يَدۡعُونَ فِيهَا بِكُلِّ فَٰكِهَةٍ ءَامِنِينَ
A cikinta (Aljannar) suna kiran a kawo musu duk wani kayan marmari, suna cikin aminci
لَا يَذُوقُونَ فِيهَا ٱلۡمَوۡتَ إِلَّا ٱلۡمَوۡتَةَ ٱلۡأُولَىٰۖ وَوَقَىٰهُمۡ عَذَابَ ٱلۡجَحِيمِ
Ba za su xanxani wata mutuwa a cikinta ba sai dai mutuwar farko; Ya kuma tserar da su daga azabar wutar Jahima
فَضۡلٗا مِّن رَّبِّكَۚ ذَٰلِكَ هُوَ ٱلۡفَوۡزُ ٱلۡعَظِيمُ
(Wannan) falala ce daga Ubangijinka. Wannan shi ne babban rabo
فَإِنَّمَا يَسَّرۡنَٰهُ بِلِسَانِكَ لَعَلَّهُمۡ يَتَذَكَّرُونَ
To kawai Mun sauqaqe shi ne (wato Alqur’ani) da harshenka, don su wa’azantu
فَٱرۡتَقِبۡ إِنَّهُم مُّرۡتَقِبُونَ
To ka saurara, lalle su ma masu sauraro ne
حمٓ
HA MIM[1]
1- Duba Suratul Baqara, aya ta 1, hashiya ta 8.
تَنزِيلُ ٱلۡكِتَٰبِ مِنَ ٱللَّهِ ٱلۡعَزِيزِ ٱلۡحَكِيمِ
Saukar da Alqur’ani daga Allah ne Mabuwayi, Mai hikima
إِنَّ فِي ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِ لَأٓيَٰتٖ لِّلۡمُؤۡمِنِينَ
Lalle a cikin sammai da qasa tabbas akwai ayoyi ga muminai
وَفِي خَلۡقِكُمۡ وَمَا يَبُثُّ مِن دَآبَّةٍ ءَايَٰتٞ لِّقَوۡمٖ يُوقِنُونَ
A cikin halittarku ma da abin da Yake bazawa na dabbobi, akwai ayoyi ga mutane masu sakankancewa
وَٱخۡتِلَٰفِ ٱلَّيۡلِ وَٱلنَّهَارِ وَمَآ أَنزَلَ ٱللَّهُ مِنَ ٱلسَّمَآءِ مِن رِّزۡقٖ فَأَحۡيَا بِهِ ٱلۡأَرۡضَ بَعۡدَ مَوۡتِهَا وَتَصۡرِيفِ ٱلرِّيَٰحِ ءَايَٰتٞ لِّقَوۡمٖ يَعۡقِلُونَ
Da kuma sassavawar dare da yini da abin da Ya saukar daga sama na arziki, sai Ya raya qasa da shi bayan mutuwarta, da kuma jujjuyawar iska, akwai ayoyi ga mutanen da suke hankalta
تِلۡكَ ءَايَٰتُ ٱللَّهِ نَتۡلُوهَا عَلَيۡكَ بِٱلۡحَقِّۖ فَبِأَيِّ حَدِيثِۭ بَعۡدَ ٱللَّهِ وَءَايَٰتِهِۦ يُؤۡمِنُونَ
Waxannan su ne ayoyin Allah da Muke karanta maka su da gaskiya; to da wane zance ne za su yi imani bayan (zancen) Allah da ayoyinsa?
وَيۡلٞ لِّكُلِّ أَفَّاكٍ أَثِيمٖ
Tsananin azaba ya tabbata ga duk wani maqaryaci mai yawan savo
يَسۡمَعُ ءَايَٰتِ ٱللَّهِ تُتۡلَىٰ عَلَيۡهِ ثُمَّ يُصِرُّ مُسۡتَكۡبِرٗا كَأَن لَّمۡ يَسۡمَعۡهَاۖ فَبَشِّرۡهُ بِعَذَابٍ أَلِيمٖ
Yana jin ana karanta masa ayoyin Allah, sai ya doge yana mai girman kai kamar bai ji su ba; to ka yi masa albishir da azaba mai raxaxi
وَإِذَا عَلِمَ مِنۡ ءَايَٰتِنَا شَيۡـًٔا ٱتَّخَذَهَا هُزُوًاۚ أُوْلَـٰٓئِكَ لَهُمۡ عَذَابٞ مُّهِينٞ
Idan kuma ya san wani abu daga ayoyinmu sai ya xauke su abin yi wa izgili. Waxannan suna da wata azaba mai wulaqantarwa
مِّن وَرَآئِهِمۡ جَهَنَّمُۖ وَلَا يُغۡنِي عَنۡهُم مَّا كَسَبُواْ شَيۡـٔٗا وَلَا مَا ٱتَّخَذُواْ مِن دُونِ ٱللَّهِ أَوۡلِيَآءَۖ وَلَهُمۡ عَذَابٌ عَظِيمٌ
A gabansu akwai (wutar) Jahannama, kuma abin da suka tsuwurwurta (na dukiya da waninta), da abubuwan da suka riqa majivinta ba Allah ba, (duk) ba za su amfana musu komai ba; suna kuma da (sakamakon) azaba mai girma
هَٰذَا هُدٗىۖ وَٱلَّذِينَ كَفَرُواْ بِـَٔايَٰتِ رَبِّهِمۡ لَهُمۡ عَذَابٞ مِّن رِّجۡزٍ أَلِيمٌ
Wannan (Alqur’ani) shiriya ne; waxanda kuwa suka kafirce da ayoyin Ubangijinsu, suna da (sakamakon) wata mummunar azaba mai raxaxi
۞ٱللَّهُ ٱلَّذِي سَخَّرَ لَكُمُ ٱلۡبَحۡرَ لِتَجۡرِيَ ٱلۡفُلۡكُ فِيهِ بِأَمۡرِهِۦ وَلِتَبۡتَغُواْ مِن فَضۡلِهِۦ وَلَعَلَّكُمۡ تَشۡكُرُونَ
Allah ne wanda Ya hore muku kogi don jiragen ruwa su riqa gudu a cikinsa da umarninsa, don kuma ku nema daga falalarsa don kuma ku gode
وَسَخَّرَ لَكُم مَّا فِي ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَمَا فِي ٱلۡأَرۡضِ جَمِيعٗا مِّنۡهُۚ إِنَّ فِي ذَٰلِكَ لَأٓيَٰتٖ لِّقَوۡمٖ يَتَفَكَّرُونَ
Ya kuma hore muku abin da yake cikin sammai da abin da yake cikin qasa gaba xayansu daga gare Shi. Lalle a game da wannan tabbas akwai ayoyi ga mutanen da suke yin tunani
قُل لِّلَّذِينَ ءَامَنُواْ يَغۡفِرُواْ لِلَّذِينَ لَا يَرۡجُونَ أَيَّامَ ٱللَّهِ لِيَجۡزِيَ قَوۡمَۢا بِمَا كَانُواْ يَكۡسِبُونَ
Ka ce da waxanda suka yi imani su yi gafara ga waxanda ba su damu da ni’imomi ko musibu na Allah ba[1], don Ya saka wa mutane game da irin abin da suka kasance suna aikatawa
1- Watau domin Allah zai saka wa bayinsa muminai masu haquri.
مَنۡ عَمِلَ صَٰلِحٗا فَلِنَفۡسِهِۦۖ وَمَنۡ أَسَآءَ فَعَلَيۡهَاۖ ثُمَّ إِلَىٰ رَبِّكُمۡ تُرۡجَعُونَ
Duk wanda ya yi aiki nagari to kansa ya yi wa; wanda kuma duk ya munana to a kansa; sannan wurin Ubangijinku ne kawai za a mayar da ku
وَلَقَدۡ ءَاتَيۡنَا بَنِيٓ إِسۡرَـٰٓءِيلَ ٱلۡكِتَٰبَ وَٱلۡحُكۡمَ وَٱلنُّبُوَّةَ وَرَزَقۡنَٰهُم مِّنَ ٱلطَّيِّبَٰتِ وَفَضَّلۡنَٰهُمۡ عَلَى ٱلۡعَٰلَمِينَ
Haqiqa kuma Mun bai wa Banu Isra’ila littafin (Attaura) da hukunci da annabta. Muka kuma arzuta su da tsarkakan (abubuwa), kuma Muka fifita su a kan talikai
وَءَاتَيۡنَٰهُم بَيِّنَٰتٖ مِّنَ ٱلۡأَمۡرِۖ فَمَا ٱخۡتَلَفُوٓاْ إِلَّا مِنۢ بَعۡدِ مَا جَآءَهُمُ ٱلۡعِلۡمُ بَغۡيَۢا بَيۡنَهُمۡۚ إِنَّ رَبَّكَ يَقۡضِي بَيۡنَهُمۡ يَوۡمَ ٱلۡقِيَٰمَةِ فِيمَا كَانُواْ فِيهِ يَخۡتَلِفُونَ
Muka kuma kawo musu (hujjoji) mabayyana na addini; to ba su sassava ba, sai bayan da ilimi ya zo musu don hassada a tsakaninsu. Lalle Ubangijinka zai yi hukunci a tsakaninsu a ranar alqiyama game da abin da suka kasance suna yin savani cikinsa
ثُمَّ جَعَلۡنَٰكَ عَلَىٰ شَرِيعَةٖ مِّنَ ٱلۡأَمۡرِ فَٱتَّبِعۡهَا وَلَا تَتَّبِعۡ أَهۡوَآءَ ٱلَّذِينَ لَا يَعۡلَمُونَ
Sannan Muka sanya ka a kan wata shari’a ta addini, to sai ka bi ta, kada kuma ka bi soye-soyen zukatan waxanda ba sa sanin (gaskiya)
إِنَّهُمۡ لَن يُغۡنُواْ عَنكَ مِنَ ٱللَّهِ شَيۡـٔٗاۚ وَإِنَّ ٱلظَّـٰلِمِينَ بَعۡضُهُمۡ أَوۡلِيَآءُ بَعۡضٖۖ وَٱللَّهُ وَلِيُّ ٱلۡمُتَّقِينَ
Lalle su ba za su maganta maka komai ba daga Allah. Kuma lalle azzalumai sashinsu masoya sashi ne; Allah kuwa Shi ne Majivincin al’amarin masu taqawa
هَٰذَا بَصَـٰٓئِرُ لِلنَّاسِ وَهُدٗى وَرَحۡمَةٞ لِّقَوۡمٖ يُوقِنُونَ
Wannan (Alqur’ani) izina ne ga mutane da shiriya da rahama ga mutanen da suke sakankancewa
أَمۡ حَسِبَ ٱلَّذِينَ ٱجۡتَرَحُواْ ٱلسَّيِّـَٔاتِ أَن نَّجۡعَلَهُمۡ كَٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ وَعَمِلُواْ ٱلصَّـٰلِحَٰتِ سَوَآءٗ مَّحۡيَاهُمۡ وَمَمَاتُهُمۡۚ سَآءَ مَا يَحۡكُمُونَ
Yanzu waxanda suka aikata munanan (ayyuka) suna tsammanin za Mu sanya su ne kamar waxanda suka yi imani suka kuma yi kyawawan ayyuka, ya zamana rayuwarsu ta duniya da mutuwarsu sun zama daidai? Abin da suke hukuntawa ya munana
وَخَلَقَ ٱللَّهُ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضَ بِٱلۡحَقِّ وَلِتُجۡزَىٰ كُلُّ نَفۡسِۭ بِمَا كَسَبَتۡ وَهُمۡ لَا يُظۡلَمُونَ
Allah kuma Ya halicci sammai da qasa da gaskiya, don kuma a saka wa kowane rai irin abin da ya aikata, alhali kuma su ba za a zalunce su ba
أَفَرَءَيۡتَ مَنِ ٱتَّخَذَ إِلَٰهَهُۥ هَوَىٰهُ وَأَضَلَّهُ ٱللَّهُ عَلَىٰ عِلۡمٖ وَخَتَمَ عَلَىٰ سَمۡعِهِۦ وَقَلۡبِهِۦ وَجَعَلَ عَلَىٰ بَصَرِهِۦ غِشَٰوَةٗ فَمَن يَهۡدِيهِ مِنۢ بَعۡدِ ٱللَّهِۚ أَفَلَا تَذَكَّرُونَ
Shin kuwa ka ga wanda ya xauki son zuciyarsa (shi ne) abin bautarsa, Allah kuwa Ya vatar da shi a kan yana sane[1], Ya kuma rufe jinsa da zuciyarsa, kuma Ya sanya yana a kan ganinsa, to wane ne zai shiryar da shi in ba Allah ba? Me ya sa ba kwa wa’azantuwa?
1- Watau ya vatar da shi bayan ilimi ya zo masa, saboda Allah ya san cewa ya cancanci vata.
وَقَالُواْ مَا هِيَ إِلَّا حَيَاتُنَا ٱلدُّنۡيَا نَمُوتُ وَنَحۡيَا وَمَا يُهۡلِكُنَآ إِلَّا ٱلدَّهۡرُۚ وَمَا لَهُم بِذَٰلِكَ مِنۡ عِلۡمٍۖ إِنۡ هُمۡ إِلَّا يَظُنُّونَ
Suka kuma ce: “Ai ba wata (rayuwa) sai rayuwarmu ta duniya, da za mu mutu, kuma mu rayu (watau ‘ya’yansu)[1], ba kuwa wani abu da yake hallaka mu sai juyin zamani”. Alhali kuwa ba su da wani sani game da wannan; ba abin da suke yi sai zato
1- Watau bayan sun mutu ‘ya’yansu za su ci gaba da rayuwa.
وَإِذَا تُتۡلَىٰ عَلَيۡهِمۡ ءَايَٰتُنَا بَيِّنَٰتٖ مَّا كَانَ حُجَّتَهُمۡ إِلَّآ أَن قَالُواْ ٱئۡتُواْ بِـَٔابَآئِنَآ إِن كُنتُمۡ صَٰدِقِينَ
Idan kuma ana karanta musu ayoyinmu mabayyana, ba su da wata hujja sai kawai su ce: “Ku zo da iyayenmu idan kun kasance masu gaskiya.”