وَمَا يُغۡنِي عَنۡهُ مَالُهُۥٓ إِذَا تَرَدَّىٰٓ
Dukiyarsa kuma ba za ta amfane shi ba idan ya gangara (cikin wuta)
Partager :
إِنَّ عَلَيۡنَا لَلۡهُدَىٰ
Lalle bayyana hanyar shiriya a kanmu yake
وَإِنَّ لَنَا لَلۡأٓخِرَةَ وَٱلۡأُولَىٰ
Kuma lalle lahira da duniya namu ne
فَأَنذَرۡتُكُمۡ نَارٗا تَلَظَّىٰ
Don haka ina yi muku gargaxin wata wuta mai ruruwa
لَا يَصۡلَىٰهَآ إِلَّا ٱلۡأَشۡقَى
Ba mai shigar ta sai mafi tsiyacewa
ٱلَّذِي كَذَّبَ وَتَوَلَّىٰ
Wanda ya qaryata ya kuma ba da baya
وَسَيُجَنَّبُهَا ٱلۡأَتۡقَى
Kuma lalle za a nesantar da mafi taqawa[1] daga gare ta
1- Da dama daga cikin malaman tafsiri sun bayyana cewa a nan ana nufin Abubakar As-Siddiq ().
ٱلَّذِي يُؤۡتِي مَالَهُۥ يَتَزَكَّىٰ
Wanda yake ba da dukiyarsa yana neman tsarkaka
وَمَا لِأَحَدٍ عِندَهُۥ مِن نِّعۡمَةٖ تُجۡزَىٰٓ
Ba kuwa wani da ya yi masa wata ni’ima da za a saka masa (a kanta)[1]
1- Watau ba yana ciyar da dukiyarsa ne don ya saka wa wani a kan wata ni’ima da ya yi masa ba.
إِلَّا ٱبۡتِغَآءَ وَجۡهِ رَبِّهِ ٱلۡأَعۡلَىٰ
Sai dai don neman Fuskar Ubangijinsa Maxaukaki
وَلَسَوۡفَ يَرۡضَىٰ
Kuma lalle zai yarda (da sakamakon da za a ba shi)[1]
1- Watau gidan Aljanna a lahira.
وَٱلضُّحَىٰ
Na rantse da lokacin hantsi
وَٱلَّيۡلِ إِذَا سَجَىٰ
Da kuma dare idan ya yi tsit[1]
1- Watau ya lulluve komai da duhunsa, mutane su shiga mazaunansu don su yi barci.
مَا وَدَّعَكَ رَبُّكَ وَمَا قَلَىٰ
Ubangijinka bai bar ka ba, kuma bai qi ka ba
وَلَلۡأٓخِرَةُ خَيۡرٞ لَّكَ مِنَ ٱلۡأُولَىٰ
Kuma lalle lahira ta fi maka alheri a kan duniya
وَلَسَوۡفَ يُعۡطِيكَ رَبُّكَ فَتَرۡضَىٰٓ
Kuma lalle Ubangijinka zai ba ka har sai ka yarda (da abin da Ya ba ka)
أَلَمۡ يَجِدۡكَ يَتِيمٗا فَـَٔاوَىٰ
Shin bai same ka maraya ba sai Ya haxa ka (da mai kula da kai)?
وَوَجَدَكَ ضَآلّٗا فَهَدَىٰ
Ya kuma same ka marashin shiriya Ya shiryar (da kai)?
وَوَجَدَكَ عَآئِلٗا فَأَغۡنَىٰ
Ya kuma same ka matalauci Ya wadata (ka)?
فَأَمَّا ٱلۡيَتِيمَ فَلَا تَقۡهَرۡ
Don haka maraya fa kada ka yi masa fin qarfi
وَأَمَّا ٱلسَّآئِلَ فَلَا تَنۡهَرۡ
Mai tambaya[1] kuma kada ka daka masa tsawa
1- Watau mai neman taimako saboda buqata, ko mai tambaya don neman sani.
وَأَمَّا بِنِعۡمَةِ رَبِّكَ فَحَدِّثۡ
Amma kuma game da ni’imar Ubangijinka sai ka ba da labari
أَلَمۡ نَشۡرَحۡ لَكَ صَدۡرَكَ
Shin ba Mu yalwata maka qirjinka ba[1]?
1- Watau ya hore masa son sauraren wahayin da yake yiwo masa da kuma juriya a kan gallazawar mutanensa.
وَوَضَعۡنَا عَنكَ وِزۡرَكَ
Muka kuma sauke maka nauye-nauyenka[1]?
1- Watau Allah () ya gafarta masa duk wasu laifuka na baya da na nan gaba idan za su samu.
ٱلَّذِيٓ أَنقَضَ ظَهۡرَكَ
Wanda ya nauyayi bayanka?
وَرَفَعۡنَا لَكَ ذِكۡرَكَ
Muka kuma xaukaka maka ambatonka[1]?
1- Watau kamar ambatonsa a cikin kiran salla da iqama da tahiya da sauransu.
فَإِنَّ مَعَ ٱلۡعُسۡرِ يُسۡرًا
To lalle tsanani yana tare da sauqi
إِنَّ مَعَ ٱلۡعُسۡرِ يُسۡرٗا
Lalle tsananin yana tare da sauqi
فَإِذَا فَرَغۡتَ فَٱنصَبۡ
Saboda haka idan ka gama (harkokinka) sai ka kafu (wajen bautar Allah)
وَإِلَىٰ رَبِّكَ فَٱرۡغَب
Sannan kuma ka yi kwaxayi wajen Ubangijinka kawai