranar ni’imtattu ne
لِّسَعۡيِهَا رَاضِيَةٞ
Masu gamsuwa ne da (sakamakon) ayyukansu
فِي جَنَّةٍ عَالِيَةٖ
(Suna) cikin Aljanna maxaukakiya[1]
1- Watau xaukaka ta daraja da xaukaka ta muhalli, domin gidajen Aljanna benaye ne wasu kan wasu.
لَّا تَسۡمَعُ فِيهَا لَٰغِيَةٗ
Ba a jin zancen banza a cikinta